Header Ads
Showing 252001 words to 255000 words out of 274096 words

Chapter 85 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1361

Ads at the middle of Article

biyo namiji amma baki iya bincikar meke faruwa ba. Kuma ki tabbatar Fudail ya raka ki har cikin gidan da kika fito, karuwa kawai."


Ajiyar zuciya kawai nake tare da fatan Allah ya kai ni gida, ina fita ko ta kan Fudail ban bi ba, nayi tafiya ta, duk da Yasaka dakaru raka ni, sannan ya shiga cikin dakin.
"Amma Sultan wannan bai dace ba, matar ka kake zargi da wasu abubuwan, wallahi ban yarda da abinda Abrad ya faɗa ba, domin kowa yasan Ikram kin tsantsiyya ce. Bata ji kama da irin matan da suka watsar da mutuncin su ba, Haba Sultan yau kome aka gaya maka akan Ikram bincike shine akan gaba, zata baka hadinka."


"Kai ma ina zargin ta baka kanta, ai tun tana Madinatul Mah nake ganin kusancin ka da ita."
"Subhanallahi Ubangiji yayi mana tsari da mugun ji da mugun gani ban tab'a aikata abinda zai dame Ni ba, kuma da kake ihun kana jin haushin Ikram matar da nake so da bakinta ta gaya min maza sun yi mata fyade, da na bincika na samu haka ne nace ina sonta, ba dan kome ba, sai dan ƙaddarar da ta haura kanta."


"Ai kace matar ka sauran wasu karti ne shi ne ni zaka bani shawaran na zauna da wata dattin."
"Aamaan idan yayi maka ka zauna da Ikram idan bai maka ba ka rabu da ita, tana da masoya bila'adadin. Ba kanta farau ba, ba kanta karau ba. Amma ka sani kana dab d kuka da idanun ka."


"Fitar min a daki, ka je ka zauna da Ikram. Tunda baka ganin laifin da aka min. Allah ya isa tsakanina da ku har da Ikram da duk wanda suka ci amanata kuma ka gaya musu yau zamu wuce idan sun gadama su bani ita idan basu gadama ba su bar ta tayi ya bin mazan da ta saba."


Kallon da Fudail yake mishi baki sake sai dai ya rasa bakin magana, kallon shi yake. Yadda fuskar shi tayi ja, idanun shi ya kad'a jajjur. Girgiza kai yayi sannan ya juya tare da barin d'akin, yasan sharrin kishi ne da kuma shaidanin mutum irin Abrad.


Lokacin da na isa gida, ana ruwan sama me ƙarfi, a hankali naje bakin kofar shiga shashin Sultan Mu'allim na zauna ruwa na sauka a kaina, kuka nake mara amfani, gashi duk bayin da suke shashina sun fito nima na, tare da Rahil hango ni suka yi na zauna tare da kifa kaina akan gwiwata,na saka hannuna na rungume gwiwar.


Kuka nake tare da jin kamar zuciyata zata buga, ji nake kamar zan mutu zunzurutun bakin ciki, gabaki daya na rasa inda yake min dad'i, ji nayi duniyar tayi min zafi. Kai na har yana min wani irin bugawa kamar ana buga min da guduma, komawa Rahil yayi ya tawo da Sultan Mu'allim, juyawa yayi tare da cewa.
"Ku kyale ta, karku mata magana idan ta gama zata bar gurin, a yanzun kuma tana iya kin kula kowa, an jima idan bata bar gurin ba kai min magana "


Ya fada tare da nufar cikin dakin shi, yana jin kamar zuciyar shi zata buga, yaji labarin ta tafi gurin Mehran,kuma an gaya mishi fadar da suka yi akan ta ne, toh meye ya faru a tsakanin su ukun?
🤣😹 Am always love Chakwakiyya 🤦🏼‍♀️🤨
[5/22, 7:48 PM] Mehkram1256: +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat
Book3
_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayen Mu_


12...
Ruwan da ake yi ne ya kare a kaina kaf, lokacin kuwa ana shirin shiga sallah azhar. Ruwan ya dauke idanun sun kumbura sosai dakyar na mike ina rawan sanyi, ko gabana bana gani, na isa kofar shiga falon sultan.


Dakyar na tura kofar, na zube a gurin yana zaune a kilishi dauke kan shi yayi yana karanta Alqur'ani, rarrafawa nayi har gaban shi. Bakina yana rawa hawaye na zuba daga idanuna.
"Atta! Don Allah ka saka shi ya sake ni. Na fada auren."


"Don Allah Atta kace mishi na fasa auren, kaji Atta. Don Allah na fasa auren na zan auri Mehran ba." Na fada ina kuka. D'ago kai yayi yana kallona..sannan ya mike tare da rufe Alqur'anin ya fita abun shi.
Da sauri na bi bayan shi ina ihu.
"Wayyo Allah na, Atta don Allah karka tafi ka bar ni don Allah ka saurarre ni!"


"Karku sake ta fita." Ya bada umarni ga dakarun da suke bakin kofar falon shi, nayi kuka nayi danasanin kuntatta musu da nayi akan Mehran. Ta kofar dakin shi na fita, tare da nufar cikin gidan ina kuka. Duk inda na wuce bayi ne ke zuɓewa, ina shiga na same shi tare da sauran yaran shi da jikokin shi. Har da kakata Sultanah Amrah, zuɓewa nayi a gaban su ina kuka tare da rokon su.


"Don Allah Karku kai Ni gare shi wallahi na fasa auren, ku bani koma waye. Ni ku zab'a min ko a cikin bayi ne zan zauna dashi bana son Mehran, don Allah Atta. Ummyn ki saka baki bana son, Ummana,"(wato Sultanah Balkisu Ikram) da sauri na rarrafa gaban Rahil ina kuka.
"Yayana don Allah na fasa karka yarda ya tafi dani." Kuka nake shima kuma daurewa yake baki daya kukan da nake yana d'aga musu hankali.
"Ka tafi da ita a rufe kofar d'akin ta, kazo muyi magana."


"Don Allah Karka tafi dani ka bar ni a tare da kai, don Allah Yayana kar a tafi dani. Wallahi mutuwa zan yi. Mehran ba Masoyina bane na gaskiya. Yayana karka tafi dani."
Haka yake jana. Ina ihu tare da cewa na fasa auren, Sultanah Amrah kasa hakuri tayi sabida kuka ya ci karfin ta.
"Toh meye amfanin rashin jin maganar magabatan ki, kowa sai da ya gaya miki illar abinda kike so, amma kin ki kula kowa gashi tun ba a kaiki SAMAIND zaki fara fuskarta matsala wani irin taurin kai ne gare ki, baki jin magana. Ke daya kin dagula mana lissafi.
Haba wannan wacce irin ƙaddara ce take bibiyar rayuwar ki, daga wannan sai wannan a nimo mana Mehran din ya sawwake mata. Na gaji ita daya ta rage min a duniya, nake jin sanyi idan wani abu ya same ta wallahi ko Askandariya zata zama toka sai na yaki Mehran me yake ji dashi! Yarinya karama ya addabi rayuwarta na gaji da wannan wulakancin. Ko wacce amarya murnan rabuwa da dangi take zata fara rayuwar yanci amma dubi Jarumar yarinya ta koma tana tsoron auren shi meye yayi mata haka da zafi. Rahil Maza ka kira."


"Koda ya kira shi Sultanah Amratu, koda Mehran yazo sai dai ya tafi da ita amma na zai tab'a yarda ya rabu da ita ba, ne nasan haka zai iya faruwa naki yarda da auren shi. Amma ita ta saka Rahil a gaba da fitina, gata nan jiya masaukin shi taje karya ne? Meye ya kai ki? Kinsan abinda kika min?" Jikina ne ya dauki tsima.


Yana kallona cikin madaukaciyar fushi da damuwa, ya nuna ni da yatsa.
"Kamar ki dauki takalmin kafarki ne ki mare ni dashi haka kika karya min alfahari na, Ikram kika bi dare kika tafi har gidan Sultan Aamaan Mehran! Da mijin da zaki aura yayi magana kika ce mishi bashi kanki kika yi" ya karshe maganar cikin tsannanin takaici.


Tasowa Sultanah Amrah tayi tare da rufe Ni da duka, basu hanata ba, domin sun san kimar da na lalata, tarbiyyar su na watsawa kasa, darajar su na keta. "Ku bani takobi na sare kan karya! Mu zaki lalatawa darajojin mu? Mu zaki lalatawa kimar mu? Me muka miki haka da zafi."


Kasa magana nayi kukan ma yatsa cak, haka tayi ta dukana har aka ce ga dan sako daga gurin Sultan MEHRAN.
"Kace ya shigo."
Da sauri ya fita ya gaya mishi.ina kwance a kasa, Fudail ya shigo cikin nutsuwa, gani na a kwance ya sashi karasowa da sauri. Rike rigar shi nayi cikin kuka nace mishi.
"Fudail don Allah kace mishi ya sawwake min, don Allah kace mishi na fasa auren shi. Fudail wallahi dan uwana nake so. Na fada auren shi. Don Allah ka saka baki ya rabu dani."
Ina fadan haka ina kuka wanda yafi nada.
"Amirah, ke shugaba tace. A duniya baki daya babu abinda Aamaan yake so sama dake, babu abinda Aamaan yayi mishi kuka sai ke, Aamaan ya bar mulkin shi sabida ke, yau mun tawo mun bar Samaind cikin halin fari da yunwa ya tawo ganin ki bai tab'a saka rai zai sami auren ki ba.


Wallahi sharri aka miki tare da kishi ya rufe mishi ido, idan da ina da yadda zan nuna mishi gaskiya Amirah Ikram wallahi da nayi, kiyi hakuri."


"A'a baya sona, ya daina sona ya kira Ni ballagaza, ya kirani karuwa, ya kirani datti ko don gidan da nafito Mehran ya d'aga min kaf...." Kifa min mari Sultanah Amrah tayi. Tace mishi.
"Meke tafe da kai." Wani irin kuka nake me mugun cin rai.
"Ni Ko kashe ni zaku yi don Allah karki bar shi ya tafi dani domin yayi min alkawarin azaba da ukuba."


"Yace ina bukatar tafiya yau ko za a bashi ita."
"Sultanah Amratu! A bashi ita su tafi Allah ya basu zaman lafiya."
Wani irin ajiyar zuciya na sauke tare da zuɓewa a jikin ta, ban kuma sannin meke faruwa ba, dukkan su basu damu ba, sai ma shine da yace musu.
"A'a bar wannan al'amarin zuwa gobe Insha Allah, zan mishi bayani yadda zai fahimta."


Suma kuma sai suka ga da cewa haka, dan yana fita aka kira masu kula da lafiyar mutanen fadar aka dukufa a kaina.

Sun jima kafin Allah baya basu Sa'a na farka amma kuma suka goga min abinda zai sani barci. A hankali barci me nayi yayi gaba dani.
"Gaskiya ku duba lamarin yarinyar nan, karku tsannanta mata." Sannan suka yi sallama tare da barin d'akin.


---
Lokacin da ya isa gurin ya same shi yana shirya jikin shi. Kallon tambaya yayi mishi. Dake shima a cike yake da shi yace mishi.
"Bana tunanin Ikram zata yarda ta zauna da kai domin gata can tana kuka a raba auren ku, cin mutuncin da kayi mata kuwa ta faɗa a gaban danginta. Dan haka sai ka san abinyi idan zaka saketa ne na kai musu shedar haka, toh bismillah rubuta ka bani na kai musu. Domin na barta Sultanah Amrah tana dukarta."


Jikin shi yana wani irin rawa ya fice daga dakin. Ya nufi cikin babban gida, yana shiga Rahil ya hana shi wuccewa cikin gidan.
"Ba zaka goranta mata kimarta sannan ka biyo ka ga bayan ta ba, ina tunanin ko ita ce magajiyar ƙaruwai dai haka, ka zauna ka ci mutumcin yarinyar da take mutuwar son ka. Wallahi ban zaci zaka iya amfani da haka ka kuntatta mata ba, Allah sarki so bai san inda ya dace ba.


Inda yasan inda ya dace da babu wanda ya isa ya tozarta mana ita, yarinyar da yau ya dace tayi barci cikin farin ciki da soyayya, amma kuma zauna ka juya mata baya a daren farkonta. Idan zaka iya ka turo mana sakon rabuwa da Ita."


"Kai ka isa raba ni da ita? Duk duniya babu wanda ya isa raba ni da ita, dan haka ka bani hanya na ga mata ta" ya bangaji Amir Rahil ya wuce, shi kuma ya bashi hanya ne sakamakon hango Abrad. Ya tun karo su shine ya bashi hanya, Abrad na isowa a kidime yake tambayar shi.
"Ya jikin Amirah Ikram?"
"Abun da ka aikata bai maka bane kazo karasa mana ita, Shaidani wallahi ka wuce ko na saka a maka tijara."
Ganin da gaske yake yasa Abrad juyawa yana murmushin nasarar da yayi ko babu kome wallahi ya raba masoya saura yanzun....


---
Lokacin da ya shiga cikin gidan, jikin shi a matukar sanyayye, kunyar su da abinda ya aikatawa Ikram yasa shi kasa motsi, yana kallon ƙasa. Ya kasa magana sai shirun da yayi.
"Tana wancan Dakin."
A hankali ya nufi inda aka nuna, ya shiga, da sallama hangota yayi tayi fayau gwanin tausayi, a ranshi yake jin tausayinta, amma a zahiri kallonta yake kawai dan gani yake kamar ta rasa hanyar da zata kare kanta ne ta bige da kwanciya babu lafiya, kallon kirjinta yayi wanda take numfashin yana d'agawa, abinda ya faru jiya ya dawo mishi. Sake tuna yadda suka fada duniyar jin dadi da ita, harbawa wandon shi yayi, cikin sauri ya matse ta. Karasawa yayi tare da zama a bakin gadon, yana shafa fuskarta.


Wani irin azazzaben SOYAYYAR ta yake ji yana yawo a ranshi. Kafin ya shafa goshin ta wanda yayi zafi, riko hannunta yayi tare da kallon ta, sumbatar hannun yyi yana jin wani irin tausayinta a ran shi, hannun ya kai wuyar shi yana faɗin.
"Sirrintacciya na, ba zan iya hada ki da kowa ba, kishinki girma yake dashi, shi yasa na kasa jurewa, ba zan iya yafe miki ba, domin kuwa zan hukuntaki da laifin da kika aikata min, ina nan ina jiran ki har ki farka."


Ya fadi haka tare da sumbatar goshinta, sannan ya fita daga dakin. Yayi musu sallama, sannan ya bar gidan baki daya, yana jin zafin abin a ranshi. Tabbas yayi karfin hali da ya iya shiga cikin gidan, domin kuwa ba kowani namiji bane za a ci mishi fuska yayi hakuri amma yanzun kowa ganin laifin shi yake gani.


Su kuma abin da ya basu haushi akan me zai shigo bai jajjajta halin da take ciki ba, kuma ya bude baki yayi magana yaki basu hakuri duk da yasan sun san abinda ya haɗa su, dan haka suma suka dauka da zafi sosai sun dauki zafi ainun. Shi yasa da ya fito babu wanda ya saurare shi.


Kuma shima ya dauki fushi akan abinda suka mishi, sai ya zamana an sami rashin fahimtar juna a tsakanin su.


.......
Bayan na farka na fara shaƙar kamshin turaren shi, hawaye ne suka zubo min a lumsassun idanuna, na kuma gyara kwanciya na,
"Sannun tashi ki ci abinci." Girgiza mata kai nayi alamar bana jin yunwa.
"Toh ai sai ki kashe kanki shi kan yana da wasu Kwarkwarorin bila'adadin."


"Sultanah don Allah kice." Girgiza min kai tayi tare da cewa,
"Ba a saki a gidan sarauta, kiyi hakuri ba zai iya rabuwa dake ba, da ace abinda yake zargin ki kina gidan ne, toh ba makawa za iya sake ki, sannan kuma Kinga haka laifi ne babba, dan haka kiyi hakuri kiyi hakuri kiyi biyayya Allah zai baki hakuri."


Kura mata ido nayi kwalla na zuba min, rike hannun ta nayi sannan nace mata.
"Sultanah. Ya tsane ni fa"
Shafa kaina tayi sannan tace min.
"Karki damu kishi ne, kuma nasan Indai Abrad yana raye ba zaku taɓa zaman lafiya ba keda Mehran, dan haka kiyi hakuri Insha Allah zaki yi farin ciki sosai."
Kifa kaina nayi a kirjinta ina kuka, tana shafa bayana, tare da cewa.
"Kiyi hakuri Insha Allah Ubangijin yana tare dake "
Girgiza kai nayi ina fadin.
"Umma zan sha wahala ne kawai a hannun shi, domin ya gaya min ga bakin shi, don Allah kiyi wani abu.


Zai wulakantani, Mehran baya fadan abu bai tabbatar ba. Sultanah kiyi kokarin raba Ni dashi dan Allah kiyi hakuri ki taya ni rabani dashi bana son shi yanzun na rantse miki da Allah bana kaunar Mehran...
🤔🙄Kuma dai...
[5/23, 8:16 AM] Mehkram1256: +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat
Book3
_Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayen Mu_


13....
Murmushi tayi tana shafa kaina, tare da cewa.
"Fadan masoya ne ya gaji haka, kuma ba zan iya hanawa a kaiki gidan shi ba, saboda muna son ya fahimci nagarta mu. Kiyi hakuri"
Mai da kaina nayi saman ma tashi, hawaye na zuba kamar magudanar ruwa, fita tayi itama. A hankali abinda ya faru jiya zuwa yau, ya sani jin tsanar kaina da kaina, bana fatar na rayu ma, ga baki daya ji nake kamar na mutu dan bakin ciki. Bayan na kai MISHI kai na,.sannan ya jefe Ni da kalmomin masu zafi da ciwo.


Da taimakawan bayi nai wanka tare da gyara jikina, kasancewar yau da asuba haila tazo min, kwanciya na koma, har dare ina kwance. Daga ni sai wata riga mara nauyi doguwar ce irinta sakar kasar yamma, shigowa yayi da sallama,.kai na a sunkuye ban d'ago ba dukda kuwa zuciyata tana wani irin bugawa.


Zama yayi daga cikin kujerun da suke dakin, ya kura min ido. Rigar jikina irin shara shara ne, dan haka ya kura min ido. Kafin ya dauke kan shi yana me shiru yana nazarin abinda zai gaya min me zafi.
"Naji ance kina bukatar rabuwa dani?" Da sauri na d'ago kai na, na kura MISHI ido. Tashi yayi yana zaga d'akin. Tare da bin yadda aka tsara kome na dakin.


"Kina bukatar rabuwa dani da gaske ne ko kina kokarin b'oye min cewa kin tab'a kwanciya da maza ne? Idan har da gaske baki kwanta dasu ba me yasa zaki ce ba zaki aure ba? Kenan Abrad yayi gaskiya da yace ya saba saka hannun a jikinki yana wasu abubuwan dake?"


Hawaye ne suka fara zuba min, na kasa koda d'ago kai na kalle shi, a hankali na mike tare da isa bakin kofa zan fita na bar MISHI dakin, taki biyu yayi ya saka min kafa. Tare da d'ago ni zuwa bakin gadon ya wurga ni sai da na bugu da bayana da kai na. Wani irin marayan kuka na sake tare da nishi a hankali. Ina me rike kai na, sai jinin da na fara aman shi ta baki. Abinda ya tsorata shi

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads