Showing 159001 words to 162000 words out of 201974 words
Chapter 54 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
hankali, duk da shima karfin hali yakeyi, idan da zai samu dama shima kukan zaiyi sai dai kasancewar shi namiji yasa ya dake yana lallashin ta, ita ko sai ruwan hawaye take zubar wa tana shehseka, sun zo dai dai kofar gida har mai gadi ya wangale get, wayar shi dake hannunta yayi ringing, ko dubawa batayi ta mika mishi, ganin Amir ne me kiran yasa ya daga, daga can bangaren Amir cikin yanayin tsantsar farin ciki yace"broh matata ta haihu, yanzun nan yanzu haka muna standard hospital ko sallaman mu ba'ayi ba." Aslam a ruɗe yace "iyeee kace ta haihu." Ai jin maganar haihuwa yasa ta tsaya da kukan shagwaban da take yi, tare da zazzaro manyan idanunta ta waje gabanta na faduwa tace"honey waye ya haihu" cikin washe baki yace"Amira ce" wani irin zabura tayi ta rungume shi tana faɗin "alhmdllh alhmdllh Allah mun gode maka." Tana cikin murnar kuma yaga tayi tsit, can kuma sai kuka.........
Kwana biyu kun juna shiru wlh nadan samu uziri ne kuyi tamin hakuri dai.
Oum Ummeetarh
07041130088💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}
Page 121
Ko ba'a faɗa ba yasan kukan me take yi, ta ke yaji gaba ɗaya jikin shi ya ƙara yin sanyi, haka dai ya daure ya shiga rarrashin ta, yana kwantar mata da hankali, ɗago fuskar ta da yayi gaje gaje da hawaye tayi daga jikin shi ta zuba mi shi idanun ta da sukayi jajur tana kallon shi, shima nashi idanun ya zuba a cikin nata, tare da kamo hannayen ta ya riƙe cikin nashi yana murzawa a hankali, a hankali ta buɗe bakin ta tace "ya Aslam sai yaushe ne nima zan haihu, sai yaushe nima zan samu ciki, tsoro nake yi kar ace na kasa cika maka burin ka na samun haihuwa, na San kana son haihuwa sosai kana son kaga gudan jinin ka a duniya, nima kuma ina so domin duk abin da Aslam yake so shi Asmah take so. Inajin tsoran na kasa cika maka wannan burin naka, har hakan ya janyo ka juya min baya wata rana, Wanda duk ranar da hakan ta kasan ce sai dai a kwashi gawar Asmah, domin Asmah baza ta iya rayuwa ba tare da Aslam ba, dan Allah ya Aslam kamin alkawari komai rintsi baza ka juya min baya ba." "Shiii!" Ya faɗa tare da daura dan yatsar shi akan lips ɗinta, girgiza mata kai yayi tare da cewa "kada na sake jin kwatan kwacin irin wadannan maganganun suna fitowa daga bakin ki, Aslam na Asmah ne, ruwa da iska babu abin da zai sa ya juya mata baya, iya wuya muna tare, kuma in-sha Allah zaki samu ciki ki haifa min kyawawan ƴaƴa masu kama dake, zaki shayar dasu kamar kowacce uwa, zaki basu tarbiyya irin Wanda mummy ta baki, kinji my hussy." Gyada kai tayi hawaye naci gaba da kwaran ya daga idanunta ta, sakin hannayen ta yayi, ya jayo fuskarta daf da tashi a hankali ya shiga dauke hawayen dake zubowa a idanun ta da harshen shi, yana gamawa kuma ya haɗe bakin su ya shiga kissing dinta a hankali, sai da yayi ma'ishi ya dago yana kallonta itama shi take kallo yace"oya yi murmushi." Wani murmushi tayi Wanda da gani yasan iya fuska kawai ya tsaya.girgiza kai yayi yace "wannan bai yi ba." Sake wani tayi Wanda babu banbancin dana farko, sake girgiza kai yayi yace "wannan ma bai min ba, bari kiga irin Wanda nake so." Kafin ta Ankara taji ya fara mata cakulkuli, ba shiri ta shiga kwalkwala dariya tare da kokarin zillewa tana buge hannun shi.
Ganin haka yasa ya kyale ta, shima yana mata dariya, hararan wasa ta watsa mai cikin muryar shagwaɓa tace" Kai ko ya Aslam yanzu dana mutu fa, baka San ance cakulkuli kanin mutuwa bane." Cikin kwaikwayon muryar ta yace"to ba kene kika ki yi min murmushi ba tun dazu sai kuka kikeyi kina ta min asarar hawayen ki masu daraja."dungure mai kai tayi cikin sigar wasa tare da murguɗa baki.
Dariya yayi tare da cewa "bari dai mu karasa ciki, na baki wani labari mai daɗi." Ya karashe maganar yana kokarin tada motar, riƙe hannu shi tayi tace"dan Allah ya Aslam ka kaini naga babyn mu hankali na ya kwanta." Yace"eh to da nima naso hakan, amma yanzu na canja shawara, kimu shiga daga ciki ki ɗan dumama ni sannan mu tafi." Ya kara she maganar yana ɗage mata gira tare da sakar mata wani shu'umin murmushin da ita kaɗai tasan fassarar sa, ba yadda ta iya, tunda ya bukaci hakan tasan idan ba yi yayi ba kuwa baza ta samu sa'ida ba, don haka bata ƙara cewa komai ba ya tada motor suka ƙarasa ciki.
Kasancewar tana son zuwa ganin baby duk rabin hankalin ta nacan yasa ta ringa yin komai sauri sauri, hakan kuwa yamai daidai sakar mata ragamar komai yayi ita ta buga wasan, Bayan sunyi wanka abinci ta girka musu mai sauki sukaci, basu suka bar gidan ba kuwa sai Bayan la'asar.
Koda suka isa asibitin an sallame su, Aslam yace "gida zamu je kenan." Ya faɗa yana karya kan motar ya dauki hanyar zuwa albishir inda gidan Amir yake.
Suna tafe suna hirar su ta masoya Wanda duk rabin hirar akan batun babyn su ne suma, inda musu ya barke Asmah tace namiji take so shi kuma yace mace yake so.
Wayar ta ne ya dauki ringing shuru sukayi duka ta Ciro wayar daga cikin hand bag dinta, ganin me kiran ne ya saka ta sakin murmushi, kallon ta yayi yace"wake kira." Tace "matar Dr." Ya mutsa fuska yayi alamar bai gane ba, kafin ya tambayeta wacece haka har tayi picking call din ta saka a amsa kuwwa sai ji yayi muryar batool ya karaɗe mai kunne tana cewa"yar uwa ina kika shige ne tun a asibiti nake ta zuba idon ganin ta ina zaki bullo, gashi har anyi sallama mun wuce gida shiru shine nace bari dai na kira naji ko lafiya." Murmushi tayi tace"ke dai bari yar uwa tun ɗazu naso zuwa, wani dan uziri ya rike ni, amma gani a kan hanya yanzun nan insha Allah." Dariya batool ta kwashe dashi cikin son ta tsokane ta tace "uzirin oga babba ba ai nasan shi ya rike mana ke, yana nan yana danne mana yar uwa amma in yazo nan mu yai ta wani mazurai, yana ciccin magani, fuskar nan a haɗe kamar wani na Allah, zaki rantse bazai iya kallo mace ba balle yayi eh yane da ita, to munsan komai." Wani iri wawan burki ya taka jin abinda batool ke fadi Asmah kam wani dariya me haɗe da tari ya sarke ta lokaci guda, batool tace "wlh kuwa sister ba batun dariya bane ai da ganin idanun wannan mutumin zaiyi jaraba ba kaɗan ba, dama kinsan ance irin shiru shirun nan sunfi kowa naci a wannan fanni, a fuska kamar in an saka musu yatsa a baki baza su iya cizawa ba." Dariyar da yaci karfin ta yasa ta katse kiran cikin sauri tana kallon Aslam daya kasa rufe baki tsabar mamaki da al'ajabi sai kuwa zazzaro ido yake yi yana muzurai take maganar batool ya fado mata a rai, ta kara kwashe wa da dariya har da riƙe ciki.
Shima dariyar ne ya kama shi ya shiga taya ta, Girgiza kai yayi yace"lallai ma yaran nan haka na zama a wajen su, haka suka raina ni dama, lallai ma yaran nan sunga gadon barcina ." Ya faɗa cikin tsantsar mamaki dan shi abin ya ba'in daure mashi kai inda wani ya gaya mai wlh baza yarda ba, duk da yasan batool zata aika, indai ita ce daya sani.
Cikin dariya tace "honey kasan batool shakiya ce, babu Wanda ta ragawa, idan abin ta ya motsa har su daddy yi musu take." Yace "aiko dai zata ci kaniyar ta yau a hannu na, sai ta maimaita abinda ta faɗa a gaba na badai zama da wancen ƙara min ɗan iskan ya kara koya mata fitsara ba." Cikin zaro ido tace "kai honey kar kasa naƙudan dole ya taso mata, kasan dai ko giya ta sha baza ta iya maimaita wannan maganar a gaban ka." Yace "ta ko sha mari, ai har yanzu ina nan a Muhammad Aslam ɗina nada da ta sani." Dariya tayi tace "haba dai honey matar wani ce fa." Yace "matar wani ko? To ko mijin nata ne yamin dukan tsiya zan mai balle ita dana ma wanka na goya a baya na." Dariya ta kwashe dashi tare da cewa "Dr din zaka daka." yace "kina mamaki ne ." tace "eh mana." Yace "ki tambaya kiji koda muna yara dukan tsiya nake mai yayi ta kuka hawaye da majina shaɓe shaɓe gashi fa ya fini girma a lokacin"Asmah don dariya harda hawaye ciki dariya tace "dan Allah ya Aslam ka tada motar mu wuce kar kasa cikina ya fashe dan dariya." Dariya yayi tare da ta da motar, har sun far tafiya kiran Amir ya shigo nashi wayar ɗagawa yayi yace "angon ƙarbi angon ƙarni." Amir murya cike da damuwa yace "dan uwa sun kassara ni." Aslam cikin ɗan ta shin hankali yace "su waye kuma." Amir yace "su mummy." Aslam yace "me suka yi." Amir kamar zai fashe da kuka yace"wai bana nan na je gida kwaso wasu kaya, likita ta basu sallama, wai kafin na ƙaraso sun wuce da ita can family hause wai wani acen zata yi wanka sai nan da kwana ar'ba'in zata dawo." Dariyar ƙeta Aslam ya fashe dashi tare da cewa "subhanallahi sannu." Sannan ya ci gaba da kwasar dariya irin mai kara cusa haushin nan, Amir daya gama ƙulewa cikin fushi yace "shege dan iska kawai." Tare da katse kiran ma gaba ɗaya.
Asmah tace "menene?" Yace "su mummy ke Neman su saka mishi hypertension wai matar shi suka dauke zuwa gida wani wai zata yi wankan jego a gida." Ya karashe maganar yana shan U turn da motar suka dauki hanyar family hause, tace "to shine kake mishi dariya, yau dai ga mutum gobe gare ka." Yace "ina! Ba wannan maganar , aini babu Wanda ya isa ya min irin wannan talalan mai kamar tsaki, wlh bazan yarda ba kinji na rantse idan kuma suka matsa to sai dai su bamu daki ɗaya a gidan muyi zaman wankan tare." Tace "haka kace ko to a dai yi mu gani idan tusa zata hura wuta." Yace "za kuwa ki gani Allah dai ya kaimu lokacin." Tace "Amin kuwa" ganin yadda yake tukin a slow yasa tace "dan honey kayi sauri na matsu naje naga babyn mu."
Minti 20 ya dauke su, suka iso family hause, direct kuwa part din mummy suka yi,inda suke kyautata zaton samun su. Falon mummy cike da yan uwa Mami, ya Rabi'ah, batool, Khadijah, hajiya mama, kamal, da kuma Amir. A na zazzaune fuskar kowa cike da farin ciki banda Amir dake ta ciccin magani.
Asmah ce a gaba tana sallama batool ta taso da sauri tana mata oyoyo kamar yadda suka saba yi ma juna da tirtsetsen cikin ta da ko nauyin shi bata ji, cike da kulawa ta tare ta tare da cewa"ayya yar uwa da kin bari ni na karaso na miki ai." Aslam dake Bayan su ganin sun tare mai hanya yasa yayi gyaran murya, sauri batool ta sake ta, tare da kallon gefen da ta jiyo muryar ya Aslam, suna haɗa ido ya galla mata hararan da saida babyn cikin ta yayi zillo. da sauri har tana dan risina wa tace "sannu da zuwa ya Aslam, ina wuni." Bai amsa ta ba sai ma qare hade rai da yayi kamar bai taba dariya ba, kallon shi Asmah tayi ta juya ta kalli batool da tayi tsuru ta dukar da kai kasa cikin ladabi. Kawai sai ta kwashe da dariya, ita ma hararan ya watsa mata, tare da bi ta gefen su ya shige falon, Jan hannun batool tayi suka bi Bayan shi, ita dai batool a tsora ce take, bata son taga ya Aslam cikin irin wannan fuskar, domin duk ranar daya tashi musu da irin wannan fuskar uban su yake ci, kowacce sai ta samu rabon ta a cikin su ranar ko mari ko rankwa shi.
Aslam dake gaba shiya fara karasawa gaban hajiya mama dake rugume da babyn ya asma, cike da farin ciki da wani irin so da shauki yake kallon babyn bakin shi yaki rufuwa take fuskar shi ta washe ya shiga sakin wani irin kayataccen murmushi, itama tana shigowa falon abinda idanunta suka hango mata kenan babyn dake hannun Aslam, da sauri ta saki hannun batool ta ƙarasa bagan shi tana kallon fuskar kyakkyawan yaron itama fuskar ta dauke madaukakin farin ciki.
Gaba daya mutanen falon kallon su sukeyi cike da sha'awa da tausayawa, kowa yasan yadda suke matuakar kaunar haihuwa gashi har yau allah bai basu ba, mika hannun tayi zata karbi babyn a hannushi ƙin bata yayi tare da ƙara rike babyn da kyau, sake kai hannu tayi zata karba ya kara hanata, sai kawai ta fashe da kukan shagwaba tana bubbuga kafa.
Muryar hajiya mama suka tsinta tana cewa "yayi kyau tantabaru sarakan soyayya, to muna nan dai." Cak ta tsaya da kukan da take yi kamar wacce aka danna mata stop, dariya su batool dasu ya Rabi'ah suka saka musu, harga Allah hankalinta bai kai kan mutanen dake falon ba gaba daya idanunta ya makan ce babyn su kawai ta ke gani, a kunyace ta juya ta karasa gurin hajiya mama dake zaune ta rungume ta, ture ta hajiya mama ta shiga yi da wasa tana cewa "ni daga ni dallah can karki karkare ni." Batool tace "lallai ji matar nan ma dan ma kin gode ta rungume ki, kema sister ga Mami da zaki rungume kinje kin rungume wannan taohuwar." Hada idanun da sukayi da Aslam ya dalla mata harara yasa tayi shiru.
Gaishe da sauran mutanen falon tayi su Mami ta musu barka sannan ta nemi guri ta zauna kusa da Khadijah dake ta sakar mata murmushi, Khadijah tace"naji muryar ki yar uwa amma wlh kafata tayi tsami na kasa tasowa na tare ki." Cike da tausawa take binta da kallo tayi wani ƙiba, kafafun ta duk sun kumbura. Tace "ayya sister sannu kuma Allah ya sauke ku lafiya." Gaba daya aka amsa da amin.
Hajiya mama ta kalli Aslam tace "to ai sai ka bata ɗan ita ma ta dauka ko." Kallo ta yayi tayi narai narai da ido, tayi fuskar tausayi suna hada ido ta sakar mai kallon pls mana, badan ya gaji ba ya mika mata, innalillahi Aslam ji tayi kamar ta maida babyn cikin ta gaba daya ta tattara dukkan hankalin ta akanshi tana kallo tana sakin murmushi.
Fira aka shiga yi amma ita kwata kwata hankalinta baya Kansu bata San me ake cewa ba, batool kuwa duk ta takure don duk haɗa idanun da zasuyi da ya Aslam sai ya banka mata harara gajiya tayi ta mike salin alin ta nufi dakin su Nada dake upstairs kusa dana mummy inda nan ne dakin da Amira zata zauna, tana shiga suna fitowa daga toilet da alama wanka akama Amira, batool ta kalle ta tayi wani jajur abinka da farar fata, mummy tace yawwa batool dauko babyn ki kawo shima a masa wanka, komawa tayi da nufin amsar babyn a hannun Asmah takai ma mummy ƙememe Asmah taki bata, ta kara kamkamewa sai dariya su Mami ke mata, kar she dai cewa tayi ita da kanta zata kaima mummy yaron, haka suka rankaya ita da yar Aiken suka koma sama, samun Amira sukayi ta saka kaya riga da zani harda sock da dan karamin hijjab mummy ta zuba mata ruwan zafi sai sha takeyi tana yarfe zufa, ga ɗakin dunɗum ko fanka ba'a kunna ba balle Ac, kallon juna sukayi suka sake kallon Amira
dake kurban ruwan zafi, takr batool taji cikin ya bada ƙulululu.....
,
Oum Ummeetarh
07041130088.
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqanñjjn iyayen mu}
Page 122
Tana jin labarin jego jego kuma tana farƙgaban wankan nan da aka ce mata ana yi da tafasashen ruwa, yanzu kuma ganin Amira na kurban ruwan zafi sai abin ya ƙara girgiza ta wato bancin wanka da tafasashen ruwa har tafashen ruwan mutum ke sha, bata gama wannan tunanin ba taga mummy ta miƙo ma Amira kunun kanwa cike da Kofi sai tiriri yake, "oya maza maza ki kurɓe shi da zafi zafin shi ki gaggasa cikin ki jego ba abin wasa bane." Kwabe fuska Amira tayi zata yi kuka, mummy tace "oh lallai a haka da mijin ki ke neman mu bashi ke ya tafi dake gida, gashi a agaban muma kenan, to bari na gaya miki cikin ci nan naki a halin yanzu danye ne sharaf, kamar gwambo. shan abubuwa masu zafi su zasu saka ya warke, idan kuma kika ƙi sha ki ruɓe, kita wari sai dai kiga Amir ya auro galliyar amarya ya aje ki a kwandon shara." Ba Amira ba hatta batool da Asmah sai da suka zaro ido mummy tace "kwarai kuwa ba kun wani ƙolalo min idanu ba, wannan wankan da shan ruwan zafin nan da shiga ruwan zafi da tsarki,da cin abinci sosai mai jego taci abinci sosai taci tuwo tasha kunun kanwa tasha shayi ta koshi ta gasa ciki shine jego, in kika ƙi yin waɗannan abubuwan wlh kanki zaki cuta, bari na baku labari, lokacin muna yan mata a unguwar mu, wani gida akwai wata mata data haihu, taki yarda a mata wanka taki yarda tayi tsarki da kyau, taki shan ruwan zafi,wacce aka kawo mata dan ta ringa mata wanka tayi tayi da ita taki, kawai sai ta kyale ta,