Header Ads
Showing 105001 words to 108000 words out of 201974 words

Chapter 36 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1746

Ads at the middle of Article

ta kasa Ce masa, shegen bakin nan tuni ya mutu muruss tunkan lamura suyi nisa, sai kerma da jikinta keyi, kamar maijin sanyi, ohoo shi baima kulaba, burin shi kawai ya ida nufin shi yau akanta, ya wanke mata wannan rashin kunyar dake dankare a brain dinta.




Fiffige kayan jikinta ya shiga yi yana wurgawa duk inda ya samu, saida ya maida ta haihuwar uwarta, sannan ya shiga bin ko ina na jikinta da sumba, ranar babu inda Dr bash bai tsotsa ba a jikin batool, ɗama yanada haushin ta sosai ba karamin tara ta yayi ba.


Kamin wani ɗan lokacin batool ita da gunki basu da babbanci ko yatsarta bata iya dagawa, banda kerma babu abinda takeyi, tuni ta dade da barin duniyar mu, wani irin dad'i take ji yana ratsa duk wani hudon gashi dake jikinta idanunta alumshe sai karbar zazzafan romance d'in da yake mata takeyi, bata dawo hayyacinta ba saida taji wani irin mugun zafi ya ziyarci ƙasanta, kwallah wani wahalallan kara tayi, kafin tasa hannu ta shiga ture shi, ganin bazai turu mata ba yasa ta shiga kai kulki da yakushi, ta ko,ina, amma a banza dan ko gezau baiyiba.


Dr bai sarara mata ba saida ya tabbatar ya maidata cikakkiyar mace, a wannan dare..............












Kai wlh batool baki jin magana ki bada kai da lalama, a biki a sannu kamar ko wacce amarya kinki gashi kinja an miki fyade, nidai Allah yasa ma ba tear😔
















Oum ummeetarh
07041130088










Share
And
Comment
Fisabillilah🙏
💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~






FREE BOOK






DAMA TA BIYU💖 ƘIRƘIRARREN LABARI NE MALLAKINA NE BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYAMIN LABARI TA KOWACCE SIGA BADA IZININA BA❌❌❌


(In 👂👂👂 yaji gangar jiki ya tsira 👌 a kiyaye pls)






{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiy,Allah kajiqan iyayen}














Tallah!💖 Tallah!!💖 Tallah!!!💖






Albishirinku manyan mata! ma'abota kwalliya da
_Rantsattsun lesussuka💃,
_Atamfofi manya da k'anana💃
_Galla gallan shaddodi manya da k'anana muna da su kowani iri💃
_Akwai kuma yadiddikan maza kamarsu koranza,plan yard dadai sauransu💃
_Munada mayafai, takalman maza da mata,sarqoqi, awarwaraye,da duk sauran nau'ikan kayan ado na maza da mata muna dasu 💃
Akanfaninmu na""R & U""Global Enterprise Dake Nan Garin Minna Niger State, saikunzu..........


Ga numbern mu kamar haka👇
08062160424
08066891424.....


Sayan day'a ko sari acikin farashi mai sauqi👌
Kubamu odern ku,danshine aikimmu akoda yaushe da yardar Allah........👌
Sai an gwada akansan na kwaraiiii💃💃💃.....
















Page 100












Kwanci ta tashi har yau Aslam da Asmah suna neman kwashe wata uku da aure, amma babu abinda ya canza a yanayin zaman su, Aslam duk abinda zaiyi dan ya burge Asmah yi yake da Wanda ta saka shi da wanda bata saka shiba, bangaren girki kuwa zuwa yanzu ko ita baza ta nuna mai komai ba, duk wani nau'in abincin da yasan tana so ya gama kware wa a iya girkashi.




Zuwa yanzu Asmah ta dan fara sake mai fuska saidai har zuwa lokacin kamal nanan a ranta, amma ta rage jin shi a ranta ba kamar da ba farko farkon aurensu, takan zauna suyi hira da Aslam, duk da rabin hirar shi keyi, takanyi mamakin yanda ya Aslam ya koma mai surutu haka lokaci guda, kodai dama yana da surutun girman kai ne ke hana shi yi, yata wani ɗaɗɗaure musu fuska, yana musu muzurai.




Allah sarki abinda Asmah bata sani ba, Aslam bashi da surutu soyyaya ce ta mai kamun kazar kuku, ita kaɗai yake iya sake baki yama magana sosai da sosai, ita kaɗai ne yake iya sake ma fuska yayta mata murmushi kamar wani gaula, ita kaɗai ne yake iya ɓare baki yayta dariya a gabanta kamar sabon kamu, a gabanta yakan kasa controlling kanshi, yakan rasa nutsuwar shi idan yana tare da ita, wata irin soyyaya yake mata kamar wacce ta asirce shi, kuma ba ɗaya kanwar biyu, kamun Allah ne kawai daya fi na mutum.




Yau data kama ranar Friday, misalin karfe 9am Asmah ne zaune a bakin bed dinta ta caba kwalliyar ta cikin kananan kaya Riga da skirt yan kanti, skirt d'in street ne me tsagu ta baya black colour, daya matseta tsam ya fito mata da shape sosai, rigarta kuma yellow ne mai shegen kyau, dan Cass dashi, kanta kuwa ta nada wani irin turban mai kyau na yayi, cikin irin wanda take da videos dinsu a wayarta, haka takeyi kullum aikinta kenan ta caba ado mai kyau da tsari abinta, bata aikin komai daga kwanciya sai kwanciya, ko plate sai taga daman daukewa idan taci abinci, Allah sarki Aslam bawan Allah haka zaita binta da kallo yana lasar lips, gashi ko hannunta bashi da zarran taɓawa




Wannan ne karo na biyar data dago kai ta dubi agogon dake manne a Wall din dakin, fuskar ta cike take matukar da damuwa, a fili ta furta "wai mai ke faruwa ne yau, har karfe tara banji motsin shiba, anya kuwa lafiya hankalina ya kasa kwanciya ga shi gabana sai faduwa yake," daga hannunta tayi sama tace "ya rabbi kasa lafiya kalau" komawa tayi ta kwanta ta rintse ido, a zuciyarta tace bari na dan kara bashi lokaci na gani ko yau bacci ne ya kwashe har zuwa wannan lokacin bai nemeni ba,can kuma tace to kodai bai samu yimin Masan da mukayi zai min da safe bane yasa yaki nemana har yanzu, haka dai tayita sake sakenta ita kadai duk zuciyarta ba dadi.




Allah sarki Aslam jiki da jini, jiya har gurin karfe goman dare suna tare da Asmah a falo suna kallo, lafiyar shi qalau, ita tace ta fara gajiya da kallon ta mike, ganin haka yasa ya kalleta yace"mrs Asmah kardai har kin tashi" tana mika da hamma tace "eh wlh bacci nakeji," tashi yayi yana cewa "OK ba damuwa Allah ya tashe mu lafiya, muje na rakaki dakin ki " bata musa ba ta shiga gaba yana bayanta har kofar dakin ta, har ta kama handle kofar zata shige ta tsinci muryar shi yana cewa "Am mrs Asmah nace da safe mai zan girka miki na breakfast" murmushi ta saki ba tare data juyo ba tace "umm masa da miyar taushe" dan zuwa yanzu Aslam ya kware a wurin iya soya masa, badan kartayi karyaba da sai tace tunda take bata taba cin masa mai dadin nashi ba.


Dariya ya kwashe dashi yace "ai dama saida na ayyana a zuciyata yanzu zaki ce masa da miyar taushe,to karki damu gobe insha Allah idan muna da rai da lafiya, zaki farka barci ne ki tarad da masan ki yayi ready" juyowa tayi ta kalleshi, tsintar kanta tayi da sakar mai murmushi tare da cewa "thanks, gud 9t" shima murmushin ya mayar mata da martani tare da cewa "bye kiyi mafalkina kinji" tafin hannun ya kai saitin bakin shi ya sumbata muuaah💋 sannan ya hura mata.


Da sauri yasa kai ya wuce, murmushi tayi, sannan ta juya ta shige dakinta cike da kewar shi, haka kawai takeji kamar kar su rabu.




Aslam falo ya koma ya kashe tv da sauran abubuwan daya kamata a kashe idan za'a kwanta bacci, daganan kuma dakin shi ya nufa alwalan kwanciya bacci yayi ya shirya cikin kayan baccin shi, kashe wuta yayi ya haye godo yaja duvet ya gudundune bayan yayi adduan baccin ya shafe jikin shi.




Kewar tane yaji ya lullubeshi kusan kullum dama haka yake fama indai suka rabu yazo kwanciya bacci, pillow ya dauka ya rungume kamar pillow ne Asmah, daya hannun kuma ya lalubi wayar shi ya dauko hotunan ta da yake yawan daukarta ba tare da ta Sani ba, ya shiga kallo yanata sakin murmushi abin tausayi, shifa indai zai zauna da ita a haka yana ganin ta kullum yana mata hidima ya isheshi rayuwar duniya, tunda ya sameta har yau ciwon shi bai sake tashi ba , kai daker ma idan bai rabu da ciwon kwata kwata ba don dama Dr James yace idan dai ya samu abinda yake so zai iya rabuwa da ciwon baki daya.




Haka yana kallon hotunan ta har barci ya rinjaye shi, kifa wayar yayi akan kirjinshi ba tare da ya fita daga wurin hotunan ba.




Allah mai girma da buwaya cikin wannan daran ya saukar ma Aslam da wani irin zazzafan fever, ya kwanta lau abinshi, amma ya farka da ciwo, haka yata fama cikin daren nan, sai makyarkyatan sanyi yakeyi, ga jikinshi ya dau zafi, bai iya daga koda dan yatsan shi, haka yata fama har asuba ko sallah bai iya tashi yayi ba, sai bayan asuba wani wahalallan barci ya kwashe, hatta numfashin da yake fitar wa na hucin zafi ne, bai farka ba har wurin karfe goma safe.






Asmah tana cen cikin damuwar rashin ganin Aslam, tun bakwai da wani abu take ta saka ran ganin shi kamar yadda ya saba, saidai shiru har gurin takwas duk bata damu ba, ganin tara yayi yasa ta fara shan jinin jikinta ta shiga damuwa da tunanin anya lafiya kuwa, ta tashi tayi wanka ta shirya ta share dakin ta, ta koma ta kwanta har zuwa lokacin shiru, bacci ne yadan kwashe ta adan kishingiɗar da tayi, ta kishingiɗa ne da damuwan rashin ganin Aslam, batasan yadda akayi bacci ya kwashe ta ba, cikin wannan dan baccin da baifi na 30minutes ba tayi mafarkin Aslam yana cikin mawuyacin hali gashi nan kudundune ko yatsar shi bai iya dagawa, a firgice ta farka ta shiga jero addu'o'i da duk yazo bakinta, durowa tayi daga kan gadonta da sauri da niyyar taje ta duba shi, hankalin ta zaifi kwanciya, zuciyar ta ce ta shiga ce mata meye haka kikeyi ne wai kan Aslam duk kinbi kin ruda kanki, kin saka damuwar shi a gaba har kina wani mafarkin shi, kilama babu abinda ya same shi kin saka damuwar shi a rai har yana sakaki mafarkai barkatai, komawa tayi ta zauna jiki a sanyaye.




Can dai ta kasa hakura ta mike ta fice daga dakin da sauri bata tsaya ta biyem.a wasu wasin zuciyarta ba, falo ta fara dubawa bashi nan daga nan ta nufi kitchen babu ma alamar wani ya shiga kitchen din dan yana tsab yadda ta barshi jiya, dafe goshin ta tayi a fili ta furta "ina Mr Aslam ya shiga ne wai, to kodai ya fita ne, bai dawo ba" nan tayi na'am da cewa fita yayi kila, kitchen ta shiga ta Samar ma kanta abin tabawa, gani tayi bazata iya zaman falon ba hakan yasa ta hada abincin ta a tray ta dauka ta nufi hanyar dakin ta, tazo gifta daidai wani bedroom Wanda sai an wuce shi za'a isa nata taji kamar kakarin amai, bata San takamaimai wani daki Aslam yake kwana ba a gidan tunda ba shiga lamarin shi takeyi ba shike shiga nata.




Kara kasa kunne tayi dan ta tabbatar kakarin ne kokuwa kunnen ta ne ya jiyo mata karya, still ta karajin Wanda yafi na dazu karfi ma, da sauri ta tura kofar bedroom din da tray dake hannunta, dakin da duhu sosai laluabar wuri tayi ta ajiye tray dake hannunta, sannan ta kuma lalubar makunnin wuta ta kunna,take haske ya gauraye dakin.


Idanunta ne ya sauka a kanshi, daga kwancen da yake yadan yi kokari ya karkato da kanshi gefen bed din yanata kelaya amai a kasa, zaro idanu tayi tana furta Kalmar innalillahi wainnailaihi rajiun, kafin kuma ta kwasa da gudu ta karasa gareshi batayi wata wata ba ta haura kan bed d'in ta talloboshi jikinta, nan yaci gaba da kelaya a man ajikinsu ita dashi gaba daya,a mai yakeyi sosai tun yanayin na abincin dake cikin shi har ya kamo kakarin kawai yakeyi ba komai a cikin.




Da'ker suka samu kakarin ya tsagaita, sai lokacin ma ta kula da yadda jikinshi ya dau zafi zau, hankalin ta yakai matukar kololuwar tashi, yanzu ya zatayi wani irin taimakon gaggawa ya kamata ta bashi.




Aslam kam jinshi a jikin mutum saiya kara narkewa gaba daya ya sake mata dukkan nauyin shi dukda ba cikin haiyacinsa yake ba, lallabawa tayi da'ker ta samu ta zare jikinta daga nashi ta ture shi gefe, saukowa tayi ta fita daga dakin jim kadan ta dawo ta canja kayan jikin ta daya baci,hannunta dauke da kayan share share dangin su mopa da tsintsiya, aman dake kasa ta fara kwashewa ta gyara wurin tsab tayi mopping, kan gadon ta koma ta tattare bargon ta nannadeshi tayi toilet dashi ta sakashi a cikin washing machine, ta kunna dawowa tayi tana tuananin ta ina zata fara raba shi da kayan jikinshi shi, daya baci da a mai, tsayawa tayi na kusan minti biyu tana sake sake kafin kuma daga bisani tayi huɓɓasa ta haura kan gadon, yana nan kwance rigingine idanunshi a lumshe yana dauke wani irin nunfashin wahala, ba bacci yake yi ba idanun shi biyu amma baya cikin haiyacinsa.




A hankali ta mika hannunta ta shiga balle maballan rigar baccin shi ta gaba, take faffadan kirjin shi mai dauke da kyakkyawan kwantaccen suma ya bayyana, da sauri ta dauke idanunta daga kallon kirginshi, saidai kuma cikin rashin sa'a idanunta ya kuma sauka a kan cikin shi, wandonshi yadan ja kasa hakan yasa har saman marar shi ta gani, rintse idanunta ta tayi tana maimaita innalillahi wainnailaihi rajiun, take jikinta ya fara dan kerma, a haka idanu a rintse ta samu ta gama cire mai rigar gaba daya, wandon dama bai baci ba saboda duvet din daya lullubeshi shi.




Har zuwa lokacin ba abinda ya ragu daga zazzafan fever dake damun shi, tsayawa tayi akanshi idanunta sun cika da kwallah, yanzu meya kamata tamai dan ya samu sauki take zuciyarta ta bata ansa da ki nemo Dr yazo ya duba shi mana, sai lokacin ta tunada abinda ya kamata tayi kenan tun kafin ta tsaya share a mai, tunani ta shigayi yanzu wani likita zata kira ita bata San wani likita ba, tana cikin wannan sake saken ne idanunta ya sauka akan handset dinshi da rabin shi ke karkashin Aslam ma'ana ya kwanta akan wayar sobada dama wayar nakan kirjinshi barci ya kwashe shi.


Janyo wayar tayi cikin sa'a babu security ko daya, yana nan a yadda yake wato a wajen gallery, da hoton ta ta fara cin karo cike da mamakin take bin hoton da kallo, tabas idan ba idanunta sun mata karya bane hotone da aka daukeshi anan gidan, ajiye mamakin ta tayi a gefe tuna abida ke gabanta, ta fita daga gallery din ta shiga contact, letter D ta danna take sunan Dr James ya bayyana a farko, dan haka bata tsaya duba sauran lambobin ba ta antaya mai kira.






Dr James a na ɗaga wayar yace "hi Mr Aslam" da sauri Asmah ta katseshi da cewa "ba shi bane Dr matar shi ne" Dr James yace "oh madam, lafiya kuwa meke faruwa ne" dan tun a muryarta ya fahimci akwai matsala Asmah ta bashi amsa da cewa"Dr Mr Aslam ne baida lafiya mun tashi da safe na same shi cikin matasanancin fever" Dr yace"Jesus! yanzu kuna ina ne" Asmah tace "gidan shi dake London road," Dr yace"OK ganin nan zuwa yanzu ki kwantar da hankalin ki madam, komai zai daidaita".




Bayan sun gama waya komawa tayi ta tsuguna a bakin bed din tana karema kyakkyawan fuskar shi kallo cike da tsantsar tausaya, idanunta tuni sun fara zubar kwallah ba tare da ta sani ba.




Tana a haka taji diran motar Dr a farfajiyar gidan, da sauri ta nufi falo tana isowa yana danna doorbell, har tana hadawa da gudu gudu ta karasa ta bude mai kofa, kwata kwata ta manta da sigar dake jikinta saida taga Dr na binta da kallo sama da kasa, yasa ta sha jinin jikinta, daurewa tayi ta nuna mai dakin da Aslam yake bayan sun gaisa,ita bata shiga ba sai ta zarce dakinta ta zumbulo dogon hijabi ta dawo, koda ta shigo tuni Dr James ya dukufa akan Aslam yana checking dinshi, neman guri tayi nesa dasu kadan ta tsaya.






Minti ashirin Dr James ya dauka kafin ya dago ya kalleta yace "madam karki damu fever ce kawai irin wanda stress ke haifarwa, yanzu zan daura mai drip na bashi injection da magunguna zazzabin zai sauka" gyada mai kai kawai tayi.




Cikin ten minutes ya gama aiwatar da duk abinda yace, magungunan ya dauko ya mikawa Asmah , tare da gaya mata yanda zai dinga sha, nuna mata yadda akeyi cire drip yayi, yace idan ruwan ya kare ta cire mai , ya samu ruwan dumi yayi wanka yasha ko tea ne sannan yasa magani, insha Allah zaiji sauki.




Godiya ta shiga yiwa Dr dake ta faman tartare kayan aikinshi a jaka zai wuce.




Bayan tafiyar Dr James zama tayi ta rafka tagumi hannu bibbiyu ta saka fuskar Aslam daya koma bacci a gaba tana kallo, tuni tama manta da breakfast dinta ko yunwar ma bata ji, a haka har ruwan ya kare, daidai nan kuma Aslam ya farka wannan karan yadan fara dawowa haiyacinsa saboda alluran da Dr yamai masu kyau ne sosai suna matukar yin aiki cikin kankanin lokaci.




Da sauri ta matsa kusa dashi tana mishi sannu, juyowa yayi ya kalleta duk da halin ciwon da yake ciki hakan bai hanashi sakar mata murmushi ba, cikin jin daɗin ya fara samun sauki tunda gashi har yana murmushi tace"alhmdllh sannu Mr Aslam bari na hada maka ruwan dumi kayi wanka kamar yadda Dr yace" bata jira amsarshi ba ta fada toilet ta hada mai ruwan wankan, fitowa tayi , yana kwance yadda ta barshi idanunshi akan kofar toilet din , don tunda ya rakata da kallo ta shige, bai dauke idanunshi a wurin ba fitowa tayi still ya binta da kallo, karasowa tayi gabanshi tana cewa "na hada maka ruwan ka daure ka tashi kaje kayi wankan" shiru taji ba'a amsata ba hakan yasa ta kalle shi, girgiza mata kai yayi yana murmushi ta gane yana nufin bazai iya tashi bane, gani tayi ya miko mata hannu alamarta taimake shi ya tashi, mika hannu tayi ta kamo nashi tanaja yunkurawa daya sai gata a jikinshi kane kane ta fado, baida lafiya jikinshi ya sake ya mata nauyi baza ta iya dagashi ba, shi kuma

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads