Header Ads
Showing 165001 words to 168000 words out of 201974 words

Chapter 56 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1747

Ads at the middle of Article

harsu afnan,a hannun su babyn take wuni sai tayi kuka ake kawo mata ita ta bata nono su kara daukar ta.


A bangaren Dr bash kuwa dirama suke kwasa da maah sosai, kwata kwata ta hana shi sakewa ya kasa samun yadda yake so, daya lallaba ya shige ɗakin batool sun dan keɓe,minti biyu zata kwala mai kira, haka dole zafi fito yana gungumi, idan har ya samu ya zauna tare da ita ya Daɗe to a falo ne cikin mutane .




~MALAYSIYA~




Yau kimanin watanni biyar kenan bayan haɗuwar zee da Dr bala, tun ranar da ta ambata wa Dad zata koma Gidan mijin ta ya nuna bacin ranshi bata sake furta kalma makamanciyar wanana ba, ta kyale shi ta zuba wa sarautar Allah ido har zuwa iya wa'adin data dibar mishi, a bangaren mom kam tayi iya bakin kokarin ta sosai wajen ganin ta shawo kan Dad amma abin yaci tura, karshe ma yace idan ta sake tada mai maganar a bakin auren ta, tun daga lokacin ta saka ma bakinta ta sakata ta kulle bata sake koda bashi labari mai kama dana Aslam ba.


Yau ne ta kama little Aslam ya cika shekara ɗaya, kuma yau ne Dad shirya mai gagarumin taron birthday irin na ƴaƴan gata Wanda zee bata San da zancen ba don ita ma tana can tana nata shirin da ba Wanda yasan na meye daga Allah sai ita.


Karfe Tara na safe Dad ya fito daga dakin shi cikin shirin fita mom na biye a bayar shi, har ya sa kai zafi fita zuciyar shi ta kasa jurewa yau tun safe baiji motsin su ba, baiji ko da kukan little ba, alhali ba haka ta saba yi ba duk safiyar Allah takan fito ta iske shi a dakin shi ta gaishe shi ta bashi little su gaisa, yau gashi har zai fita bata zo ba kuma baiji koda motsin ta ba. Kallon mom yayi yace "dubo min daughter kiga ko lafiya yau kwata kwata banji motsin ta ba." tace "wlh nima haka, ka riga ni furtawa a baki ne kawai dama yanzu nake shirin in ka tafi na shiga na dubota"ta karashe maganar tana nufar hanyar dakin zee.sallama tayi shiru ba amsa haka yasa tayi knocking nanma shiru , kawai sai ta murda kofar ta shiga, tana shiga ba zee a dakin ba little hakan yasa tadan kasara bakin toilet tana magana don duk tunanin ta tana toilet saidai jin ba alamar motsin kowa a toilet yasa cikin tashin hankali ta tura kofar toilet din nanma wayam ba kowa, ai da sauri ta dawo tana gaya wa daddy bata ɗakin cikin mamaki yace "bata dakin! to ina taje" mom tace "wlh nima ban sani ba." Bai yarda ba hakan yasa ya nufi dakin zee din da kanshi mom ta rufa mai baya, yana zuwa ko sallama bai samu daman yi ba ya tura kofar ya faɗa ɗakin, karaf idanunshi ya sauka akan farar linkakkiyar paper akan makeken bed din ta ta daura Biro ta danne shi, baki na rawa ya nuna wa mom papern tare da cewa "meye wancen".........












Dan Allah ku dinga comment mu samu mu gama littafin nan wlh na gaji nasan Kuma kun gaji ko?








Oum Ummeetarh
07041130088


💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~




FREE BOOK




{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}






*ASSALAMUALAIKUM SISTERS*


Abun da mamaki ta yanda watan axumi yaketa qaratowa cikin Dan taqin lokaci.
Me kika tanadarwa kanki dama yaran mu yar uwa?
Munada kyawawan kayan Yara na dinki masu kyau sosay d bama zakice dinkawa akayiba yaro/yarinya sufito gwanin burgewa kowa yanasan barka,07046881166


Kayanmu sauqinsu yyi har kamar kyautane,zaki iya samunsu dga 2k harzuwa abunda yyi Sama,kizo kiyi sarin kayanmu kisamu alkhairi me tarin yawa,07046881166


Akway takalma Suma kyawawa daga kan 1k zuwa sama,07046881166


Sannan munada tsala tsalan frames d madubai n gyaran gida masukyau d arha sosay,07046881166


Akway leshina d atamfofi,abayas sewanda kikazaba duk a farashi mesauki,07046881166


Karna cikaku d surutu ku kira:07046881166 domin qarin bayani,karku manta alkhairin Tari maganin mantuwa zaku iyashiga Instagram handle namu don ganin kayayyakinmu: everythng_handmade,


Semunjiku 07046881166








Page 123




Wani irin zaro ido mom tayi, lokacin da idanun ta sukayi arba da abin da yake nuna mata, gaban ta ne ya shiga faɗuwa hankalin ta ya tashi, cikin rawar jiki ta ƙarasa gaban bed ɗin ta miƙa hannun ta dake karkarwa ta ɗauki pepan ta miƙa mishi. Kasa amsa yayi sai zuba mata idanu da yayi yana binta da kallo kamar wani dolo, ganin haka yasa tayi karfin halin warware linkakken fefan ta fara karanta abin da ke rubuce a bayyane kamar haka:


Amincin Allah ya tabbata a gareku yaku iyayena, barkan ku da wannan lokaci, kafin nace komai zan fara da Baku haƙuri akan abin da zaku tsinkaya a cikin wannan bakar wasiƙar, ina me neman yafiya da sanya albarkan ku a duk inda nake, a daidai wannan lokacin da kuke karanta wannan wasiƙar tawa, jirgin mu ya daɗe da keta hazo, zuciya ta gaza hakuri, na kasa juriya na tafi Neman aljannah ta ku sanya mini albarka, sannan kuma ku yafe min ina kaunar ku iyayena.


Tun kafin mom takai karshen karatun tuni hawaye ya gama wanke mata fuska yayin da Dad shi kuma tuni ranshi ya gama baci,zuciyar shi ta dauki wani irin zafi kamar zata fesar da aman wuta.Wani irin numfashin fusata ya shiga fesarwa, mom bata ankara da yanayin da yake ciki ba sai da taji ya fisgi fefan dake hannun ta ya shiga cukurkuɗe shi a hannun shi ya dunƙule shi da karfi, da karfi ya furta "why daughter, why Zainab me yasa zaki min haka, kece raunina ta farko a duniya, meyasa meyasa meyasaaaaaaaa?" Tuni hankalin ta ya ƙara tashi ganin halin da ya shiga cikin kankanin lokaci gaba daya ya fita daga kamanni shi idanun shi sunyi jajur jijiyoyin kanshi sun tashi.Tsoron ta Allah tsoran ta kar ciwon shi ya tashi, cikin kuka tace "Dadyn zee ka tashi duk ba wannan ya kamata muyi ba, duk yadda akayi daughter gidan mijin ta Asl..." Katse wa maganar ta yayi sakamakon lafiyayyen Marin da ya ɗauke fuskar ta dashi , tsananin firgita saida ta taune harshe, dafe kuncin tayi ta zuba mishi idanun ta da ke zubar hawaye , tun da sukayi aure da shi yau kimanin shekaru talatin kenan cif a duniya bai taba koda zagin ta bane balle har takai ga mari.


A matuƙar fusace ya nuna ta da yatsa tare da cewa cikin kakkausar murya "wannan shine hukuncin ki a duk lokacin da kikayi gigin sake ambatar sunan wannan la'anannen yaron a gaba na, nasan da haɗin bakin ki zainab ta bar gidan nan domin tun farko kin nuna kina goyan bayanta, to ki sani kiyi duk yadda zakiyi ki dawo min da ɗiya ta gaba na, idan kuma ba haka ba wallahi wallahi zan dauki ƙwaƙƙwaran mataki akan ki daga ke har wancen ƙaramin dan iskan." Yana gama faɗin haka ya fice a ɗakin a fusace da wani irin sauri kamar zai tashi sama, tunda ta ɗaura hannunta a fuskar ta kafe shi da idanu ta kasa koda kefta ido ne, ita Abdus-salam zai Mara yau akan ƴar shi, ƴar da ita ta dauki cikin ta a jikin ta na tsawon wata tara da daɗi ba daɗi, yar da ta tsaga jikin ta ta fito, par da ta shayar da ita da nononta, par da taci kashi da fitsarin ta, lallai zata nuna mishi ita ɗin uwa ce,zata nuna mishi matsayin uwa a gurin ƴarta, lokaci yayi da zata dawo daga rakiyar Abdus-salam. Tunanin ta ne ya katse jin wani irin gurnani da hayani ya na tashi daga compound din gidan, muryar Dad ta jiyo yana cewa "wlh sai na kashe ka, da haɗin bakin ka ɗiyata ta bar gidan nan, munafiki ka gaya min da saka hannun ka ko A'a." Da wani irin gudu Mom ta fito daga cikin gidan tun daga nesa ta hango shi ya shaƙi wuyar get man da ke musu gadi shekara da shekaru, sai kwalfa mishi mari yake yi bai ko kula da cewa a girme kila mutumin ya girme shi ba kokuma suzo tsara. Kara girgiza shi yayi tare da cewa a tsawa ce "Da kai nake magana fa, baza ka bani amsa ba saina illata rayuwar ka." Daidai lokacin mom ta ƙaraso gurin ta rike Dad ta baya tana ƙoƙarin ta raba shi da me gadi, ina ko gezau baiyi ba da alama ba a cikin hayyacin shi yake ba. Ganin ta kasa ga me gadi na wani irin numfashi kamar ran shi zai fita yasa ta sake shi ta durƙushe kasa tare da fashe wa da wani irin kuku, mai ban tausayi. Daidai time din kuma aka buɗo karamin get din gidan aka shigo, hango yanayin da suke cika yasa alhaji Abdur-rahaman da wani mutumi ƙaraso wa cikin gidan da gudu, ganin ƙanin nashi na shirin yin kisa yasa baiyi wata wata ba ya dauke fuskar shi da maruka har biyu lafiyayyu.


Take jini ya fara bulbula ta hancin Dad kafin kace kobo kuma jikin shi ya saki idanun shi ya shiga kakkafewa a hankali ya saki me gadi, yayi baya zai fadi da gudu daya mutumin da suka shigo da Alhaji Abdur-rahman ya tallabe shi yayin da shi kuma Alhaji Abdur-rahman ya tallabe mai gadi da shima yayi taga taga zai faɗi, ganin haka yasa Mom fasa wani irin gigitaccen ƙara tare da cewa"innalillahi wainnailaihi rajiun, na shiga uku shikenan Abdus-salam ya tafi ya barni, wayyo Allah naaa!!"




~9JA~


Niger tsate airport mekunkele. Janye take da katon trolley dinta a hannun ta na hagu yayin da hannun ta na dama ke rike da hannun ɗan kyakkyawan yaron ta dake sanye cikin wasu irin shegun kayan Sanyi masu masifar kyau kafar shi sanye da kwambas mai mugun tsada,kanshi sanye da hular sanyin dake jikin rigar ,yayinda ita kuma take sanye da kayan ta na gado ƙananan kaya riga da wando saidai ta daura after dress mai kauri a saman su yayin da ta yane kanta da mayafin rigar.
Kallo daya zaka musu ka tabbatar tafiyayyu ne daga wata kasar dabam wacce ba Nigeria ba ba kuma maƙotan ta irin su niger da sauran su ba.


Wani irin daddaɗan iska take ji yana ratsa huhun ta da duk wani kafar iska na jikin ta, rabonta da shakar irin wannan iskar tun ranar da ta saka kafar ta tabar Nigeria yau kimanin shekara daya da rabi kenan cif. Wani irin kwanciyar hankali da ta Dade bata ji irin shi bane taji ya saukar mata lokaci guda take ta shiga sauke wani irin ajiyar zuciya tana lumshe fararen idanun ta.




Daga bayan ta taji yana cewa "Hajiya salamu alaikum." Da sauri ta juyo ta sauke idanunta akan dan matashin saurayin dake mata magana, sai lokacin taji hankalin ta ya tashi sai lokacin ta tuna in da ya kamata ta dosa, take zuciyar ta ya bata amsa da gidan mijin ki mana, yayin da ɗaya sashen ke cewa gidan iyayen shi, domin sune babban matsala shin da wani ido zasu karbi little a matsayin jinin su kuma jikan su ɗan Aslam wanda basu San da zaman shi a duniya ba. Muryar dan saurayin ne ya kara katseta da cewa "Hajiya baki amsani ba Nine driver da mai gida ya turo domin na kaiki masauki." Gyaɗa mai kai kawai tayi alamar ok, amsar trolley ɗinta yayi ya nufi inda ake parking motoci ya sanya a cikin motar shi, buɗe mata baya yayi ta shiga yayin da shi kuma ya buɗe gefen driver ya shiga ya tada motor suka ɗauki hanya.


Sai da suka daidai ta akan babban titi ta buɗe baki a karon farko tayi magana"kure area zaka kaini." Dan juyowa yayi ya kalle ta tare da cewa "Ok hajiya, amma mai gida cewa yayi na kaini shaanu wani sabon ƙaramin gidanshi da ya saya kwanan nan gama keys ɗin gidan nan a hannu na." Tace "no ka kaini kure area kawai." Yace "toh hajiya." Bai sake cewa komai ba sai daukar hangar unguwar data ambata mashi yayi, motar su na kara kusantar unguwar gabanta na kara faduwa yayin da hankali ta ke kara kwanciya, ta rasa wanne ne ya rinjiyar wani tsakanin kwanciyar hankali da nutsuwar zuciyar da take ji da kuma faduwar gaban da ya tasa ta a gaba.


Dai dai kofar tamfatsetsen gidan Alhaji baba ta umarci driver da yayi parking, bai musa ba kuwa yayi parking din tare da fitowa ya buɗe mata ƙofa, ta fito sannan ya buɗe boot ya fito mata da akwatin ta, jakar ta na hannu ta rataye a kafaɗar tare da riƙe hannun little suka doshi get din gidan yayin da drivern ke binta a baya dauke da trolley ɗinta.


Cikin sa'a karamin kofar gidan a buɗe yake, da bismillah ta sanya ƙafar ta cikin gidan, hannunta rike dana little, juyowa tayi ta kalli drivern ta sakar mashi murmushi tare da miƙa mishi hannu alamar ya bata trolley ɗinta. Ba musu ya mika mata kuwa, tace " n
Nagode sosai fa." Murmushi yayi tare da cewa "Ba komai hajiya akan aikina nake." Sallama sukayi ya juya ya tafi yayin da ita kuma ta fuskanci cikin gidan tana ƙare wa ko ina kallo.


Babu kowa a compound ɗin gidan kasancewar gida ne da babu ƙananan yara a ciki, tambayar kanta take yi wani part zata dosa, sauke idanun ta tayi akan part din Mami, wanda nan ne part din da taɓa shiga har tayi zaman fiye da awa ɗaya a cikin shi.


A hankali ta daga ƙafarta ta fara takawa zuwa part ɗin mami, sai da tayi bismaillah sannan ta danna doorbell, so ɗaya ta dauke hannunta tare da jiran tsammani.


Mami da sakkowar ta kenan falon ta fito da nufin ɗaukar wayar ta data manta a falon ɗazu da safe, taji ƙarar ƙofa, hakan yasa ta nufi ƙofar ta buɗe domin duba ko wanene. Kusan suman tsaye tayi lokacin da idanun ta suka sauka cikin na zee, cike da tsantsar mamaki tace "zainab! Kece da gaske ko idona ne." Ga mamakin ta sai gani tayi zee ta sakar mata wani irin kyakkyawan murmushi, tare da kallon little dake dan jan rigar ta, sai lokacin idanun mami suka sauka akan little dake tsaye kusa da mahaifiyar shi hannunsu sarƙe dana juna.


Gaban ta ne ya yanke yayi wani irin faɗuwa rass, take ta ƙure yaron da kallo bata ko keftawa, ba kowa take gani ba fa ce Aslam a wasu shekaru masu ɗan nisa da suka shuɗe, lokacin da aka auro ta gidan tana amarya.


Dago da kai tayi ta kara kallon zee ta sake kallon little, ko shakka babu wannan jinin Aslam ne, ko shakka babu wannan jinin daddy da Abba ne ko shakka babu wannan yaron jinin Alhaji baba ne, babu bukatar ta tambayi ɗan waye domin ko makaho ne kuwa ya laluba zai tabbatar da hakan balle kuma ace mai ido biyu.


Durkushewa tayi ta maida tsawonta daidai na little kafin kuma ta kaima yaron wani irin runguma sannan ta fashe da kuka, ba komai ne ya saka mami kuka a daidai wannan lokacin ba face tunawa da irin yadda Aslam yake kaunar yaga gudan jinin shi a duniya, kamar yadda yake ta faɗi tashi yaga ya samu ɗan kanshi a doron ƙasa, ta fi kowa sanin sirrin Aslam tafi kowa sanin yadda yake kaunar yaga ya haihu, yana iya boye ma kowa sirrin shi a duniya amma banda ita zata iya rantsuwa banda Asmah data kasance abokiyar rayuwar shi itace mutum ta biyu da zata bugi kirji ta faɗi wanene Aslam.


Ɗagowa tayi tana share hawaye ta kalli zee tace "Zainab muje cikin gida wannan lamarin ba abinda zaki tunkare ni da shi ni kaɗai bane." Daukar little tayi ta ta rungume ta doshi part din Alhaji baba,yayin da zee ta rufa mata baya.


Kabbara Alhaji baba ya shiga yi a bayyane yayin da hajiya mama ta shiga sharar kwallah, a lokacin da suka yi arba da little. Tuni jikin zee yiyi sanyi mekefaruwa ne,to kodai Aslam ya mutune, take gabanta yayi wani irin mummunar faɗuwa, take itama hawaye suka shiga wanke mata fuska hannun mami dake zaune kusa da ita ta damke da karfi Wanda saida mami ta juyo a firgice ta kalle ta, ganin hawaye a fuskarta yasa mami bule baki da sauri da nufin tambayar ta mekefaruwa saidai muryar ta ya katse ma mami hanzari, cikin sheshekar kuka tace"Mami ya mutu ko, Aslam ya mutu ya barni ko."Da sauri mami ta shiga girgiza mata kai kafin ta bule baki tace "A'a zainab karki sake faɗin wannan Kalmar Aslam bai mutu ba yana nan da ranshi da lafiyar shi." Zubawa mami idanu tayi tana kallon ta bawai dan ta yarda da abin da take gaya mata ba, ita yanzu idan ba ganin Aslam tayi ido da ido ba babu wanda zai ce mata yana raye ta amince.


Mummy ce ta fara shigowa falon domin amsa kiran gaggawar da Alhaji Baba ya mata, a ruɗe take matuƙa don tasan irin wannan kiran gaggawa daga Alhaji baba, ba karamin muhimmin Abu bane, tana shigowa idanun ta akan little dake rungume a jikin hajiya mama ya sauke, wani irin wawan burki ta taka, yayin da doguwar sallamar da ta rafko ya katse, bakin ta ne ya shiga rawa alamar tana son ta furta wani Abu amma kuma ta kasa buɗe baki, hajiya mama ne tace tana share hawayen farin ciki"kyayi abinda yafi haka ma Aisha karaso ciki." Mami ne ta Ƙarasa gare ta ta riƙo hannunta zuwa cikin falon ta zaunar da ita kusa da hajiya mama, mummy kam dama bata iya ruɗewa ba, lokacin da tayi arba da zee sai ta kura mata ido kamar tana son ta tuno inda tasan ta harga Allah ji tayi kamar an mata

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads