Header Ads
Showing 192001 words to 195000 words out of 201974 words

Chapter 65 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1751

Ads at the middle of Article

lafiyan su yan wata shida har an gama halittan su, bai basu bayanin komai ba saida ya gama daidai ta komai, duk wani abin da ya kamata ya mata yayi, ya bata duk wani taimako da ya dace sai da ya tabbatar yanzu komai normal, sannan ya nemi ganin mijin ta a office din shi, jiki a sanyaye Aslam ya tafi don tunda daddy ya gaya mai mekefaruwa jikin shi yayi sanyi, musabaha sukayi da Dr nasidi shima matashi ne dan akalla zasuzo tsara da Aslam din, dan da alama ma sunsan juna, bayan Dr ya nuna mai wurin zama ya zauna, farin takarda ya mika mishi tare da cewa " Da farko dai zan fara da cewa Congratulation Mr Aslam." Ya fada yana sakin kayataccen murmushi, kamar wani gaula haka ya tsaya yana kallon shi, zaka rantse baijin yaren da Dr nasidi keyi ne,ganin bai amsa faifan ba yasa Dr sake cewa "karbi mana dan uwa." Kamar mara jini a jiki haka ya miƙa jhannu shi nya karɓa,koda ya karba bai iya budewa ba sai rike wa yayi gam kamar wanda aka ba tikikin shiga Aljannah, Dr ganin bai bude ba yasa yace ka "Bude mana." Ba musu kuwa ya warware faifan ya fara binshi da idanu, wani irin yam yam yam haka ya ringa ji yana ratsa tsakanin kanshi da zuciyar shi, tabbas ba barci yake yi ba idanun shi biyu amma kuma abinda yake gani a rubuce jikin faifan ne yasa yake gani kamar mafarki yake, bayani ne akan cikin Asmah watannin Cikin da matsalar Cikin da kuma saka hannun Dr akan tabbatar da cewa yayi duk abin da ya dace yanzu komai nomal abu daya ne babu adadin babies din wannan kuma ya bar musu su jira ranar haihuwa, yana gama karanrawa dago kai yayi yace "Dr a mafarki muke ko a ido biyu?" Dariya Dr ya kwashe dashi, indai irin wadan nan bankauran ne ya saba gamo da su iri iri amma nayau na Aslam ya bashi dariya sosai, cikin zolaya yace "ko nadan mare ka ne sai ka tabbatar" ga mamakin shi saiji yayi Aslam yace "eh Dr pls ka mareni kozan dawo cikin duniya ta." Sai kuma hawayen farin ciki shaaa wanda shi karan kanshi Aslam din baisan wanda suka zubo ba, can kuma ya mike ya kaima Dr nasidi runguma,yana zuba mishi godiya, shikam dai Dr dariya yake yi, yana kara yimai congrat, lokacin daya fito daga wurin Dr zee da mummy suna dakin da aka ba Asmah bed rest na awa uku, daddy ne kawai a wajen daga yadda ya hango Aslam yana tafe da kuzarin shi fuskar shi a washe dauke da madaukakin farin ciki ba kamar yadda ya tafi ba yasa tun kan ta karaso ya mike ya tare shi, shima ganin haka yana zuwa kawai ya fada jikin Daddy ya rungume shi gagam cikin farin ciki ya shiga cewa "Alhmdllh daddy husnah tana dauke da ciki na, Ashe ciki ne da ita daddy har na tsawon wata shida bamu sani ba." Cike da mamaki daddy yace "Ciki fa kace Aslam, wane irin ciki, kodai baka ji da kyau bane." Yace "wlh daddy naji da kyau haka Dr ya fada kuma ya bani bayanin komai a rubuce." Da sauri ya sake shi tare da mika mishi faifan da Dr ya bashi, daddy na gama karanrawa ya fuskanci gabass ya daga hannu ya shiga jerowa ubangiji kirari, mutane sai kallon su suke yi, abinka da Nigeria, suko ko a jikin su basu san ma suna yi ba, zaro waya Aslam yayi tare da cewa "daddy bari na kira umminmu na sanar mata." Hana shi daddy yayi ta hanyar kama hannunshi suka nufi dakin da su mummy ke ciki. Asmah na kwance tana maida barcin da bata samuyi jiya ba,zee na zaune a kujeran dake gabanta ta zuba tagumi yayinda mummy keta safa da marwa ta kasa zaune ta kasa tsaye jira kawai take Aslam ya dawo daga wurin Dr taji menene ke damun Asma'un ta, suna shiga ta dakata tare da juyowa da sauri ta kalli Aslam cikin yanayin damuwa tace "me Dr yace?" Bai iya amsata ba sai wani irin kyakkyawan murmushi daya ke binta dashi, daga ita har zee sororo suka tsaya suna kallon shi, daddy ne da har yanzu faifan nan ke hannu shi ya miƙa mata tare da cewa, "Dr yace nan da wata hudu amaryar ki zata iso sai ki fara shiri." Bata bi takan zancen daddy ba dan a halin yanzu bata shi take ba, tun kafin ta gama karanta bayanin dake rubuce ta zube a gurin ta shiga gabatar da shujudul-shukur, tana dagowa kuma ta rungume Aslam tana hawayen farin ciki ta shiga ce, "Alhmdllh! Alhmdllh! Alhmdllh ala kulli halin Allah kun gode maka." Aslam kam murna kan murna wai yau shine Mummy ta rungume kai da alama dai idanunta sun rufe ne bata san shita rungume ba, shi yanzu ko bindiga za'a saka mai aka, yaushe zai iya tuna when last ya kiji a jikin mahaifiyar tashi, zee ma tayi farin ciki sosai dan koda ta samu cikin ta na biyu bata yi irin farin cikin da tayi a yanzu da bayyanar cikin Asmah ba. Tun a asibitin suka shiga buge bugen waya suna gaya wa yan uwa da abokan arziki, baga Aslam ba baga mummy ba kai har daddy ba'a barshi a baya ba wannan karon, tunda Aslam da daddy suka shigo dakin ta farka, sai dai bata bude idanun ta ba,duka abin da ke faruwa a kunnen ta, hawaye ne kawai ke ziraro wa daga idanunta ba tare da kowa ya kula ba, suna can suna ta murna da buge bugen waya, kan kace kwabo kuwa tuni asibiti ya fara cika da yan uwa kwace ce musu akayi asman ta haihu, daddy tafiya yayi bayan komai ya lafa ya bar mummy idan anyi sallama Aslam ya maido ta, Dr ganin sunyi yawa adakin yasa yace su fita zuwa waje a bata dama ta huta nan da awa biyu ma zai basu sallama su tafi gida gaba daya, duk fita sukayi a dakin aka barta ta huta kamar yadda Dr ya bukata, Aslam ne bayan Dr ya tafi ya lallabo ya koma dakin ba tare da kowa ya kula da shi ba, tun dazu yake ta neman wannan daman na samu ya kebe da ita ya zama shine mutum na farko da zai fara yi mata wannan albishir din, a kujeran sake facing dinta ya zauna tare da kama hannayenta ya rike, ya tsirawa fuskar ta idanu yana kallonta, haweye da yaga yana zirarowa a hankali ta gefen fuskar ta ne ta tabbatar mai da idanun ta biyu, murmushi ya saki a hankali cikin rada yace "Bazan hanaki zubar da hawaye ba husnah ta, ki zubar da abinki nasan na farin ciki ne dan nima na zubar da nawa." A hankali ta ware idanuwan ta akan fuskar shi, tace "Ya Aslam da gaske ne, abin da nake ji kuna fada cewa wai ina dauke da juna biyu har na tsawon wata shidda, kenan nima zan haihu kamar kowacce mace." Girgiza mata kai ya shiga yi cike da karfafa gwuiwa yace "kwarai husnah kina dauke da ciki Dr ya tabbatar mana da haka, insha Allahu very soon zaki haihu ki zama uwa kamar ko wacce mace." Mikewa tayi zaune ta fada jikin shi ta rungume shi ta fashe da kuka tare da cewa "Ahmdllh alakulli halin Allah mun gode maka, wlh zuciya har yanzu ta Gaza daukar lamarin da sauki ji nake kamar zata fashe tsabar farin ciki." Murmushi yayi yace "Haka Allah yake lamarin sa, mahakurci dama ance shine nawadaci wata rana." Kamar yadda Dr yayi alkawari awa biyu kawai suka kara ya basu sallama tare da bata magungunan da zata ta amfani dashi na nasara dana musulunci, suka dunguma zuwa gida,ranar Asmah ta kara tabbatar lallai ita yar gata ce, sai tururuwan zuwa gaishe ta akeyi ana taya ta murna, tare da al'ajabin yadda lamarin ubangiji ya kasancewa, wadan da ke nisa kuwa sai kiran waya akeyi har daga dangin mahaifanta itama. Kamar jira cikin yake yi a gano shi, ko sati ba'a rufe ba ta kama wani irin laulayi mai zafin gaske, duk abinda ya kamata ace tayi su tun ciki na karamin batayi ba sai yanzu, take kuma cikin ya fara wani irin girma yana fitowa fili da kadan da kadan kafin ta rufe wata daya da bayyanar shi ya fito rass ya zama wani tukeke kamar dan wata tara ba bakwai ba, ga laulayi daya sakata a gaba ba dama ta ci abinci sai amai ba dama ta shaki abin da bai mata ba sai amai , tuni ta koma abin tausayi duk wanda ya ganta sai yaji kamar ya zubar mata da hawaye,da kanta tace ta barma zee kwanan ta sai ta haihu, kafin wata na takwas girman cikin ya fara basu tsoro,kuma duk bayan sati biyu Duke zuwa asibitin Dr nasidi yace musu ba komai normal ne karsu damu, wannan suke samun relief, tana shiga watan haihuwa mummy tace ya tattarota ya dawo da ita gaban ta dan ita tsoro take ji,kar nakuda ya taso mata gida babu wani babba daga ita sai zee kuma dukansu bawai sun san kan abin sosai bane, shima bai musa ba haka nan ya kaita, aka koma aka zura sa sarautar Allah idanu kowa ya dukufa da addu'a ba dare ba rana, Aslam har masallatai da makarantun islamiyya yake bi yana bada saraka akan lamarin, Asmah kam tana jin jiki ba kadan ba ko tashi bata iyawa ita kadai cikin rinjayanta yakeyi sosai, ta dena zuwa awo sai shi Dr ya biyo ta gida ya duba ta, yana kuma kara kwantar masu da hankalin akan cewa komai na tafiya yadda ya kamata su dai kawai su dage da addu'a, har ta fita wata na tara shiru haihuwa zaizo bai zoba tun suna saka rai yau gobe jibi amma shiru kake ji wai malam yaci shirya yasha ruwa, mummy kam tuni ta rufe fita ko ina, Aslam ma kullum a gidan yake wuni kwana ne kawai bai taba yi ba haka zai saka ta a gaba yana taimaka mata suyi ta zagaye gidan suna exercise. Ranar da cikin ya shifa wata na goma sha daya ta wayi gari garau ranar dan har wani karfi takeji na musamman ba kamar kullum ba, dan ranar har mikewa da kanta takeyi kuma tayi exercise sosai da kanta ranar ba tare da ta jira Aslam ba, koda ta gama exercise din ta a falo ta samu mummy, sannu Mummy ta mata har tana tsokanar ta da cewa in ta haihu sai ta Zane babyn dan ya wahalar mata da ƴarta ya shige cike ya nemi guri ya kwanta to dai a kwai ranar ƙin dillanci, tana murmushi tace "mummy bari na watsa ruwa na dawo." Koda ta shiga dakin da aka ware mata a ƙasa tube dogon rigar ta na robaroba tayi ta daura zanin mummy babba ta shiga toilet, ita karan kanta tana mamakin karfin da lafiyar da take ji yau a jikin ta wanda rabon da taji irin shi tun kafin baiyanar cikin ta, tsugunawa tayi da niyyar yin fitsari, ji tayi marar ta yadan daure kasa mikewa tayi daga tsugunan da tayi, cikin abin da baifi minti biyu ba taji wani irin nishi mai mugun karfi ya taso mata daga tsakiyar bayan ta, kafin tayi wani yinkuro sai ji tayi wani abu na kokarin rasto kasan ta ya fito duk da bata san ko menene ba ta tsorata ainun kwala kiran sunan mummy tayi da mugun karfi, mummy dake falo bata kai ga tashi ba a gigice ta mike ta nufin dakin da Asmah ta shiga dan yin wanka ko kafin ta karasa toilet din har baby daya ya fado, da sauri mummy ta ta karasa ta tallabo ta tana fadin "subhanallahi." Ina! Asmah bata san inda kanta yake ba kafin ta kai ga kara cewa a wani abu wani babyn ya kuma fadowa, bata gama mamaki dayan ma ya fito fit tare da mabiya a lokaci guda.....




ba editing ayi hakuri


Oum Ummeetarh


07041130088
💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~




FREE BOOK




{Nasaukar da wannan book ɗin ga duk wacce ta rasa hahaifiya Allah kajiƙan iyayen nu.}




Page 132






Wani irin haihuwa Asma'u tayi mai ban mamaki gaba d'aya da tasowar na'kudan da haihuwar tayi shine cikin abinda baifi minti biyar ba, tsabar rud'ewa mummy rasa me ya kamata tayi, tayi ,kukan jinjiran daya karad'e kunnenta ne ya yasa ta dawo cikin hayyacinta da wani irin sauri ta fice daga toilet d'in jakar da suka had'a kayan haihuwa ta bud'e, zazzage shi tayi ta d'auki kwalin reza da sauri ta koma toilet d'in, yanke cibiyan tayi ta d'auki zanin ta da Asmah ta rataye ta raba shi uku ta nad'esu a ciki ta kaisu kan bed ta jere su, ta koma toilet d'in, heater d'in ruwan zafi ta kunna ta daidaita shi cikin abin da baifi awa d'aya ba mummy ta gama gyara Asmah da babies d'inta ba tare da kowa a gidan ya sani ba,Asmah tuna barcin gajiya ya kwashe ta babies d'in ma da suka ji ruwan zafi shiru sukayi basu sake kuka ba tunda suka yi tunda sukayi na fadowa duniya wanda yake wajibi. Sai da ta tabbatar komai ya daidai ta sannan ta d'auki wayar ta daddy tafara kira, dan shaida wa wannan daddad'an labarin mai dauke da abin al'ajabi, yana zaune a office ya ga kiran mummy ya shigo sai da gabanshi yadan fad'i kasancewar yasan ya barta da mai lalura a gida , da sauri ya d'aga dan dama shima yana jiran ya d'an samu saukin aiki ne ya kira su yaji ya Asman take, haka yakeyi kusan duk inya fita bayan wasu y'an awanni sai ya kira yaji ya take, ko amsa sallaman ta na kirki baiyi ba ya shiga tambayar ta Asmah da lafiyar ta, murmushi tayi mai sauti tare da cewa "To daddyn Asma'u kyakkyawan labari, amma sai an bani goron albishir." Jin yadda take ta sakin murmushi yasa ya tabbatar lallai abin mai girma ne, cikin d'an yanayin za'kuwa yace "fad'i duk abin da kike so zan baki." Tace "ka tabbatar." Yace "In kina so sai na rantse." Tace "ba sai ka ranste ba, goro na shine (No kishiya in my hause)." Dariya yayi yace "har kullum kedai zancen ki kenen, kuma na sha fad'a miki tunda kuruciyar mu kin isheni riga da wando rayuwar duniya A'isha ta." Dad'i taji ya mamaye mata zuciya cikin yanayin farin cikin da take ciki a yau tace "nagode sosai mijina abin alfaharina." Yace "yanzu dai duk ba wannan ba, ki Adana min wad'an nan dad'ad'an kalaman naki sai na dawo gida, fad'a min albishir dina dan wallahi na 'kagu naji." Dariya ta shiga yi mai, cikin son taja mai rai, sai da taga ya koma rok'on ta cikin marairaice murya kamar zaiyi kuka, sannan tace "Asma'u ta haihu." Zaro ido yayi tare da cewa "wacce Asma'un, kee! A'isha bana son irin wannan tsokanar, dan Allah." Tace "wallahi ta haihu kuma yaya uku rerass." Nan fa Daddy ya k'ara yarda cewa lallai tsokanar shi take, duk da yasan cikin Asmah ya wuce watan haihuwa bai taba bata haihuwa yau ba, saboda garau ya baro ta gida baiga wani alamar nak'uda a tare da ita ba, kuma da fitar shi da kiran wayar mummy tace mai Asmah ta haihu duk baifi awa biyu ba, jin shi shiru yasa mummy katse kiran ta, tasan dole zai kira kokuma ya biyo baya dan ya tabbatar, bayan daddy Ummi ce next da mummy ta kira sannan Mami, duk wanda ta gaya wa Asmah ta haihu sai ya karya ta, Mami ma ko katse wayar basuyi ba sai gata a part d'in mummy da ta diro kamar daga sama, tana tabbatar wa kuwa ta shiga murna tana hamdala kamar ta taka rawa dan farin ciki a wani bangaren kuma tana al'ajabin yadda wannan lamarin ya kasance, can kuma ta shiga kiran su batool d'aya bayan d'aya tana fad'a musu. Mummy da kanta ta je ta sanar wa hajiya mama da alhaji baba, aiko tare suka dawo part din ta da hajiya mama, kan kace kobo magana ya karad'e family Asmah ta haihu yan uku, duk wannan bidirin Aslam bai da labari dan mummy bata kira shi ba Mami kuma tayi tunanin mummy ta gaya mai shi yasa bata kira shi ba. Ya gama shirin shi na tafiya office kenan suna sallama da zee yana ce mata zai biya yaga jikin Asmah kafin ya tafi, ita kuma tana bashi sallahun gaisuwa wayar shi tayi ringing, Amir ne mai kiran hakan yasa bai bata lokaci ba wajen daga wa, daga can bangaren Amir yace "angon k'arni angon k'arni congratulation d'an uwa, yanzu Abba ke kira na wai Asmah ta sauka, gaskiya baka da kirki shine ka kasa kira na sai Abba ne ke gaya min." Duk wannan surutan na Amir tuni Aslam ya dena fahimtar shi dan karshe ma dauke wayar yayi daga kunnen shi yana sake maimai ta kalaman Amir, wai Asmah ta sauka, sai ya rasa ma wani irin sauka yake nufi to, bai gama wannan mamakin ba wani kiran ya sake shigo wa daga Dr bash shima dai congrat yake mai, wannan karan dai dakatar da Amir yayi da cewa "kai dan uban ka yi min dalla² wacece ta haihu wai kuke ta rigar rigen kira na zaku rudar dani." Daga cen bangaran Dr bash yace "wai kai a komai saika saka iskacin ne? kana da wata mata Asma'u ne banda Asmah bamu sani ba, nima ina hospital yanzu teema ke kirana wai Asmah ta haihu yan uku yanzu Mami ta kira ta itama ." Duk wannan bayanin na bash ma iska

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads