Header Ads
Showing 36001 words to 39000 words out of 201974 words

Chapter 13 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

2232

Ads at the middle of Article

d'aya abincin ya fita ranshi , mummy ta rusa mai shirin shi miqewa yayi ya fice fuuu ya nufi tsohon d'akin , yabar amir nan yana tsokanan shi ko kulashi baiyi ba,


Amir yace zama ka dawo hanya ne uban yan taurin kai , zanga karshen wanna girman kan naka, kana son yariya amma girman kai ya hana ka yarda , kuma insha allahu Asmah sai kamal donni bana goyan bayan qarya ehee,


Kwanciya yayi a kan tsohon bed d'inshi yayi ruf da ciki, tambayar kanshi ya shiga yi shin wai da gaske sonta nake, to indai wadannan abubuwan da nake ji game da ita sune so, meyasa banjin hakan akan zee da take matata da mukayi auren soyayya, kai ina hakan bazai taba zama so ba, saidai in wani mugun abin tamin, tunda dama jikar Mallam ce, wayar shi ya dauka ya shiga Google don yin bincike akan alamomin soyayya,




,( hmmmm su Mallam Aslam an shiga ajin sanin alamomin soyayya, Allah ya bada sa'a😅)






Zee kam yau taga rayuwa, tun karfe biyu take saka ran ganin Aslam, shiru shiru har la'asar , yunwa ta gama sakad'arta, duk tayi laushi, kitchen ta nufa ko zata iya sarrafa wani abun ta samu ta zuba ma tumbinta, indomie ta dauka guda biyu , duba bayan ledan tayi anan taga yadda ake dafawa, nan tayi ta bin method din da taga ni a bayan ledar indomin har ta samu ta kammala da'ker, duk da haka ba wani dadi haka dai ta cuccusa, maganin yunwa , baza baza tayi da kitchen d'in kamar ba dazu Aslam ya gama share wa ba , nan ta bar shi haka ko cokali bata wanke ba , amma dai yanzu ta kashe hot plate d'in,




Aslam sai kusan magriba ya gama binciken da zaiyi a Google, duk wani amsa da yake nema ya same shi, yanzu kam ya tabbata son Asmah yakeyi soyayya mai tsanani ma kuwa ,soyayyar da tun baisan kanshi ba tun bai gama zama cikakken mutum ba take fama da ita, soyayyar da ta qullu a gani na farko, soyayyar da ta dauki tsawon shekara goma sha biyar a cikin zuciyarshi tana wahalar da ruhin shi, yanzu wa zai tunkara, ta ina zai fara, yasan duk ta inda yace zai fara akwai babban matsala, shawara d'aya, ya yanke shine zai fara ta kanta , zai fad'a yaqin neman soyayyar ta yasan idan yayi nasara a kanta komai zai iya zuwa mishi da sauqi, (hmmmm Aslam kana ruwa)


Sai qarfe takwas Aslam yabar yabar gidan bayan ya cika tumbinsa da abincin da momi ta aiko mai d'azu, saida ya sake biya wa sashen mummy ko zai samu, qara ganin Asmah, amma kowa ma bai samu gani ba , haka ya shiga motar shi ya tayar ya nufo gida cike da fargaban mai zai tarar kuma,,






Yana shiga harabar gidan ya tarar ba daya motarshi dake fake a compound din gidan , sharewa yayi ya shiga falon bai kawo komai a ranshi ba, yana shiga baiga zee a falo ba , duba dakinta yayi baibganta ba nan ya shiga kwala mata kira shiru, neman duniya yama zee a gidan bata nan, neman gurin yayi ya zauna a falon ya rafka tagumi,




Zee kam tana ganin 7:30 yayi Aslam bai dawoba , taci kwalliyar ta ta dauki key motar shi ta bar gidan a cewarta baza ta iya zama ita d'aya a gida kamar mayya ba, yawanta ta dinga yi kamar yadda ta sabayi a gida, dama duk qafarta qaiqayi take mata kwana biyu nan da tayi bata fita ba, bata nan bata can haka ta dinga yawo , saida taga tara tayi ta biya safara food tayi take away ta kamo hanyar gida



Tun a wurin parking ta ga motar da Aslam ya fita da ita alamar yana ciki kenan tabe baki tayi, ta dauki ledarta ta nufi cikin falon , bako sallama ta shiga ,






Aslam dagowa yayi ya kalleta cikin bacin rai yace"daga ina kike" tace "nad'an fita shan iska ne' yace"wa kika tambaya " tace "bangane wa na tambaya ba, kana nufin idan zan fita a gidan nan saina tambayeka,' yace "of course saboda zamana kikeyi a gidan nan' wani murmushin rainin wayau tayi tace " haba dai sai kace wata qaramar yarinya da duk inda zani saina tambaya"yace " haka kikace ko to wlh kika sake fita a gidan bada izinina ba sai na nuna miki true colour na" tabe baki tayi ta wuce ciki abinta bata ba maganar shi wani muhimmanci ba,


A d'akin ta taci abincin ta ta yadda take away din a gurin taci gaba da sana'ar tata na charting,




Aslam kam zama yayi abun duniya duk ya ishe shi, lamarin zee ya fara gundirar sa, ganin baida wani abinyi yasa ya ciro wayar shi ya bud'o hotunan Asmah da yayi saving , ya kunna yana kallo' inya qare ya sake danna play kamar wani mara abinyi,


Zee ganin shiru shiru Aslam bai shigo ba yasa ta tashi ta biyo bayan shi don ta bashi hakuri a tunanin ta fushi yayi don ta fita ba izini , tana sakkowa falon ta hangoshi ya duqufa yana kallo a waya, baima san ta sakko ba, bi tayi ta bayanshi ta duqa don ganin me yake kallo haka,


Bata San sanda ta qunduma wani irin ashar ba ganin , hotunan wata kyakkyawan young lady na yawo akan screen din wayar shi, juyowa yayi da sauri yana kallonta , itama kallonshi tayi tana zazzare ido cike da masifa tace"wace yar iska ce wannan kake kallo"..........








💖More comment more typing💖










Oum ummeetarh
07041130088




Share
And
Comment
Fi sabillah🙏
💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~




FREE BOOK






{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}












page 51 & 52








Ranshi ne yayi mugun baci jin kalmar da ta jefi Asmah da shi, na yar iska, cikin tafasan rai yace "waike zainab me yasa baki da hankali ne, saboda ina kallon hotanta shine zaki kirata da yar iska. Kinsan ko wacece ita a gare ni,". Tace "kwarai kuwa yar iska , inba yar iska ba me hotanta yakeyi a wayar mijin wata,inba karuwanci da iskanci ba, naga dai ba kanwarka bace balle ". Miqewa Aslam yayi tsaki ranshi na qara baci , yace "bari kiji wannan da kike kira yar iska karuwa tafi min ke sau dubu"


Juyawa yayi da niyar wucewa d'akin shi ya barta nan tsaye, don inyace zai biye mata zai aikata mata abinda zaizo ya dame su daga baya , don bazai iya jurar jin irin zagin cin mutunci da takema Asmah ba,


Aiko tayi kukan kura tasha gabanshi taci kwalar shi, don Kalmar daya fad'a na Asmah ta fita so dubu ya dake ta sosai , cikin masifa da zafin kishi tace " karuwar taka ce ta fini sau dubu" ranshi ya fara tafasa cikin tsawa yace"keee jahila karki qara kiranta da karuwa" itama cikin tsawan tace" na fad'a karuwa karuwa karuuu" ji kake tauuu! Ya dauke ta da wani irin gigitaccen marin da bata taba zata ba ,


Zee bata San sanda ta sake Aslam ta zube a gurin tana kurma ihu ba , don ba qaramin shigarta marin yayi ba, ita zata iya ranstuwa tunda tayi wayau ba wani mahalukin da ya taba marinta a fuska, tsallaketa yayi ya haura sama , yana huci don ranshi in yayi dubu ya baci,




Saida ta gama ihun kukanta na kusan awa d'aya ta tashi ta haura sama ,ta dauki wayar ta , ta danna ma Dad call, ko la'akari da can yanzu dare ya tsala batayiba,




Dad na daga wayar ta qara fashewa da wani gigitaccen ihu kamar lokacin aka mare ta ,


Cikin rudewa da tashin hankali Dad ya miqe tsaye yana tambayar ta "daughter lfy?, kina inane? meya same ki? meke faruwa?"


Cikin sheshsheqan kuka tace "Dad mari na yayi"


Cikin yanayin masifa da bala'i Dad yace"whattttt! Mari,? wani dan kazakaza uban ne ya mare ki" tace "Aslam ne" yace "mijinki kike nufi " tace "eh" yace "yanzu kina inane" tace "d'aki na" yace "passport dinki na kusa " tace "eh Dad" yace "gobe da asuba kibar mishi gidan shi , ki biyo jirgin karfe bakwai na safe ki taho Malaysia, shi kuma ki barni da d'an Abu kazakazan uba , sai na ladaftar da shi ladaf tarwan da bazai qara marmarin Marin wani mahaluki a duniyar nan ba, sai yasan ya taba one and only daughter alhaji abdussalam naira," zee tace "Dad ni bazan iya qarqare kwana a gidan shi ba yanzu zan fita na tafi airport d'in na qarqare kwana zuwa Safiya,". Dad yace "da kyau daughter , haka nake son mutum yasan ciwon kanshi, kar kije airport ki kwana ki kama d'aki a hotel mafi kusa dai zuwa safen" tana share hawaye tace "to Dad "


Lallashinta Dad ya dingayi har tayi shiru kafin sukayi sallama, nan Dad ya labartama mom abinda ke faruwa , aiko ranta har yafi na Dad baci,


Had'a kayanta tayi cikin qaton trolley ta dauki passport d'inta ta fito nata jan trolley da'ker,


Aslam yana shiga d'akin shi zama yayi bakin bed ya rafka tagumi, haka kurum ya dinga jin. Ba dadi akan marin dayama zee bai kamata ya mareta ba, kwanan su nawa da aure da za'ace har an fara kai mari, wata zuciyar kuma tace , ita taja koma mai ka mata akan me zata dinga danganta maka Asman ka da karuwa, wata zuciyar kuma ta bashi shawara akan yaje ya lallasheta, ko ba komai kishin ka ne yasa ta furta wannan kalma akan Asmah, inda bata Sonka baza ta damu ba,


Da wannan shawaran ya miqe da nufin zuwa d'akin ta, ganin gilmawanta yayi da qaton akwati tana ja , bin bayan ta yayi yana kira"zee baby, zainab, zee, my luv"


Ko kallon shi ba tayi ba balle ta amsa, sauri ya qara ya cimmata a falo, hugging d'inta yayi ta baya, tsayawa tayi cak da tafiyar da takeyi ta saki hannun trolley , ganin haka yasa Aslam cikin rad'a da muryar lallashi da kwantar da hankali cewa, "ina mai baki haquri akan kuskuren dana aikata na marin wannan kyakkyawan fuskar taki, nasani rashin fahimtane ya kaini da aikata miki hakan , kishi nane yasa kika fad'i mummunan kalma akan Asmah, kuma ba'a kishin mutum sai ana sonsa, na sani zainab kina sona nima kuma ina matuqar qaunar ki , auren soyayya mukayi da juna, kar mu bari shaid'an yayi tasiri akan mu, kiyi hakuri zainab ki yafe min,"


Juyowa tayi ta bashi wani irin kyakkyawan runguma, ta fashe da kuka, ita karan kanta tasan idan tace zata iya rabuwa da Aslam , ta yaudari kanta , bata taba son wani mahaluki kamar yadda take son Aslam ba apart from iyayenta, ta haqura amma ta qullacin wannan yarinyar data yi dalilin da mijinta ya mare ta , ta tsaneta bata kaunarta bata fata ma Allah ya hada ta da ita a zahiri, idan kuwa suka hadu saita tafka mata rashin mutunci,


A hankali ya ringa shafa bayanta cikin sigar rarrashi, yana gaya mata kalaman soyayya masu ratsa zuciyar masoyi a kunneta ,


Luquss tayi a faffadan girjinshi,tana sauke ajiyar nunfashi, anan gurin aka bar trolley ya kwana , ranar ta bashi had'in kan da tunda sukayi aure bata taba, bashi irin shi ba,




Aslam ranar yasha bidirin shi kamar ba gobe, sai dai duk inda ya shafo a jikinta sai Asmah ta fado mai a rai, tunani ya dingayi da ace itace da yasan sai yafi haka jin sweet,




Iyayen zee ranar basu koma bacci ba saboda, tsabar bacin, rai , ita kuma gata can jikin mijinta suna shàn luv tama manta da abinda ya faru,


(Hmmmmm tsakanin miji da mata sai Allah)


Washe gari da asubahi , saiga kiran Dad , nan ya tambayeta, tana hotel dinne tace "a'a bata je ba, Aslam din ya bata haquri sun daidaita dama laifinta ne, aiko nan Dad ya rufeta da fad'a abinda bai ta'ba mata ba tun tasowanta,haquri ta shiga bashi, da'ker ya haqura kuma yace duk abinda Aslam ya mata karta kuskura ta qara sanar mai , taje ya yafe ma Aslam ita, ita dai ta yarda tunda baice dole dole ta dawo ba aida sauqi,




Kwana uku suka kwashe suna barzar luv , sai nan nan akeyi da juna, Aslam tun ranar bai qara zuwa family hause ba amma duk matsin da zaiyi Asmah nanan maqale cikin zuciyarshi, hotunan ta dake wayarshi bai daina kallo akai akai ba amma saiya faki idon zee gudun sake afkuwar wani matsalan,




tsawon kwana ukun nan duk wani aiki na gidan Aslam keyi tun daga shara wanke wanke wankin toilet girki, shi keyi zee kam ko taye don ta riga ta gaya mai ya nemi yan aiki, ita ba baiwa bace, kuma inya gama girki ba kunya har ta fishi ci wani bin,




Yau Monday Aslam zaiyi resuming aiki hutunshi ya qare, suna ta shi da safe yace ta shirya ya ajiyeta a gida ta gaida su mummy da yamma inya dawo ya biya ya dakko ta badan tasoba ta amince , don mom ta Riga ta mata hudubar dangin miji basa da mutunci tayi taka tsantsan dasu,






Suna isowa mai gadi na bude get motar bello driver ne ya sawo kai ya ya dauko su zahra zai kaisu school, Asmah ce a gaba kusa da bello gaisawa sukeyi yana dan tsokanan ta , tana murmushi kasancewarshi mai yawan barkwanci,




Aslam tuni ya hade rai don gani yayi kamar, bellon ma soyayya suke, bello na gaishe shi yayi kamar baiji ba , a ranshi kuwa fadi yake ya zama dole ya bugama bello warning akanta karya qara daukarta a gabon mota haka suna fira kamar wasu masoya,


Zee bata kula da su ba amma su sun ganta sarai a gaban mota, sun dauki harya batool tace," nifa gasky matar ya Aslam dinnan haushinta nakeji, kwata kwata bata kwanta min a rai ba, da ganinta zatayi wulaqanci, kuga yadda take wani huhhura hanci a gaban mota"


Zahra ta kar'be da cewa" saidai ta wulaqanta su wlh badai ni ba , ba sai ka nuna kasan da mutum zai samu daman wulaqantaka ba, "


Amira tace "ay shiyasa ranar da mummy tace yaushe zamuje muga d'akin amarya , nace mata sai mun shirya, haka kawai , muje mijinta ya dizgamu a gabanta ta rainamu,don kunsan halin ya Aslam shima wani bin ba mutunci ne dashi ba"


Asmah tace "kudai kar kuyi shedar zur ku bari ta muku kafin ku qaras, "


A haka suma qaraso school din su zahra na sussukan zee, Asmah na kare mata


(Allah sarki Asmah baiwar Allah ,zee nacen ta kullaceki ke kuma kina nan kina kare mata fad'a😕)




Aslam na parking part zee ta fito, tana wani kallon gidan a yatsine, part din mami ya fara kaita , mami ta tarbeta da fara'a tana lale lale da y'ata, daga tsayen da take a wani d'age ta gaida mami da ina kwana, taja bakinta ta tsuke sai bin falon takeyi da kallo, mami ta amsa da "lfy qlau zainab,ya gida ya baqunta , da fatan kuna lafiya ba wani matsala dai ko" ke mai karatu inkin tanka zee ta tanka, shiru tayi tana dai tsaye abinta kamar mashi,




Mami a ranta taji ba dadi , amma a fuskarta bata nuna ba , saima cema zee tayi ta zauna mana, zama tayi akan kujera ta daura qafa daya kan daya,


Aslam gaba daya kunyan abinda zee tama mami ya gama kamashi, harara ya dinga balla mata , yana mata alamar , ta amsa ma mami mana, tabe baki tayi ta dauke kai daga kallon shi,


Aslam gaisar da mami yayi a ladafce kamar yadda ya saba, mami ta amsa mai cike da kulawa, yace" mami gata nan in tayi ta shishiga sauran part's d'in ta gaishesu, ni zan wuce office sai na dawo' mami "tamai addu'a da fatan alkhairi " yasa kai ya wuce,




Ruwa da leman kwalba mami ta gabatar ma zee, ba sannu bare nagode ta dauka ta sha,


Dan zama mami tayi tana d'an mata hiri , nan ma shiru, sai charting dinta take, mami a ranta tace, lallai Allah ya had'a Aslam da yar iskan mata,


Ganin abin zee d'in harda rainin arziki yasa mami fita sabgarta ,karshema, ta tashi ta bar mata falon,


Aslam na office amma tunanin Asmah da bello da takema murmushi yaqi barin barin brain dinshi, can dai ya kasa haquri ,ya dauki waya ya kira bello , ya wanke
Shi tas ba laifin fari bana baqi , ya kuma tamabyi lokacin da zai koma ya daukosu, gaya mai bello yayi, nan yace kar yaje shi zaije ya dauko su da kanshi , shidai bello mamaki ya gama kashe shi gaba daya. a ranshi yace wata sabuwa inji yan caca, meke shirin faruwa ne haka, yanzu kamal ya kirashi yace kar yaje dauko su Asmah shi zaije, dama sun saba haka da kamal d'in, yanzu kuma ga Aslam shima, jan dan bakin shi yayi ya tsuke koma meye gaba zai nuna inda rai da lpy.




Uku daidai Aslam ya isa school d'in su Asmah , Asmah da zahra department d'insu daya dan haka, tare suka fito daga lecture da suka shiga 2 to 3 pm, nufo inda ya kamal ko Mallam bello suke tsayawa in sunzo daukarsu sukayi,


Tun daga nesa zahra ta fara hango kamar ya Aslam ne jingine jikin motar shi, a gurin da aka saba jiransu in anzo daukarsu. Suna qara matsowa kuwa ta tabbatar shi d'in ne, riqe hannun Asmah tayi gam cikin rada rada tace"Asmah ya Aslam' itama sai lokacin ta kula dashi, zahra tace "meya kawo shi nan kuma Allah yasa dai lfy"




Qarasawa sukayi , dagowa yayi idanshi akanta itama dai kallon shi takeyi , wani kyakkyawan murmushi ne ya subuce mai Wanda shi karan kanshi baisan

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads