Header Ads
Showing 183001 words to 186000 words out of 274096 words

Chapter 62 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1405

Ads at the middle of Article

nayi ya finciko ni, aikuwa na sake kawai maranshi duka, sai da ya sake wata irin gurnani, wanda ya sani razana. Kamar zan tsaya sai kuma na fita cikin farin ciki, finciko Ni yayi tare da matse ni da kasa, ina ƙoƙarin mik'ewa.


"Waye kai?" Ya faɗa tare fisgar numfashin, sake kai mishi duka nayi a cikin shi, wani irin gurnani ya kuma sake min, tare da da cewa.
"Meye nayi miki?" Da sauri na kwace kaina.


"Ikram!" Tsigar jikina ne ya mike sakamakon jin yadda ya ambaci sunan, da sauri na kwace kaina baki daya bayan na kai mishi duka, a gefen cikin shi. Na fita na barshi dan nasan tabbas sai dai gawan shi ba dai wani ba, na gama da babin Mehran, tunda na samu na bar gidan, haka kawai naji zuciyata ta rabu cikin wasi-wasi, lumshe idanu nayi lokacin da naga tuno abinda yayi min, na tarkato na dawo gida.


Duk lokacin da na tuna halin da na barshi sai naji kamar baka kyautattawa kai na ba, taya ya fahimci nice? Taya na san nice? Me yasa ya gane Ni? Babu wani dalilin da na bari da zai fahimtar da nice, domin ko turaren na daina shafawa, gudun kar ja fada cikin matsala, sai gashi ya gane ni.


*200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


26


Tunda na shiga cikin gidan, na zauna dab'as a kasa tare da cire bakin mayafin fuskana, ban tab'a jin nayi kuka ba, bayan daukar fansa sai yau, zuciyata tayi rauni ainun, naji a karan kai na ban kyauta ba,. amma kuma yadda nake jin zan amshi kuskurena ne bana jin zan amsa cikin sauki domin nasan nayi laifi babba.


Amma kuma ya cancanci haka ne, ya cancanci haka daga gare ni, haka da nayi mishi shine hukuncin da ya karb'a amma kuma na kashe shi. Na kashe Mehran.


Wani irin bugun zuciya ta take yi, tare da jin kamar zata fadi kasa, kuka nake wanda ya farka dasu daga barci suka tawo kai na, zuba min suka yi bayan sun ga jini a bakina.
"A ina kika ji ciwo haka?"
"Izmah! Nimrah na kashe shi!"


Bakin su a haɗe suka tambaye ni.
"Waye kika kashe?"
Cikin mugun kuka nace musu,
"Mehran!"
"Au shine kike mana kuka? Toh an kin kyautawa kanki" kamar hadin baki suka barni zaune ina kuka. Dan tausayi sun ji amma bakin cikin taurin kaina ya saka suka juya min baya.


Nayi kukan da tun bayan rasuwar Iyayena ban yi shi ba, kai ko mutuwar Airan banyi kukan ba kamar yadda nake kuka akan na kashe Mehran, ina zaune a gurin har kusan tsakiyar dare, ga garin yayi wani irin sanyi.
Kwanciya nayi, ina sauke ajiyar zuciya kuma idanuna basu fasa zubda kwalla ba. Ina tuno lokacin da muke tare kafin mu zama abokan gaba.


Duk da bana jin dadin shi, amma kuma yaki barin koda wani abu ya cutar dani, yana tsare lafiyata da rayuwata, Yau shi na kashe sarki guda, wanda ba a tab'a yin matashin sarki irin shi na, shine yazo a karnin na baya baya, me cike da ban mamaki. Matashin da ya haɗa kome ma rayuwa na kashe shi, me yasa nake da bakar zuciya ne?


Me yasa ban Nime mutanen da suka kashe Airan ba? Amma nazo..
_Kashe miki miji yayi a daren ranar auren ku! Shin zaki yafe mishi? Idan da ace kun zama abu daya a wannan daren da yanzun kina dauke da Yaron ko yarinyar Noman, shin ke kina ganin ya cancanci a yafe mishi._


Wani irin kuka ne ya kuma dawowa min, dakyar na tashi nayi sallah asuba. Sannan na koma na kwanta, ina jin zuciyata bata min dad'i. Ba laifi bane dan na ɗauki fansa amma kuskure na aikata na kashe babban mutum irin Mehran.


...
Bayan tafiyar ikram, Fudail yaga lokacin da aka sauka a katangar gidan, amma bai kawo kome a ranshi ba, dan haka yacewa dakarun.
"Ku shirya an kawowa Sultan Mehran hari! Bari na shiga cikin gidan."


Da gudu ya shiga cikin gidan, koda yazo ma, ya sami Mehran kwance cikin tashin hankali da gurnani, Kiran Sultana yayi suka kashi dakin shi aka shiga bashi taimakon gaggawa. Fita Fudail yayi tare da dauko likitan masarautan, aka zo dashi. Ya kusan kwana akan Sultan Mehran. Dan ana kiran sallah farko yana fitowa daga d'akin shi.
"Ya jikin shi?" Inji Sultanah ta tambaye shi, ajiyar zuciya yayi sannan yace mata.
"Alhamdulillahi! Da sauki sosai, sai dai ya sami barci? Taya aka yi Sultan MEHRAN ya fuskanci irin wannan harin? Anso kashe shi ne fa, domin dukar da aka mishi kan halittar shi na d'a namiji aka dake shi zuwa marar shi, sai dukar da aka mishi a kirjin shi don Allah ku kula"


Shiru kowa yayi, ran Sultanah ya b'aci domin gani take a garin shegen bin mazan shine ya hadu da shu'umin da yayi mishi wannan dukar.


Bayan tafiyar likitan kacokan ta dauki laifin ta daurawa Fudail, Domin gani take shi yake taimakawa Mehran yake sheke ayarshi idan ba haka ba, taya zai iya dauko namiji har zuwa sama, dan haka tayi tafiyarta dakin ta bata kuma zuwa gurin shi ba, sai da gari ya waye tangaran, sannan ta shigo dakin shi, yana ganinta ya sunkuyar da kan shi.
"Meye amfanin dakarun da aka zuba su a kofar shigowa? Meye amfanin zamanka jarumi? Meye amfanin bibiyar maza yan uwan ka? Ka ga kenan babu, ba zan hana ka abinda ake so ba, amma matukar ina da iko akanka na kuma ganinka da namiji.


Gawata zaka dauka, shine karshen biyan laifin da nayi maka tunda narasa da yadda zan biyaka." Daga haka ta fita daga dakin, lumshe idanun shi yayi tare da kallon Fudail da yake mika mishi abinci. A hankali ya karb'a yana ci bai koma d'ago kanshi ba yacewa Fudail.
"Tana raye"ya faɗa tare da d'ago kai, yana kallon bakin kofar shigowa dakin, da sauri Fudail ya rufe kofar, sannan ya dawo gare shi ya d'an sunkuya yana fadin "wacece take raye?"


"Yarinyar da tabi SAURAYINTA!" Cikin wani irin azama ya d'ago kanshi, yana me jin ina zai kyaleta ta rayu, juyawa yayi zai fita yace mishi.
"Ina zaka?"
"Zanje na sare kanta!"
"Zata dawo, sai dai bana son Anne ta ji labarin, domin zata iya tsaneta domin idan ta tsane ta, ba zanji dadin ganinta a tare dani ba, kuma itama Anne ba zata ji dadin ganin mu a tare ba.


Tunanin ta ya bata cewa ni nasaka a kashe shi, ita kuma tazo daukar fansa, domin irin yadda take niman hanyar da zata kashe ni ba na kananun makasa bane, nasan na koya mata kare kanta, amma ban zata a kaina zata kare ba, na zata zata iya tsayawa kanta ne.


Alhamdulillahi tunda yana cikin koshin lafiya, babu abinda ya same ta,. mahaukaciya ta kara girma da taurin kai" ya faɗa yana dafe kanshi sakamakon yawan maganar da yayi, sannan ya lumshe idanun shi, yana jin wani irin abu a ranshi, murmushi yayi sannan kalli Fudail da yake kallon shi cike da mamaki.
"Na zare ko?"
Girgiza mishi kai yayi sannan ya maida kanshi yana cewa.
"Anya itace kuwa!"
Murmushi yayi sannan yaja bakin shi kamar ba zai magana na,sanan ya d'ago kai yana kallon shi..yace mishi.
"Na tab'a maka karya ne? Na tab'a maka musu ne? Toh ka saka ido nan da kwanaki zata dawo, kuma zaka sha mamaki." Kasa magana yayi yana kallon Mehran, dan gani yake kamar na gaskiya bane, shi yasa ya dauke maganar a matsayin mara muhimmanci.


Shi kuwa Mehran, murmushi yake lokaci zuwa lokaci, yana me kallon kofar yadda suka tukwaikuye kan su, sai ya sake murmushi. Yana jin babu wani ciwo da yake damun zuciyar shi sai ta begen ya kuma ganin ta,.da gefen fuskarta ya sani yanzun kuma zai ganta baki ɗaya.


Gabaki daya ya nemi ciwon zuciyar shi ya rasa, dan haka Yacewa Fudail.
"Ka taya ni rike sirrin ta, don Allah karka sake wani yasan meye ya faru, idan ba haka ba zan dauki mataki mara dadi akan kowa, dan haka ka kyaleta zata kuma dawowa haka da tayi ta nuna min ita jaruma ce, amma zan mata wani abu da zata cigaba da farin cikin har karshen rayuwar ta."


Kasa jure wannan yanayin yayi ya juya ya fita, bai kuma bin takan Mehran ba, bai tsaya ba, sai wajen masarautan, ya gama yawon duniyar nan bai gansu ba. Sannan ya dawo gida.


~~~
Ranar zazzabi ne ya rufe ni me mugun zafi, haka suka yi ta fama dani, tare da bani magani. Wajen karfe ɗaya na rana, na ji dadin jikina har na tashi na gabatar da sallah bayan nayi wanka, abinci suka kawo min na tab'a kadan sannan na koma na kwanta.


"Gaskiya irin zuciyarki ko a tarihi b'an taba ji ba, kiyi kokarin koyan hakuri ko dan gudun aikin dana sani, Allah kadai yasan abinda kika mishi da Yasaka ki kuka haka," inji Izmah, kasa magana nayi ina kallonta kafin nace mata.
"Kin sami labarin ya mutu ne?"
"Kai ina bana tunanin ya mutu domin da kinji gaba-daya Samaind ta dauka, kuma Kinga"


"Izmah barci nake ji" na fada mata a fusace, domin nayi mamakin da yake raye, wani sabon bakin ciki ne ya kamani, tare da kara jin lallai sai na fille mishi kai zan sami nutsuwa a raina, koda kuwa ranshi na karfe ne, dan haka na d'aga kafa na kwana biyu. Ina sauraron naji ance ya mutu, amma shiru kake ji.


.... A can kuwa tara dakarun yayi tare da basu hutu kwanaki biyar zuwa bakwai, domin yana son ya kare mata kallo ne yadda zata shigo gidan, babu masu tsaro, Sultanah kan fushi take dashi, tare da dauke kanta akan shi, duk da yana jin jiki amma haka ta cire tausayin shi ta daina shiga harkan shi, a cikin kwana biyar yaji babu dad'i, amma Alhamdulillahi, dan yaji sauki sosai.
Har kwana uku. A ranar na biyar na shirya na dauki karamin wukar yanka tuffa, na tafi dashi ba tare da tsoro ko fargaba ba, koda za a kamani ban damu ba, kawai kaina na sani. Lokacin da na isa gidan naga babu kowa a bakin kofar dan haka na haura katangar kamar yadda na saba, bayan na gama hawa kawai na hango shi a bakin kofar yana zaune tare da kallona, har na isa inda yake.


Duk da a tsorace nake, amma haka bai sani na juya ba, sai ma kara kusantarshi nake.
"Me kike bukata! Shayi ko Ruwa?"


"Ranka!"
"Toh Ikram zoki dauka idan har haka zai baki damar samun farin cikin ki har abada, amma da sharadi. Kinsan ba zan tsaya na barki ki kashe ni ba, zan yi kokarin kare kaina, san haka idan kika yi nasarar kashe ni ina miki fatan Alkhairi." Ya faɗa a sanyayye, kallon shi nayi sai kuma naji ban yarda da abinda yake nufi ba dan haka, na kasa aiwatar da kome, takowa yayi har gabana. Sannan ya saka hannun shi dukka biyu a k'ugun shi yana kallona. Cikin zafin nama na kai mishi wukar kirjin shi.
Da bayan hannun ya kare, yana murmushi me sauti, a hankali na kuma juyawa zan kai mishi duka ya kare, tare da taka kafana, sai da na sake yar kara cikin wahala, gyara tsayuwar shi yayi sanan ya kalle ni.


. Yadda yaja ya tsaya da nasan ma'anar haka da na gudu abina z amma shegen taurin kai da ya addabi rayuwata, ya sani kai mishi duka, tare da kai wukar zan soka mishi, daukata yayi, cikin wani irin yanayi, sannan ya juyar dani yana me hada ni da bango, kamar wacce aka sani na makale mishi da kafaffuna, yadda ya jingina ni, kirjin mu yana gogan juna ya sani kai mishi duka a fuska. Damtse na ya daka. Yake naji kamar an kwashe min da wani kuzarina, daya gefen ya daka shima haka, kifa kaina nayi da goshinsa.


"Ina kika shiga?" Ya tambaye ni bayan ya kai ni dakin shi ya rufe, ajiye ni yayi a gadon, sannan ya juya tare da dauko min ruwa, sannan ya mika min kasa karb'a nayi shi da kanshi ya shayar dani, kallon juna musu yi bayan na kumshe ruwan a bakina, yana ajiye kofin ina fesa mishi ruwan a fuska, saka hannun shi yayi tare da cire abinda nake rufe sauran fuskana.


Yana murmushin mugunta, tare da kallon fuskana, ajiyar zuciya yayi ta saukewa, bai kuma min magana ba, har sai da yaga na fara ƙoƙarin mik'ewa sannan, yace min.
"Toh yanzun meye laifina? Da ake kawo min wannan harin?"


Kasa magana nayi domin dai yada yake natsuwa jikina ya soma razana ni, a hankali yake balle rigar shi. Kallona yake har cikin idanuna, had'iye yawu nayi tare da cewa.
"Karka kuskura kace zaka tab'a ni, karka yarda kace zaka min abinda ban.."
Hannun shi naji akan cinyata, duka na kaiwa hannun ya janye tare da ture ni, yana murmushi yace.
"Ki koma ki shirya Mehran kainuwa ne dashen Allah, babu wanda ya dasani sai Allah, Ikram indai har zan baki damar ki huce haushinki ai kin san ba karamin dalili bane, dan haka bana son na kuma ganinki, a cikin Samaind. Idan kuma na kuma ganin ki, zan ajiye kome zan baki kyautar da bai riske ki ba "


"Kai waye da zaka ce min na bar Samaind? Ai nazo Samaind kenan sai na kashe ka zan bar kasar nan idan yaso kun kama ni karku min ta dad'i....."


*200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


27


"Mhh!" Yayi murmushi me sauti sannan ya kuma ware idanun shi akai na, kafin yace min.
"Har yanzun ke baiwa tace, dan haka na baki damar barin SAMAIND"
"Ni kuma har yanzun niman ranka nake na baka damar kayi rayuwa kafin na dawo gare ka!"


Amadadin naga fushi ko fusata haɗe da b'acin rai, sai naga kamar babu abinda ya dame shi.


Hannun shi ya kai wuyana, tare da kallon yadda nake kokarin kwace kaina. Matse ni yayi da bango, yana kallon cikin idanuna kurawa juna ido muka yi, ya sake murmushin da zaka Fahimci farin ciki ne zalla a ranshi, a hankali ya cigaba da kallon cikin idanuna. Ban san lokacin da kasala tare da kaifin idanun shi suka saukar min ba, tsintar kai na nayi da lumshe idanuna, na kifa kai na a kirjin shi, ina me rintsa idanuna kamar zan fashe da kuka.


Hannun shi ya kai haɓɓa na, tare da d'ago kai na, had'a fuskar mu yayi yana sauke ajiyar zuciya.
"Bana son rashin da'a."
"Idan nayi maka zaka yanka ni ne?"
Janyewa yayi daga jikina, tare da cewa.
"Ina lafiya, bazan iya aikin masu hankali biyu ba," da gaske Mehran Magana ya gaya min, dan haka na juyar da kaina, tare da kokarin kwace kaina.


"Me yasa kike kokarin gudu?"yadda yayi maganar muryan shi can ƙasar makoshi sai da ya kara jefani cikin wani irin kasala, domin yayi maganar ne tare da fesar da iskar bakin shi, a wuyana.
Kokarin kwace kai na nake , amma na kasa domin kuwa matse ni yayi sosai, numfashina yana fita sama sama. Shafa fuska na yayi tare da kallon fuskana sa nake kokarin b'oyewa a kirjin shi.domin wasa gaske Mehran sai da ya kashe min jiki murus. Da sauri na d'ago kai nayi cikin wani irin rawan jiki.
"Hmmm! A da kina amfani da miski, me yasa baki amfani da shi yanzun?" Yayi maganar kama wanda yasha abin maye.
Hannun shi ya kai fuskana tare da tallabo fuskar. Hada bakin mu yayi tare da lumshe kaifaffun idanun shi. Kasa motsi nayi domin ji nake numfashina yana niman barin jikina, hankalina yayi mugun tashi. Idanuna sun gaza fidda kwalla, rike rigar shi nayi ina sauke ajiyar zuciya. Tunda Uwata ta haife ni ban tab'a sanin akwai irin wannan abun ba.


Sannan banda Abrad ban tab'a ganin wanda yayi min irin wannan abun ba, cikin hikima da dabara, sai da ya min masauki a gadon shi sannan ya shiga sumbatar ko ina a jikina, tare da rawan jiki, kamar zan gudu daga gare shi, goga kanshi yake daga wuyana zuwa kirjina, ban san lokacin da na birkice mishi ba, kuka ne ya kwace min, tare da rike hannun shi.
"S...." Hada bakin mu yayi, babu duka babu zagi sai da naji kamar bakina da harshe na, rike hannun shi nayi. Ya bude idanun shi fess a kaina, tare da sumbatar wuyana.
"Karki kuma yunkurin zaki."
"Ka cuce ni! Allah sai ya saka min."
"Ai haba? Toh bari mu karasa bidirin a gadon."
Zaro idanu nayi tare da fashewa da kuka, ya kuma cigaba da jefani cikin tashin hankali, dakyar ya kyale ni, lokacin aka kiran sallah farko, har ban daki ya kai ni, wai zai min wanka bayan na san ba zan iya ganin kato a tube ba.


Sai da ma bari ya shiga kwarin wankar na juyo tare da ɗaukar kayana, tare da barin gidan baki daya. Murmushi yayi domin ko babu kome ya cusa mata tsoro ko ba dukkan ba, wanka yayi wanda rabon shi da yayi hakan tun kafin ya kwanta jinya, ga wani irin iska da yake shigan

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads