Header Ads
Showing 234001 words to 237000 words out of 274096 words

Chapter 79 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1374

Ads at the middle of Article

kai na yayi tare da kallon fuskana. Kan shi ya kawo da sunan zai hada bakin mu na kauda kaina, murmushi yayi tare da cizon kunne na, rike rigar shi nayi tare da jin saukar kwalla daga idanuna. Na bakin ciki dan Allah ya gani bana son shi a mijin aurena, a dan uwan na dauke shi amma bai Fahimci haka ba, yayi ta shige min.


"Ai da wancan banzan ne ba zaki na kuka kamar karamar yarinya ba, dake baki kaunata shi yasa kike kuka. Ikram me yasa baki sona? Ni dan uwanki ne kuma zan iya bada rayuwata domin."


"Ba zaka iya, shi daya ya bada rayuwar shi domin ni, don Allah." Dama abinda yake nima kenan, kuma ya samu. Dan haka banyi wani abun da zai nuna mishi jin dadi ko bakin ciki ba, na dai rufe idanuna. Ya gama sumbatar bakina, sannan ya janye daga jiki na, ganin har lokacin idanuna a rufe suke, ya sashi fita daga d'akin yana murmushin jin dadi.


Haka rayuwar mu yayi ta tafiya, ina zuwa shashin Sultan Mu'allim, yana bani wasu abubuwan da ya zama mallakar mahaifina, tare da wasu kyautattakar, haka zan dawo shashin Sultanah Balkisu Ikram, na zauna, shima sabida wancan wahalallen nake haka, idan a d'akin ta, domin yana shigowa zata kore shi. Haka ya sani tarewa a d'akinta, duk da kuwa d'akina na kallon nata ne, haka akayi ta gabatar min da y'ay'an gwamnonin nahiyar, tare da manyan mutanen ƙasar.


Har zuwa lokacin Mehran shi yake da kaso mafi girma a zuciyata, na kasa cire shi a raina. Na sha tambayar kaina me yasa lokacin da nake tare dashi ban ji haka ba, sai da bamu tare? Wannan amsar har yau na kasa bawa kaina amsa. Kullum da wannan nake kwana nake tashi.


"Ciki abincin mana!" Kallon Sultan Mu'allim nayi tare, sunkuyar da kaina, na tsakuri abincin na kai bakina.
"Rahil yace min har yanzun baku fahimci juna ba?" Sunkuyar da kai nayi tare da kasa kai abincin bakina.
Ajiyewa nayi zan mike yace min.
"Zauna."
Komawa nayi ka zauna, tare da damke hannuna, jikina yana rawa.
"Kar na kuma jin labarin kinyi magana akan SULTAN Mehran! Idan kuma hakan ya faru, zamu kashe baiwar da kike kauna, domin idan bamu fito miki a asalin mutane ba zaki kunyata mu. Bamu son muyi miki dole shi yasa muka baki damar ku fahimci juna. Nan da wata biyu muka baki ki fahimci waye shi idan ba haka ba."


"Taya zan Fahimci abinda kuke so? Bayan ni din ba mallakarku bace, ni bana son lusari." Dukar tabirin yayi tare da kallon Sultan Mu'allim.
"Atta kana jin abinda harshenta yake faɗa." Kallona yayi sannan ya kuma maida kanshi ga Ikram.
"Haka zaki zauna dashi domin baki da mijin da ya wuce shi."


Mikewa nayi zan bar gurin Rahil ya taka rigar jikina, karar yagewar jikina, naji kallon shi nayi ban san lokacin da na wanke shi da mari ba, sai da ya firgice. Tabbas yayi kuskuren babba, amma kuma marin da tayi mishi shine mafi girman wulakanci da aka tab'a mishi. Shafa fuskar shi yayi sannan yace.
"Atta! Marina tayi."
"Me yasa ka taka mata rigarta? Matar da zaka aura bata bukatar tilastawa, kasan tana da wanda zuciyarta yake so kai kuma ka same ta ne a sama. Karka sake haka ya kuma had'aku."


Juyawa yayi sannan ya cigaba da cewa.
"Ke kuma za aka kaiki gidan horo."


"Atta!" Ya kira sunan Sultan Mu'allim, murmushi yayi sannan ya d mishi.
"Idan na yanke hukunci ko kaina bana saurarra dan haka, Bhaiq kazo ka tafi da ita."


Ban yi gardama ba dan haka na amince aka tafi dani.
"Atta don Allah."
"Matar da zaka zauna da ita ta mare ka, me kake tunanin nan gaba zata aikata? Dan haka ka bari a nuna mata girmanka da darajarka."


Jikin shi a matukar sanyayye ya bar gurin cin abincin, bai tsaya ko ina ba, sai gidan kakan shi na gurin Uwa wazir. Zama yayi cikin nutsuwa sannan ya gaishe shi, tare da yin shiru. Kasa magana yayi yana kallon yadda Rahil din ya nutsu, kafin ya ce mishi.
"Ina jinka!"
"Dama dama dama.."
"Ka nutsu kayi min magana!"inji kakan shi, nutsuwa yayi kafin ya fadi abin da ya kawo shi. Da kuma dalilin da yasa aka rufe Ikram. Kallon son kai yayi mishi,
tsantsan domin kuwa banda son kai babu abinda ya hango a maganar Rahil.


"Tun lokacin da ka bayyana soyayyarta a ranka na gaya maka cewa ka rabu da ita, amma fir ka kiya, sai ma goyan bayan da kasamu daga danginka, ba wai Ikram nace bata sonka kai ne baka dace da rayuwarta ba, ai duk wanda yaga yadda ta bar kasar nan bayan ta gama maka aiki har ta kai da ta nuna ita ta mutu zaka fahimci akwai soyayya a cikin tafiyarta, amma zuciyarka dake a rufe take kaki yarda akan lallai ita kake buƙata
"


"Amma kuma taya gida bai koshi ba za a dauka akai waje? Taya ina sonta zan kyaleta ta tafi yanki mafi hatsari da ganganci da rayuwa? SAMAIND cike take da rayuwa da mutuwa! Kuskure daya idan mutum yayi mutuwa tafi kome sauki a rayuwar shi. Uwa uba zunzurutun makircin da yake cikin masarautan. Kaka nazo ne domin niman hanyar da Ka fidda ikram, idan ba zan samu ba na hakura nayi tafiya ta"


Kallon shi yayi na tsawon lokaci kafin yace mishi.
"Ta yaro kyau take bata karko, Ba zan daina gaya maka ba Ikram bata dace da rayuwar ka ba, Ka barta tayi rayuwarta da wanda take SO Ni dan taimaka maka, amma ba zan tab'a tilasta mata ba,.kuma ba zan mata dole kamar yadda kuka mata ba, zan bata goyan baya ta auri wanda take so."


Mikewa yayi cikin fushi zai fita, har ya isa bakin kofar kakan Yace.
"Kai ake bukatar ka zama sarki, idan har baka san yadda ake sadaukarwa ba yaushe zaka yiwa Al'ummar ka adalci? Ita saboda jarumtarta ake bukatar ta a jikinka, me yasa ba zaka zama jarumi ba kamar ita? Amma karka tilastawa zuciyarta yake cike da kaunar wani. Domin kana ji kana gani zaka yi danasanin rayuwa."


Fita yayi daga cikin gidan, ya nufi can babban shashin. Inda ta zube a gaban Sultanah Balkisu Ikram.
"Me yasa bani da Sa'a? Me yasa kowa yake min kallon mahaddami? Ni ne ban dace da Ikram ba ko ƙaddara ta ce bata dace da ita bane? Sultanah a tunanina ni Maraya ne, samun Ikram ne ya sani fahimtar ni me galihu ne, me yasa Ikram ta sani nake jin ni ba kome bane?


Me yasa a kullum nake jin nayi son kai? A duk lokacin da na kalli Ikram sai na dinga jin a raina nayi son kai sama da kome a rayuwar mu, tunda ta dawo cikin gidan nan ban tab'a ganin ta dauki takobin domin kare kanta ba, me yasa?"


"Sabida zuciyarta tana wani guri na daban, kaunar da take mishi ba boyayya bace, yadda take kuka akan shi ya tabbatar min ita din ba kowa bace a fagen SOYAYYA! Zai yi wuya ka hada soyayyar da Jarumta, amma kuma ana ana iya hada soyayya da yaki koda kuwa haka zai bada damar a shafe alkarya guda! Akan soyayya tana iya haifar da juyin juya halin a cikin masarautan! Akan soyayya akan iya shayar da sarki guba domin cimma manufar Soyayya! Irin soyayyar Ikram da Mehran! Idan ba ayi takatsantsar gurin nuna musu bambanci rayuwa ba, dole dayan su yayi rayuwa dayan su ya mutu?


Soyayya ce ta shiga tsakanin zubda jini! Kasancewar dukkan su sun kasance, a cikin lambu. Ba zance shine ƙayar ba amma tabbas haka ya nuna min cewa soyayyar su kamar fure ne cikin ƙaya. Gashi da kyau amma kuma haka za a hakura da shi,.idan kuma ka nace kana so. Ba makawa kayar zata illata ka. Idan kuma ka hakura dole haka zaka ji ranka ya raya maka soyayyar furen da take ciki ƙaya. A halin yanzun..Ikram ta kasance fure cikin ƙaya ce.


Duk inda Mehran yaƙe yana faffutikar ganin ya iso gare ta, idan ma shi bai isa gareta ba, ita tana kokarin isa gare shi"


"Taya bayan tana gidan bada horo? Haka ba zai yiwu ba
" Ya faɗa tare da kallon kakan shi.
"Zai yiwu mana, kai abinda ka sani kenan. Ita kuma abinda ta sani zata aikata. Kayi hakuri da Ikram domin ita zuciyarta tana ga Mehran..kai ma ai akwai shukrah da take sonka me yasa ba zaka hakura da Ikram ba?"


Ka sake yayi yana kallon kakar su, kafin yace mata.
"Me yasa kika ce haka?"
Gyara zama tayi sannan tace mishi.
" Kai anan gabaki daya cikin masoya da dangi kake, Mehran kuma cikin makiya yake rayuwa, da ace yana cikin dangin shine da suke kaunar shi ba zata tab'a komawa gare shi ba"


" Amma kuma ai dan daukar fansa ta koma gare shi. Domin rama abinda yayiwa Nu'man."


Dariya tayi sannan tace mishi.
"Waye ya gaya maka k'iyayya ce ta kaita gare shi? Duk wanda ya gaya maka ta koma ne domin rama abinda yayi mata toh yayi karya, soyayya ce ta maida ita da ɗaukar fansa ne ba zata tab'a amsar tayin shi ba, da ɗaukar fansa ne ba zata tab'a yarda ta amshi ragamar auren shi ba, kasan inda ake kurman Kaunar! Toh ka zuba ido zaka ce na gaya maka Allah ya bamu nisan kwana"


"Yanzun Nanna duk soyayyar da na mata ya tashi a banza Kenan? Na sota iya so babu algus me yasa na rasa ta? Soyayyar ta nake mata babu cutarwa a cikin shi amma me yasa ba zan same ta ba? Don Allah Nannah ki taimaka min na same ta. Dan itace abokiyar rayuwa ta...."
[5/22, 7:48 PM] Mehkram1256: +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat


_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


04


Murmushi tayi tare da ɗaukar ruwan da yake gabanta ta kurb'a, sannan ta dauke kanta kana ta cigaba da cewa.
"Ba zan ce ka hakura da ita ba, domin ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare, wayallah kayi nasara wayallah kuma ka fadi wannan shine abinda zan gaya maka."


"Amir SULTAN yana niman ka" a hankali ya juya tare da kallon Bhaiq, sannan ya tashi tare da bin bayan shi. Suna shiga ya zauna a gaban Sultan Mu'allim da Wazir. Shiru duk suka yi sannan Sultan yayi gyaran murya yana faɗin.
"Kaje ka tawo da ita"
"Toh Atta mun gode." Daga haka ya juya ya bar gurin su, yana kara godiya. Bayan fitar shi Wazir ya kalli Sultan."ina ganin me zai hana ka hakura da wannan hadin da zaka yi ka barta ta akan zab'in ranta, tunda shi Rahil yana da masoya babu amfanin a tirsasata yin abinda bai dace ba."


D'ago kai yayi sannan ya sake wata wadatacciyar murmushi kafin yace mishi. " Koda Rahil bai ce yana sonta ba, bana jin zan barta ta auri wani bayan shi, tunda kuma yace yana sonta sai naji faduwa tayi daidai da zama, abinda nake buƙata ne Allah ya kuma biya min bukatar, dukkan su mallakina ne!"
"Allah ya huci zuciyar ka, ba wai ina nufin wani abu bane, sai dai idan har aka bata wanda take bukata haka kamar karin daraja ce ga masarautan mu, Yar mu tana auren Sarkin Samaind ka duba abinda idanun basira mana."


Lashe bakin shi yayi tare da sunkuyar da kanshi yana wasa da furfuran kanshi, sannan ya kalli Waxir ya sake wata ƙaramar murmushi yace mishi.
"Eh na hango katin ci-gaba amma bana jin a raina haka wata masalaha ce, babu cigaban da zata kawo ma, sannan babu wani abinda zai bayyana mana na cigaba dan tana auren Sultan Aamaan Abdus Samad Mehran! Kawai haka ba wani abun azo a gani bane dan babu wani Cigaba da za a ce an samu dan kawai tana auren Sarkin Samaind!"


Shiru Wazir yayi yana kallon yadda Sultan Mu'allim, kasa yayi da kan shi ya kuma cigaba da cewa.
"Sultan akwai matsala domin Ikram bata son shi da Aure a matsayin d'an uwan ta dauke shi, kuma haka ba zai tab'a kawo zaman lafiya, ido da ido kuke wariya akan ta, kuna nuna mata dan ita mace ce, ba zata zab'i abinda take so ba, sai shi?


Haka zai sanya tayi ta mishi kallon ya fita daraja a gaban ku, sannan haka zai sanya tayi ta jin ina ma bata dawo gare ku ba, ban san yadda zan gaya maka kuna cusa k'iyayyar ku a zuciyar ta ba, amma tabbas babu adalci a tsarin ku."


Shiru yayi sannan yana nazarin abinda Wazir ya faɗa.


...
Ina zaune sai gashi ya shigo, kallona yayi sannan ya sake murmushi yana faɗin.
"Bilqisul Ikram!" Dauke kai na nayi ina murmushin bakin ciki, takowa yayi har ina nake zaune. Durkusawa yayi tare da kifa min mari, sannan ya d'ago kai na, tare da yana kallona. Murmushi yayi sannan yace min.
"Baki isa ba! Kinyi kaɗan Ikram marina kika yi? Idan da kin dake ni, yanzun baki isa ba."


Tofa mishi yawu nayi tare da kallon shi har cikin idanun shi. Share fuskar shi yayi tare da wani irin murmushin takaici. Mikewa yayi sannan tare da cewa.
"Ku kunce hannun ta, tare da kawo min ita shashina." Ya faɗa tare da ficewa daga dakin, tunda suka kunce hannun, suka tasa keyana har shashin shi, tunda nake da Mehran bai tab'a nuna min karfi ba, bai tab'a kawo min farmaki ba, yau sabida soyayyar shi Rahil yake nuna min karfi. Tunda na shiga ya saka ni a gaba da bala'i, domin karfi da yaji ya fara kokarin keta min rigana. Dakyar na kwaci kaina, yana ganin haka ya kuma shake ni tare da matse min nonuwa na, kuka ne ya kwace min tare da kallon shi.
"Me yasa kake son lalata min rayuwa? Tunda nake da Mehran bai tab'a kawo min hari ba, kullum mutuntani yake tare da girmamani, na kwana a daki daya da Mehran na kwana a jikin Mehran hannun shi bai tab'a isa cinyata ko kirjina ba, bai tab'a kawowa a ranshi zai iya amfani da karfi ba. Yau d'an uwana yake son keta min mutuncina sabida nace bana son shi!"


Murmushi yayi sannan ya mike tare da ture ni, ya nufi ban dakin shi yana ji kamar zuciyar shi zata fita, bai dan me yasa yake jin babu dadi akan Ikram ba, kuma ba kome ya janyo haka ba, sai dan yadda take nuna soyayyar Mehran a sama da kome. bata tausayin shi kamar yadda take nuna mishi da, yanzun ga baki daya ta tsane shi sabida Mehran, da zai ga Mehran tabbas sai ya kashe shi. Ya tsani Mehran ya tsani rayuwar shi. Kuma Insha Allah sai ya raba ta da kimarta koda kuwa ba zai same ta ba.


Kafin ya fita na tashi tare da ɗaukar alkyabar shi na saka, sannan na nufi shashin mu. Tunda na shiga na zube a tsakar dakin na sake wani irin kuka me mugun cin rai, ina tuna Mehran. Ga baki daya naji na tsani kai na, me yasa a daren da nake duba shi ban bashi kai na ba, koda kuwa ace haka zai janyo min jifa ranar Amarcina.


Kuka ne ya kuma kwace min, shigowar Ruwaida da Izmah ya sani juyawa ina kallon su, zama suka yi sannan suka ce min.
"Abinda kike babban Abin kunya ne, ace yau kina kuka akan SO, WALLAHI ABIN GORI KIKE AIKATAWA UWAR DAKINA DON ALLAH KARKI KUMA ZUBDA HAWAYEN KI SABIDA SO"


Dafa kafana Izmah tayi sannan tace min.
"Kiyi hakuri Ikram!"
Rintsa idanuna nayi.tare kifa kaina akan cinyar Izmah tana shafa min gashina, sallamar Ruwaida tayi tana kallon yadda nake zubda kwalla.
"Ikram ki daina kukan nan, kiyi hakuri Insha Allah idan Mehran ne rabonki zaki mallake shi idan kuma ba rabonki bane shi Allah ya sassauta miki halin da kike ciki."


Haka tayi ya rarrashina, har barci ya dauke ni. Gyara min kwanciya tayi tare da jera min matashin a kaina. Kallon Ikram tayi cikin damuwa, tana tuno abubuwan da suka faru, a baya tabbas wannan kadai ya ishi me hankali fahimtar hikimar Ubangiji, duk wannan zafin yanzun duk babu. Sai sanyin da tayi gabaki daya ta zama wata iri mara amfani. Bata iya fada bata iya rigima babu zafin rai babu kome sabida so tayi watsi da kome.


~~~
SAMAIND


Kimanin wata daya kenan, kallon juna Jasrah da Mahlika suka yi cike da mamaki, jin likitan masarautan yana tabbatar musu da cikin da Azizatul Nissah take dashi. Saka su mutuwar tsaye. Shi kan shi Mehran kura mata ido yayi. Tabbas ya kwanta da ita tun daga lokacin da ya sha maganin ba sau daya ba ba sau biyu ba.


Yasha Narjis ta kawo mishi ita, amma kuma bai tab'a kawowa a ranshi zai mata cikin ba. Domin idan ya tuna duk abinda yake da ita bawai yana mata yadda zata ji dadi bane yana mata yadda zata wahala ta gudu ne ya sami abinda zai kafa hujja dashi sai ga cikin shi ya isa kafa

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads