Header Ads
Showing 75001 words to 78000 words out of 274096 words

Chapter 26 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1377

Ads at the middle of Article

Kafe ni yayi da ido, tare da riko hannu na, cikin madaukaciyar damuwa yake karanta sakon cikin idanuna.
"Karki fara abinda kike shirin aikatawa? Karki fara abinda zai kai mu ga biyan bashin a tsakanin mu, karki yarda kishi ya zama a tsakanin zubda jini. Zan baki farin ciki mafi daraja da kima. Ki zauna anan zan baki mamaki tare da saka ki farin ciki."


Hannun shi ya kai kan cikina, tare da cewa.
"Zan baki kome har da ajiyata ki ajiye min Airan ki ajiye min Abbinki da Abbina, Mehran zai baki .."


"Idan ta kama ma rayuwata Zan baki kinji sannan indai akan musulinci ne na yarda zan yi shi karki ji kome, zan amshi musulinci karki yarda ki matsa daga cikin wannan daular, wato da nace naga wanda zai tsalleke sansani na yazo daukar ki shine ke zaki tsallaka ki tafi. Don me yasa kike da taurin kai. Me yasa ba zaki Fahimci abinda. "


Kura min ido yayi yana son yayi magana amma babu wata kalma da zai yi amfani da ita sai kame kame, sai kuma kallona da yake yi, bana son wannan yanayin na shi, jana yayi gadon shi, tare da zaunar dani muna kallon juna, kasa magana yayi yana kallon cikin idanuna, na kasa cewa kome shima haka. Sai kallon juna muke.. da ace zai bude kirjin shi tabbas abinda yake rubuce ba kome bane sai sunanta.


Shine a manne a bangon zuciyar shi, rike hannunta yayi yana murzawa a hankali, yana kallon yadda ta lumshe idanunta, hawaye na zuba, tsintar kansa yayi da sumbatar gefen kuncinta, yana share mata kwalla da hannun shi. Janyo ta yayi zuwa kirjin shi, suna kwance tare da shafa bayanta.


"Me yasa ba zaki hakuri ba? Kaddarar mu daya ce" ya faɗa a sanyayye, d'ago kai nayi ina kallon shi tare da girgiza mishi kai, alamun a'a, dafa bayana yayi tare da kai hannun shi dukkan biyu ya dafe daidai inda kai na yake a kirjin shi yana me danne gurin, wanda nake jin bugun shi har cikin rai na.


"Kirjina yana min ciwo!"
Yadda yayi maganar a raunane sai da ya bani tausayi, tare da saka hannuna dukkan biyu, na rungume shi ina kara jin sautin bugun zuciyar shi.


"Ki zauna da Ni mana" ya faɗa a hankali, sama da koda yaushe,
"Mehran zanen ƙaddarata tana wani gurin kayi hakuri."


"Ki bar bani hakuri, na shirya mana farin ciki, kinji nan dina bugawa yake sama da yadda yake bugawa a baya."


Na kasa rike kuka na, haka na kasa fahimtar kome nake ji akan shi, amma duk da hakan zan tafi ba zan zauna da shi ba, zan. Juya Ni yayi daga kan shi, na koma saman shi, zuba min idanun shi yayi tare da kallon cikin idanuna.
"Sirrintacciya"
Ya fadi sunan kasar makoshinsa, tare.
"Heydar"
Na fada can kasa kasa, hada hancin mu yayi tare da gogan juna, hannuna na kai wuyar shi tare da cusa wa cikin gashin kan shi, ina kallon yadda shima yake cikin damuwa.
"Mehran! Kanwata da nake faffutikar ganin ta sami rayuwa me kyau ta rasu, bani da kowa sai Allah, bani da gata sai na shi. Me yasa ba zaka cika mana kudirin mu ba, alkawari muka yiwa Junan mu, me yasa zaka yi amfani da karfin mulki ka dakatar da masoyan juna. A matsayin ka na adali karka cusa son Zuciya a cikin wannan yanayin."
Daga hakan na janye jikina daga gare shi na sauka baki daya daga gadon, fita nayi daga gidan baki daya. Na nufi wajen gari. A hankali nake tafiya har na isa inda nake tsammanin.


Zama nayi a kasar wata bishiya, na fashe da kuka, rana zafi inuwa kunna, haka nake ji kirjina zafi, ashe shi yaji dadin da ya fadi kirjin shi ka ciwo ni kuwa bani da bakin magana,.
"Baba Uwaisul Qarni!" Shafa jikina nayi naji ashe babu sarewan, wani irin kuka ne ya kuma kwace min, tare da kiran sunan shi a hankali. Sanyin da na fara ji ne nayi maza na lumshe idanuna. Ina sauke wasu irin kwalla.
"Barka da zuwa jikata, zo nan" da sauri na bude idanuna akan shi, tare da matsawa kusa dashi na daura kaina, akan kafadar shi. Kukan da nake yi ne, tare da shasheka.
"Toh kiyi hakuri! Kuka me kike yi? Kinawa Sultan Mehran kuke ne ko kinawa Noman Anwarulkharim kuka?"
Kasa magana nayi tare da d'ago kai na,.ina kallon shi.
"Idanun ki suna fadan min gaskiya me yasa ba zaki fahimci muradin ki ba? Me yasa kike son saka kowa kuka? Karki bawa kowa samar sakaki kuka domin wata rana da hakan za a sakaki kuka. Sannan kiyi hakuri tare da rungumar ƙaddararki saura kiris kici nasarar farko amma kuma kome zai lalace. Ki duba girman haka mana."


Kukan da nake ne ya kara yawaita, tare da kallon shi. A hankali ya mike tare da sauko ruwa a cikin wani akushin azurfa ya bani. Na amsa a hankali tare da kafa kai na na sha ruwan me mugun sanyi ga dad'i, yace min.
"Ki duba girman dalilin da ya gaya miki wasu kalaman ai abin a bayyane take, ki sallame NOMAN ya koma haka Allah ya nufa, kaddarar ki tana tare da Mehran."
"A'a baba wannan ba halacci bane, wannan son kai ne, taya zan rabu da mutumin da tun kuruciya make tare dashi"


"Toh shi kenan, Allah ya tabbata da Alkhairi." Daga hakan bai kuma ce min kome ba, sai ma dauke ni da yayi na dawo inda nake, rike da akushin nan. Mik'ewa nayi tare da nufar cikin gidan sarautar, anan naga an bazama nima na. Yana tsaye hannun shi goye a bayan shi, ya zuba min ido, tsintar kai na nayi da kasa tafiya kafaffuna sun min nauyi, sakamakon irin kallon tuhumar da yake min, ina isa inda yake, ya juya min baya tare da cewa.
"Rakshan ku kai ta kebantaccen shashi."
Babu musu suka wuce dani haramtacciyar fada, inda aka watsa ni a cikin gidan, tasowa tayi tare da d'ago ni.
"Sannun Ikram! Kinyi namijin kokarin da babu wanda zai iya, gashi nan dai saura kiris kuma kin fado daga tafiyar mu.".


"Wai meye yasa kika sani wannan aikin ne?" Rike hannu na tayi. Sannan ta kalle ni.
"Da farko naso yaudarar ki ne, kamar yadda ya zama dabi'u ga duk wani ahalin gidan sarauta, dan haka na saka ki a cikin kaddarar Aamaan, daga baya sai na Fahimci kece kika iya razana min mutanen da ban razana su ba, Ranar da ya nime baki wakiliyar shi na Fahimci ya isa matakin da ya dace na dakatar dake haka kin gama min kome, amma sai na.
#Mai_Dambu
```Book one free ne, book two da three na kudi ne 200₦ ta bank 0472282105 ki katin mtn ta wannan Number +2347035133148 ko ta wannan Number 08130269641```
#Mai_Dambu
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: ᎠᎪႮᏞᎪᎻ 𝘉𝘐𝘠𝘜
Book 1
Mai_Dambu


BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM


Page 36


Kidime na fara bin hanyar da naga ya bulla, da gudu gudu, sauri sauri. Har na kusan cimma shi tare da kiran sunan shi.
"NOMAN!!!!"
Na kwala mishi kira, fisgo ni aka yi da sauri na juya ina kallon shi, tare da juyawa nayi tare da kiran shi da cewa.
"NOMAN! Don Allah kazo." Kiran shi nake Mehran yana ja na, har yaga dai zan tara mishi jama'a, sakani barci yayi ta hanyar tab'a wuyana, sannan ya sabani a kafad'ar shi, muka shiga masarautan wanda babu nisa da kasuwan.
"Ka tabbatar ka nima shi, karka sake ya rayu!"


Yana nufar kofar da zata kaika cikin farfajiyar dakaru ne a ko ina, suna ganin shi dauke da mace, suka shiga zuɓewa a gaban shi, har cikin gidan ya nufa da Ikram, ran shi na kara b'aci, tabbas lokaci yayi da zai dakatar da ita ga shiga harkan kowani namiji, tunda ya fahimci yanzun ta haɗu da wancan banzan.


Haka ya ajiye ta, yayi ta yawo a turakar shi zuwa cikin falon shi, yana jiran Fudail. Kamar ya tafi yayi aikin da kanshi, amma babu halin haka yayi ta zuba mishi ido.
--- Haka Fudail ya gama niman me kama da Noman bai samu ba, karshe dai ya dawo babu wani labari.


~~ Waiwaye.
Oman.
Zuba mishi ido Azizatul Nissah tayi tare da cewa.
"Kazo da al'amari me girma, amma zan taimaka maka, domin inda Ikram take ba sauki shiga gurin amma zan maka lamani daya, shine zan fita da kai ka gudu, ka tafi SAMAIND tana cikin fadar kasar, a matsayin baiwa. Amma maganar gaskiya Yayana da Nawwas cutarka zasu yi ba wai zasu bar maka ita bane.


Yayana yana sonta, Ni kuma ina son Nawwas, shi kuma yana sonta, amma idan suka rasata zasu zauna lafiya sannan kai ma zaka same ta a cikin salama, idan kuma ka sake suka fahimci hakan tabbas zasu yi yunkurin kashe ka ne."


Ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon Sarwat sannan yace mata.
"Na amince."
Haka kuwa suka shirya tare da fita bayan gari, karshe dai Noman da Sarwat suka gudu abin su..tafiyar da zasu yi a jirgin ruwa kwana biyu, sai gashi sunyi shi a cikin kwana ɗaya rak da wuni guda, ranar da suka shiga garin ranar Mehran ya dauki Ikram zuwa Madinatul Mah.


Yaso ya bisu, amma babu halin haka. Domin Sarwat ya hana shi.
"Akan me zaka hanani bin bayanta?"
"Ikram tana tare da Sultan Aamaan! Idan ka sake ka bisu wallahi yagalgala namar ka zai yi, sannan kuma ya hanaka ita, d'azun naji wasu dakaru suna maganar cewa, ai dan ya bata Wakiliyar shi ce, Mahaifiyar shi ta azabtar da ita, dan haka baka san yadda aka yi har ya zame ta a matakin wakiliya ba, don Allah karka manta ni Maraya ne, daga kai sai ita nake dasu. Idan ka sake wani abu ya same ku, zan iya mutuwa."


Kurawa Sarwat idanun yayi cikin tausayi, haka ya danne damuwar shi, har ya shiga fadar Sultan a matsayin me kula da dabobbin da ake ci, duk yana jin kome akan Mehran da Ikram, yanayin da yaji labarin ne ya kashe mishi jiki, anya zata yarda ta dawo gare shi kuwa? Yadda kowa yake fadan albarkacin bakinsa.


Lokacin da leken Mehran ya wuce a tunanin shi da ita suka wuce, sai daga baya ya lura babu kome a keken, shine ya juya tare da bin bayan inda keken ya fito, ya hango irin kallon da sukewa juna ita da Mehran, yaji zafin haka da kishinta, wato har ta manta dashi ta faɗa rayuwar wanin shi, yana nan yana dakin soyayyarta.


Ko lokacin da ta hango shi kallon tsana da k'iyayyar yake mata, bawai kallon nazo gare ki mu koma bane.


Shi yasa daga ta gan shi yayi maza ya b'acewa ganin ta, abin tausayi. Yana tafe hawaye na zuba daga idanun shi tare da danasanin akan zuwan shi da yabar ta kawai yasan Allah zai bashi wacce ta fita, amma haka ya dibo jiki ya tawo ba tare da sanin abin da take cikin shi ba.


Muryanta da ihunta yana dankare a cikin ƙwaƙwalwar shi.
"Noman kayi hakuri mu koma daga inda muka fito."


Share kwalla yake tare da cewa,
"Bazan iya komawa ba, zan tsaya har sai itace tace min na koma zan koma, amma zan tsaya mata. Don Allah koda ina da rai ko bani da rai ka tsaya mata. Kalabi ce a tsakanin rawuna. Don Allah ka bata kariya."
"Me yasa kake fadan haka? Me yasa kake niman kashe min zuciya ta, don Allah karka sare da wuri hakan"


"KISHI a tsakanin zubda jini! Ba zan iya dauke kai na akan abinda Zuciyata ta rayu da son shi ba, koda zan iya rasa rayuwata sai na dauke ta mun bar yankin nan. Daga nan zuwa ranar da za'a fara zab'en matan sarki kasaka ido zan nimo ta"


Ya faɗa tare da juyawa ya nausa cikin dajin.
~~~
"Noman! Noman karka tafi kabar ni, Ina sonka" na fada tare da ware idanuna akan Mehran da yake kallona, idanun shi tayi jajjajur, huci yake kawai cikin shi ya kama da wuta, shi daya san halin da yake ciki. Kofin ruwa da aka ajiye mishi ya dauka ya shanye tass, sannan yayi wurgi da kofin. Ya taso yana hada hanya, tare da kallon ta.
"Ni zaki yagawa mutunci a cikin al'umma ta, Ni zaki ketawa haddi? Lallai kuwa zaki kan Karen da kike kira da Noman akan farantin karanunakan SAMAIND anyi gunduwa gunduwa da namar shi."


"Lallai da kayi kuskuren da har karshen rayuwarka kana dana sani, Aamaan Kace zaka kashe min Masoyina? Kace zaka saka kan shi a saman tire karannuka suci naman shi? Ubangiji ya baka sa'a, kai Izza da mulggki haihuwar ka aka yi dashi, Ni kuma na rantse da Allah sai na nuna maka mafi girman izza da takama, ka tab'a min Masoyina!"


Shiru nayi ina kallon shi, kafin na zube gwiwata biyu, na hada hannu na tare da cewa.
"Ka saka Ni duk abinda zaka saka Ni, ka min duk abinda zaka yi dan daraja Soyayyar da kakewa Iyayen ka, na zama fansa ga rayuwar Noman. Idan akwai abinda kake bukata ka" bakin shi rawa yake tare da kallo na, jikin shi babu inda baya rawa, zama yayi a gaban ta yana kallon yadda take kuka, tabbas yayi kuskuren ajiye ta, a matsayin sirrintacciyar shi.

Me yasa zuciyar shi bata mishi adalci ba, me yasa ba zata iya hakura da zama da ita ba, kuka take sabida wani? Ba dan shi ba. Kura mata ido yayi yaga da gaske dai sabida Noman take kuka sai yaji zuciyar shi kamar zata fado, magana yake son yi amma kamar an cika mishi iska a kirjin shi zuwa wuyar shi, kura mata ido yayi. Dakyar Allah ya bashi ikon furta mata.
"Sabida shi kike kuka?"
D'ago jajjayen Idanu ta tayi tare da saukewa, sannan na ce mishi.
"Taya bazan yi kuka ba, watanin goma sha ina wata duniya yana wata duniya, Aamaan me yasa ba zan mishi kuka ba! Don Allah."


Girgiza zai yayi tare da mik'ewa yana faɗin.
"Na haramtawa kowani namiji ke har abada."
"Wani irin son kai ne haka? Idan dan budurci na nake faffutikar ganin bayan shi, zoka amsa. Ka kyale mana rayuwar mu"
Na fada da karfi, sake kofin ruwan hannun shi yayi tare da juyawa yana kallona, ina tsaye tare da yaga rigar jikina, har kasa. Warware daurin kirjin na fara yana kallona, cike da al'ajabi, har na ware ya fadi kasa. Cire komai nayi ina kallon shi.


Tare da zuba gwiwata a kasa, ina warware gashin kai na, sannan na d'ago mishi maganar da yayi jiya.
"Duk da bani da daraja, na kuma zubda wani darajar, ka barni ka rayu da shi. Ko kuma sakamakon da zai biyo baya ba zai maka kyau ba."


Tab'e baki yayi tare da barin d'akin ranshi a b'ace, ya nufi shashin Mahaifiyarshi, tunda ya isa ta mika mishi wani tulu da ruwan giya, ya jima rabon shi da sha, amma yau da yake cikin damuwa, yana sha'awan sha ko zai yi barci, dan haka ya shiga tultula shi a cikin shi sai da ya shanye tass, sannan ya lumshe idanun shi, so yake yayi magana amma ya kasa, baya son tarwatsa mata damuwar shi tunda bata koya mishi yadda zai fadi na shi damuwar ba.


Abinda ya sani ya ginu akan kaɗaici kuma yana da yakinin kadaicin ce ajalin shi haka yayi ta nazarin abinda ya faru, gefe daya surar ta yake mishi gizo, duk da ba wata shahara tayi ba, ko wani abu da zai nuna a cike take ba, amma kuma hakan yana da matukar muhimmanci ya bashi aji na musamman, dan haka ya lumshe idanun shi, kana ya kuma buɗe shi, kamar yanzun yake hango tsayayyen kirjinta tare da d'an karamin cibiyarta wanda yake dige a shafaffen maran ta zai ce ko ciki ne oho, idan bai kaucewa gani ba, bayan da cikin a hade suke, juya mishi ita akayi yana kallon tudun cinyoyin ta tare da hango bayanta wanda ya fidda wani fadi gashi kamar dasa mata akayi.


Lumshe idanun shi yayi tare da sake murmushin jin dadi, yana kallon inda take mishi gizo, kuma dago kai yayi yana kallon yadda take juya mishi, tsintar kan shi yayi da wani irin yanayi, ya mike a hankali.
"Ina zaka Mehran?"


Girgiza mata kai yayi sannan ya ficce daga cikin shashinta, ya nufi nashi. Tunda ya shiga ya same ta ta saka kayan, b'ata fuska yayi sannan ya koma saman kilishi ya zube daga nan dai barci.
Wanda yake cike da mafarkai, akan Noman ya gudu da ita, haka yayi ta walagigi da niman ta, har ya gaji, mafarki daya yake nanata kan shi, har giyar ta sake shi ya farka, tana kwance.


Tun daga lokacin ya saka idanu akan Ikram, wacce ta kuma lalacewa, bata cin kome idan zata yi sallah tayi ta faduwa kenan, sabida rashin abincin da bata ci, amma taurin kai irin nata, ya hanata hakura da burinta, ita kawai ta fita daga gidan.


Bayan kwana biyu, aka bata wakiliyar shi, sosai bayi mata suka sami yanci a cikin su har da Inam, wacce take hannun Sultanah Hoyam. Tunda

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads