Header Ads
Showing 129001 words to 132000 words out of 274096 words

Chapter 44 - DAULA BIYU Complet Document .txt

Ads the beginning of article before Image

09 Jul 2024

1381

Ads at the middle of Article

tayi lub lub, fuskar shi da tafad'a ta taimaka wajen fidda hanci shi har baka.


Gefe guda ga wata yar kasumbar da ya tara, yayi wani irin kyau, yana zaune cikin isa da mulki, yan mata hudu ne da Jasrah ta biyar su, lokaci zuwa lokaci yana yawan kallon kofar shigowa harabar, mace d'aya tal yake dako! Shin zata zone? Ko ba zata zo ba? Wannan ita ce tambayar da yakewa kanshi tun da aka saka lokacin da za ayi abun.


Yake fatan Allah ya kawo ta, ya kuma kawo sanadin da zata zo, dan haka yana zaune a gurin har aka fara gudanar da abinda aka tarasu suyi. Mikewa Fudail yayi sannan yace musu.
"A bisa wannan zab'en da za ayi muna maraba da yan matan da suka zo kama daga wasu yankunan kasar zuwa na nan cikin gidan.


Sannan akwai Amirah Azizah tana nan tafe itama, akwai kuma wata wacce Sultan bai bayyana mana sunan ta ba, tana nan tafe. Dan haka wannan zaben ba wani zab'e bane kece zaki zabawa kanki damar zama da Sultan MEHRAN.


Kasancewar shi mutum me son cin abinci daga makusantan shi, yasa ya baku daman dafa mishi abinci me sauƙin yi, tare da sarrafa alkama da wasu dangin sa, sannan kowa yasan yadda ake dafa shayi a sha. Toh Sultan Mehran yana cikin mutane masu sun shan shayi, sai kuma wasu abincin da kika san anayi a cikin masarautan ku, zaku iya sarrafa shi indai zaki iya ci kuma Sultan yaci, bismillah..


Sanan a cikin gwajin mu akwai tambaya akan sarauta, dan haka zaku iya farawa kuna da lokaci daga nan har azhar."


Tsuru tsuru suka yi tare da kallon Fudail, domin dukkan su Amirorin basu aikin kome a gidajen su.


Bayan Amira Jasrah, sai Yasmin Bint Mir Umdatuddawla, sai Ramziya yar Mir Jazib, sai Sawda yar Mir Rabib, shigowar Azizatul Nissah, Kanwar Sultan Abrad. Ya saka Mehran d'ago kanshi da sauri yana kallonta. Dauke kanshi yayi tare da maida shi kan abinda yake gaban shi. Yana jin babu dadi a ranshi. Tabbas ya rasata ya kuma tabbatar da haka ne ta hanyar ganin yadda yan matan suke kokuwar sarrafa girki.


Ga kanshi ya cika ko ina, amma a gurin Sultan Mehran ba haka bane, fuskarshi bata da walwala, ya wani sunkyar da kanshi, sake maimaita bayanin da Fudail yayi, sannan ya shiga kallon Azizatul Nissah da tayi tsuru tsuru,kafin ya fara aikin da ke gabanta.


Haka suka yi ta aiki tare da gabatar da kome har kusan lokacin salla yayi, sannan aka turo dakaru suka tsaya a gurin dan suma sun idar da sallah.


Bayan kamar minti talatin suka kuma dawowa, nan aka shiga kwashe abincin tare da jera su, a gaban Mehran kowacce idan ta ajiye zata rubuta sunta da inda tafito. Murmushi Fudail yayi domin dai kamshi ya ishe shi.


A hankali aka shiga dibawa Sultan din tare da zuba mishi a wani tire, a hankali ya dauki data kofi me kyau ya wanke hannun shi,sannan ya dauki abincin yayi loma daya, cak yayi tare da kallon Yan matan da iyayen su da suka zo suma ganin abinda yake faruwa.


Kallon Fudail yayi tare da mishi alama ya bashi abinda zai juye abincin bakin shi. Yana juyewa ya kalli, shi sannan ya tura mishi, shima yayi loma daya , zubda yayi tare da ajiyeta a gaban Mir Umdatuddawla, wato abincin Yasmin.


Mika mishi abincin Jasrah akayi ya kalli Amir Hood, sannan ya dauki abincin ya kai lomar bakin shi. Kallonta yayi sannan ya dauke kan shi, tare da zubda abincin a cikin abin zubda. Ruwa ya sha, idanun shi sunyi jajjur,dauran kofin ruwa yayi tare da sha sosai, sannan ya mikawa Fudail yana zuba loma ya furza yana niman ruwa.


Dauka abincin Azizatul Nissah yayi, ya kura mata ido, sannan ya kai loma daya,.sake kallonta yayi sannan ya maida kan shi dakyar ya had'iye sannan ya mikawa Fudail, shi kuma yaci ya mikawa Nawwas, sai Ramziya. Itama haka aka ajiye nata, kafin aka ɗauki Na Sawda.aka tab'a ajiye mata yayi tare da mik'ewa ya wanke hannun shi. Shayin aka fara jera mishi, dukkan dai ba a cewa Kome, kallon iyayen su yayi sannan yace musu.


"Ana tilastawa boya koyan yadda zata iya kyautatta iyayen gidanta me yasa Yaran ku baku koya musu yadda zasu rike mazajen su ba. A cire batun mulki ni mutum ne mai mugun son naci abinci daga cikin muhalina, yau gashi abin kunya yaranku da kike kaunar su, sun gaza bani abinda zancl. A haka kuma idan naji ace min mijina. Toh gaskiya ina son abinci."


Ya faɗa tare da dafe goshin sa, sabida ya gaji daga surutun da yake yi..kallon su yayi.
"Fudail ka ji dasu." Sannan ya mike tare da barin gurin.


"Abisa wannan namijin kokarin da kuka yi, toh mun kara muku shekara daya zuwa biyu,ku koyi yadda ake sarrafa girki, domin koyi girki da zuciya daya karku yi tunanin zaki dawo ki hada mana zafin kai dan ba kyalle ku zamu yi ba.


Sannan ku mai da hankalin ku, Allah ya bada nasara, karku manta an sami kusakurai dayawa, a cikin abincin ku. Dan haka wata shekara idan muka hadu ku tabbatar kunyi abinda ya dace.


Sannan akwai kyautar da Sultan Aamaan Mehran ya bada a baku kowaccen ku!" Jinjina kai suka yi, sannan ya bawa dakaru umarni a mikawa kowa kyautar da Mehran ya basu, yan kunne ne na duwatsun lu'lu'u da sarkan su. Amsa suka yi tare da godiya.


Tunda suka juya suka fita shi kuma Fudail ya shigawa Manyan fada magana yadda zasu fahimta.
"Kuma kun ji yadda abincin yake ba? Toh zaku iya taimaka musu, ta hanyar amfani da zaman da zasu na koyan girkin, don Allah su maida hankalin su sosai, idan ba haka ba wata shekara haka zasu yi ta fama da shi. Mutum ne me son cin abincin."


Kallon shi suke, cike da takaici dan zunzurutun wulakancin a rasa abinda za a saka yaran su, shine girki. Jinjina qarfin halin Mehran suka yi sannan suka mike tare da barin gurin. Har zasu wuce. Amir Hood yace mishi.
"Fudail ka tambaye shi baya tsoron guba ne?"


"Ai shi ba matsroraci bane? Mutum ne me wankakken zuciya, da yana tsoron guba da tuni yayi bankwana da duniya, su koyi yadda zasu saka mishi gubar yaƙe bukata." Inji Fudail,


Juyawa suka yi suna kallon shi, kafin suka fita, daga gidan. Tabbas sunyi sake barin Sultan Mehran ya sami damar abokin kirki a tare dashi dan haka ba zasu kuma barin yaran su, zama mishi mutanen kirki ba. Domin yin haka zai iya dakushe Muradin su.


~~~
"Toh ya kuka yi dasu?" Sultanah Fazilatul nisa ta tambaye shi.
Hannun shi dukka biyu idan kirjin shi, ya juya yana kallon ta, sannan ya sauke ajiyar zuciya, yana kallon waje.
Ita kam ta fara gajiya da wannan shegen miskilancin Mehran, ayi mutum magana ma sai kayi mishi jan aji kafin ka amsa, shegen yanga tayi mishi yawa. Had'iye yawun bakinta tayi tare da sake jefa mishi tambayar,


Niman gurin zama yayi sannan ya kalle ta, kafin ya sauke idanun shi yace mata.
" Basu iya ba!"


"Kamar Ya?"
Sake dauke kanshi yayi sannan ya cigaba da abinda yake yi, kwana biyu nan ya tsani magana, dan haka yadda yake tambayar shi kamar watsa mishi ruwan zafi take, dan haka yaja bakin shi ya tsuke,duk yadda taso yayi magana fiir yaki tanka mata, kuma yaki d'ago kai yayi magana.


Juyawa tayi zata bar gurin, muryan shi ya dakatar da ita, cikin sanyayye yanayi yace mata.
"Afwa Anne! Bana son magana ne!"
Goge kwallar da yake sauka mata tayi sannan ta girgiza mishi kai tana faɗin.
"Babu kome, Allah yasa mu dace!"


"Amin!" Ya faɗa a sanyayye, domin ya fahimci tana cikin damuwa, duk da har yau zargin shi take yana bin maza, shigowar Fudail ya katse shiru su. Shi kuma ya koro musu bayanin yadda suka yi da amir Hood.



"Hmm!" Yace tare da sunkuyar da kanshi kasa, yana wasa da yan yatsun hannun shi.
"Me yasa kai baka son ka fadi abinda yake ranka? Me yasa kake yunkurin rena min hankali? Idan anyi magana sai kace Hmm! Wato ga mahaukaciya kai baka san halin mutumin nan bane da zaka ce hmm! Kasan yadda nake jin damuwar shirunka? Da zance maza ne yanzun zaka dauki maganar da muhimmanci,"


Kasa danne dariya Fudail yayi yana,toshe baki yayi. Fuskar Mehran a sake, duk da babu fara'a amma zaka fahimci, kalmar mazan da takira ya sanya shi sake ranshi domin ya fahimci ranta ya b'aci, dauke kan shi yayi tare da lashe bakin shi.
"Fudail mahaukaciya ka gani ne?"
"Afwa Sultanah!" Ya fadi haka yana fita, dan ya kuma tinzara ta, ya bi bayan Fudail da wani irin shegen kallo.
"Aamaan!" Ta daka mishi tsawa, da sauri ya dauke kanshi daga bayan Fudail.


*200₦ ta bank GTBNK Ramlat Abdulrahman 0472282105 ki katin mtn 300 ta wannan Number +2347035133148 Zahrah Adda Ramlat ko ta wannan Number 08130269641..* Mai_Dambu...
[5/19, 4:13 PM] Addah Ramla💃🏼: _Wannan littafin na kuɗi ne! Idan baka siya ba, karka karanta! Idan ka karanta kuma ka fadi ALKHAIRI ko kayi shiru Allah ya jikan Iyayena_


22
D'ago kai yayi yana kallon ta, tare da hango girmanta da darajarta a cikin kwayar idanun ta, wani irin rike kanshi yayi tare da jin babu dad'i, yadda take kuka tana fada, yayi matukar d'aga mishi hankali sama da kome a duniya.


"Ni ban hanaka niman macen da kake bukata ba, amma Aamaan me zaka yi da maza? Meye abin so a abinda Allah ya tsinewa masu aikatawa, Mehran! Baka da burin da ya wuce kaga ina zubda kwalla ko tausayin zuciyata baka yi, ina laifin na sami rangwame da mutuntawa akan idanuna kake kallon wani namijin, wallahi ba zan ji dar dan ka kalli mace akan idanuna ba.


Amma babban kuskure ne naga kana bin namiji da kallo, wannan abin babu dadin ji balle gani, na had'aka da Allah ka daina bin maza."


Kallonta yake, ya ma rasa yadda zai mata bayani ta fahimta, dan haka yace mata.
"Kiyi hakuri!" Daga haka ya mike ya bar mata falon, shi kam bai san me zai ce mata ta fahimta ba, amma shi Allah ya gani babu namiji a gaban shi. Matan ma Ikram ce, kuma yau da akayi taron Nan ya tabbatar ba zata dawo ba, ya sashi tattara kome nata ya nime katon makulli ya bude kasar zuciyarshi ya binne ta a cikin shi, yayi alkawarin duk yadda ya sami me son shi dan Allah zai bata damar zama dashi.


Amma ikram kan ya manta da ita a ya ajiye ta a inda baya tunanin zata kuma dawowa rayuwar shi. Shi bawai ya tsane ta bane, amma kuma baya son ta tuna abinda ya kuma hada su a baya can,shi yasa ya dauke kanshi daga ita ya kuma boye ta a cikin mizanin shi. Baya kuma son wani ya tuna mishi ya tab'a ganin ta ma. Sabida Allah ka dai da Fudail suka san yadda yayi ta biyan fatake kudi dan su bincika mishi inda take, sau biyu yana tura Fudail GIZERA, kuma amsar daya ne babu labarin ko tana raye, na farko bayan labarin mutuwar ya riske shi na biyu Fudail da Sarwat, sai kuma fataken da yake biyan su, ana niman ta.


Kullum yayi Sallah itace take fara samun addu'ar shi kafin ya daura da iyayen shi da shi kan shi, amma babu kome kamar a wurga dutse cikin ruwa, shi kan shi yasan dai yana cike da kewarta, amma ya bar batunta ya ajiye kome,
"Sultan" Fudail ya kira sunan shi, a hankali ya bude idanun shi da suka yi jajjur.
"Dama zan baka hakuri ne, da abinda Anne tayi maka, sannan yanzun na sami labarin, wai Ikram."
Dakatar dashi yayi ta hanyar d'aga mishi hannu!
"Sultan!" Nuna mishi hanya yayi, duk yadda yaso, fahimtar da shi kasawa yayi asalima zuba mishi ido, Fudail yayi tare da cewa.
"Allah ya huci zuciyar ka!"


Ya fita daga dakin, ya nufi waje. Yana gyara zaman wandon shi wanda haka ya faru akan idanun Sultanah ne.


Kasa magana tayi sai yankan jiki tayi, a gurin ta zube sumammiya. Fitowar Mahlika ta ganta kwance shine ta fasa ihu, duk suka taru akanta, yana zuwa ga suka kama kama da ita zasu dauke ta, yana zuwa ya dauke ta cak yayi d'akinta da ita, sannan suka shiga ƙoƙarin ta farka, dakyar ta farka, tana ganin shi ta rintsa idanun ta,tare da juya kanta daga gare shi, tana ajiyar zuciya.


Riko hannun ta yayi, ta daka mishi tsawa, sai da ya janye. Wani irin kuka ne ya kwace mata, ta juya musu baya. Duk sai jikin shi yayi sanyi.
"Nagode sosai! Ni zaka b'atawa rai? Ni kake kokarin tozartawa, abinda Mahaifinka bai yi ba, Mehran shi kake aikatawa? abinda Abdus Samad bai tab'a gwadawa ba, Mehran shi kake aikatawa? Mehran meye a jikin Namiji?"


Hannun shi ya kai keyar shi sannan ya sauke ajiyar zuciya kafin yace.
"Ina ganin kamar ai an gama wannan maganar ba? Toh meye na dawo dashi? Ni wallahi ban tab'a abinda kike zargina ba, ni rabona da Y'a mace kusan shekarar goma sha biyar, na gaji wallahi." Ya faɗa a gajiye tare da barin d'akin, ranshi yayi masifar b'aci.


Bai tab'a sanin cewa zai iya fuskatar tozarci ko zargi haka ba, sai yau duk sai yaji ranshi ya b'aci, taya da girman shi zai dinga fuskantar matsala haka? Duk kamewar shi sai an jefe shi da irin wannan kalmar,. Baya son tashin hankali da reni yasa shi ƙin amincewa da yaran da aka turo mishi yau, domin yasan halin Yaran da suka taso cikin gidan sarauta ba tarbiyya bace suke samu wadatacce, kawai ana koya musu mulki ne da kirsa da kisisina, sai makirci da iya kwanciya da namiji a gado, shima dan kar a sami matsala ne a goran ta musu, amma tabbas baya sha'awar macen da aka haifeta a gidan sarauta. Domin abinda zata bukata mulki ne..


Shi kuma baya da ra'ayin macen da zata bukaci mulkin yafi ra'ayin wacce zata, shirya musu soyayya da jin dadin rayuwa, shi mutum ne da ya rasa kulawa a gurin Uwarshi, dan haka yake niman kulawar mace da zata damu dashi, kuma zata samu da matsalar shi, bawai wacce zata maida hankalinta akan mulki kacokan ba.


Ikram ce ta fado mishi tsaki yaja tare da juyar da kanshi, duk halin da yake ciki itace sanadin haka, domin ita ta gudu ta bar shi, da bata tafi ba tabbas da yana nan ya cika kudirin shi akanta, ya kuma bata matsayin da koda bata so. Amma sai ta zab'i muradun zuci tayi gaba abinda ga abinda tafiyarta ya haifar mishi.


Yasan koda Fudail ya wanke shi ba zai wanku ba a gaban Sultanah Ikram ce zata iya wanke shi tass, ta kuma mishi adalci.


Ajiyar zuciya ya sauke akai akai. Yana kuma sake jin tsanar dalilin da Yasaka Ikram tafiya ta barshi gashi babu ita babu labarinta, duk inda yake tsammanin ganinta, an je bata nan.


~~~
Merocco.


A hankali ake bashi magani, yana sha tare da kauda kanshi, yayi sannan yace musu.
"Kun sami labarin ta?"
Shiru suka yi, Sultan Mu'allim ya bude baki zai magana ya dakatar dashi.
"Don Allah! Ka barni na tafi, ka barni na nimo ta, daga nan na san dole."
"A'a ba zan iya barinka ka tafi ba, zan saka mutane su nimo min ita, nima jini na ne Ikram"


"Ikram?" Ya tambaya yana kallon Sultan Mu'allim, sannan ya kauda kanshi.
"Taya ta zama jininka bayan mu kana da wasu yaran ne?"


Shiru yayi sannan ya faɗa mishi wacece Ikram, tashi zaune yayi tare da zaro idanu. Yana murmushin jin dadi kamar bashi yake yada kai kamar an yanke mishi kunne ba, sai gashi yana murmushi da jin dad'i, kafin kace kwabo sai gashi ya ware kamar da wanda ya sha jinya na wasu watanin ba, zunzurutun ya saka Ikram a ranshi, murmushi yayi lokacin da aka rike mishi hannu za a kaishi ban daki yayi wanka, shi daya sai hango daren amarcin su yake, tare da rufe idanun shi. Dakyar yayi wanka ya fito aka bashi kaya ya saka, ya zauna yana kallon su.


Abinci aka jera mishi da kanshi yaci bai yarda an bashi ba, yana yi yana murmushi. Har ya gama. Kallon Kakan shi yayi yace mishi.
"Sultan yaushe za a fara niman ta, dan gaskiya nima zan tafi"


"Me yasa kake azarbab'i?" Ya tambaye shi, dake Rahil irin mutanen nan masu fadan gaskiya kome kayi sai dai kayi bai wani damu ba, yacewa kakan.
"Kaunarta nake? Ina sonta a matsayin matan aurena, so nake na ajiye ta a matsayin Uwar yarana, don Allah ka taimaka min?"


Tabbas yayi abinda ba kowa yake yi ba, ya fito ya bayyana sirrin zuciyar shi, akan mace rike hannun shi yayi tare da cewa.
"Toh ka ajiye haka a ranka indai ina da Iko da ita Insha Allah Bilqisul Ikram Matarka ce!"


Gyada kai yayi tare da murmushi. Yana faɗin.
"Nagode Sultan!"


Mikewa yayi sannan yace mishi.
"Ka ci abinci! Kasha magani sai ka kwanta ka huta. Mijin Ikram!" Murmushin jin kunya yayi tare da sunkuyar da kanshi yana dariya.


---
Kallon dakarun yayi sannan yace musu.
"Ku kira min Waziri."
Da sauri suka

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads