Showing 108001 words to 111000 words out of 201974 words
Chapter 37 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
yasa karfin shi ya tashi jinta rike shi baisan ba karfi kirki gareta ba, sai gashi ta biyo shi.
Dago da kai tayi tana zare ido, idnunsu ya sarke dana juna,kallon juna sukayi na kusan 30sec, kafin da sauri ta yunkura ta dire kasa.
Daurewa yayi ya daddafa katakon gadon ya mike da'ker yana layi jiki ba kwari, yana mikewa kuwa jiri kwashe shi zai fadi tayi azaman taroshi tasa dukkanin ɗan karfinta ta rirrike shi a haka ta taimaka mai har suka shiga toilet, zaunar dashi tayi akan abin da ake zama a toilet d'in juyawa tayi zata fita karaf taji an riko hannunta, da sauri ta juyo ta kalle shi, marairaice fuska yayi kafin a hankali ya bude bakin shi yace"pls mrs Asmah ki taimake ni kimin wankan" wani irin zaro😳idanu Asmah tayi cike da tashin hankali.....
Tabdijam lallai Asmah kya zaro ido koni dake cikin Celine ina dauko rahoto saida na zaro ido😳balle ke
Oum ummeetarh
07041130088
..
Share
And
Comment
Fisabillilah🙏
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
DAMA TA BIYU💖 ƘIRƘIRARREN LABARI NE MALLAKINA NE BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYAMIN LABARI TA KOWACCE SIGA BADA IZININA BA❌❌❌
(In 👂👂👂 yaji gangar jiki ya tsira 👌 a kiyaye pls)
{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiy,Allah kajiqan iyayen}
💖Tallah!💖 Tallah!!💖
💖Tallah!!!💖
💖
Albishirinku manyan mata! ma'abota kwalliya da
_Rantsattsun lesussuka💃,
_Atamfofi manya da k'anana💃
_Galla gallan shaddodi manya da k'anana muna da su kowani iri💃
_Akwai kuma yadiddikan maza kamarsu koranza,plan yard dadai sauransu💃
_Munada mayafai, takalman maza da mata,sarqoqi, awarwaraye,da duk sauran nau'ikan kayan ado na maza da mata muna dasu 💃
Akanfaninmu na""R & U""Global Enterprise Dake Nan Garin Minna Niger State, saikunzu..........
Ga numbern mu kamar haka👇
08062160424
08066891424.....
Sayan day'a ko sari acikin farashi mai sauqi👌
Kubamu odern ku,danshine aikimmu akoda yaushe da yardar Allah........👌
Sai an gwada akansan na kwaraiiii💃💃💃.....
Page 101
Ganin ta tsaya kallonshi tana zare ido yasa ya marairaice fuska tare da cewa"pls mrs Asmah ki taimaka min" ganin zai karyar mata da zuciya yasa ta fizge hannunta da sauri ta fice daga toilet d'in, ko hauka takeyi ita ta ina zata iya mai wanka katoto dashi, yanzu shi ko kunya sai ya iya tubewa zirr a gabanta, lallai maza sai abarsu, yoo shi baisan riga ma da babu ajikin shi daure kawai tayi ba, tunda ta cire mai Riga har yanzu bata yarda ta sake kallon shi ba, kunya takeji balle kuma ace ya cire harda wondo.
Saida ya kwashe kusan 15 minutes a zaune yadda ta barshi kafin ya lallaba, ya mike da'ker ya fara wankan, bayan ya gama lallabawa yayi, yayi brush da alwala da daddafa bango ya samu ya fito daure da tawul, bata dakin dan haka ya samu ya lallaba ya zauna bakin bed,
Asmah kam tana dakin tunda ta barshi a toilet, jin motsin zai fito ne yasa tayi sauri ta fice a dakin dan tasan ba kunya ya ishe shi ba kar yazo ya fito mata haka zirr, dining ta nufa inda kayan tea suke, nan ta samu Kofi ta hada mishi tea mai kauri da zafi zafin shi, saida ta kwashe kusan 15 minutes tasan dai duk tsiya zuwa wannan lokacin ya gama shiri ya saka kaya,daukan dan karamin tiran data daura kofin tea d'in tayi ta nufi dakin da sallama a bakin ta ta tura kofan dakin, yana nan zaune a bakin bed d'in tunda ya fito toilet ya zauna bai motsa a wurin ba jira yake tazo ta taimakeshi ta dauko mai kaya ya saka yayi sallah,
Kallo daya tamai tayi saurin dauke kai daga kallonshi gabanta na faduwa, lallabawa tayi ta duka kusa da kafar shi ta ajiye mai kofin tea d'in, tace "ga tea nan na hada maka kasha, sai kasha magunguna" mikewa tayi tana niyar barin dakin, dan gaba daya jikinta rawa yake yi, ganin shi zaune daga shi sai tawul,har takai bakin kofa ta tsinci muryar shi yana cewa"pls mrs Asmah karki barni, kizo ki taimakeni ki saka min kaya nayi sallah" daskarewa tayi a gurin bayan ta zaro duka idanuwanta waje,kamar wacce aka dannawa pause, a zuciyarta tace innalillahi mutumin nan na neman ya kasheni da sauran kwanaki a duniya, ta kasa juyowa tayi abinda ya sakata ta kuma kasa yin gaba, har kusan 3minutes a haka ganin da yayi bata da alamar yin gaba ko baya yasa ya kara cewa "pls to ko ciromin kayan kizo kiyi daga sif" jin haka yasa ta daure ta juyo bata kalli inda yake ba ta wuce gaban wardrobe din tace "wani irin kaya zan ciro maka" yace "kowanne" jin haka yasa ta duba side din da jallabiyas suke ta ciro mai wani sabo mara nauyi, ta duba gurin kana nan kayan shi ta dauko mai singlet da boxer ta hado mai dasu.
Mikamai tayi ba tare da kalle shi ba, amsa yayi da gangan ya hada harda hannunta ya riko, a zuwan bai sani ba,da sauri ta fisge hannunta,kallon yayi yace "oh sorry" cewa tayi "kasa kayan kasha tea din bari na baka waje" yace "ki tsaya pls karki wuce" kamar zata ce wani sai kuma idanunshi dake kanta suka mata kaifi da yawa, bata ce komai ba ta samu guri a gefe ta zauna ta juya mai baya, daga zaunen da yake ya saka boxer, singlet d'in ya dauka zaisa amma yadda zai daga hannu ma wahala yake bashi, yayi yayi ha saka rigar ya kasa, ita kuwa Asmah tunda ta juya mai baya bata juyo ba balle tasan wainar da yake toyawa, ganin bata da niyar juyowa balle taga halin da yake ciki ta taimaka mai yasa ya saki wani kara mai sauti"ahhhccchh" a firgice ta juyo ta kalleshi gani tayi ya dafe kirjinshi yana yamutsa fuska kamar kirjin na mishi ciwo, bata san sanda ta isa gabanshi ta rirriko shi ba, sai faman sannu take jera mai ba kakautawa,ganin haka tuni ya kara narkewa ya sake mata nauyin shi duka a jiki, tuni tama manta da kunyar da takeji na ganin shi ba riga, cikin yanayin zafin ciwo yake cewa"rigana, rigana ki sakamun Rigana" jiki na rawa ta dauki singlet din ta saka mishi, duk rabin jikinshi na najikinta, da'ker take iya ture shi taja mai singlet din da kyau, a haka ta saka mishi har jallabiyan ma, tanayi tana "sannu na saka maka , sannu sannu" gyada kai yayi yana yamutsa fuska, ya daddafa gado ya mike yana layi, tashi tayi zata rikoshi yace "shimfida min pray mat, nayi sallah" da sauri ta dauka ta shimfida mai, nan ya kabbara sallan a tsaye ya fara amma karshe a zaune ya karkare, dan da gaske yana jin jiki, dan ma yana da dauriya sosai ne.
Tana gani ya idar ta dauki kofin shayin ta mika mai, kin amsa yayi ya girgiza mata kai alamar bazai sha ba, marairaicewa tayi tace"pls ka karba kasha ko kadan ne sai ka samu ka sha magani" da gangan yaki karba so yake ya sakata ta bashi a baki, Asmah ta kada ta raya amma yaki karba, saida yaga tana niyyar fashe mai da kuka ya bude baki da'ker yace"to kiyi hakaru karkiyi kuka zan karba, amma bazan iya sha da kaina ba, saidai in zaki taimakeni ki bani a baki" dake a matse take da yasha yasa ta amince zata bashi d'in.
Gyara zama tayi a gaban shi tana dibo tea d'in da cokali tana kaiwa bakin shi, yana sha yana yamutsa fuska kamar baiso, dan samun guri ma, idan ta debo wani bin ma bai karba saiya gauce fuska gefe, kamar wani dan karamin baby, haka zata ta bin shi da cokalin duk inda ya juya fuska, sai ya gama wala ta ya amsa, a haka ya shanye tea tass ba tare da ya Sani ba, sai gani yayi ta ajiye kofin, kallon cikin kofin yayi yaga wayam, saida yadan zaro ido yana mamakin yadda akayi ya shanye tulin shayin nan shida baida lafiya, ko lafiyar shi kalau ma baya wani shan tea da yawa.
Tana lura da yadda ya kalli kofin yadan zaro ido hakan yasa tace "ko a karo maka ne" da sauri ya girgiza kai alamar A'a, tashi tayi ta fita da cup din can kuma sai gata ta dawo da goran ruwa mara sanyi da wani cup, komawa tayi mazaunin ta nada ta bude ledar maganin ta ballo mai duka Wanda zaisha a lokacin ta mika mai ba musu ya karba ruwa ta tsiyaya mai a cup ta mika mai, karba yayi yasha maganin, yana yamutsa fuska.
Cup d'in ta dauka ta mayar kitchen ta dawo, kallonta yayi ya nuna mata breakfast dinta da ta ajiye tun dazu har ya sandare ya huce, sai lokacin ta tuna bata karya ba, dauka tayi takai kitchen ta ajiye dan bata jin zata iya cin wani abinci a halin da take ciki a yanzu.
Tana fita ya tashi da'ker ya lallaba ya koma kan bed ya kwanta, baifi 10minutes da kwanciya ba bacci ya kwashe shi, koda Asmah ta dawo dakin ta samu yayi bacci, fitowa tayi a wuce dakin ta ta dan kwanta itama bata dade da kwanciya ba bacci ya kwashe ta, ba ita ta farka ba sai karfe 2 da gudu ta duro daga gadon tana salati tunawa da Aslam da tayi watakila ya tashi tun tuni yana jin yunwa, ga kuma maganin shi, dakin shi ta nufa har zuwa wannan lokacin bai farka ba , ajiyar zuciya ta sauke ta fice daga dakin, kasancewar ba sallah zatayi ba yasa direct kitchen ta nufa, tunani ta shigayi na me zata girka masa mai sauki a matsayinsa na mara lafiya, haka ta tsaya ta saka wancen ta kwance wancen, karshe dai ta yanke shawaran dafa mai spaghetti jelop ta maishi mai ruwa ruwa ko zai iya ci, take ta daura sanwan cikin abinta baifi minti talatin ba ta gama dafa haddenden jellop din taliya mai ruwa ruwa da yaji kayan lambu, ga kuma kifi busasshe irin manyan nan da tayi amfani dashi, kwashe wa tayi a kula ta ajiye, ta gyara kitchen din tsab, komawa tayi dakin, ta dubo ko ya farka, samun shi tayi zaune bakin bed ya dafe kanshi, amsa mata sallama yayi a hankali,karasawa tayi gaban shi tace"sannu Mr Aslam ka tashi ya jikin" dagowa yayi ya kalleta tare da sakar mata murmushi, dadi taji ganin jikinshi da sauki, tunda gashi har ya tashi da alama ma yayi sallah, itama murmushin ta sakar masa tare da cewa , "tunda naga kamar har kayi sallah bari na zubo maka abinci kaci, kasha maganin ka na rana" bata jira amsar shi ba ta fice daga dakin, kitchen ta nufa ta dauko kular abincin da plate da spons da su ruwa duk ta hado komai akan tray ta dauko.
A kan dan table d'in dake dakin ta ajiye, sannan tayi serving dinshi taliyan da uban yawa ta mika mai, kin amsa yayi ganin haka yasa tace "Mr aslam pls ka amsa kaci, idan baka cin abinci baza ka warke da wuri ba, in kuma bakason wannan abincin ne sai ka fadi wani kalan da kake so na girka maka" da sauri ya girgiza mata kai, alamar A'a yanaso, don tunda ta bude kulan abincin daddan kamshin girkin ya buge shi miyon shi ya tsinke ranshi ya biya, kawai dai wayau yake so ya mata ta sake bashi a baki kamar dazu, dan dazu ba karamin dadin hakan yaji, tsabar farin ciki ya Asmah na bashi abinci da hannunta, koda bacci ya kwashe shi mafarkin abin yatayi.
Ganin yayi shiru yasa tace "bakace komai ba" kallon ta yayi yana yamutsa fuska alamar yana jin jiki da ciwon yace"pls ki sake min irin taimakon dazu ki bani a baki na, bazan iya ci da kaina ba," tausayi ya bata yadda taga yana yi da fuska ta San ba karamin jin jiki yakeyi ba, ba musu ta matsa gaban shi zata zauna shi kuma yana zaune bakin bed, da sauri ya taro ta ya zaunar da ita a kusa da shi, a gefen shi, bata damu ba ta dago plate din tana diba da fork tana bashi, kadan kadan, sai amsa yake yana kallon fuskarta yana murmushi, ji yake kamar tunda yake bai taba jin daddaɗan jellop din spaghetti irin wannan ba, zuciyar shi wasai, bai ankara ba sai emty plate, da matukar mamaki yake kallon plate d'in, a zuciyar shi yana aiyana yanzu duk tulin abincin nan ya cinye, lallai yayi babban aiki, magani ta ballo tabashi ta, ta tsiyaya mai ruwa ta mika mai, yanzu kam dan samun guri har ruwan shan maganin cewa yayi,ta bashi har zata ƙi zuciyarta ta kwabeta da cewa ki mishi Asmah ciwo yafi gaban wasa, kinsan inda kene kike cikin wannan halin abinda zai miki sai yafi wannan da kike mai, daga yanzu dai ki lallaba kimai duk abinda ya bukata har zuwa yaji sauki.
Bashi tayi yasha ya kalleta yace "nagode mrs Asmah," murmushi kawai tayi ba tare da ta amsa ba ta kwashe kwanukan abincin ta fita dasu, sai lokacin hankalin ta ya kwanta ganin Aslam yaci abinci yasha magani, zuba abincin itama tayi kadan a plate ta zauna taci a kitchen d'in, jin ulsa na so ya tashi mata.
A haka Aslam da Asmah suka wuni Asmah jinya takeyi tuburan tsakanin ta Allah, motsi kadan idan yayi zata isa gareshi a firgice tana tambayar shi menene me ke mishi ciwo a ko a kira Dr da dai suransu.
Yayinda Aslam zuwa lokacin ya ji garass sosai kawai sai dan kafin jiki ne, Wanda shi kuma dama sai a hankali, ammafa ko a fuska bai Nuna mata yaci sauki ba, abubuwa iri iri yake mata tsabar samun guri yanzu ko magana zai mata har wani shagwaba shagwaba yake hada wa da shi common toilet zai shiga sai ta tallabo shi, abincin dinner kuwa data kawo bata tsaya wahalar mika mishi ba direct ta zuba ta dinga bashi, ko musa babu ya amsa.
Jinshi yakeyi kamar wani sabon dan yaye , gani yake duk tsawon rayuwar shi bai taba riskar wuni mai dadin wanna ba.
Asmah na tare dashi har wurin goma da rabin dare, duk ta gaji libis burinta ya kwanta ta samu itama ta wuce dakin ta ta kwanta ta huta,ta kaishi toilet yayi wanka daker, ya fito ta dauko mai kayan bacci, ya sa wandon ta saka mai riga, ya hau gado ya kwanta, duk zuciyar shi ba dadi yasan tabbas sun kusa rabuwa kenan dan yana kwanciya ya tabbata dakin ta zata koma itama ta kwanta, tunani ya shigayi na abinda zaiyi ya hanata tafiya dakinta, take ya saki wani murmushi bayan ya samu salutation.
Tsaki ya fara saki ƙanana, yana dafe kai, dagowa tayi da sauri ta kalleshi, tace"lafiya Mr Aslam meke faruwa kuma ko jikin ne" cikin yanayin yamutsa fuska kamar da gaske ya nuna mata kanshi alamar kai ne ya tasar mai, ganin haka tace "ayya sorry" tana dawowa dakin ta zauna, tana mai sannu yana gyada kai.
Zamanta da kusan 20minutes ya fara lumshe idanu, dan bacci yakeji, itama daga zaunen da take sai gyangyadi takeyi, can ya bude ido daya ya kalleta, tausayi ta bashi ganin yadda take bacci a zaune, gadai shi yayi dabara ya hanata tafiya sai dai kuma kamar ya shiga hakkinta, yake gani, wani dabaran ne ya sake zuwar mai, nan take ya fara rawan sanyi yana karkarwa har hakorin shi na haduwa yana bada sauti, da sauri ta ware idanunta jin sautin karan haduwan hakoranshi ga kuma nishi da yakeyi a wahalce.
Baiwar Allah bata San sanda ta dira gabanshi ba, cikin tashi hankali ta shi furta "innalillahi wainnailaihi rajiun, na shiga uku, Mr aslam dan Allah karka mutu, na shiga uku ni Asma'u" take ta haura kan bed din ta tallabo shi jikinta tuni har hawaye sun fara sintiri a fuskarta, tsabar rudewa ko kula da jikin shi ba zafi batayi ba, Aslam kam da'ker ya bude baki a wahalce murya na rawa rawa yace "pls mrs Asmah ki rungume ni sanyi nakeji, ki rungume ne na samu dumin jikin ki sanyi zai kashe" yana fada karkarwar da yakeyi na karya na daduwa.
Bata San sanda ta fada jikinshi ta kamkameshi ba, tana hawayen tausayin sa, jinta a jikinshi gaba dayanta haka, saida wutar kanshi ya dauke na wucin gadi, ga tudun boobs dinta yana ji a kirjinshi, lumshe ido yayi yana sauke ajiyar zuciya, hannu yakai ta bayanta ya rungumota shima, a hankali kuma jikin nashi ya daina karkarwan da yakeyi hakoran shi suka tsaya da haduwan da sukeyi.
Jin haka yasa Asmah tayi tuananin rungume shin da tayi ne yasa ya daina jin sanyin da gaske, shiru tayi lafe a jikin shi tana sauran bugun zuciyar shi, a haka taji yana suke numfashi alamar bacci ya daukeshi.
Ajiyar zuciya ta sauke itama ta maida idanunta ta lumshe ta Lula duniyar tunani da tausayin halin da aslam yake ciki a haka bacci barawo yayi awan gaba da ita.
Aslam jin tayi bacci yasa ya bude idanunshi dake lumshe,ya sauke ajiyar zuciya tare da sakin wani miskilin murmushi, a baiyane yace"Allah nagode maka da kakawo min karshen wannan game ɗin cikin sauki, husnah daga yau kin shiga uku dani, na samu saukakekken hanyar da zan miki kamun kazar kuku, ni danasan zakiji tausayi haka idan banida lafiya Ai da tun farko na kirkiri rashin lafiyar karya"..............
kuyi hakuri da kura kurai banyi editing ba🙏
Oum ummeetarh
07041130088.
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
DAMA TA BIYU💖 ƘIRƘIRARREN LABARI NE MALLAKINA NE BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYAMIN LABARI TA KOWACCE SIGA BADA IZININA BA❌❌❌
(In 👂👂👂 yaji gangar jiki ya tsira 👌 a kiyaye pls)
{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiy,Allah kajiqan iyayen