Header Ads
Showing 9001 words to 12000 words out of 201974 words

Chapter 4 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1696

Ads at the middle of Article

tukkunna kafin kace zaka aurad da qannenka" ,,,, Sosa qeya yayi yace "nayi aure ke kuma nayi yaya dake matas, ai daga kanki na rude qofa "hajiya mama tace"ja'iri maji ma gani ai"


Duk wannan bidirin da akeyi asmah bata wajen, hasalima ko haduwa da aslam din batayiba tunda ya dawo tana jin qaran diran motocinda sukaje tarboshi ta shige toilet su kuma su batool basu jirata ba suka wuce abinsu, yanzuma da suke zaune basu lura bata wajenba , don hankalinsu gaba daya nakan yayan nasu, haka ya wuni tareda yan uwanshi, sai dare ya samu ya huta sosai .


Saida aslam ya kwana bakwai da dawowa amma bai hadu da asmah ba yana son ya tambaya ko anmaidata gidan kakantane bayan tafiyarshi, amma sai wani zuciyar yace mishi to kai ina ruwanka ma da wannan yarinyar mai kwala kwalan idanu kamar fitilan mota, kawai sai ya share zancen ya basar, sai a rana ta takwas da dawowarshi ya shiga part din mummy ya tarad da yan matan dukansu harda asmah da batason zai shigo yanzuba data gudu d'aki , gabanta ne yayi kwance kwance ya bada rassss, amma sai ta dake , gaishe shi suka shiga yi daya bayan daya ya, yana amsawa a dake kamar yadda ya saba amsa musu can baya, asmah ne qarshen gaishe shi,
Suna hada ido gabanshi ya shiga faduwa kamar yadda yakemai a can baya, harma yaso yafi na da , dakewa yaya ya amsa mata kamar yadda ya amsawa sauran wato a dake, tashi suka yi dukansu zasubar falon don ya hanasu zaman falon indai yana nan, sai kace falon shi,


daidai zasu hau step din da zai kaisu sama, da yake dakinsu na upstairs ne ya daka musu tsawa da cewa "ke zonan". Dukansu suka juyo amma sai yayi pointing din asmah yace "ke mai idon kamar na kwadi, dake nakeyi" dukkansu kallon asmah sukayi suna don sunsan ita yake kira mai idon kwadi, don sudai basu tabajin ya kira sunantaba saidai yace mai idon kwadi ko mai idon mazuru ko kuma yace mai idon mayu ,
Su kuma basuga iabin idanun asmah ba su haslima I don't a birge su yakeyi, ji sukeyi dama su keda irin idanunta,...


Sanin da tayi ita yake kira da mai idon kwadi ya sakata nufoshi zuciyarata kuwa sai bugawa takeyi da qarfin gaske, anashi bangaren ma hakane saidai daurewa yakeyi karta rainashi ,..
Tsayawa su zahra sukayi suka fasa tafiya wani mugun kallo ulya watsa musu, sum sum suka bace a falon,


Dan duqawa tayi a gabanshi tace "ya aslam gani " saida ya gama hararanta yace waike wacce irin mayya ce, Ashe dama har yanzu kina gidan nan baki koma gidan ubanki ba , hawayene suka fara tsere a fuskarta jin yadda ya ambaci marigarin babanta, dago dara daran idanunta da yake kira da idon mayu tayi ta sauke cikin nashi idon,, bugan da qirjinshi keyi ne ya ninku, fiskewa yayi yace "bazaki daina kallona da wadannan shegun idanuwan nakiba na mayu , saina tsokale miki su" saida ya gama zage tass ya qare da cewa "wlh na tsaneki ban yana tsanar wani Abu araina kamar yadda na ysaneki ba ". Tsaki yaja yaci gaba da cewa "shima wanna kinibabben tsohon mai shegen iyayin tsiya garin shegen kwashe kwashen shi na tsiya ya ya kwaso mana jaraba ".
Dan qurawa fuskarta ido yayi kafin ya tattaro miyan bakinshi ya tofa mata a fuska sannan yace "tashi ki bani guri kafin inyi qasa qasa dake a wajan nan,... mayya kawai nafi qarfinki wlh kurwata kurr "


Tashi tayi bata ko ganin gabanta ta wuce dakinsu, tana shiga ta fashe da wani irin kuka ta fada jikin batool data tarota su zahrama tasowa sukayi suka rirriqeta cikin kuka take fadin"na tsaneka bana bana sonka bana qaunarka, kuma bazan taba kaunarkaba har qarshen rayuwata,....na tsaneka!na tsneka!!na tsaneka aslammmm "
Ta qarashe maganar da qara fashewa da , rarrashinta suka shigayi donsu a ganin su dukanta yayi kamar yadda ya saba shiyasa take kukana nan






**********
Gaskiya fans in banga comment ba bazan sakeyin posting ba tunda naga kamar bakujin dadin labarin shikenan kawai gamma mu haqura,
Don in baku comment sai naga kamar Baku karantawa ne jikina duk yayi sanyi.


Tom gsky inbanga comment ba zan tsaya da typing ba gdy kadai nakeso ba wasuma ko godiyan basu iyayi,


To sai Ku zaba ko kuyi comment ko indaina typing 😡😡😡😡😡😡


Date: Oct 6, 2022


💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~


FREE BOOK




{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}




Page 23 & 24




Biki nata gabatowa yau saura kwana goma , kota ina sai shirye shirye akeyi , amma banda amarya Asmah , ta zama wata iri da ita kullum cikin kuka, amma batayi gaban mutanen gidan, shiga toilet takeyi ta kulle kanta taci kukanta ta koshi,......


Aslam ne ya fito daga part din Alhaji baba ranshi a hade da kaganshi kasan ranshi a mugun bace yake idanun shi yayi jajur.....direct part dinsu na samarin gidan ya nufa , da baya da baya ya fada kan daya da cikin manya manyan sofa set d'inda ke falon hannayenshi ya hada cikin juna ya dunqulesu da karfi...rintse ido yayi yana sakin wani zazzafan nunfashi ,......ba komai ne ya jefa shi cikin wannan yanayin ba sai d'an kace nace daya faru tsakanin shi da alhaji baba..... Aslam ya kafe kaida fata na cewa bazai auri Asmah ba nan dai alhaji baba ya shiga rarrashin shi, rufe ido Aslam yayi ya shiga zazzagawa alhaji baba rashin kunya yana gaggaya mishi maganganun dayasan zai fusata shi har yasa yayi fushi yace a fasa auren, saidai kuma hakan bata faruba don alhaji baba miqewa yayi ya wawwanke Aslam da zafafan maruka har guda har sau biyu sannan ya nuna shi da yatsa yace "kai Muhammad wlh karya kakeyi baka isa ba, ni zaka kawowa rashin mutunci," nuna shi da yatsa yayi yace "to ko ubanka abdullahi bai isa ba, ballantana kai qaramin alhaki, kuma ka sani aure ne sai an daura babu fashi, kaje kayi duk abinda zakayi, dai dai nake da kai , duk rashin kunyar dake damunka ni nan zan sauke maka shi"hmmm ran maza ya baci,.... Miqewa Aslam yayi yace "yace haka kace ko to shikenan" yayi kwafa ya fice daga falon..... Dalinlin shigar shi halin da yake ciki kenan, saqa ya shiga yi da warwara har ya samar wa kanshi famitan da yake ganin zata fille mishi, mataki biyu zai dauka idan ya kwada na farkon bai yuwuba, to zai aiwatar dana biyu Wanda zai girgiza kowa,


Asmah bata qara tsanar Aslam ba sai ranar da yasa mummy ta turo mishi ita part dinsu , mummy da kanta ta shiga har d'akinsu , ta sakata ta wanke fuska ta shafa hoda da 'kolli, Wanda rabonta da su tun ranar da zataje gidan alhaji Mallam , hijab ta zumbula har qasa ta dauki hanky tana tafe tana share hawaye da majina ,


mummy kam ganin ta tafi ba musu yasakata a ranta ta dinga yin hamdala tana murna gani take duk yadda akayi sun fara sasanta Kansu ne tunda gashi har yana kiranta su tattauna, Dan shi cema mummy yayi zasu Dan tattauna ne yaji shirye shiryen ta akan bikin,




Asmah na qara kusantar part dinsu Aslam gabanta na tsananta faduwa haka dai ta daure ta qarasa ta shiga falon da sallama a bakinta , ganin shi tayi zaune a falon sanye da qananan kaya yayi kyau sosai fuskarnan nashi a hade ba alamar mutunci, amma ita a idonta gani takeyi ba Wanda ya kaishi muni a lokacin , ko sallamarta bai amsaba ya watsa mata wani mugun kallo mai cike da tsana .....tsugunawa tayi daga can gefe ta rakube kamar tana jira ace tak ta ruga da gudu, watazabgegiyar wuqa Aslam ya zaro daga cikin gidanta mai shegen kaifi irin Wanda tsab za'a iya fille kan mutum dashi tashi daya, miqewa yayi daga inda yake zaune da wuqar a hannun tsirara , nufo inda take tsugune yayi gadan gadan , ganin haka yasa jikin Asmah ya fara rawa ta sadaqar yau kwananta ya qare,tasan tabbas Aslam zai iya mata abinda yafi kisa ma a yadda ya tsanetan nan, don haka ta fara maimaita Kalmar shahada a zuciyarta rintse idonta tayi da qarfi donma kar taga sanda zai caka mata , ji tayi yace cikin tsawa"keee mayya look up " dago da kanta tayi da sauri jikinta na rawa cike da tsoro , guntun murmushin mugunta ya saki saboda hango tsantsar tsoratan da tayi a cikin kwayar idonta, dama abinda yake son gani kenan kafin ya kora mata kyakkyawan warning din da yake son ya mata .........


Waning ya shiga kora mata da kashedin cewa , idan ta kuskura ta bari aka daura auren nan har aka kaita gidan shi a matsayin matarsa saiya yankata da wannan wuqar ya kasheta kowa ya huta, ya qarashe maganar yanayin alamar yankata da hannun shi,
nan ya tsatsara mata abinda zatayi da zaisa afasa auren. Kuma karta kuskura ta bari sunan shi ya fito, ya qare da zageta Tass kafin yace ta bace mai da gani ,.....
Aikam da sauri ta miqe ta fice daga part din cikin gudu gudu sauri sauri tana sharar hawaye, ta shige part din mummy, allah yasa mummy bata falo tana dakin daddy don haka direct dakinsu ya wuce ta fada kan gadonta tanata risgan kuka abin tausayi , su batool dake zaune zugum zugum suna zaman jiran dawowarta, dama tunda ta wuce jinin su a qumba yake, sai gani sukayi ta shigo da kuka dama sun tsammaci hakan, lalkashinta suka shiga yi cike da tausayawa, gani duk sun shiga damuwa yasa ta tsayar da kukanta, amma a ranta ta qudiri aniyar saidai Aslam ya kasheta amma baza taba aiwatar da. Abinda yace tayi ba, ta yarda in an kaita gidanshi ya yankata ,


Sannu bata hana zuwa yau gashi saura kwana uku daurin auren Aslam da Asmah , masha Allah gidan alhaji baba kam ya cika da jama'a baki na nesa dana kusa duk sun hallara , sai shirye shirye akeyi ,..


Duk wani gata daya kamata amarya yar gata ta samu Asmah ta sameshi , musamman ummi ta dauko wata mai gyaran amare tun daga suleja ,... Matar shahararriya ce sosai ta fanin gyaran amare ciki da bai , qyara Asmah ta shiga yi tsakanin da Allah don ba qaramin kudi ta amsa ba , saidai kuma amarya kwata kwata bata bata hadin kai yadda ya kamata don gaba days bata cikin walwala saidai tana qoqarin boyewa,


Ko program da aka tambayeta cewa tayi ita baza tayi komai ba, mami ne tace ba'ayi hakaba ita ta shirya mother's night ran alhamis ran juma'a ayi walima 4pm to 6pm a alkausar hall inyaso in andawo walima asa lalli washe gari a daura aure, haka ko akayi.......


Ta bangaren Aslam kam ganin shiru shiru ba a fasa biki ba saima qarin shirye shirye da akeyi, yasan lallai Asmah batayi abinda yasata ba, don inda tayi ya tabbatar alhaji baba zai dakatar da maganar auren nan , kwafa tayi cike da jin haushin duk wani mai hannun ciki wannan hadin including daddy da mummy , don haka ya qidiri aniyar aiwatar da mataki na biyu wanda yasan shine kankat, koda amir ya sameshi da maganar da maganar tsare tsare da gayyatar friend dinsu, hawa yayi kanshi da masifa yana neman ya sauke haushi a kanshi , qyale shi amir yayi yaci gaba da abinda ya kamata , ya gayyato friends dinsu tun daga na nan gida Nigeria dake mabanbantan garuruwa har na qasashen qetare da sukayi karatunsu tare, da kuma abokanan aikinsu, ba qaramin gayyata amir yayiba , har dinner yaso ya hada amma ganin aslam din yaqi bashi hadin kai yasa ya bar maganar dinner ,friend dinsu da amir ya gayyata suka fara isowa ,wasu kuma na kiran Aslam a waya suna mishi murna abin ba qaramin qona mai rai yakeyi ba , kowa ma haushi yake bashi mussamman ma amir dake ta wani zaqewa yana wani gayyata, ga cikin gida nan ma bai tsira ba daga ace ya bada kudin kaza sai ace ya kawo kaza, karshema ganin za'a dame shi ya tattara yanashi yanashi ya bar gidan ba tare da sanin kowaba , ya kama daki a hotel babu Wanda yasan inda yake, ya kuma qudiri aniyar yadda alhaji baba ya tilasta mishi auren wannan mayyar yarinyar mai idon mayu to wlh saiya kunyata shi tunda dai ya dakatar dashi, amma yaqi ji har yana marin shi , to yaje ya daura shi kuma yayi alkawarin ana daurawa zai saketa, yasan indai ya saketa aranar da aka daura musu aure ba shi kenan ba kunga dole a qyaleshi da wannan auren jarabar , qilama alhaji baba yayi fushi ya aurama amir ko kamal ita a ranar, hakan ce kuwa ta kasance don da wannan matakin aslam yayi amfani ya rattabawa asmah saki aranar da aka kaita gidanshi a matsayin matarsa zabin iyayensa






CIGABAN LABARI
Date: Oct 5, 2022


💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~


FREE BOOK


{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}




Page 21 & 22


Haka rayuwa yaci gaba da tafiya, tsakanin Aslam da Asmah kuwa babu abinda ya canja saima abinda ya qaru, tunda ya dawo walwalarta a gidan gaba d'aya ya ragu ba qaramin uzzurama rayuwarta yakeyi,




Saida ya cika wata uku cif da dawowa ya huta sosai har ya kama aiki a daya daga cikin kamfanonin Abba a matsayin general manager na kamfanin,
Alhaji baba ya kira dukkan yayanshi ya gaya musu qudirinsu shida aminshi Alhaji Mallam akan son had'a Asmah da Aslam aure,
Dukkan su sunyi farin ciki sosai saidai daddy ya kawo qorafin maganar karatun Asmah d'in, nan Alhaji baba ya sanar dasu yadda suka yi da Alhaji Mallam ranar da zai dauko Asmah na cewa baya son tayi karatun boko ya wuce secondary, dukkan su sun gamsu duba da yanayinsa na babban malamin addini, shike ma wasu fadan su aurad da yayan su in sun kai minzali kunga ai bazai bar nashi ba,


Sosai mummy taji d'ad'in wannan maganar don dama tunba yau ba takeda wannan buri ,


Nan Abba ya sake kawo maganar ko Aslam da Asmah din suna son juna , nan Alhaji baba yace ko basu son juna sai anyi wannan lamari saje can su daidaita, abar komai a hannunshi shi zai sanar musu da kanshi, nan dai meeting ya tashi kowa zuciyarshi fal farin ciki domin Asmah yarinyace nutsatsaya mai hankali da duk wasu iyaye na gari zasuso ta kasance surika a garesu


Alhaji baba da Aslam zaune suke a sitting room din Alhaji baba , fuskantarsa Alhaji baba yayi yace "Muhammad Aslam ba komai yasa na kiraka ba sai domin inason muyi wata magana dakai mai muhimmanci kuma na fahimtar juna, inason kabani aron dukkan hankalinka nan ,". gyada kai Aslam yayi yace "ina saurarenka alhaji" nan alhaji baba ya shiga sanar dashi abinda suka yanke nason hada shi aure da yar uwarshi Asmah cikin kwantar da murya alhaji baba yake mai magana da lalama,,... Tun kafin alhaji baba ya gama jawabinsa gaba daya aslam ya jiqe da zufa duk sanyi AC daya cika falon kuwa , qure alhaji baba yayi da ido kamar ranar ya fara ganin shi, daqar ya bude baki yace meyasa saini zaku aura ma ita meyasa bazaka aura mata wani cikin jikokinka ba , naga dai bani kadai bane jikan naka ai, to ni baba so akai kasuwa, idan hada zuri'ar Allah da annabi za ayi a aura mata kamal mana ko amir naga ai suma jikokin kane, kuma suma sun isa aure, to barin gaya maka gsky mallam tsoho bana son yarinyarnan bana kaunarta bata cikin tsarin matan da nake burin yin rayuwar aure dasu, don haka kayi gaggawar kwance wannan kullin da kayi , donni inada wacce nake son aura, wayyayya mai aji yar boko ba irin wannan kucakar yarinyar ba,"yana gama fadin haka ya miqe ya fice daga falon a fusace,
Alhaji baba da mamaki ya gama kasheshi a zaune kasa ma magana yayi tunda yake wani daga cikin jikokinshi bai taba mai rashin kunya irin Wanda Aslam ya masa yau ba , shiru alhaji baba ya zauna yanata saqe saqe a zuciyarshi kafin daga bisani ya saki wani qayatatccen murmushi a fuskarshi bayan ya samarwa kanshi mafita,


Aslam ranar daqar bacci ya daukesa bayan ya samarwa kanshi mafita yasan tunda alhaji baba ya fara wannan maganar to sai ya aiwatar,yasan tsohon da hegen nacin tsiya , don haka ya qudurci zai samu Asmah ya buga mata kyakkyawan warning akan karta kuskura ta amince da wannan hadin, yamasan ita karankanta baza tayi gogin amin cewa da auren shi ba,
Haka aka ci gaba da shirye shirye Asmah bata da labari , su zahra kam sunji lbr saidai ba wacce tayi qarfin halin sanarda asmah a cikinsu , don su karan Kansu ranar da suka fara ji abin ya matuqar firgitasu ya basu tsoro don su kadai sukasan irin tsanar da Asmah da ya Aslam sukai wa juna....


An tsaida lokacin biki nan da wata daya masu zuwa, alhaji baba ya tura Asmah gidan alhaji Mallam tace ta musu kwana biyu kuma ta duba jikin Mallam din Dan kwana biyu baiji dadi ba, da murnarta ta shiya kayanta don ta kwana biyu rabonta da gidan ,

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads