Header Ads
Showing 60001 words to 63000 words out of 201974 words

Chapter 21 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1709

Ads at the middle of Article

shi zai tsinke, saida alhaji baba yace ya isa haka...............




















💖more comment more typing💖








Oum ummeetarh
07041130088










Share
And
Comment
Fisabilillah🙏


💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~




FREE BOOK








{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}












Page 71 & 27










Washe gari kuwa iyayen Dr suka zo ba bata lokaci akayi abinda za'ayi, a take suka bada kudin komai da ya kamata su bayar na àl'ada, iya mazan gidan ne kawai suka san da maganar don hatta mummy da mami basu Sani, balle kuma su Asmah.




Ummi mahaifiyar Amir da ke zaune a abuja yau ta sauka kasancewar da ita za'aje dubai domin siyayyan kayan amare, ita da mummy zasuje, don mummy cewa tayi ita da kanta zata je ta zabar a yan matàn ta kayan daki domin tafi kowa sanin abinda kowaccen su take so,da kuma kalan da take so.




Yan matan Mummy ba karamin murna sukayi da zuwan Umminsu ba, kamkameta sukayi suna murna da tsalle kamar wasu yan three - three years, Amira kan baya taja tana murmushi da sunsusne kai, ita ala dole tana jin kunyan ummi, matsayin ta na mahaifiyar Amir.


Dagowa ummi tayi ta kalli Amira cikin zaro ido da mamaki tace , "me zan gani haka yau ni Aminatu, Amira yau ni kuma kike jin kunya, oya oya zokima umminku oyoyoo" ta fada tana jawo amira ta rungume ta , "wani Amir d'in wofi zai shiga tsakanina da daughter na, karna sake ganin haka ki sa a ranki ke na haifa ba Amir kinji" gyada kai Amira tayi tana murmushi.




Haka suka wuni tare tana ta jansu da hira , tsaraban kayan kyaran data fara zuwa musu dashi ta babbasu wadan da zasu fara amfani dashi tun yanzu,irin su sabulu wanka da turaren wanka dana jiki , Dana wanke kai da dai sauran su, don tace maganar gyaran amare na hannunta ita zata musu komai na gyara , aiko karkuso kuga murna, wurin amaren.




Kwanan ta biyu da zuwa jirgin su ya daga zuwa Dubai ita da mummy,




Alaka zakanin M,M da Asmah sai kara karfi takeyi, kullum cikin charting suke, koda wasa Aslam bai taba tauko mata zancen abinda ya shafi aure ko saurayi ba , don yana tsoran jin abinda zai iya saka zuciyar shi bugawa.




Yau dai suna ciki charting Asmah tace, "friend wai ko na tambayeki ki mana " yace " ina jinki Allah yasa na sani" tace"kina aure ne?" yace "A'a kawa me kika gani" tace "ba komai nadai tambaya ne, niko kinga biki na saura sati uku yau insha Allah".




Wannan magana ba karamin sharking ya saka zuciyar Aslam ba, shi yama manta da batun cewa zatayi aure tunda ya samu yana charting da ita 24 hour yasa yake jinshi cikin nishadin da yasa ya manta abin da ke gaban,




sauka yayi daga online ɗin don ji yayi gaba daya zazzaɓi ya rufe, hankalin shi ya tashi nan take duniyar ta shiga juya mai, ba shiri ya nemi guri ya kwanta.


Asmah na jira kawar tata ta bata amsa taji shiru karshe ma taga bata online, bata kawo komai a ranta ba saima hoton zannuwan ankon yinin bikin data tura mata, tare da short voice na cewa idan aka buga invitation card zata turo mata , sai taga programs d'in bikin gaba daya.




Wasa wasa Aslam ciwo sai karfi yake yi ,ya lallaba ya tashi yasha magani amma kamar bai shaba, tun yana iya daurewa har abin yaso yafi karfin shi.






Waya ya dauka da'ker ya lalubo number Dr bash ya danna mishi kira, lokacin da kiran ya shigo wayar bashi dawowan shi kenan faga aaibiti , so yakeyi yayi wanka ya huta zuwa yamma kuma ya lwka batool don ya kwana biyu rabon shi da ita tun ranar da alhaji ya kirashinnan, ji yakeyi kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi a gabanta.




Bashir yana daga wayar, Aslam yace"bash don Allah kazo gida ka same yanzu yanzu " yana yin maganar tari ya sarke shi ya shiga yi ba kaukautawa.




Daga yanda bashir yaji muryan Aslam yasan ba lafiya, tambaya ya shiga yi "Aslam, Aslam meke faruwa " ina Aslam bai amsa shi ba don tari yaci karfin shi, cikin gaggawa bashir ya mike ya kwashi wasu daga cikin kayan aiki da yake dasu a gida da allurai da magunguna ya shiga motar shi ya nufi gidan Aslam d'in, yana shiga direct cikin main falon ya dosa , a kwance a kasa ya hango Aslam , da alama ya fado ne daga kan kujeran da yake kwance.


Da sauri ya karasa ya dago sa , ganin halin da yake ciki take ya gano inda matsalar take, kasancewar shine likitan daya duba shi last cikin tashin hankali ya shiga furta"Aslam why why, meyasa make neman ka kashe kanka saboda mace for god sake".




Kwantar da shi yayi ya koma mota ya tsintsinto duk abinda yasan zai yi amfani dashi don taimakawa Aslam din, allura ya fara yi mishi, ya daura mishi ruwa , nan take ya shiga sauke ajiyar zuciya barci mai nauyi yayi awon gaba da shi, guri bashir ya nema ya zaune a kujeran dake facing d'in na Aslam d'in ya zuba tagumi da hannu bibbiyu yana kallon shi.




Saida yayi baccin awa hudu lafiyayyau sannan ya farka, to jikin dai da dan sauki, har lokacin bashir na tare dashi bai motsa ko nan da can ba, tasowa yayi ya taimaka mai ya zauna.


Cikin lallama bashir ya shiga yi mai fada akan abinda yake yi nason hallaka kanshi, yace "kayi hakuri Aslam, komai idan kaga mutum bai samu ba a rayuwa ba rabon shi bane, akan me zaka saka damuwa har haka a ranka, nidai shawaran da zan baka shine ka karfafa zuciyarka, karka bari kaima kanka lahani a banza, addu'a ya kamata ka dage dashi, yanzu ciwon ka dabe dade da lafawa ba ke neman tashi har fiye da yadda yayi maka kwanaki, zuciyar ka na daf da bugawa, idan kai baka son rayuwanka mu muna sonka,".




Dagowa Aslam yayi da'ker ya kalli bashir a hankali ya bude baki yace "bashir bazaka gane halin da nake ciki bane, ba Wanda zai gane irin radadin da nake ji a zuciyata sai wanda ya taba shiga makamancin halin dana ke ciki a yanzu, kayi hakuri bashir amma bazan iya cireta a zuciyata na, domin bani na saka ta ciki ba Allah ne , ya sakata, shi zaka taya ni roka ya cire sonta tunda ba alkhairi bane a gareni, ka bani iya taimakon da zaka iya bani kawai kaje abinka "




Girgiza kai Dr bash yayi, magunguna ya bashi da kuma alluran da zai dinga zuwa duk bayan kwana biyu yana mishi , harna sati biyu, allura ne mai kyau kuma zai taimaka ka mishi sosai akan ciwon shi, nuna mishi yadda zaisha magani yayi, sannan yayi mai sallama ya fice jiki a sanyaye.






Kwanan su mummy takwas a Dubai suka dawo duk wani siyaya da zasuyi sunyi shi cikin aminci har kayan ma sun rigasu sauka a 9ja.


Washe garin dawowar su, ana saura sati biyu biki , dangin Barr Adam suka kawo lefe, dan kari! kar kuso kuga kayan set d'in akwatina mai guda shida shida da kit ne aka kawo har set uku, kowannen su makare da kaya na ganin na fada, abin ba,a cewa komai,


Wani washe garin kuma aka kawo na Asmah dana Amira, woohoho wani kaya sai amale, set hudu hudu ne na akwatina masu guda hudu hudu da kit, mami ne ta hado kayan tana daga zaune a gida tayi siyayyarta, ta online wurin wata kawarta da take saro manyan kaya daga kasashen duniya, kusan yawancin komai na akwatinan iri daya ne saidai banbancin size da kuma colour.




Har zuwa wannan lokacin batool bata San da batun ta da Dr bash ba, saidai su mummy da mami duk sun Sani, kuma sunyi farin ciki, sosai.


Washe gari kuma aka kawo kayan batool daga gidan su Dr bash, shima dai masha Allah abin ba'a cewa komai ita kuma set biyu aka kawo mata mai guda goma goma da kit,




Lokacin da aka kawo kayan su batool basa nan sunje kai dinki, koda suka dawo tararwa sukayi an bude akwatina a falon mummy ana kallo, cikin da mamaki natool ke tambayar ummi, "kayan waye wannan kuma , inace an gama kawo lefen , ko karowa sukayi ne".




Mami ta kalleta da murmushi a fuskarta tace"nakine batool yanzu aka kawo daga gidan su Dr,kaiii kaya sunyi kyau Masha Allah, gaskiya basuyi kauron komai ba komai yaji masha Allah".




Jin abinda mami take cewa yasa batool sakin murmushi , don ta dauka mami zolayar ta take yi don mami kan zolaye su wani bin, bata dauki maganar serious ba , haurawa ma sama tayi abinta don fitsari takeji, suma su Asmah biyo ta sukayi , don in ana kallon kaya basa zuwa kallo don kar ace sunyi , rashin kunya , har zuwa yanzu cikinsu ba wacce taga kayanta,




Asmah zama tayi ta kunna data , kwana biyu tana ta tsumayin sabuwar friend dinta amma har yanzu rabonta da hawa online tun shekaran jiyan can, dan bata fuska tayi, bata ji dadin hakan ba ,koba komai sun saba cikin kankanin lokaci, ita kanta tana mamakin yanda tayi sabo da kawarta m,m haka cikin sauki, duk da kasancewar miskila,.




Tana cikin wannan sake saken ne wayar ta tayi ringing, wani kyakkyawan murmushi ne ya kufce mata ganin sunan Wacce ke kiranta , my sisi, picking tayi , tare da sallama, acan bangaren /Khadijah ta amsa fuskar ta cike da farin cikin isowarta minna lfy, bayan sun gaisa cike da kewar juna khady tace "ya Asmah albishirinki" cikin zakuwa tace "goro fari Sol my sister" Khady tace "yanzu haka ina mobile a tsaye ,yanzu motar mu ta sauka, ko minti biyar bamuyi da sauka ba" zabura Asmah tayi ta mike zaune"dan girman Allah da gaske kikeyi khady" dariya Khadijah ta kwashe da shi jin yadda duk yayar tata ta rude, tace"wlh yaya, da gaske nakeyi, AI bazan iya jira muzo tare dasu mimi ba , wai su fa sai cikin week din biki zasu zo, nidai kam bazan iya jira ba , na roki didi shine fa da kyar ya barni saida nayi kuka, tukun na" cikin tsananin jin dadi Asmah tace, "kai sister gaskiya naji dadi sosai wlh ,ki jirani yanzu gani nan zuwa na dau keki".






Suna ajiye wayar ta kalli su zahra da suke jira ta gama waya su tambayeta wacece ta rigasu da cewa"Khadijah ce fa tazo daga kontagora yanzu haka wai tana mobile zanje na daukota ne" tana gama fadar haka ta fice cike da daukin ganin yar kanwar tata,.




A falo ma sanar masu mami zuwan Khadijah tayi da kuma daukota da zatayi daga mobile, dukkansu sunyi murna da zuwan Khadijah , sannan suka mata a dawo lafiya,.




Bakin get ta nufa domin ta samu bello don ya kaita ta taro Khadijah, tana isa motar ya kamal na shigowa cikin gida, ganinta yasa yayi saurin yin parking ya fito daga motar daga wurin aiki yake don sanye yake cikin bakaken suite dinshi na lauyoyi,.




Itama ganin haka yasa ya kalleshi fuskarta dauke da murmushin kauna tace" sannu da dawowa farhatal kalb " cikin jin dadi yace "yawwa nurul ayn, ina zakije haka cikin rana, nifa bana son kina shiga rana , wannan kyakkyawan fuskar taki bata dace da jin rafin rana ba" murmushi ta saki tace"wai Khadijah Ce ta iso tana mobile shine nake son naje na daukota " yace "A'a A'a kice sisin mu ne tazo oya muje mu dauko ta" ya karashe maganar yana nufar motar shi ya shiga , itama bin bayan shi tayi suka fice daga gidan don dauko Khadijah.






Ummi ne ta shigo dakin su batool bayan tafiyan Asmah kallon batool tayi , kasancewar haka take mu'amala dasu kamar kawayenta , tace "waii batool kinga kayan ki kuwa zankadi gsky Dr shima yayi kokari ya narka dukiya sosai a lefen nan".




Kallon mami takeyi cikin rashin fahimta, tace.............










Kuyi hakuri yau ba editing saboda lokaci zai kure ban fara typing din da wuri ba , kuyi hakuri da kurakurai😁
















Oum ummeetarh
07041130088














Share
And
Comment
Fisabillilah🙏
💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~














FREE BOOK












{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}














Page 73 & 74














Dagowa batool tayi cikin rashin fahimta ta kalli ummi tace "umminmu dan Allah ki dena min irin wannan wasan wlh dakin faɗa gabana faduwa yake yi,"dariya ummi tayi ganin dai kamar batool bill hakki bata yarda da abinda ta faɗa , tace "wlh dagaske kayanki ne ,kinsandai baki bina bashin rantsuwa ko". batool cikin dan fargaba ganin harda ranstuwa ummi tayi tace"kaya na to waya kawo kaya,wa zan aura?" ita farabanta ɗaya kar ya zama ɗaya daga cikin almajiran alhaji Mallam.




Tunanin ta ne ya katse jin ummi na cewa"wanda kika tura mana ,shiya kawo kaya, ko su nawa Kikà ba dama da har kika kasa tantance wàñne daga cikin su ya kawo kaya,".


Cikin son tà fashe da kuka tace,"ummi dan Allah ki gayamin wlh da gaske nakeyi bansan wa zan aura ba," ummi tace "ikon Allah sai kallo ,to bshir ne , ina nufin Dr bash".




Wani zabura tayi ta mike tana dafe kirji, nan ta shiga maimaita innalillahi wainnailaihi rajiun, daura hannu tayi akai a baiyane ta shiga furta "na shiga uku na ni fatima batula kun kasheni, shike nan tawa ta kare" can kuma sai hawaye shar kamar an bude famfo.




Ummi dasu Amira kuwa mai zasuyi imba dariya ba , aiko ganin haka yasa batool kara sautin kukanta , kuka kuwa sosai bana wasa ba, harda sheshshka, tun su ummi na daukar abin wasa har lamarin ya fara basu tsoro.






Tafe suke suna hirar su mai ɗaɗi irin ta tsàntsàr màsoya, fayyace mata irin dokon soyyayar ta da yayi ne tun baisan menene so ba, sai gashi kafin ya bayyana kanshi gareta , mai afkuwa ta afku, wato aka aura mata Aslam nan ya shiga baiyana mata halin daya shiga lokacin da zancen haɗa ta aure da Aslam ya riskeshi, har rashin làfiyan ɗaya kwanta na ciwon rashinta saida ya bata làbari, kafin kuma daga bisani allah ya kara bashi dama ta biyu akan ta,.




Dariya ta shiga kwasa, cikin dariya tace "ashe ragwazozo ragon maza zan aura,wato harda kwanciya ciwo kayi , Ashe haka kake sona, da yawa" kallonta yayi shima yana murmushi yace"aini nafi ragwazozo ragon maza ragwanci indai akanki ne," cikin jin ɗaɗi tace" gaskiya naji dadi da Allah ya bani masoyi irin ka, kuma ina màka albishir da cewa zakayi alfahari dani ya kamal , domin zan zame maka farin cikin gidan duniyar , kai harma da kiyama insha Allah".




Da haka suka karaso mobile, tun daga nesa Asmah ta hango Khadijah, matashiyar budurwace mai kimanin shekara goma sha bakwai a duniyà, doguwa ce sosai don tamafi Asmah tsawo, siririyace sosai don Asmah ta dan fita gwabi kadan , saidai akwai boobs da hips kamar dai Asmah, sanye take da riga da skirt na atamfa , am mata dinki daidai jikin ta , mayafinta da takalmi ta to mach ne da atamfar ta kafadarta rataye da wani kyakkyawan karamin jaka mai hannun chain , fuskarta kuwa bajau da make up , idanunta sanye da wani faskeken sun glasses pink colour daya kusa rufe rabin fuskarta, saidai ba karamin kyau ya mata ba dogon hancinta ya fito zirr, dashi, tsaye take ta maida hankalinta kan motacin dake wuce wa akan titi, hannun ta rike da hannun katon trolley dinta pink colour mai hotan Barbie a jiki, Khadijah kam yar wanka ce ta bugawa a jarida.




Da sauri Asmah ta bude marfin motar ta fito da dan gudu gudu ta nufeta, itama sai lokacin ta lura da tahowar Asmah, aiko sake hannun trolley din tayi suka ba juna kyakkyawan runguma, kamal ma fitowa yayi daga motar shi bayan ya gyara parking , ganin sunki sake juna kuma hankalin mutanen wajen ya fara yowa Kansu , yasa kamal dake tsaye bayan su yin gyaran murya, sake juna sukayi kowacce fuskarta yalwace da farin ciki, zare tafkeken glass din dake fuskarta tayi, wow nace saboda ganin tsananin kama da nayi Wanda idan ba yan biyu ko yaya da kanwa uwa daya uba daya ba , ba'acika samun shi ba, fuskarta sak na Asmah harda manyan idanuwan su iri daya ne, banbancin su kawai yanayin jiki ne, da kuma tsayin da Khadijah tafi Asmah,






Fuskar ta dauke da kyakkyawan murmushi ta sauke idanun ta cikin na kamal,wow ta furta a zuciyarta, cikin zare idanunta masu masifar kyau irin na Asmah tayi, hakan kuwa ba karamin kyau ya kara mata ba, cikin yanayin muryanta na masu surutu da saurin baki tace "laaaa ya kamal dama kaine, wlh banganeka ba sai yanzu, ina wuni mun sameku lafiya ya shirye shirye," cikin dan murmushi yace "ban amsawa , ai dama bazaki gane ni ba tunda bata ni kikeyi ba ta sis dinki kikeyi" hade hannayenta tayi tace"afwan ya kamal , wlh ya Asmah ne na tara kewarta da yawa shiyasa," dukansu dariya sukayi kafin kamal ya dauki trolley dinta ya saka a boot, suka shiga motar suka nufo gida, Asmah a gefen kamal , khady kuma a baya.




A can gida kuwa batool abin nata ya soma wuce hankali , rarrashinta ummi ta shigayi ganin haka kuwa yasa ta fara wani mimmikewa tana wasu sambatu , ita aladole ta hau iska , sai cewa take , wlh bana sanso wlh karku aura min shi in ba haka ba zan kashe kaina, wayyo na shiga uku, abidai yayi kamari,zahra cike da tsoro ta fice da gudu don ta je ta sanar da su mummy abinda ke faruwa , don ita gaba ɗaya ta tsure, tunda suke cikin su ba wacce ta taba hawa iska sai yau da batool ta hau na karya.


Su

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads