Showing 39001 words to 42000 words out of 201974 words
Chapter 14 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
sanda hakan ta faruba, ba Asmah da akama murmushin ba hatta zahra da ke gefenta saida shock ya kamata ta zaro ido,
Asmah kam suman tsaye tayi tunda take a rayuwarta zata iya cewa yaune rana ta farko da Aslam ya mata murmushi mai sunan murmushi ba murmushin mugunta ba,
Husnah ya furta a kan la'b'bansa ,
husnah ta maimaita sunan kamar yadda ya fad'a, dage mata gira d'aya yace yes my husnah............
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fi sabillah🙏
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO ~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah ya jigan iyayen mu}
Page 53 & 54
Waige waige ta farayi alamar tana neman wacce ya kira da my husnah, daidai nan su batool suka qaraso , suma ganin Aslam ya basu mamaki , gaidashi sukayi, sannan suka ce, zahra , da Asmah suzo suje ya kamal na jiran su a get, yau bazai qaraso ciki ba sauri yakeyi, kafinma su gama rufe baki tuni Asmah ta kama hanyar get, ranta fal mamakin Aslam, to kodai kunnenta ne ya jiyo mata karya, kai ina kunnenta ne ,bataji mai ya fad'a da kyau bane, anan ta watsar da maganan bata wani dauke shi da muhimmanci balle ya dameta,
haka suka qarasa har wurin motar ya kamal , suka shiga ya ja su zuwa gida,
Aslam kam suna barin shi a wurin , ya naushi iska , ranshi na matuqar tafasa , ganin yadda ta wuce ta barshi a tsaye kamar wani sakarai , a fili ya furta wato daga an ambaci sunan shi ko tsayawa ta saurareni batayiba ta tafi gareshi ni kuma ta barni a tsaye kamar mara aikin yi ko, zakuyi bayani wlh
Daga ke har shi yau zan kawo karshen wannan cin amanar naku
zabura yayi ya fad'a mota ya bi bayan su kamal a guje, kamar ana binshi a baya, ranshi na tafasa, yau zaije ya samu kamal ayi wacce za'ayi , yau za'ayita ta qare komai zai faru ya dad'e bai faruba
Zee taga idi yau, dan mami tunda ta haura sama bata qara waiwayarta ba , yunwa ne ya fara sakadarta, tun tana daurewa, hardai ta miqe zaune ta rafka tagumi , da hannu bibbiyu, ta ajiye waya , juice da ruwan da mami ta ajiye mata d'azu tuni ta shanye, sai goru nan,
Ya kamal na fakin ,suka fito zasu wuce, Jakarta ya dauka kamar yadda ya saba har ta kama hanya zata bi bayan su zahra ,ya kira sunanta da "my Asmah", juyowa tayi tana kallon shi da murmushi a fuskarta itama cikin sassanyar daddadar muryarta tace "na,am my kamal" murmushin fuskarshi ne ya fad'ad'a, bata taba kiranshi da wannan sunan ba sai yau wani dad'i yaji ya lullubeshi,
Yace "me Aslam yajeyi a makarantarku" dan shiru tayi kafin tace"nima ban sani ba kawai ganin shi mukayi kuma kafin wata magana ta had'a mu, ka iso shi kenan muka wuce muka barshi a can" wani d'an murmushi takaici kamal ya saki kafin yace"ni nasan meya kawo shi, na riga na gama gane take takensa tun ba yau ba , amma kuma na lashi takobin wannan karan bazai taba bari yayi nasara a kaina, inason na roqeki wata alfarama dan Allah asma,u" kallan shi tayi da daradaran idanunta , da suka fi komai fusgar mutum idan yana kallonta, cikin sanyi jiki tace"wacce irin alfarma ce wannan ya kamal, ka fad'e ta, indai batafi qarfina ba zan maka bi'izinillah" yace "inaso ki bani dama na sanar ma magabatan mu batun soyyayar mu, domin na fara ganin alamun wasu suna mana bita da kulli" bata fahimci inda maganarsa ya dosa ba amma bata wani tsaurara binkice ba tace"nà amince maka indai hakan zai faranta ranka masoyina"
don ba qarya itama yanzu ba kadan ba take jin ya kamal din har cikin zuciyarata , saboda kulawar da yake nuna mata da irin soyayyar da yake nuna mata , da irin kyautatawan shi a gareta, har , yakai matakin da zata iya hakura da karatun ta, ta auri Kamal , ta amince daga baya ta qarqare karatun a d'akin sa , tunda tasan ba zai hana ta ba,
Kallonta yayi cikin tsananain farin ciki fuskarshi na qara fad'ad'a da murmushi yace"da gaske kike my luv " gyada mai kai tayi itama tana murmushi,
Daidai lokacin Aslam ya danno kan motar shi cikin gidan a guje , hangosu suna sakarma juna murmushi ya qara fusatashi aikuwa ya nufo Kansu gadan gadan , zuciyarshi na gaya mai yabi takan kamal kawai kowa ya huta ,
Da wani irin zafin nama kamal ya kauce ganin mota ya nufosa gadan gadan, Asmah kam duqewa tayi ta daura hannu akai ta Riga ta gama sadaqarwa ta mutu kawai, daidai da ita ya taka wani irin mahaukacin birki ,
A wani irin fusace ya fu bud'e murfin motar ya fito , zagayowa yayi ya kama , hunnun Asmah cikin bacin rai da rufewar ido ya figeta zuwa part din mummy , da sauri kamal ya rufa musu baya,
Dan Allah kuyi hakuri wlh kwana biyu bana samun time sosai ne , kuyi manage da wannan ba yawa, karkuyi fushi fa mutanena😄
Oum ummeetarh
07041130088
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa Mahaifiya, Allah kajiqan iyayen,}
Page 55 & 65
Kokawar fisge hannunta takeyi amma ta kasa, karfi ba d'aya ba , bai tsaya ko ina ba sai tsakiyar falon mummy,
Mummy dake zaune a falo tana amsa kiran daddy ta wayar tafi da gidan ka(telephone) dake falon sai ganin Aslam tayi ya shigo a fujajan. riqe da hannun Asmah yana janta ita kuma tana ciccijewa,
Bata san sanda tayi wurgi da wayar hannunta ba , ta miqe tsaye tana sallallami,
Sakin hannunta yayi yana huci ya nunata da yatsa , yace " ke wlh baki isa ba karyarki tasha karya ki wulaqantani, nayi tattaki nabar tarin aiyukan dana keda shi a office na tafi makarantarku saboda ke , amma kika wulaqanta ni kika wuce kika barni , kika bi wani banza maci amana ko, ta daga ke har shi zanyi maganin ku , baza ku mayar dani mahaukaci ba wlh"
Mummy ce cikin tsawa ta katse shi da cewa " kai Aslam wai meke damunka ne haka, kana cikin haiyacin ka kuwa, " yace "kwarai mummy cikin haiyacina nake, yarinyar nan tana neman ta zautar dani , mummy soyayya fa takeyi da kamal , " mummy tace " toh so what! Idan tana soyayya da kamal,ina ruwanka meya shafeka, yace " mummy bazan iya jurewa bane zuciyata zata fashe idan na ganta tare da ko wani d'a namiji bama kamal kadai ba " mummy tace " akan wani dalilin zuciyarka zata fashe, kai asuwa" yace " zuciyata zata fashe ne a dalilin ina sonta ina kaunarta, bazan iya jurar ko wani namiji ya rabeta ba , mummy bazan iya ba "
Mummy kamar saukar aradu taji zancen shi ya daki zuciyar ta, duk da ta ruga ta hasashe wani Abu dama, cikin wani irin mamaki mummy tace "what! me kace, Aslam kanada hankali kuwa , ta barin gaya maka idan mafarki kakeyi ka farka kada ma ka bari wani yaji wannan maganar a cikin gidan nan,"
Asmah kam suman tsaye tayi jin yau Aslam da bakin sa yake furta yana sonta yana qaunarta , bata san sanda ta bude baki tace ",wlh mummy karya yakeyi , ya Aslam baya sona baya kaunata, ba kuma zai taba sona ba , ya tsaneni , tun ban mallaki hankalin kaina ba nasan da hakan, kamar yadda nima na tsaneshi , bana sonsa bana kaunarsa kuma bazan taba sonsa ba, har qarshen rayuwa ta, mummy ya kamal nake so shine masoyina na hakika , shi nake kauna , mummy kuma da shi zan rayu"
Kamar saukar wuta a maqoshi haka Aslam ya dingajin saukar kalaman ta cikin zuciyarshi, cikin wani irin zafin kishi da rufewar ido , ya isa gabanta ya shaqo wuyarta , cikin managa ihu ihu yake cewa " ni kike cewa baki so husnah, ni kike cewa kin tsana bazaki taba soba har warshen rayuwarki , a gabana kike cewa kina son wani d'a namiji bani ba , to wlh sai kin sona ko kina so ko bakya so sai kin aure ni kin zauna dani har qarshen rayuwarki , domin kuwa domin ni kadai aka halicce ki"
Kokawar kwatar kanta takeyi a hannunshi ta kasa , sai zazzare I do takeyi, mummy cikin kururuwa ta daura hannu a kai tana kiran sunan Allah ,
Cikin tsananin fusata da zafin zuciya kamal yayi wani sufa ya shaqi wuyan Aslam ta baya muguwar shaka kuwa, baisan sanda ya saki Asmah ba yana sake ta ta tafi sululu zata fadi , batool da Amira , da hayaniyar da suka ji daga falo ya fito dasu daga d'aki ba shiru, suka tarota ta fad'o jikin su,
Kokawa kwatar kanshi ya shiga yi har Allah ya bashi sa'a , nan kuma aka shiga kaima juna kulli, baji ba gani, dambe sosai kamar wasu yan wrestling ,ko wanne zuciya na diban shi , basu ko sauraron kukan da mummy ta keyi tana kiran sunan su, zahra da saukowarta kenan daga upstairs, don sanda su batool suka fito tana toilet , ganin abinda ke faruwa ta fita compound din gida da gudu tana kiran sunan duk Wanda ya zo mata baki cikin mutanen gidan,
Daddy ne ya fito daga part dinsa sanye da jallabiya ta baibai, kallo d'aya zakasan a matuqar fusace yake, tun lokacin da yake waya da mummy , yaji ta yarda wayar ta kama sallallami, ya kasa kunne yana sauraran meke faruwa , gaba , daya ji yake kamar in ya riqe Aslam ya kama duka kar ya barshi har saiya kwantar dashi a asibiti,
Zahra karo tayi da Abba da shima dawowar shi kenan daga aiki , riqeta yayi ganin a rude take yana tambayar ta meke faruwa kasa managa tayi sai nuna mai part d'in mummy kawai takeyi,
Daidai nan zee da mami ma suka qaraso garesu , ganin tana nuna part din mummy yasa da gudu suka dunguma zuwa can,
Daddy na shiga falon , daidai lokacin Aslam ya samu sa'ar kaima kamal naushi a gefen kumatu , take baking shi ya fashe yana tsartuwar jini, wani gigitaccen tsawa, daddy ya daka musu ba shiri suka rabu , kowa na sauke munfashin fusata, qarasawa gaban Aslam yayi ya daukeshi da wani irin gigitaccen mari kafin ya dawo haiyacinsa ya qara daukesa da wasu marukan har gida biyu,
Dafe kumatu yayi , yana bin daddy da wani irin kallo, nuna shi daddy yayi da hannu cikin tsakanin fusata, yace" fita kabar gidan nan kafin na rufe idona na bud'e mutumin banza mutumin hofi" bude baki yayi zaiyi magana , daddy ya katseshi da cewa " I said get out from dis hause" Abba ne ya qaraso yana tambayar meke faruwa ne , kowa shiru yayi an rasa Wanda zai maida ba'asi ,
Daidai nan alhaji baba ya qaraso falon hajiya mama na rufa mai baya, ganin da ya musu a tsaye cirko cirko yasan ba lafiya ba , yana zaune a falon shi, shida hajiya mama , bello ya shigo cikin rudewa yake shaida mai wani Abu na faruwa a part din daddy , don a idonshi zahra ta fito tana neman agajin mutanen gidan,
Bai tambayi ba'asi ba saida ya nemi guri ya zauna , umartan su yayi da cewa kowa ya zauna, ba musu kuwa kowa ya nemi guri ya zauna a qasa daddy da Abba suka zauna a qasa wurin qafar alhaji baba, suka sakashi a tsakiya, Asmah na kwance jikin mummy , su batool ma duk suna rakube kusa da mummy su, zee ma na zaune kusa da mami, kamal da Aslam ma duk suna zaune ,
Gyaran murya alhaji baba yayi zai fara magana saiga Amir ya shigo shima guri ya samu ya zauna kusa da Aslam,
Kallon mummy alhaji baba yayi yace "Aisha meke faruwa "mummy kwallar da ta taru a idontane ya sauko kan kumatunta, share wa tayi kafin cikin sanyi murya ta labartawa alhaji baba abinda ya faru A to Z shuru falon ya dauka , kowa da saqe saqen da yakeyi a ransa , alhaji baba baiba kowa daman magana ba sai mummy don haka ba wanda ya isa yayi magana a d'akin,
Mummy na gama wa, alhaji baba ya watsa ma Aslam wani mugun kallo, wanda yasa gaban Aslam yankewa ya fadi , cikin murya mai dauke da amon bacin rai yace" ina fatan har yanzu baka manta da maganar dana taba fada maka watannini baya da suka shud'e ba, to idan ma ka manta bari na tuna maka, ni Muhammad nace ko bayan raina ban yarda , wani cikin yayana ya qara daura maka aure da Asma'u ba , ballantana kuma ina Raye da raina da lafiya ta," wani murmushin takaici alhaji baba yayi , ya maida dunansa kan kamal yace" kamaluldeen da gaskene kaida Asma'u kuna son junan ku, " kamal yace"eh alhaji, har mun dai daita ta bani dama naje na samu ,su daddy da maganar,"
Alhaji baba yace "masha Allah , komai yayi daidai, ni Muhammad, a matsayina na wanda aka wakilta na aurad da Asma'u na baka aurenta kuma na tsayar da lokaci nan da wata uku masu zuwa insha Allah,"
Kusan gaba d'aya muatanen falon saida fuskarsu ta nuna farin cikin a bayyane, except Aslam da yayi kamar ya kurma ihu
Ci gaba alhaji baba yayi da cewa Abu na gaba" suma y'an uwan Asma'u wato y'an biyu da kuma Amira na basu nan da wata daya daya ko wacce ta gabatar da nata manemin domin kuwa gaba daya za'a had'a ayi bikin tare da na Asma'u da kamalu idan yaso kowacce taje ta qarqare karatun ta a dakin mijinta, duk kuma wacce bata da tsayayye ni zan Neman mata miji na gari na hada ta da shi, na riga na gama yanke wannan hukuncin koda na mutu yau kada a fasa ai wayar da wannan lamari"
Gaba daya kowa na falon yayi farin cikin , saidai zuciyar yan matan mummy cike take da fargaba, ko wacce na tunanin wa zata gabatar a matsayin mijin aure , a cikin wata d'aya masu zuwa, har gwara amira don jiya jiyan nan ya Amir ya gabatar mata da kanshi a matsayin masoyinta , yanzu haka ma bata bashi amsa ba, duk da ta riga ta gama aminta dashi, a cikin zuciyata , dama tun can ya amir na matuqar burgeta,
Amir ne ya dan sunkuyar dakai yana Sosa keya kamar wani Mara gaskiya , yace "Allah ya qarama alhaji lpy da Nisan kwana inada watsa magana mai muhimmanci da nake son nima na gabatar maku, na tabbata zata sanyaku farin ciki matuqa,"
Kallo ne ya koma kan amir d'in, alhaji baba yace" fad'i maganarka kai tsaye Amiru nuna saurarenka"
Qara qasa yayi da kai yace" nima nida kanwata yar uwata Amira mun daidaita kanmu"
Masha Allah masha Allah haka kowa na falon yake fadi tun daga kan alhaji baba, hajiya mama, daddy, mummy, Abba, mami,kowannen su yayi matuqar farin ciki da jin wannan batu na Amir,
Murmushin jin dad'i alhaji baba yayi yace"masha Allah Abu yayi kyau Amiru Allah ya tabbatar mana da alkairi"
Da amin aka shiga amsa wa. Kowa zuciyarshi wasai amma manta da batun wani Aslam a fallon,
Miqewa yayi a fusace ya kalli alhaji baba yace " dama na Dade da sanin baka kaunata a cikin ahlinka , to shiken nan Abu yayi kyau, ga gidanka nan yau zanbar makakaida yayanka , daga rana mai kama ta yau bazan qara tako qafa ta cikin gidan nan ba, " kafin ya kai karshen rashin kunyarshi tuni , daddy ya miqe ya qara sauke mishi wasu zafafan zarukan da sukafi na dazu shigarshi matuqar , hankada shi daddy yayi ya fitar dashi daga fallon ya wugo shi waje,
Cikin matuqar fusata ya nufi motar shi ko waiwayen baya bai qarayi ba, ganin haka yasa mami miqar da zee tsaye tace "zainabu kibi mijin ki"
Da sauri ta rufa mai baya don ita wannan hukinci na alhaji baba ba qaramin dadi ya mata ba , ji takeyi kamar ta goya alhaji baba ta zaga garin minna.......
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fi sabillah🙏
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wanny book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Page 57 & 58
Da mahaukacin gudu ya bar gidan bayan zee ta shiga motar , saura kadan yabi takan me gadi,
Allah ne kadai ya kaisu gida lpy don Aslam gaba d'aya baya cikin haiyacin sa,
Yana yin parking ya fice a fusace ko qala baice ma zee ba,
Direct d'akin sa ya nufa ya kulle kofar ta ciki ya bar key a jiki,
Kan bed dinshi ya fad'a rigingine , ya shiga sauke wasu irin ajiyar zuciya, kai da kaji kasan bana lfy bane
Zee kam ganin ya fice baice mata kala ba , ko ajikin ta, hakan ko kadan bai dameta, ita yau jinta takeyi wasai , saima wani nishadi na musamma daya risketa , a yau Wanda ta dad'e batayi irin shi ba,
Cikin yan waqe waqenta tana rausaya ta shiga falon, ganin baya nan , ta ta'be, ta haura sama abinta, dakin ta ta shiga tayi wanka tayi sallan azahar da la'asar, sai lokacin ma ta tuna da yunwan da takeji dazu,
Kitchen taje ta dafa indomie ta zauna taci , har lokacin bataji motsin Aslam ba, nan tabàr plate d'in ta wuce dakinta ta kwanta ta kama sana'ar tata (charting),
Har dare ba motsin