Showing 159001 words to 162000 words out of 274096 words
Chapter 54 - DAULA BIYU Complet Document .txt
ba, sai tashin hankali da damuwa. Kura mata ido yayi yaga yadda take dariya da farin ciki. Ji yayi wani kamar zai fashe da kuka domin kuwa yana hango yadda Abrad ya kwanta da ita, tare da hango Yadda Numan yayi ta juya ta a shimfid'ar shi.
Wato maza biyu sun keta mishi alfarman shi, sunci mutuncin shi sama da yadda ake cin mutuncin wani a duniya, da takalmi suka dauka suka dake shi da shi ba zai mishi ciwo irin wannan da Abrad yayi mishi ba, ji yayi duk wata alfarmar da yake dashi ya tsinke gani yake kamar duk wata mutuncin shi sun tsinka mishi. Duk da yasan tayi aure baya jin haka yayi mishi ciwo kamar yadda Abrad ya nuna mishi ya kwanta da ita..mafi kololuwar ɓaci rai da ya tab'a ji a ranshi kenan.
Dan haka ya bar abin a ranshi kafin yasan mafita.
***
Had'iye yawun Abrad yayi tare da juyawa yana kallon taron jama'a da suke watsewa. Ba dai Ikram Yar Joindah bace?
. tabbas idan yarta ce ta haramta mishi, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun me yasa haka ya faru dashi. Lallai dole ya dakatar da kome ya tsaya Domin rusa Mehran da ya ikram, idan ba haka ba tabbas zai yi biyu babu, ya kwadaitu da jikin Ikram, dan haka koda zai mutu ya dawo wallahi sai ya shiga ya mata faca faca da ruwan jikin shi.
Wannan shine tunanin da ya tsaya a ranshi, dan haka yayi wucewar shi zuciyar shi daya..yana haduwa da Nawwas ya gaya mishi abinda ya faru. Ba karamin kaduwa Nawwas yayi na, tare da cewa.
"Wallahi baka da kirki! Me kake shirin aikatawa? Yarinyar da babu aure a tsakanin ku shine zaka shirya mata mugun makirci haka..toh wallahi zan gaya mata gaskiyar abinda kake shirin aikata mata domin ta farga daga abinda kake shirin aikata mata ai wannan rashin imani ne idan kanwarka aka yiwa haka ba zaka ji dadi ba, dan haka wallahi dai na gaya mata idan ban sami ganinta ba zan gayawa Mehran dan yaji abinda kake shirya musu.. son kan ka yayi yawa toh wallahi ba zan tab'a barin ka, ka lalata musu rayuwa ba, tunda kai kana da naka rayuwar!"
"Nawwas ni kake gayawa Magana? Toh naga wanda ya isa ya dakatar da ni." Ya faɗa da karfi, nan fada yaso kaurewa a tsakanin su, dakyar wasu daga cikin dakarun suka raba su.
Cikin fushi Nawwas yace mishi.
"Wallahi ina sane da kome da ka aikata, kyale ka nayi kawai amma wannan karon zaka sha mamakin abinda zai faru."
Cikin mugu mugun fargaba ya kalli Nawwas, sannan ta danne abinda yake ranshi.
"Na gina ka da hannuna, sannan Ni zaka kashe. Tabbas kai butulu amma zan baka lokaci ka nime yafiyana kafin na fusata akan ka." Inji Abrad.
Dariya Nawwas yayi cikin takaici da haushi yace.
"Wato kai har dama ake bani na nemi yafiyarka? Toh karka yafe min, ka zauna a gurin na kyale ka ne, amma tabbas idan akwai wanda ya dace da Ikram ni ne ba kai ba, domin ni na fara sonta lokacin da na sayo ta." Hannun shi ya saka a cikin aljuhun shi sanan ya ciro jakar kudin da Abrad ya bashi lokacin da ya tura ya sayo mishi ikram.
"Wannan Shi ne, jakar kudin da ka bani, ita kuma da kudina na sayo ta, dan haka karka kuma alakanta kanka da ita, domin ni na barwa Mehran ita."
.ihu Abrad yayi tare da kaiwa kasa duka, yana fadin.
"Wallahi baka isa ba, Ikram tawa ce wallahi sai na kashe ku dukkan ku, akan Ikram sai kashe kowa domin ita tawa ce. Kai ma ka fara gudu domin na kyale ka zanyi ba."
Wannan rigimar bata yi musu dad'i ba, domin karfi da yaji suka zama abokan gaba, kuma Abrad yayi alƙawarin sai ya kashe Nawwas shima kuma yayi alƙawarin sai ya fadi gaskiya kafin ya kashe Abrad. Da kyar aka fidda Nawwas daga cikin gidan, domin fadar sun tayi ƙamari Sosai.
~~~
Yana zaune yayi shiru tun da ya idaar da sallah, yake kallon waje yana son ganinta amma idan ya tuna zantuntukarka Abrad sai yaji kirjin shi yayi zafi, shigowar Fudail a karo na biyu ya sashi d'ago kanshi yana kallon shi.
"Sultan MEHRAN! Ikram tana son ganawa da kai."
"Kace mata ba yanzun ba."
Ya faɗa fuskar shi a daure,
"Toh sai yaushe Mehran?" Na tambaye shi lokacin da na shigo d'akin, juyar da kai yayi tare da cewa.
"Ka fitar min da ita bana son ganinta." Ya faɗa tare da juya min baya.
"Akan me baka son gani na? Meye nayi maka da zafi da kak'i kallona, ko baka so na zama abinda kake bukata bane?" Na tambaye shi muryana yana rawa,
Mikewa yayi tare da nufo ni, bai yi wata wata ba, ya riko damtsen hannuna ya turo ni waje, sannan ta kalli Fudail shima ya fita dan baya son magana.
Kasakai nayi ina kallon kofar Mehran, na rasa gane abinda Mehran yake nufi dani, kallon Fudail nayi domin shi daya ne kawai zai fidda Ni cikin duhun da nake ciki.
"Karki ga laifin shi. Sultan Abrad yayi mishi wasu maganarki wanda ban san me ya gaya mishi ba."
Bakina yana rawa na kura mishi ido, sannan na juya tare da barin shashin sa, na nufi inda nake da zama, a hanyar wucewa ta naji Kwarkwarah shi wato Sakeenatu binti Abu Waqqas tana faɗin.
"Idan mace ta isa bata bin namiji shi yake binta" halin da nake ciki bana jin zai barni nayi magana kawai na kad'a kai nayi gaba abuna, sabida ba zan iya daukar tashin hankali biyu ba, ga nashi ga na wad'anda ban san kansu ba.
....
Tunda na zauna nake kallon madubi, abisa ka'idar zan kai mishi abinda da kuma zama dashi dan hira, sai dai shigowar Sultanah ta zuba min ido.
"Me yasa Mehran ya bukaci Jasrah bake ba."
Murmushi nayi sannan nace mata.
"Eh naje d'azun nan kuma gaskiya ni bana son na amshi ragamar shi sai ranar da aka daura min igiyar shi a kaina, su kuma suna da damar shiga gare shi. Tunda matar da zai aura ce ni kamata yayi nabi tsarin addini da na Ubangijin."
Takowa tayi gabana, sannan ta zauna kamar yadda na zauna..kafin tace min.
"Addinin ki da Ibadar ki yasani mishi kwadayin ki, idan ba wani abu me karfi ba,.nayi imani da Allah ba zaki juya mishi baya ba, domin kuwa babu kwaɗayin duniya a ranki don Allah ga Mehran nan ki tsaya mishi Insha Allah zaki yi nasara."
Murmushi nayi domin kuwa ban san me zance mata ba, amma kuma ina tunanin zan mata yadda ta bukace ni.
*Ana dara ga dare yayi....*
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: *200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...
_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_
36
Kasa gane kan MEHRAN nayi kowa yana jin dadin mu'amala dashi ban dani, tun Fudail yana ƙoƙarin gano yadda zai magance matsalar mu ya kuma sassanta mu, abin yaci tura. A cikin kwana uku kacal Mehran ya nunawa kowa baya tare dani, domin kuwa Zanyi kokarin tinkarar shi domin magana yana gani na zai mike ya nemi hanyar barin gurin. Ko kuma yana gani na zai tsira fushi da b'ata rai.
Bana jin dadin haka ko babu kome bai dace sabida Abrad ya gaya mishi magana ya nemi juya min baya, ranar da ya nime jasrah. Dan sai da tayi kwana uku a cikin turakar shi, kafin hudun ta fito, nan ne tana fitowa aka bata matsayin (Lady royal) tafi kwarkwarah ta kuma fi karfin a kirata da kuyanga, matsayi ne wanda yafi na kwarkwarah. Shi yasa tana fitowa ta fara gudanar da aikinta yadda ya dace. Abinda ta fara shine ta turo da wasikar lallai sai dai ina fitowa cikin su ina cin abincin.
Sannan ta zab'a min bayi mata guda biyu, sannan ta turo min su.
Ajiye takardan nayi sannan na kalle su, a tsanake kafin nace musu.
"Nagode! Sannan ku gaya mata bana bukatar kowa, ina da yan uwana na jikina bana bukatar masu taimakona. Batun cin abinci kuwa kice mata shima na gode ni mace ce kamar zinariya baka cin abinci a gaban kowa sai wanda ya ajiye ni da kuma yan uwana."
Haka suka fita abinsu, ban san me ya faru ba, sai gata tare da Mahlika. Suna zuwa basu yi wata wata ba, tasa aka rufe Izmah da Nimra da duka.
_Dole zasu biyo ki! Musamman yadda suka fahimci kina da matsala da Mehran, kiyi kokarin dauke Kanki kansu_ inji Fudail.
Dauke kai nayi haka suka musu lillis, kafin suka juyo kai. Tare da takowa har gabana, sauran matan suna bayan ta.
"Na saka doka kuma dole kibi yadda nake son domin nice budurwan masarautan. Idan zaki ga Mehran dole sai kin biyo ta hannuna."
Ban kalli inda suke ba, dan haka suka juya suka fita. Da sauri na isa gurin su Izmah zanyi magana tace min.
"Karki damu, ai Sultanah ta gaya mana. Dole zaki fuskanci wannan yanayin, ta bamu hakurin mu tayaki jurewa, Babban matsalar ki kama Mehran a hannunki, idan kika kama shi har abada ba zaki kuma fuskarta matsala ba."
Hawaye ne ya zubo min tare cewa.
"Dole na nimo Abrad, naji meye ya gayawa Mehran haka?" Kallona suka yi sannan suka ce.
"Babu Matsala a fitar ki? Don Allah Karki kuma yin abinda zai jefa ki cikin matsala."
"Babu kome zanje ba zan jima ba. Kayanki zaki bani Nimrah." Had'iye yawun tayi sannan ta mike ta cire, sakawa nayi sannan na fita a saɗaɗɗe. Ina samun na bar harami na sauke ajiyar zuciya. Ban tsaya ba, sai masaukin su. Ina zuwa na sami Nawwas yana tare da wasu dakarun. Ka rasawa nayi gurin shi. Sannan nayi mishi magana.
"Ikram!" Ya ambaci sunana da mamaki.
"Ina Abrad?"
"Yana cikin gidan!" Nufar hanyar cikin gidan nayi, ban tsaya ba sai da na dangana da cikin dakin da yake. Tun a bakin kofar shiga, na dauki takobin shi. Ina shiga na same shi da mace shi banyi wata wata ba, na saka mishi tsinin takobin a kirjin shi.
"Meye ka gaya mishi?"
"Dama nasan zaki zo aiki, abinda na gaya mishi kike son sani?"
"Maganar banza nake son ji?"
"Wannan kuma duk ke ta shafa, dan haka ina tayaki murna domin tarko na d'ana miki kuma yanzun haka Mehran yana bayanki! Zai zo ya same ki a cikin gidan nan."
Cikin fushi na yanke shi da kaifin takobin, cike da mamaki yake kallona idanun shi waje.
"Ko zaki kashe ni ba zan fasa gaya mishi magana ba, kuma zaki gani da idanun ki idan ya karaso!" Cikin mugun b'acin rai na kuma dukar shi da kasar takobin, abinda ya bashi damar riko hannuna, daidai lokacin da Mehran ya bude kofar dakin kenan.. shi kuma ya fisgoni na fada kanshi. Ya kuma yi amfani da karfin ya juyar dani akan idanun Mehran.
Juyawa yayi tare da barin kofar d'akin, ina mik'ewa na kai mishi duka a gaban shi dai da ya suma..sannan na fita na damu yana tafi ko dokin shi yaki dauka haka Fudail shima ya kasa hawa kan dokin Nawwas yana bin shi tare da mishi magana. Amma bai kula shi ba. Da sauri na sha gaban shi.
"Aamaan ka saurarre Ni, wallahi yadda kake tsammani ba haka bane."
Dariya ya saka wanda tunda nake dashi ban tab'a ganin shi yana dariya ba, sai murmushi. Sosai yake dariya har da dafe bishiya.
"Aamaan don Allah ka saurarre ni, wallahi nayi kuskuren zuwa amma kayi alakari da abinda ya baro ya kawo ni gurin shi."
Kura min ido yayi sannan yace min.
"Kiyi yadda kike so! Gashi nan nan da sati daya zaki koma inda ake bukatar ki."
"Mehran me yasa kake son tilasta zuciyarka ganin laifin da ba nawa ba?"
"Akan me ba Zanga laifin ballagaza karuwa makashiya, sha-sha-sha me kwanciya da mijin Kanwar mahaifiyarta? Akan me zan yiwa kaina adalci bayan ta sani kawo datti cikin masarautan da babu dad'i a cikin shi. Ke kazama ce. Wallahi da iya auren Numan kika yi zan yarda na zauna dake akan kwanciya da wancan kazamin, zaki iya tafiya. Amma karki yarda ki bar min kome da yafito daga hannunki."
Ban tab'a ganin abinda ya sani kuka har na kasa hawaye ba, sai kalaman Mehran, yayi min zafi da ciwo. Ina kallon shi ya bar ni a gurin kuka nake sosai. Kamar raina zai bar jikina Mehran ya min mugun zato. Haka suka tafi Nawwas kadai ya zauna a kusadani yayi ta bani hakurin. Karshe haka na mike tare da barin gurin.
***
Tunda na shiga cikin gidan ban kuma sha'awan fita ko kofar gidan ba, sai da naji labarin ana bikin maidawa Mehran kujeran shi, ban ko leko ba Kwarkwarorin shi suka yi ta bidiri, a lokacin Fazilatul nisa ta Fahimci akwai tashin hankalin a tsakanin mu, ta same shi ayi magana yaki bata lokacin shi sai uzirin da yayi ta kawo mata, ni kuma na kasa cewa kome.
Ranar da akayi bikin da yamma Baƙi daga Merocco da Askandariya suka zo. Kukan da nake sabida farin ciki ya kasa misaltawa.
Tunda suka shiga falon shi. Yake juye- juye, yana niman ta inda zata fito. Cikin shigar alfarma nayi sallama a katon falon shi. Suna zaune.
Da sauri ya mike tare da nufar inda nake yana faɗin.
"Salsabilah na." Rungume ni yayi tare da sauke ajiyar zuciya. Kuka ne ya kwace min tare da kai hannuna na rungume shi..ina kuka sosai.
"Kiyi hakuri, gani nan nazo gare ki babu wanda zai kuma saka ki kuka kinji.". Jinjina mishi kai nayi tare da rike rigar shi. Kokarin danne tashin hankalin da yake ciki yake amma tabbas da ace mutanen gurin zasu Fahimci halin da yake ciki da su da kansu zasu bukaci Amir Rahil ya sake Ikram dan ji yake kamar kirjin shi zai fashe da tashin hankali.
Zafin da yake ji ya hana shi sakat, dan haka ya dauki ruwa ya shanye tass, sannan ya dauke kanshi daga gare su. Janye jikin nayi tare da kallon yan uwa da dangin mu, zama nayi a kusa da sultanah Amrah,. Wacce kamar ta daya da Ummyn mu, zama nayi ina me jin kuka yazo min tunda na kifa kaina a kafad'arta nake kuka, domin nayi imani da Allah idan na tafi ba zan kuma dawowa SAMAIND ba.
"Ya isa haka?" Ta faɗa min a sanyayye, Wazir din Merocco ne ya fara bayani a hankali tare da girmama juna, sannan ya kuma faɗa mana makasudin zuwan su.
"Alhamdulillahi mun gode Sultan Mehran, gashi zamu dauke maka ita, sannan muna me baka hakuri abisa abinda zamu gaya maka. Mun yiwa Ikram Miji Amir Rahil. Wanda shine Sarkin mu na gaba, dan haka zaka yi hakuri da yadda muka zo a makare."
A razane na d'ago kai na, ina kallon Rahil da yake ta zabga min murmushi. Sannan na maida kai na, ga Mehran wanda ko a jikin shi babu abinda ya dame shi.
Cikin dakewa ya kalli inda nake amma kuma zuciyar shi sai girgiza take, sannan ya fesar da iskar bakin shi kafin tace musu.
"Babu damuwa! Allah ya bata zaman lafiya..Insha Allah nima zan so zuwa bikin"
Kura mishi ido nayi hawaye na zuba daga cikin idanuna. Ina kuma kallon shi. Dani zai yi Yakana??? A kaina zai saukar da YAKANA?? Wato sabida rashin adalci ya gwammace ya hakura da aurena saboda na tab'a mu'amalantar wani da namiji, rike hannun na, Sultanah Amratu tayi tare da cewa.
"A duk lokacin da muka ga hawaye a kan idanun jama'ar muna da yakinin suna cutuwa ne da mulkin mu. Amma idan aka wayi gari munga wahale akan sarauniyar mu, tabbas muna da yakinin abu biyu ya sata kuka. Farin ciki da bakin ciki,. imma soyayya mara iyaka,.indai akwai daya cikin biyun da nayi magana akai toh wajibi ne Ikram tayi hakuri tare da YAKANA!"
Yadda take maganar babu wanda zai fahimci magana take sabida yadda take yi a sanyayye, share kwalla nayi sannan.. na sake mata murmushi, kafin muka nufi cikin gidan. Muka shiga hada kayana,. Ita kuma Sultanah Amrah ta nufi Shashin Sultanah Fazilatul nisa, anan suka shiga hira, mazan kuma aka kai su masaukin su.
Banda Rahil da yace babu inda zai je, ina zaune ya turo naje. Tunda na isa gurin a bakin wani tafkin da agwagi suke wanka, muna zauna dashi.
"Tun bayan tafiyar ki nayi ta jinya."
"Toh Sannun;"
Rau-rau yayi da fuska, kamar zai fasa ihu.
"Na zata zaki tambaye ni akan me nayi jinyar?"
"Toh kayi hakuri, ?gaya min akan me kayi jinyar."
Dariya yayi sannan yace min.
"Akan sonki mana" kallon shi nayi domin banyi mamaki ba, amma kuma ni bana jin wannan yanayin a tare dashi, ji nayi kamar ana kallon mu na juya. A hankali, sake labulen tagar shi yayi. Nima a sanyayye nake kallon ruwan gabana. Ina me jin zafi da ciwon abinda ya faru.
---
Kallon yake tun da suka fito yake kallon su, bai tab'a ganin mutanen da suka dace da juna kamar Rahil da Ikram, a hankali ya sauke ajiyar zuciya bayan ta juyo tana kallon shi, sake labulen yayi.sannan ya kalli Fudail ya ya jima da shigowa.
"Me yasa kayi shiru ba tare da ka gaya musu yadda kake kaunar ta ba? Me yasa ka xabi'a YAKANA akan kaunar da kake mata?