Showing 21001 words to 24000 words out of 201974 words
Chapter 8 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
jira shi, mai gadi ya wangale get motar yaya kamal ya kunno kai cikin gidan , zahra na ganin shi ta fara murna tace "yawwa ga ya kamal nan ma bar in roqeshi ya kaimu" Asmah dai shiru ta mata, da sauri zahra ta nufi motar kamal daya paker ko fitowa bai kaigayi ba , ta window tadan duqa tace "sannu da dawowa ya kamal " d'agowa yayi jin magana ta window ganin zahra ce yasa shi sakin murmushi sannan yace"yawwa zahra'u ya gida ". tace "lpy qlau, don Allah ya kamal ka kaimu tunga road mu amso dinkin mu na biki da zamusa gobe , munzo bello ya kaimu wai baya nan ya Aslam ya aikeshi" kamal yace "kai zahra na gaji fah bakiga dawowa na kenan daga gurin aiki ba gashi lokacin masallaci ya kusa "marairaice fuska tayi tace "don Allah ya kamal, tana hade hannayenta alamar roqo🙏,
dagowa yayi ya kalleta ganin yadda ta marairaice yace"dondai kece fa sis zahra, da batool ce da ba inda zanje, shiga muje na kaiki"tsallen murna tayi tana jin dadi tace "nida Asmah ne " daga murya tayi tace "Asmah zo muje ya kamal ya kaimu" bude gaban mota tayi ta shiga ,Asmah tazo ta bude baya itama ta zauna sannan tace "sannu da dawowa ya kamal ya aiki" ta cikin madubi ya kalleta kafin ya amsa mata da "lpy qlau my Asmah" Rivas yayi da motar mai gadi ya bude musu get suka fice daga gidan,
Kamal ta cikin madubi yake Satan kallon Asmah dake zaune a bayan mota duk d'agowan da zatayi kuwa sai sun hada ido
Dai dai zasuhau kan babban titin da zai kaisu tunga road suka gifta motar Dr bash, shida Aslam da amir ne acikin motar, zasuje gida ne donyin shirin sallan juma'a, kasancewar motar Dr bash mai duhun gilashi ne , kuma basu San motar shi ba balle Susan ko sune aciki, suko su Amir rass suka gane su,sboda dukkan su sunsan motar kamal kuma glass d'inshi fari ne ana iya ganin na cikin motar,
Bash dake tuqi ya kalli Amir dake gefen shi yace "wai dan Allah Amir na tambayeka mana" Amir yace"inajinka Allah yasa na sani" bash yace "yammatan da na gani a motar kamal yanzu su waye" Amir yace" meyasa kake tambaya " bash yace "kaga wannan na bayan motar" Amir yace "eh Asmah kenan" Dr bash yace "tun ranar dana fara ganinta washe garin ranar dana dawo 9ja wlh zuciyata ta kamu da sonta ko baccin kirki bana iyayi saboda tinaninta, amma kullum nama Aslam maganar ta saiya shareni kokuma yace min shi bai ganeta ba, alhali ranar muna tare na fara ganinta ta fito daga part din mummy" Amir ya juyo ya kalli Dr bash yace"da gaske kakeyi bashir " bash yace "na taba maka irin wasan nan ne"Amir yace"aiko zan shige maka gaba indai da gaske kake don wlh yarinyace na tsattsatsiya mai hankali, duk Wanda ya samu daman aurenta kuma ya saki yayi babban asara," ya qarashe maganar yana kallon Aslam ta madubi, bash yace"to wacece ita a gare ku". Amir yace "kanwarmu ce, jikan alhaji Mallam cefa ba kasan shi ba babban malamin nan aminin alhaji baba, kasan shi ai" bash yace "sani kai, da muna yara har kwana na tabayi a gidan shi da mukaje da Aslam ruwan sama ya tare mu sai muka kwana, tsohon kirkine wlh" Amir yace " to jikan shice ta wurin danshi na fari alhaji aminu mai rasuwa. marainiyace iyayenta sun rasu tun tana qarama a gidanmu ta tashi, sunanta Asma'u". Bash yace "Allah sarki Allah ya jiqansu, to ita wacce ta zauna a front sit dinnan fa" Amir yace yan biyu ne fa baka ganeta bane zahra ce fa". bash yace "haba don Allah" amir yace "Allah kuwa" bash yace "eh lallai girman mace ba wuya yan biyu ne suka girma haka , Allah mai iko, to amira fa?' bash ya sake tambaya murmushi Amir ya sake ganin an ambaci sanyin idayanshi yace"tana nan lpy itama ta zama ammata, ko Aslam,?" Ya fada yana dan juyowa ya kalli Aslam ,
Aslam da tun dazu ranshi ke tafasa jin abinda suke fad'a ya watsawa Amir mugun kallo ya dauke kai, ranshi in yayi dubu ya baci, kwata kwata a rayuwarsa baya son raini da qasakanci, amma ya lura bash da Amir suna Neman ja mishi raini a gurin qananan yaran daya goya a bayan shi, yaran da yake kallo har yanzu a mastayin jarirai, daidai lokacin mai gadi ya bude musu get suka shiga gidan don yin shirin masallaci.....
Har qofar shagon dinkin kamal ya kaisu, ya kuma biya cikon kudin dinkin, basu wani tsattsaya ba ,suka dawo gida domin lokacin sallah ya kusa, kamal dimma inbaiyi sauri ba da'ker ya samu sallah,
Don haka yana sauke su zahra ta dauki ledan kayan ta fara yin gaban ,tana cewa"ya kamal mun gode Allah ya saka maka da alheri,' ta shige ciki, Asmah ma godiya ta masa ita ma, ta fito zata wuce tanama zahra qorafin bata jirata ba,
Kamal ya kira sunanta , juyowa tayi ta sauke mishi wadannan dara darn idanun nata daya sashi jin wani yarrr ajikin shi ,murmushi ya sakar mata tare da cewa " I hope kin gama tunanin ko", shiru tayi , yace "well ki shirya anjima zanzo naji amsata " gyada mai kai kawai tayi , yace "OK barin je masallaci saina dawo ' to kawai tace mishi tayi gaba, shima motar ya koma yayi Rivas ya fice daga gidan don zuwa masallaci.......
Oum ummeetarh
07041130088
Share
and
comment
fi sabilillah🙏
Date: Oct 15, 2022
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rada mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Page 37 & 38
Itama Asmah direct sashen mummy ta wuce, a falo ta samu su zahra da ummi da yan biyu sai bude dinkunan sukeyi suna kallo, kowacce ta dauki nata, tana gaisar da ummi batabi takan su batool ba ta upstairs ta hau direct ta wuce dakinsu, ruwa ta watsa ta dauro alwala daya daga cikin abayan da ya kamal ya sai mata ta dauki wani maroon color mai shegen kyau yaji tsone ta ko ina,ta saka abinka da farar fata ba qaramin kyau ya mata ba, sallan azahar tayi tana idarwa, ko abinci bata nema ba ta hau gado ta kwanta, tana tunani a haka bacci ya kwasheta....
Ummi jin shiru Asmah bata sauko ba yasa tace Alhasan yaje ya kirata,tazo ta duba nata dinkin,
Dawowa Alhasan yayi yace"tana bacci". Ummi tace "ikon Allah bacci kuma, jiya fa bakuyi bacci da wuri ba"
Haka sukaita sabgoginsu a falon mummy saida aka kira la'asar zahra ta haura sama donyin sallah,
Su kuma su amira suka bi Ummi part din hajiya mama, .
Har lokacin bacci Asmah keyi, alwala zahra ta dauro ta gabatar da sallan la'asar, saida ta idar ta tashi Asmah, ganin batada niyyar motsawa,
Tana falkawa taga zahra tace "subhanallahi bacci nayi ashe" zahra tace"eh gashi har an idar da la'asar ". Da sauri ta miqe ta shiga toilet ta d'auro alwala, pray mat din da zahra ke nilkewa ta amsa ta shimfida ta gabatar da sallah, koda ta idar zahra bata d'akin, don haka itama ita saukowa qasa tayi, falo ta samesu yanzu harda mummy da wasu daga cikin dangi,
Gaishe su tayi ta wuce dining don tafara jin cikinta na kiran ciroma, abinci ta zuba kadan taci, ta tashi daga dining din ta dawo falo akaci gaba da hira da ita,
Hanifa ce ta shigo falon mummy. Da dan tsalle tsallenta na yara, don hanifa kwata kwata batafi shekaru hudu ba , direct gun Asmah ta nufa ta fada jikinta tare da cewa"Anty Acmah wai kijo inji Uncle kamay" gabanta ya fadi tunawa da tayi dazu yace zaizo yaji amsarsa, amma ta dake tace "yana inane Uncle kamay din" ta fada cikin kwiykwayon muryar hanifa mai tsami, "yaya garden " hanifa tace , dan lakace hancinta Asmah tayi tace"oya kije kice masa ina zuwa" tom" hanifa tace kafin ta zura da gudu ta fice , mummy na kiranta ko amsawa batayi ba balle ta juyo,
Ten minute ta qara zaune a falon, kafin ta tashi ta haura sama , d'akinsu ta shiga gaban mirror ta tsaya , ta dauki turarenta mai sanyin kamshi ta fesa kad'an, kwalli ta zizara a fararen idanunta masu sheqi sai man lebe data shafa mai d'anqo, mayafin abayan jikinta ta dauka tayi rolling dinshi,
ba qaramin kyau tayi ba farin kyakkyawan fuskarta sai shining yake, wayarta ta dauka tare da zura wani plat shoe mai kyau ta sauko falon, kusa da mummy take tadan rusuna dai dai kunnenta tace ," mumyy wai ya kamal na kira na " "ok" Mummy tace mata , don haka ta nufi hanyar fita palon, batool ne tace "sister sai ina" alamar tana zuwa ta mata da hannu ta fice daga palon,
Hanyar garden ta nufa cikin takunta na natsuwa, garden din yana cen ta bayan gidan ne, don haka sai an wuce part din su Aslam dake farkon gidan kafin a isa garden din,
Dai dai ta gifta kofar part din shi kuma Aslam ya fito don ya amsa call, kasancewar falon cike yake da abokanan shi, hayaniya yayi yawa,
Ita bata ganshi ba amma shi ya ganta kuma ya gane itace kasancewar yaga gefen fuskarta datazo giftawa,
Samun kanshi yayi da tambayar kanshi ina kuma wannan yarinyar zata je?, ba mai bashi wannan amsar
Haka kawai ya samu kanshi da bin bayanta a hankali yanda bazata ganshi ba, gani yayi ta nufi garden ta bud'e dan guntun get din wurin ta shiga, ci gaba da binta yayi ba tare da ya bari ta sani ba,
Tana shiga ta hango ya kamal zaune akan wani shimfidadden kafet mai laushi, zaune yake yana facing cage na tsuntsayen kanari kala kala sai shawagin suke yi gwanin sha'awa, hankalinshi gaba d'aya ya raja'a akansu.
Qarasawa tayi tare da yimai sallama, juyowa yayi kyakkyawann fuskarshi dauke da murmushi yana amsa mata
Sai a lokacin Aslam dake la'be yaga ahse kamal ne don da baiga fuskarshi ba kasancewar ya juya baya, gani yayi kamal din ya nuna mata gefen shi yace ta zauna, zaman kuwa yaga tayi dan nesa kadan da kamal d'in,itama tana facing cage din,
Samun kanshi yayi da jin haushin ganin su haka da yayi, a zuciyarshi yace yadda suka zauna dan Allah sai kace wani miji da mata kokuma budurwa da saurayi,tsaki tsaki yaja a fili , wata zuciyar ce ta kwa'be da cewa to kai ina ruwanka, tsaki ya kuma ja ya juya zai wuce,
Saidai kuma me! Samun kanshi yayi da son jin abinda zasu fad'a,
Kamar Wanda ake controlling dinshi da remote haka yake bin umarnin zuciyarshi,
Samun kanshi yayi da qarasawa cikin garden din sad'af sad'af. Yadda baxasuji takun step d'inshi ba.
Gurin ya samu dan nesa dasu yadda zai iyajin abinda suke fada ya zauna , kasancewar sun juya mai baya yasa basu ganshi ba, shiko hakan yamai dai dai,waya ya dauko ya qara a kunnenshi kamar yana amsa call nan ko dukkan hankalinshi na Kansu , yayi hakane koda zasu juyo su ganshi sai yayi pretending..
Kamal ya juyo ya kalli Asmah yace" my Asmah" barka da juma'a, dan boye fuskarta tayi tana murmushi alamar taji kunyar sunan da ya kirata dashi, shima murmushi yayi mai sauti yace "yau kuma kunyata kikeji ne,". Still batace komai ba, ya qara cewa "to shikenan ina jinki, bani amsata" shiru tayi kanta na qasa bata ce komai ba, kamal ganin shurun nason yayi yawa ne yace"ke nake saurare my Asmah"
Dagowa tayi ta kalleshi shima din ita yake kallo, idanu suka had'a tare da sakar ma juna murmushi , saurin kauda kanta gefe tayi, sannan a hankali kamar mai ciwon baki tace"na amince da soyayyarka ya kamal Allah ya shige mana gaba,'. Tana gama fadin haka ta saka kanta cikin qafafunta ta 'boye fuskarta, alamar kunya,
Aslam dake zaune a bayan su, da sauri ya dago kanshi yana kallonsu jin abinda Asmah ta fada
What!!! Soyayya, gaban shine ya shigafaduwa, hankalinshi ya tashi, tsoro da firgicine suka ziyarceshi a lokaci daya,
Shi karan kanshi baisan dalilin shi na shiga wannan yanyinba daga jin wannan maganar,
Kamal ko jin amsar data bashi wani irin farin ciki ne ya lullu'beshi, juyowa yayi ya kalleta fuskarshi cike da farin ciki yace "da gaske kike my Asmah". Kanta dake cikin cinyoyinta ta girgiza mai alamar eh,
Hannu ya daga sama yace "Allah na gode maka da kasa wannan baiwa taka ta amince da soyayyata cikin sauqi, ya Allah ka mallakamin ita cikin sauqi,". Sauke hannayenshi yayi ya juyo ya kalleta yace"nagode my Asmah kuma na mika alqawrin insha Allah zaki sameni miji daya tamkar dubu"
Dago kai tayi ta marairaice fuska tace"sai dai ina buqatar wani alfarma a gare ka ya kamal" yace "yace wani irin alfarma kike nema " tace "so nake maganar soyayyan mu ta zama sirri tsakanin nida kai, banason kowa ya sani har sai na kammala karatuna," yace "saboda me" tace "saboda bana son na rasa daman yin karatu a karo na biyu, domin muddin alhaji Mallam yaji wannan maganar nasan bazai barni nayi karatu ba , aure zaimin kuma banaso" ajiyar zuciya kamal ya sauke yace "karki damu indai don wannan ne bazan sanar ma kowa ba, nima bana son ayi auren yanzu sai mun qara fahimtar juna, kafin nan kin kammala karatun ki". , d'ad'ine ya lunlu'beta, jin y amince da maganar ta.
Aslam sad'af sad'af ya tashi ya fice daga garden d'in yana hard'e hanya,
Idan ya fahimci inda maganganunsu ya dosa , kenan soyayyace suka kulla a tsakanin su
Kai! Ina! Hakan bazai taba faruwa ba , wannan ai cin amana ne, kamal yake son yamai, bai taba tunanin kamal xai mai haka ba , yarasa dawa zaiyi soyayya saida ex wife dinshi,
Lallai baiga ta zama ba , bazai taba barin hakan ta faru ba , to ta haramta ga duk wani d'a namiji indai jininsa ne, taje can ta nemi mijinta a wani familyn badai nasu ba
Da wannan tunanin ya qarasa part d'insu, inda ya taradda abokanan nata firansu kamar yadda ya fita ya barsu.....
Guri ya samu ya zauna yana saurarensu baicewa kowa komai ba,jikinshi duk a sanyaye, su karan Kansu abokan sun lura da sauyin da ya samu yanzu yanzu daga fita amsa call,
Asmah kam kimanin awa d'aya suka dauka suna firan su kafin suyi sallama ta koma cikin gida........
Jama'a gobe daurin auren Aslam dinku da zee his luv 🤏😎 general invite to all readers of dama ta biyu💖. Kudai ku biyoni muje yanzu wasan zai fara,
Much luv 🥰🥰🥰to all masoyan dama ta biyu, ina jin dadin comment dinku👍🥳
Oum ummeetarh
0704 1130088
Date: Oct 16, 2022
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Page 39 & 40
A haka wunin ranar ya qare jikin Aslam a sanyaye minti kadan tunanin kamal da Asmah ya fadomai a rai, minti kadan hoton su lokacin da suka sakar ma juna murmushi ya fado mai a rai, da'ker ya samu ya yaqi zuciyarshi yayi fatali da wannan tunanin, yaci gaba da harkokin gaban shi, har zuwa dare,
Dare nayi anan ne ya raina kanshi don kasa bacci yayi. Sai tunane tunane yake, yana saqa yadda zai ruguza wannan soyyaya na cin a mana, yasan ko yakai maganar wurin manya babu mai goyan bayan shi, zasuce meye hujjan shi na hana kamal Auren ta tunda shi ya qita, zasu zata ko sonta yake, shi kuma yanzu a zuciyarshi babu burbushin sonta ko kad'an a ciki zee dinshi ita kadai ce a ranshi ita yake so itace za'binshi, itace irin macen da yakeso wayayya yar boko, shi mai zaiyi da wata Asmah baya sonta baya kaunarta, hasalima shi ya tsaneta, kuma tsanan da ya mata ne yasa baya son ta auri wani makusancin shi,
(kai dai kasani Mallam Aslam muna nan muna jiranka ka gama kewaye kewayenka zaka dawo kan hanya ne😬)
Da ire iren wadannan tunaninkan yaketa juyi akan makeken bed dinsa, baiyi aune ba sai ji yayi ladan na kwada kiran assalatu, zabura yayi ya miqe tsaye ya kunna wutan d'akin ,kallon shi ya kai kan agogon bangon dake d'akin biyar saura kwata ya gani, mamaki ne ya kamashi na tsowan lokacin daya dauka yana tunani, da haka ya shige toilet ya dauro alwala raka'atanil fajir ya gabatar kafin ya wuce masallaci.
A can ya taradda mazan gidan duka,manya da yara , baqi da yan gida, ana idar da sallah miqewa yayi yaje ya gaisar da iyayen shi , da kuma alhaji baba , su amir da kamal ma hannu ya basu sukayi musabaha,sannan ya fice daga masallacin bai jira kowa ba , don bacci yake son yayi kafin lokacin tafiya daurin aure yayi, Amir ne ya biyo bayanshi da sassarfa yana cemai "haba ango kasha kanshi , na zainabu Abu mai tagyayen suna bako jira" share shi yayi bai tanka ba , a haka suka iso part dinsu na samari, Amir nata tsokanan shi yaqi tankawa ,
Kowannen su daki ya shige , Aslam bacci yake ji sosai don haka yana shiga dakinshi ya haye kan bed dinshi ya duqunqune cikin bargo sai bacci, ko azkar da karatun alkur'anin daya sabayi kullum bayan asuba bai samu yayi ba, bacci ne ya kwashe shi mai nauyi, kasancewar bai samu bacci da daddare ba,
Daurin auren qarfe Tara na safe za'ayi don haka , su Abba da daddy da abokansa , da duka wani mai niyyar zuwa wajen daurin auren qarfe takwas kowa ya shirya,
Amir ne ya sakko downstairs cikin manyan kaya harda babban riga