Showing 78001 words to 81000 words out of 201974 words
Chapter 27 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
gaya maka shine, Aslam ga zabi nan alhaji ya kuma maka a karo na biyu," duk da yasan da maganar amma jinta daga bakin mahaifiyar shi saida gaban shi ya yanke ya fadi kamar yanzu ne ake gaya mai batun, ji yayi kamar yace ma mummy wacece ita, amma ba hali don babu yar haka a tsakanin su.
Ci gaba mummy tayi da cewa " Allah ne ya mallaka maka ita ba wayon ka ko dabaran ka bane, muma iyayenka ba iyawar mu bane,haka ma Alhaji, dan Allah Aslam ka riketa amana marainiyace gaba da baya, mune gatan ta Kaine gatan ta Allah ne gatanta,kar naji kar na gani,ka kula da hakkokinta da Allah ya daura maka, ka wanzar da farin ciki a duniyar ta, kada ka kuskura ka bayi ruwan hawaye su kwaranya daga idaniyarta, ka wanzar da murmushi akan fuskarta, ka maye mata gurbin iyayenta data rasa, kamar yadda muka maye mata a lokacin da take a gaban mu" Aslam kam duk abin da mummy ke fada shiga kawai sukeyi ta right su fita ta left, jinta kawai yakeyi, shi a duniya akwai macen da ta isa ya mata duk wadanan abubuwan da mummy ta lissafo inba husnah ba, ya daiji zai sauke mata hakkokinta da Allah ya daura mai,amma batun farin ciki , murmushi waye waye saidai tayi hakuri dashi.
Tunanin shi ya katse jin mummy na cewa "shi kenan, nidai iya abinda zan iya gaya maka kenan jeka Allah ya maka albarka kaida yan uwanka ,Allah kuma ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyaba" addu'o'i mummy ba karamin faranta mai rai sukayi ba , take ya shiga amsawa da amin thumma amin , kafin daga bisani ya shiga kwasan godiya.
Daga part d'in mummy part din Alhaji baba yaje, suna tare da hajiya mama, Aslam yayi matukar mamakin ganin yau Alhaji baba ya sakar mai fuska ya amsa gaisuwar shi cikin kulawa, idan ba karya idanunshi suka mai ba kamar harda murmushi ma yaga yadan mai.
Gaishe su ya shigayi cike da ladabi da girmamawa, bayan sun amsa ya musu ban gajiyar biki, kafin ya mike ya koma kusa da hajiya mama ya zauna ya kalleta yace "madam ya akayi ne," tace "gawa taki rami idonka kenan, wai lallai Asma'u ta cire tuta, wanwar takai maza kasa tana daga zaune mike da kafafu, to Allah dai ya baku zaman lafiya" ga mamakin sa ji yayi Alhaji baba yace "wannan ne maza, ragwazozo dai ragwan maza," hajiya mama tayi dariya tare da cewa "aikai ya gado" hararan wasa ya watsa mata, cikin dariya tace" bar wani harare harare, ko kuma yanzu na tara yan jikokina na basu tsohon tarihi, suji yadda Aslam ya gado wannan ragwanci".
Aslam kam na gefe yana kwasar dariyar wannan lamari, yadda tsofaffin nan ke gudanar da rayuwarsu kamar wasu sababbin ma aurata abin na matukar birgeshi cikin dariya yace"a bankado mana wannan tsohon tarihin gaskiya ,bari na taro yan kannai na muzo mu zauna mu sha story," dakuwa Alhaji baba yamai tare da cewa "ungo naka Aslam tashi ka wuce ka barmin sashe na" haka dai suka dan taba wasa yau harda Alhaji baba abinda Aslam ya manta rabon shi da ganin hakan, bayan sun gama ne kuma ya daura da nasiha akan zabin da yamai, yana yi yana mai wasu irin zaurancen da Aslam din kwata kwata bai gane inda ya dosa ba, a part din ya wuni sai la'ar suka fito shida Alhaji baba zuwa masallaci daga nan kuma bai koma can ba sai ya nufi part din daddy nan ya tsaye har magriba, inda yaje yayi sallah harda isha'i, daga nan suka shigo tare da Abba, tare suka yi dinner a part din mami, bayan sun gama suka dan zauna hira , Abba ganin Aslam baida niyyar cewa zai tashi ya wuce , yasa yace"Ahh Aslam ya kamata kazo ka tafi gida haka anbar amarya ita kadai tun jiya, maza tunda jiki da sauki aje a ganta ko" murmushi yake ya shiga yi yana dan sose keya, mami tayi murmushi tare da cewa "ya kamata kuwa son aja a duba min lafiyar yata" mikewa yayi ya musu sallama,rakoshi Abba yayi har parking lot. ya shiga motar shi ya tayar ya dauki hanya a zuciyar shi sai sake sake yakeyi.
Baiso Abba ya tuna da batun wucewar shi ba , dan shi so yayi ya lallaba yayi shigewar tsohon part dinsu ya kwanta abinshi,dan bayajin zai iya zuwa gareta a halin da yake ciki yanzu na rashin husnan shi, shawagin shi ya dingayi a gari sai gurin sha biyu dare ya dawo layin yayi parking d'in motar can nesa kadan da gidan , ya lallabo a hankali ya kwankwasa get, mai gadi cikin dan baccin shi da baiyi nisa ba, yaji ana knocking din get kasa kasa, tashi yayi ya dauki torchlight da gora ya nufo bakin get din tare da tambayar wanene,Aslam cikin kasa kasa da murya yace "nine Mallam madu Aslam ne", mai gadi yace "yallabai ne" Aslam yace "eh nine" bude get din mai gadi yayi bayan ya tabbatar da cewa Aslam d'in ne, sadaf sadaf ya shigo ,mai fadi yace cikin dan rudewa tunda abune da bai taba faruwa ba"lafiya yallabai " Aslam ya amsa da lapiya lallabawa yayi ya shige tsohon part d'in su ya lalibi dakin shi ya shige ya kwanta.
~AMIRA~
Amir kwata kwata bai bi ta a hankali ba, hasalima kanshi kwancewa yayi tunda ya dafeta, bai kara sanin inda kanshi yake ba, kuka takeyi tana rokanshi yayi hakuri amma ina baima San tanayi ba, yakushi cizo kuwa yasha shi yafi cikin buhu, tun tana magiyar da kai yakushi har tayi tsit numfashi ya dauke.
Duk wannan bidirin dake faruwa Amir baida labari yana cen duniyar sama, saida yayi good five round, sannan yadan fara jin daidai, duk da haka bawai abin ya sake shi bane.
Karfe hudu saura na dare ya kyaleta, bawai dan ya gamsu ba saidan shima ya gaji, kwankwason ciyo yake mai da kafafun shi da bayanshi , jikin ma gaba daya, to abinka da sabon shiga
Kwanciya yayi a gefenta take baccin gajiya ya kwashe shi bashi ya farko ba sai karfe takwas na safe.
Bai lura da halin da take ciki ba saida ya lallaba ya shiga toilet ya tsarkake jikin shi, da'ker ya samu ya gama ya lallaba ya fito,gaba daya zazzabi ke neman rufeshi,
Kasancewar ko ina a rufe yake rufe ruf, ga kuma manyan labulayya masu kauri yasa dakin ya kasance da duhu.
Wutar dakin ya kunna mai haske, nan take idon shi ya sauka akan gadon, wani irin yankewa gaban shi yayi ya fadi, baisan sanda ya kara mika hannu ya kashe wutar ba, take dakin ya koma da duhun shi, innalillahi wainnailaihi rajiun ya shiga jerowa take zazzabin da ke neman rufe shi d'azu ya rufeshi rufe yanzu.
Jinin da yaga ya bata bed sheet din ba karamin daga mai hankali yayi ba,
Ganin tsayuwar baida amfani yasa ya kunna wutan ya lallaba ya karasa kan gadon, ya tallabota, hankalin shi bai idasa tashi ba saida a ya kula bata numfashi.
Jijjgata ya shiga yi yana kiran "baby baby dan Allah ki tashi baby karki mutu, na shiga uku, innalillahi wainnailaihi rajiun" gaba d'aya ya rude ya rasa ma da mai zai taimaketa , duk wani tunani na kanshi ya a lokacin ya shafe, Abu daya kawai ya iya zuwa mai a rai shine ya kira mami.
Harya dauki waya zai kira mami wani zuciyar ta kwabe shi da cewa kasan wa make shirin kira kuwa mahaifiyar Amira ce fa, canja akalar kiran yayi da niyar kiran mummy saidai by mistake ya kira ummi bai kula ba duk a rude yake jikin shi na rawa.
Ummi dake ke kan hanyar dawowa daga bidda fshigonwan su cikin minna kenan suna daidai kure market kiran Amir ya shigo wayarta.
ummi na dagawa bai jira komai ba ya shiga cewa "mummy ta mutu mummy Amira ta mutu gata nan mun tashi da safe, bata numbashi innalillahi wainnailaihi rajiun " ciki tsananin rudewa da tashin hankali yake magana daga ji ma kasan ba a cikin haiyacin sa yake ba , ummi bata tsaya jin karshen zancen shi ba ta katse kiran tare da daura hannayenta duka biyu a aka , anty Jamila dake gefenta ta shiga tambayar ta lafiaya meke faruwa, ba amsa sai cewa driven tayi ya kaita albishir, shi direba baisan albishir ba , sai anty jamy ne keta mai kwatance har suka isa gidan.
Tana nan yanda take bargo kawai ya iya rufa mata, ummi na shigowar ita da anty Jamila ta shiga kwada sallama a main falo, da sauri ya mike zumbur ya fito sanye da jallabiya, yayi matukar .mamakin ganin ummi a maimakon mummy ,cikin tashin hankali ummi tace " ina Amiran" nuna mata sama yayi , tace "wuce ka kaini inda take nace" ba shiri ya juya da sauri, rufa mai baya su kayi .
Suna shiga ummi ta yaye bargon daya rufa mata, wani irin zaro ido waje tayi, ganin abinda ya dauke wutan kanta na hucin gadi, tafa hannu anty Jamila ta shiga yi taba sallallami.
Ummi kam mikewa tayi , batayi wata wata ba ta shararawa Amir mari kafi ya gama dawowa haiyacinsa ta kara sauke mishi wani, cin kwalar shi tayi cikin bacin rai ta shiga furta, "kai wani irin baqin mugu ne haka, dama baka da tausayi da imani har haka ban Sani ba, kasheta kayi niyyar yi da kome?" Gani bai bata amsa ba ta sake jijjgashi tace "nace kasheta da kayi niyya?".
Anty Jamila ne ta kama hannun ummi ta banbare a jikin shi tana cewa"ba wannan bane a gaban mu yanzu umminsu" toilet ta shiga ta hada ruwa a bathtub mai dumi sosai tazo ta ciccbi Amira ta wuce da ita toilet, kallon Amir da yayi tsuru tsuru ummi tayi, tace"tsayuwan me kake mana aka kana binmu da kallo" sadaf sadaf ya fece daga dakin sai lokacin ma ya tuna baiyi sallar asuba ba.
Anty Jamila na sakata aruwan dumin ta sauke wani marayan ajiyar zuciya, kafin ta , ta shiga cewa "wayyo Allah mummy Asmah batool zahra kuzo ku taimake ni,na shiga uku, yaya amir dan Allah kayi hakuri kamin rai, wayyo zan mutu zafi zafi yaya amir" haka ta ringa wasu irin sambatu abin tausayi, girgiza kai anty jamy tayi, ta fahimci gaba daya Amira bata cikin hayya cinta, gasata tayi da kyau, ta nado ta a tawul suka fito, kwantar da ita tayi jikin nan ya daura zafi zau,.
Falo ta fita ta samu ummi ta gaya mata sun fito, ummi tace "to na kira wata kanwar mijna Dr ce anan garin take aure tana hanya" anty jamy tace"yawwa to shike nan dama maganar da zanyi kenan," zama tayi itama kusa da ummi suna jiran zuwan Dr.
Zaman su ba dade wa Dr ta karaso, har dakin Amira anty Jamila ta rakata bayan sun gaggaisa, bayanin komai ta mata, ta fice ta barta da Amiran. Duba ta ta farayi ta gani ko akwai tear, subhanallahi Dr ta furta bayan taga irin aika aikar da Amir yayi, ita kanta ta dade bataga irin wannan case din ba,ta matukar tausayawa Amira.
Dinki ta mata bayan ta kashe zafin wurin, ta daura mata Karin ruwa, ta rubuta wasu magunguna ta bayar tace a siya tayi amfani dashi kuma ta d'in ga shiga ruwan zafi akai akai, insha Allah nan da 3 days zata warware, shi kuma Amir kar ya kuskura ya kara kusantarta sai ta warware sosai.
Bayan tafiyan Dr ummi kiran amir tayi bayan ta gama mai fada sosai, tare da tabbatar mai da cewa da zata wuce abuja shida ganin ta sai tayi wata biyar kwarara, tunda yace shi baida hanakali, bashi takardar maganin tayi yaje ya siyo.
Ranar a gidan ummi ta wuni tana kula da Amira bayan ta kira waya ta labarta ma mummy komai dake faruwa, mummy kan tausayin Amira harda kwallah tayi, take ta shiga jimamin halin da sauran ukun yammatan nata suke ciki suma.
~ASLAM~
Saida ya jera kwana uku kwarara yana satan kwana a family hause ba Wanda keda labari,sai tsakar dare zaizo ya kwanta da asubar fari ya bar gidan kafin kowa ya fito daga shi sai mai gadi sukasan da hakan, koda wasa kuwa baije gidan amaryar shi ba, a kwana na hudu ne Allah ya toni asirin shi, ya dawo sadaf sadaf zaiyi shige wurin sha biyu dare, karaf a idan Abba dake tsaye jikin window, mamaki kuwa kamar ya kashe Abba, da asuba ya tirke mai gadi nan ya labarta mishi kaf abinda ke faruwa a yan kwanakin nan, godiya Abba yamai ya wuce yana sake saken ta ina zai fara.
Da misalin karfe takwas na Daren ranar Abba ya daga waya ya kira Aslam, ya riga ya gama samo mafitan yadda zai bullo wa lamarin, bayan ya daga Abba yace "son ya kwana biyu ya karfin jiki ya kuma amarya" Aslam ya "jiki alhmdllh ,amarya kuma tana lafiya," Abba yace "masha Allah kakoma gida ne ko? inason ka rakani wani guri ne" Aslam yace "eh Abba ina gida ne amma bari na fito yanzu" Abba yace "ok to in kuma kana ganin amarya zata damu ku taho tare kawai"Ai da sauri ya amsa da "A'a Abba ba damuwa tace zata zauna naje na dawo ba matsala" Abba yace to shi kenan sai ka iso, ya ajiye wayar tare da saki murmushi yàce ja'iri dani kake zance.
Sai kusan tara Aslam ya iso gidan dan karya yakeyi baya gida hasalima yana nisa da unguwan sosai hakan yasa ya bata lokaci kan ya iso.
Yana isowa baikai ga parking ba Abba dake zaune cikin motar shi yama jiran shi ya fito, shima yana parking ya fito , bayan sun gaisa Abba ya nunamai motar yace muje ko.
Ba musu ya shiga motar Abba suka bar gidan, Abba na tuƙi yana dan janshi da hira, yahuza suya sport , Aslam yaga sun je Abba yace mai" jira ni a mota pls 10 minutes" ya fice zuwa cikin wurin, har zuwa lokacin Aslam bai kawo komai a ranshi ba.
Bayan minti kadan Abba ya dawo ya bude bayan mota ya ajiye siyayyar da yayi ya shiga motar suka ci gaba da tafiya, saida suka gama shawagi a titi sannan Abba ya daki hanyar London road,.
Kallon Aslam yayi yace "bari na sauke a gida tunda dare yayi gobe bello ya kawo maka motar da safe", da sauri yace "A'a Abba ba damuwa muje kawai na dauke," Abba yace"kaidai bari tunda gashi har mun kawo gidan goben bello ya kawo maka motar, kaje gida kabar min daughter ita kadai" ba yacce Aslam ya iya dole haka yayi shiru, ya kudiri aniyar Abba na ajiye shi a bakin get inya bada baya shi kuma zai fice abinshi, ga mamakin shi gani yayi Abba yana danna horn a bakin get, mai gadi kuwa cikin azama ya wangale get, Abba ya kutsa motar shi ciki.
Yana parking ya fito ya bude bayan motar ya dauko manyan ledodi guda biyu, har lokacin Aslam na zaune jiki a mace baida niyyar fitowa daga motar, Abba yace "fito mana son kai nake jira fah" jiki a sanyaye ya balle marfin motar ya fito, mika mishi ledar yayi tare da cewa "oya ga tsarabar daughter akai mata saida safe" karba yayi yana sakin murmushin yake yace"to Abba ta gode saida safe" jira ya danyi irin Abba ya shigayi motar nan shi kuma ya samu ya gudu amma ga mamakinsa gani yayi Abba ya jingina da jikin motar ya nuna mai hanyar plat din da ke gabanshi,.
Sai lokacin Aslam ya fara hasashan wani abu to kodai Abba ya gano shine, wani busasshen miyau ya hadiye mukut, tare da kama hanyar nufar kofar plat din, har ya kai bakin kofa ya tsaya ya waigo still idanunta Abba nanan akan shi, dole yayi shahada ya murda handle din kofar ga mamakin sa gani yayi kofar ya bude, a zuciyar shi yace lallai ma yarinyar nan haka take barin kofa a bude abinta, shigayi yayi da sallama a bakinsa kasa kasa...................
Ba editing🙏
Oum ummeetarh
07041130088
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacceta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Page 87 & 88
Tun daga ranar da aka kawota cikin gidan a matsayin amaryar mai gida, har yau da take cikin kwana na biyar bata saka angon a idanunta ba, hakan kuma ko kaɗan bai dameta ba, harkar gabanta takeyi hankalinta kwance, ita rashin zuwan nashi ma ya mata daidai dan bata buƙatar ganin fuskar shi a halin yanzu.
Yau data kama kwana na hudu tun safe data tashi baƙi takeyi, yan ganin zuwa ɗaki, basu suka sarara mata ba sai wurin magarib, gyara gidanta tayi dukda ba wani datti yayi ba ta kunna burner turaren wuta take ko ina ya ɗauki kamshi,bayan ta idar da sallah isha'i ta shiga kitchen ta dafa jellop din couscous, daidai cikin ta, kwashe wa tayi a kula ta ajiye,ɗakinta ta koma tayi wanka tana fitowa gaban mirror ta tsaya tayi shafe shafenta, tare da feshe jikinta da daddaɗan turarukanta, masu shengen ɗaɗin kamshi da tsadar gaske, wasu sleeping dress ta ciro sababbi fil, ruwan light pink ta sanya, dogon gashinta dake daure da ribbon ta warware, dan bata iya kulle shi in zata kwanta damunta yakeyi, cumb ta dauka ta kwantar dashi, take kuwa ya sakko har kusan tsaki yar kafaɗunta, dan man leɓe ta shafa kaɗan, sanna ta fito ta nufo kitchen ta dauki couscous dinta ta hada da kwalin exoctic, da