Showing 171001 words to 174000 words out of 201974 words
Chapter 58 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
sake bijera mana ba, baka isa ka sake bijere wa umarni mu ba, domin mu muka haife ka ba kai ka haife mu ba, wanda kayi a baya ya isa haka, kuma zainab zata koma dakin ta, ta share ta zauna a yau kamar yadda Alhaji ya fada, ni kuma umarni nake baka, kada kuma ka bari naji wani Abu mara kyau ya taso daga ɓangaren ka, zan saka idanu sosai a cikin gidan ka." Kallon zee yayi dake ta risgar kuka mara sauti yace "anjima ki shirya zan mayar dake ɗakin ki da kaina, a karo biyu, idan ya isa shi ɗan halak ne ya hanaki shiga." Yana kaiwa nan yasa kai yabar falon yana huci, duk shiru sukayi ana sauraren daddy an rasa mai karfin halin bashi hakuri, dama duk wurin Abba ne zai iya, kuma shima a wannan karon yana supporting din daddy akan hakan domin shima ranshi ya baci sosai akan abin da Aslam din yayi, mikewa mummy tayi itama ta kalle shi tace"daddyn ku ya fanshe ni ya gama fadin abin da duk zan fada, ga zainab nan ta dawo zata zauna a dakin ta, a bisa umarnin mu, idan kuma itama ma zaka sake ta ne to bismillah dama ba yau ka fara ba, Amma ka sani muddin kayi mata wani abu mara daɗi, zaka haɗu da matsanancin fushi na irin wadda baka taba gani ba." Ita ma bin bayan daddy tayi ranta a bace ba tare da ta kalli kowa ba a falon.
Shiru falon ya dauka babu mai koda kwakwkwaran motsi ne.kowa ka kalla a lokacin fuskar sa a jagule, musamman Aslam da idanun shi sukayi wani irin jazur jijiyoyin kanshi suka fito, hankalin shi ya tashi, ba wai maganar komawar zee gidan shi bane ya daga mishi hankali, illah tsananin fushin da ya gani akan fuskar iyayen shi, abu na biyu kuma Asmah, yana tausayin ta, ita din marainiya ce ita din abin tausayi ce, ga halin da take ciki na rashin samun haihuwa, sannan kuma a dauko zee a ce su zauna a tare, shi kadai yasan wacece zee, domin shi ya zauna da ita a baya, yasan abin da zata iya aikatawa da wanda baza ta iya ba, duk wannan kukan da ta keyi tana cewa ta shiryu menene da menene shifa ba yarda yayi ba, abu daya zaisa ya yarda shine idan ya gani a aika ce amma wai dan wannan kururuwar nata duk bai dame shi ba, sannan kuma ga matsalar mahaifinta, shin yanzu da sanin shi ta taho gare shi da yardan shi da amincewar shi kokuwa A'a gaban kanta tayi, domin a wannan karan bazai juri cin zarafi daga gareshi ba sai dai ayi wacce za'ayi shi yasa tun forko baiso ya karbe ta ba, dan shi kadai ya hango abin da ya hango amma yanzu kam alkalami ya riga ya bushe.
Muryar hajiya mama ne ya katse mishi tunani, "Muhammad, nima dai yau zan magantu akan sha'anin rayuwar ka a karo na farko, kada ka kuskura kace zakayi musu ko wani Abu akan wannan hukuncin da mahaifan ka suka tsayar, kuma ma in banda abin ka Muhammad ai nasan kai karan kanka har zuciyar ka baza kace baka kaunar Zainab ba, domin kuwa soyayyar farko yana da tasirin da ba kasafai ake ayi cireshi a zuciya ba, ɓacin raine kawai yasa kake ganin kamar ka tsane ta baka sonta har kake gani baza ka iya zama da ita a karo na biyu ba, nidai rokon da zan maka shine ka bata *dama ta biyu*, kamar yadda ta nema, na tabbatar zaka sha mamaki, to waima banda abinka Muhammad ai kana son zainab har yanzu tunda har ka kaunaci abin da ya fito daga tsatson ta, a duk sanda mace ta fita daga zuciyar namiji yakan tsane komai daya shafe ta ciki harda yayan da suka Haifa a tare, ka daure ka bata *dama ta biyu* na tabbatar zakayi alfahari da ita a gaba, nasan duk wannan kauke kaucen kanayi ne saboda Asma'u, to karka damu Asma'u yarinya ce natsattsiya mai hankali da hangen nesa, ina mai tabbaatar maka baza ka samu matsala da ita ba, ka haɗa kan matan ka kuje ku zauna in sha Allah wata rana sai kayi alfahi da hakan." Nan kuma ta dawo da hankalin ta kan Asmah da zee, ta shiga yi musu nasiha mai ratsa zuciya mai kashe dukkan gaɓɓai mai tausasa zuciyar mutum duk karfin ta, falon yayi tsit bakajin komai sai shehsshekan kukan Asmah da zee, hajiya mama ta ɗaure su da jijiyoyin jikin su. Ba iya su kadai nasihar ta taba ba hatta mami da Abba dasu Amir sai da jikin su ya mutu, sai da ta tabbatar sunyi laushi, sannan ta kare da yi musu addu'an zaman lafiya da samun zuri'a dayyiba, bayan ta gama ta mike a hankali cike da nutsuwa tabi bayan mijin ta.
Bayan tafiyar hajiya mama, Abba ne ya daura da nashi, kafin a karshe ya rufe taron gaba daya da addu'a.
Mikewa Asmah tayi tana share hawaye ta fice daga falon, ba tare da ta ko kalli inda Aslam yake ba, da kallo suka bita har mami ta buɗe baki zata tsayar da ita Abba ya daga mata hannu, shima Aslam yunkurin bin bayan ta yayi, still shima Abba ya dakatar da shi badan yaso ba ya dawo ya zauna, idanun shi a kanta har ta fice daga falon.
Tafe take tana harɗe hanya kamar wacce tasha ta maku. Can cikin zuciyar tane take ji yana mata ciwo, da ace ita butulu ce da ta buɗe baki a yau tace su mummy da da daddy dama gaba daya ahalin nan basa kaunar ta, sai dai ita karan kanta ta sani idan ta fadi haka sai Allah ya tuhume ta a ranar gobe kiyama, ina zata saka zuciyar ta ne taji sanyi, kishin mijin ta take, tausayin kanta take, babban tashin hankalin ta ɗaya, shin menene makomar ta, a nan gaba a gurin Aslam, tunda gashi ya dawo da uwar gidan shi, uwar danshi, first luv dinshi, wacce take da mahaifan Haifa mishi ƴaƴa, wacce zata iya cika mishi burin shi na duniya, ta sani dole nan gaba Aslam ya ƙi ta ya komawa matar sa saboda ita ɗin ce take da abin da zata iya saka shi farin ciki da shi.
Da wannan tunanin ta ƙaraso falon mummy ba tare da ta sani ba, dan gaba daya idanun ta sun rufe bata ganin gaban ta. Mummy dake nan tsaye a falo ta kasa zaune ta kasa tsaye sai safa da marwa takeyi, jin motsin mutum a kofa ya saka ta saurin juyowa ganin Asmah ce ya saka ta saurin nufar ta ta rungume ta a jikin tsam kamar wacce za'a kwace mata ita, jinta a jikin mutum wanda ta tabbatar mummy ce yasa ta fashe wa da wani irin kuka mai ban tausayi, ita kanta mummy hawaye ne ke ziraro mata, ba kowa zai fahimci ciwon Asmah ba sai wanda ya taba riskar kanshi a irin halin da ta riski kanta a yanzu, ita din abin tausayi ce a halin yanzu, tafi kowa jin zafin wannan lamarin domin kuwa ita uwace ga Asmah, dole duk wata uwa ta gari a lokacin da ɗiyar ta shiga damuwa tafi ɗiyar shiga damuwa, haihuwar Asmah ne kawai bata yi ba amma a halin yanzu zata iya rantsuwa babu wanda ya kaita jin ciwon Asmah a zuciyar ta, ta goyi bayan zee ta dawo ne badan wani manufa ba sai dai sani da tayi cewa ɗa na kowa ne kuma ko ba komai suma sun aurar a wani gidan baza su so haka ya kasance da nasu ƴaƴan a ki karbar su ba, sannan bugu da ƙari tayi amfani da Karin maganar nan ta hausawa da su ke cewa kaso naka duniya ta ki shi, ka ki naka duniya ta so shi.
Muryar Asmah ne ya katse mata tunani, cikin kuka tace "mummy shike nan zan rasa ya Aslam, shike nan lokacin rabuwar mu ya gabato,mummy ya Aslam zai juya min baya ko?"goge hawayen ta tayi kafin kafin ta tausasa muryar ta tace"wa ya gaya miki haka Asmah? Kar na sake ji kin fadi haka Aslam bazai taba juya miki baya ba domin kuwa yana tsananin kaunar ki."tace "Mummy tsoro nake ji gabana faduwa yake yi." Mummy tace "Kiyi ta maimaita inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, zaki samu sauki a zuciyar ki." Gyada kai kawai ta ringayi tare da sauke wasu irin ajiyar zuciya, dago ta mummy tayi daga jikin ta, ta tallaɓe ta nufi ɗakin ta da ita. Zaunar da ita tayi a bakin bed ta taba jikin ta zafi zau kuwa daman tasan za'a rina, magani ta kalli ta bata dakyar ta haɗiya tana gama sha sai amai shaa, cike da tausayawa mummy ta tallabe ta, har ta gama a mayar da duk abin da taci, toilet ta kaita ta kuskure baki ta wanke mata fuska, ta zame mata dan kwali ta zuba mata ruwan sanyi a kanta, sannan ta tallabo ta ta dawo da ita dakin ta kwantar da ita akan bed ta gyara wurin, ko kafin ta gama tsabtace gurin bacci ya kwashe ta, sauke ajiyar zuciya mummy tayi tare da rage mata karfi Ac ta fice daga dakin ta ja mata kofa a hankali.
A tare Aslam dasu Amir suka fito daga falon Alhaji baba, Kamal yana sauri zai koma gurin aiki don dama excuse ya dauka, hakan yasa bai shiga cikin gidan ba ya fada motar shi jiki a sanyaye yabar gidan, wannan abin da ya faru ya taba mai zuciya sosai, kwarai ya tausaya wa Asmah.
Amir kuwa bayan Aslam yabi domin ganin duk yadda ya duburbuce ya susuce a halin yanzu yana bukatar mai kwabatar mishi da hankali, binshi yayi da sauri ya kama hannun shi hakan yasa Aslam sauke mishi jajayen idanun shi, gyada mishi kai Amir yayi kafin a hankali ya shiga jan shi suka fara tafiya, parking lot suka iso ya buɗe motar shi gidan baya ya ce ma Aslam "Bismillah bro magana nake so muyi." Shiga motar yayi Amir ya maida kofar ya rufe tare da zagayowa ta daya side din shima ya shiga ya zauna tare da rufe kofar, a tsanake ya kira sunan Aslam cikin kamewa hakan ya tabbatar wa da Aslam cewa maganar da zai fada mishi mai muhimman ci ne, shima tattara dukkan hankali da nutsuwa shi yayi ya baiwa Amir din, domin a halin yanzu yana bukatar wanda zai rarrashe ya kwantar mashi da hankali shi ya bashi shawara ta gari, kuma yana da tabbacin zai samu duka wandannan abubuwan daga dan uwan shi abokin shi yayan shi Amir.
A can falon Alhaji baba kuwa zee mami da Abba ne kawai suka rage.
Abba kam dan nasiha ya ƴara ma zee din ita kadai, akan cewa ta kwantar da hankalin ta kar abin da Aslam ya faɗa ya firgita ta, shima ɓacin raine ya saka ya faɗi haka taje ta kwantar da kai tayi ladabi tayi biyayya, ta nuna mishi da gaske ita ɗin ta canja daga yadda ya santa a baya, in sha Allah komai zai daidaita, ta toshe kunnen ta ta rintse idanun ta danne zuciyar ta akan dukkan abin da zata fuskan ta daga wurin Aslam, idan tayi hakuri naɗan wani lokaci komai mai wucewa ne. Nutsuwa tayi ta bada dukkan hankalin ta tana sauraren nasihar Abba, bayan ya gama tashi yayi ya fice daga falon nan mami ma ta daura da nata. Daga karshe kuma suka baro part din alhaji baba suka dawo na mami.
Kusan awa daya suka kwashe yana bashi baki tare da kwantar mai da hankali yana kuma kara koya mai dabarun yadda zai zauna dasu su biyu ba tare da ya shiga hakkin daya ba, sai da Amir ya tabbatar ya kwantar mai da hankali, daga karshe ya dinga zolayar shi har sai da yaga yayi murmushi, kafin ya barshi, nan sukayi sallama, Amir ya tafi gidan shi yayin da Aslam ya nufi part ɗin mummy, domin duk abin da yake yi karfin hali ne kawai saboda bai San halin da take ciki ba.
Koda ya shiga bai ganta ba mummy kawai ya samu a falo, zama yayi suka gaisa ba wani sakin fuska, daga gaisuwar kuwa duk zama sukayi shiru, yana ta zuba idon ganin ta ina zata fito shiru gashi har yana neman kwashe awa ɗaya a zaune, can dai ya da ya gaji, yace "Mummy husnah tana ciki ne ina son tazo mu wuce." A dake tace "eh tana ciki amma yanzu tana barci ka je kawai bayan isha'i sai ka dawo ka dauke ta." Tana gama faɗin haka ta mike tayi ciki domin ta gama abin da ya zaunar da ita a falon.
Badan yaso ba dole ya sa kai yabar gidan domin dai mummy bata daukar wargi, balle yadda ranta ke bace yau gaba daya......
Oum Ummeetarh
07041130088
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}
Page 126
Kamar yadda daddy ya faɗa karfe biyar na yamma daidai ya sauke zee a farfajiyar gidan Aslam, makulli part ɗinta daya amsa a hannu Aslam ɗazu ya damka mata, har kasa ta tsuguna cike da ladabi tana godiya, yace "Ba komai zainab ɗa na kowa ne, Allah ubangiji ya Baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba." Ta na tsaye har motar shi ya bar harabar gidan, mai gadi ya maida get ya rufe. mai da kallon ta tayi kan ɗaya plat ɗin da yake nan sak irin nata, ji tayi wasu siraran hawaye sun ziraro mata ko shakka babu nan ne part ɗin Asmah, compound ɗin gidan tabi da kallo tsab tsab dashi yana nan yadda ta sanshi a baya, sai dai a yanzu yafi da kyau sosai nisa ba kusa ba, domin ga dukkan alamau yana samun gyara da kulawa fiye da lokacin da ta ke gidan a baya.
Jiki a sanyaye ta ƙarasa gaban na ta part ɗin ta saka makullin da daddy ya ba ta buɗe, sai da ta yi addu'o'i sosai sannan ta kama hannun little suka shiga da sallaman ta a bayyya ne. Falon dumɗum da dubu ba haske kuma ko ina a kukkule, makunnin wuta ta laluba ta kunna take kuwa haske ya gauraye mai falon, bin ko ina ta shiga yi da kallo, take ranar ta, ta karshe a falon ya shiga dawo mata fresh a kwakwalwar ta, ranar da take ta malelekuwa a tsakiyar falon nan jini na kwaran ya daga jikin ta, ranar da Aslam ɗin ta ya saka hannu ya buge ta kamar yana bugun kato tsaran shi, kallon little tayi da yake ta wasan shi, a falon babu damuwar komai a tare da shi, samun kanta tayi da durkushewa a hankali a gurin da take tsaye tare da fashe wa da kuka tunawa d tayi duk abubuwan da suka faru akan zuwan shi doron duniya ne, gashi karshe duk gwagwarmayar da aka sha sai da ya shaki iskan duniya, tayi imani da maganar magaba ta da suke cewa, a duniyar nan babu wanda ya isa ya kashe wani ruhi face sai idan lokacin wannan ruhi yayi, sai dai kawai mutum ya zama sanadi amma badai shi ya kashe shi ba, Allah ne mai kashe wa kuma mai rayawa a duk sanda yaso, shi yake fitar da rayayye cikin matatce haka nan shi yake fitar da matatte cikin rayyaye kamar yadda ya faɗa a cikin alkur,ani mai tsarki.
Ta kusa kwashe 30 minutes a haka sai kuka take tana ƙara tunani da miƴa wuya akan lamarin ubangiji, sai da little ya gaji da wasan shi ya dawo ya faɗa jikin ta yana ce mata zai sha ruwa sannan ta dawo hayyacin ta.
Ko ina yayi kura a part ɗin tun daga kan falo kitchen dakunan barci toilets da sauran su, gashi kuma yamma yayi, hakan yasa cikin sauri ta kau da duk wani tunani da damuwan ta gefe, cike da himma ta fara gyara falukan ta cikin kankanin lokaci ta ƙalƙale shi fess nan kuma ta koma kitchen shima haka tamai ta goge na goge wa ta wanke na wanke wa, dakin barcin ta ta shiga yana nan yadda ta barshi ga kayayyakin ta nan ba'a kawar da komai ba, toilet ta shiga ta fara wanke wa sannan ta dawo dakin shima, ko kafin ta gama duk wadannan abubuwan magrib ta gaba to alwala ta daura, tayi sallah, sannan ta duba store kayan abincin ta data bari na nan yadda ta barsu komai akwai amma bata jin zata iya cin komai a cikin suu, ga kuma little dake ta dan mata kukan rigima alamar yana jin yunwa, hijjab ta zura tare da dauko kudi ta nufi bakin get, mai gadi na ganin ta cike da mamakin ya shiga gaishe ta, rabon shi da ita tun ranar da ya kira hajiya makofciyar su, suka dauke ta rai a hannun Allah zuwa Asibiti,tun daga ranar kuma bai gani ko jin labarin ta ba, yau kuma koda yaga Alhaji babba ya sauke mace da yaronta ta shiga ciki bai taba tunanin ita bace, yadda ta amsa mishi a mutum ce ba kamar a baya ba da wani bin ma sai taga dama zata daga mishi hannu shi karan kanshi abin ya bashi mamaki, cikin girmamawa da dan jin nauyi ta gabatar mai da bukatar ta nasan ya siyo mata ruwan gora saboda sha, taliya idomie da kayan shayi sai mai dasu magi, da dai sauran abin da zata bukata nan kusa irin su sabulu da amo sannan ya biyar ya mata takeaway a safara foods, ba tare da damuwa ba kuwa ya amsa da to ta kawo ba damuwa, kudi mai yawa ta bashi wanda yafi karfin abin da ta bukata tace harda na napep amma dan Allah yayi sauri saboda yaro. Sai lokacin ya kalli yaron, zaro idanu yayi cike da