Header Ads
Showing 54001 words to 57000 words out of 201974 words

Chapter 19 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1713

Ads at the middle of Article

cikin trolley ya fita ya shiga motar shi ya bar gidan da mahaukacin gudu,


Me gadi kam tun ganin yanda ya shiga gidan d'azu da gudu yasan ba lafiya ,wani Abu Mara kyau na faruwa,ganin fitar Aslam a haukace jikin shi duk jini, yasa da gudu ya nufi falon yana shiga yaga zee a sume ga fuskarta duk a kumbure ga jikinta duk jini, sallallami ya shiga jerowa kafin kuma ya fita da gudu ya debo ruwa ya watsa mata,






Aslam kam direct family hause ya nufa saida yayi horn mai gadi ya bude mai get kuma ya masa qarsawa cikin gidan, tsayawa yayi yana tunanin ta yadda zai saka kafar shi a cikin gidan yau..............






Oum ummeetarh
07041130088






Share
And
Comment
Fisabilillah🙏.
đź’–DAMA TA BIYUđź’–


BY


~AYSHA NALADO~




FREE BOOK






{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
















Page 67 & 68














A galabaice ta shiga sauke numfashi, idanunta arufe , me gadi kam daura hannu yayi aka ya shiga fareti, shikam yau ya shiga uku ya zaiyi da rayuwar sa ,


Fita yayi da gudu makota, ya shiga buga musu get, me gadin Gidan ne ya taso ya bude mishi, kasancewar sunsan juna, nan ya shiga rattabamai abin da ke faruwa, shima cikin jimami ya nufi cikin gidan, hajiyan gidan ya samu ya gaya mata abin da, me gadin .gidan Aslam ya gaya mai,




Hajja fati Macece mai tausayi, dattijuwa ce bata da miji, saidai tanada yaya manya maza da mata, wasunsu ma sunyi aure, anan take zaune,yar gata ce, dan ba abinda yayantsa basa mata, kuma itama metro ce a general hospital,




Cikin tashin hankali ta zari hijabinta ta bi bayan shi, har cikin falon mai gadin gidan Aslam ya mata jagora,




Ganin halin da zee ke ciki yasa hankalinta ya qara tashi, kallo daya ta mata ta gane inda matsalar take kasancewar ta babban ma'aikaciyar jinya mai matsayin metro, dagata tayi ta shigar da ita toilet din dake falon ta hada mata ruwan dumi ta saka ta ciki,


Sosai ruwan ya ratsa zee, take numfashinta ya fara daidaita ta fara bude idonta da suka lumshe, don batasan inda kanta yake ba ,


Saida ta gasata da kyau, ta barta a toilet É—in tace ta lallaba tayi wanka, suje asibiti taga Dr,


Fitowa hajja fati tayi ta shiga gyara falon ,duk inda ya baci, saida ta gogeshi tas ,koda ta gama zama tayi a falon tana jiran zee, shiru shiru zee bata fito ba don haka ta tashi ta leƙa toilet ganinta tayi a zaune a toilet din ta gama wankan ta daura tawul amma fitowa ya gagareta domin baza iya tafiya ita kaɗai ba jiri take ji sosai,





Kamata hajja fati tayi suka fito daga toilet É—in zaunar da ita a falo tayi ta haura sama ta duba É—akinta ta dauko mata kaya marasa nauyi , dubawa tayi bata samu pad ba don haka ta aika mai gadi ya siyo musu , bata tayi ta saka, ta saka kayan sannan ta ce ta jirata ta dauko mota suje asibiti,




Duk abinda ke faruwa zee hawaye takeyi, tana sauke ajiyar zuciya, ta kasa tsaida hawayen dake bin idanunta, ta ƙudiri aniyar ko Aslam ne autar maza ta rabu da aurensa , tunda ya saka hannu ya mata irin wannan bugun dan kawai ta zubar da ciki,




Tayaya akayi yasan ta zubar da ciki waya faÉ—a mishi bayan daga ita sai beebalo sai allah suka san da wannan zancen,




Lallaɓawa tayi ta miƙe daƙer ta dauki wayar ta ta kunna , lambar dad ta kira, yana ɗagawa ta fashe da kuka tace "dad zai kasheni , dad kazo ka rabani dashi bana sonsa na fasa auren dad zan koma na zauna tare daku,kazo ka daukeni kar ya kashe maka ni"




Dad cikin tashin hankali yace"daughter meke faruwa, waye zai kasheki , " cikin kuka tace "Aslam ne" nan ta labarta mishi abin ya faru , aiko ran Dad in yakai dubu ya baci,take fuskar shi tayi jajur zabar bacin rai har wani tiriri yaje jin yana fita daga kunnuwanshi, nan ya shiga aunawa Aslam zagi da É—iban Albarka kafin daga karshe yace ta bi hajja fati zuwa asibiti, kuma tasa idon ganin shi a nigeria nan da wasu Ć´an awanni, zaizo saiya koyama aslam hankali, saiya gwammace da bai taba haÉ—uwa da ke a duniya ba ,







Karfafa zuciyar shi yayi ya rufe ido ya danna kan motar shi cikin gidan, yana parking ya fito, ina zai dosa yanzu , part din mami, haka zuciyar shi ta umarce shi, can É—in ko ya tunkara,mami tana ganin shi tasan ba lafiya ba daga yanayin da taga fuskar shi a mugun hade idanun shi jajir, can kuma ta lura da jinin daya bata mai jiki,


Innalillahi wainnailaihi rajiun ta shiga maimatawa kafin da sauri mami ta iso gareshi ta mika hannu ta rike mai hannayenshi, cikin tashin hankali ta shiga furta "my son meya faru, meya sameke , daga ina kake haka, meke faruwa"


Zaunar da ita yayi akan cushion shima ya zauna suna fuskan tar juna, a hankali ya bude baki yace"mami me na mata da zata saka min da irin wannan mummunan sakayya, mami na cancanci haka daga gareta, mami zee ta zubar min da cikina dake jikinta," cikin kaduwa mami ta shiga sallallami, tana tafa hannaye,


Tace "garin yaya ta zubar da cikin kun samu wani sabani ne" yace " wlh mami ba abinda ya haÉ—ani da ita, to mami imma wani Abu ya hadani da ita saita zubar min da ciki" mami tace"kai waya gaya maka, yanzuma ina zainab din take", kwashe komai yayi ya gayama mami tun daga message din da beebalo ta turomai har zuwa wutowar shi nan gidan, amma bai gaya mata a sume ya wuto ya bar zee,


Shiru mami tayi cike da tausayin shi hawaye ya cika mata idanuwanta,




"Yanzu kaje kayi wanka ka canza wadannan kayan da suka lalace, sai kazo musan abinyi, miƙewa yayi zuwa part dinsu, direct dakin shi ya shiga domin yayi abinda mami ta umarceshi,"


Yana wucewa mami tabi bayanshi da kallon tausayawa, gsky Aslam baiyi sa'ar mace ba, a dan shekarun shi wadanda da kaÉ—an suka haura talatin , yana fama da irin wanan kalubalen Rayuwa kala kala, ga rashin dacen mata, ga kuma soyyaya na dawainiya da zuciyar shi , da tana da iko da babu abinda zai hana ta aurawa Aslam Asmah a karo na biyu, kozai samu saukin Rayuwa,


idan ya auri Asmah ya rage wani matsalar daga cikin mastalolin rayuwar shi ,


sai yaji da batun zainabu , amma tasan bata da wannan ikon, Abu daya ta San zata iyayi, shine tausa kamal ya janye daga neman auren Asmah ya barma Aslam, a matsayin ta na mahaifiyar shi,


to tasan ko tayi haka tayi a banza, tunda dai ta Riga tasan wanene mahaifin mijinta wato alhaji baba , kaifi É—aya ne baya magana biyu idan yace yes ta zauna haka zalika idan yace no, shima ta zauna,


mutum É—aya ne take da tabbacin duk fadin duniyar nan zai iya canja maganar alhaji baba, amma duk da hakan baza ta zuba Ido kawai ba, zatayi wani Abu akan lamarin,




Koda yayi wanka kwanciya yayi a dakin yana nazarin abinda ya faru yau tundaga farko har karshe, koda yazo kan beebalo diga ma lamarinta question mark yayi,❓zai binciketa don bai yarda da ita sosai ba, idan ya gano da hannunta acikin wannan lamarin zai hukuntata hukunci mai tsanani ba ita kadai ba, da koma wanene , mai hannu akan salwantar mashi da gudan jinin shi ,


Haka ya zauna yayi ta saƙe saƙe , ko sallan magriba da isha, a ɗakin yayi bai fita ko ina ba, babu Wanda yasan ya kwana a gidan hatta mami tayi tsammanin ya fice daga gidan ne,


duk Wanda yaga motarshi baya kawo kamai a ranshi, daddy ne ma daya dawo da daddare yaga motar yadan zargi wani Abu, koda yama mummy maganar tace baizo ba saidai ko amir ne ya kawo motar gidan, bai wani gamsu ba , yadai barshi da niyar da safe zai tambayi mai gadi,






Washe gari da misalin karfe biyar na asuba jirgin da Dad ya biyo daga Malaysia zuwa Nigeria yayi landing a airport na garin minna, direct kuma general hospital direban da yazo daukar shi ya wuto dashi,


A Amenity word aka bama zee gĂ do tun jiyan da sukazo likitoci sun dubata nan suka yi iya kokarin su suka tsayar mata da jinin da take zubarwa, sannan suka daura mata ruwa, sannan sukace aje a siyo jini za'a kara mata, don ta zubar da jini ya wuce misali, hajja fati tambayar zee tayi ko ina mai gidanta taga har sun kwana bai zo ba , bayan jiya zee ta tabbatar mata da cewa yasan abinda ya sameta, cewa kawai tayi baya nan,


Tun daga haka hajja fati bata kara mata wani tambayar ba, ita dai tana taimakon ta ne saboda Allah da kuma kasancewar ta mace mai tsananin tausayi,




Daidai lokacin kuma dad ya iso. cikin asibitin, Amenity ya nufa kamar yadda zee ta fad'a mai a waya, ganin yadda zee ta koma ba ƙaramin tashi hanakalin dad yayi ba , take ranshi ya kara baci fushin shi ya lunku sosai fiyeda da, take ya ciro waya ya kira wani tsohon abokin tun na yarinta, ɗan sanda ne mai babban muƙami, ya sanar dashi yana son a kama Aslam a mai duka , a kulle shi a cell, kullum ana dukan shi, kuma kar a bada beli shi ga ko waye har sai shi ya bada umarnin a sake shi,




Nan ya buƙaci da mutumin ya turo account number, take kuwa ya tura da account number din ganin yawan makudan kuɗin da dad ya mai transfer yasa ba shiri, ya aika yara mota uku zuwa gidan su Aslam domin a kamo shi,




Dad daga nan kuma ya nufi office din Dr don jin taka maimai meke damun zee, Dr yamai bayanin komai harda batun jini Leda daya da akeson za'a kara mata, take Dad yace a dibi jininshi tunda iri daya ne da nata haka ko akayi,






Da asuba ma Aslam bai fito masallaci ba, a daki yayi sallah asubah don kwata kwata baya jin dadin jikinshi ma,




Daddy bayan sun idar da sallah ,ya tambayi me gadi Aslam ya shigo gidan ne, nan kuwa mai gadi ya tabbatar ma da daddy cewa ya shigo tun jiya da yamma kuma dai baiga fitar shi ba yana da tabbacin yana cikin gidana, har yanzu,






Tun kafin su fito daga masallacin jini yar motar police ya karade layin gidan gaba daya, koda suka fito sunyi matuqar mamakin ganin motocin police É—in a kofar gidan su, da sauri suka karasa wurin su bayan sun gaisa Abba yake tambayar ko lafiya wa suke nema, nan wani baki me murtukakken fuska gabjeje da shi yace, "Aslam muke nema", abba yace "lafiya dai ko" mutumin Wanda da alama shine shugaban tawagar ya kara cewa"zamu tafi dashi office idan kana son jin Karin bayani zaka iya bin bayan mu" Abba yace" Aslam baya gidan nan banan bane gidan shi,"daddy ne ya katse Abba da cewa yana "cikin gidan ku shiga ku taho dashi,"


Abban da sauri ya maida kallon shi ga daddy da yayi wannan maganar,


Daddy ne ya musu jagora har zuwa part É—in su Aslam É—in, sauran mutanen gidan basu San meke faruwa ba , kasancewar da sassafe ne kowa na daki wasu ma sun koma baccin bayan asubahi,




Yana zaune akan sallaya yana mika kukan shi ga mahaliccin shi yaji bugun kofa, ba kakkautawa, gaban shi ne yayi wani irin faduwa haka kawai yaji hankalin shi bai kwanta da wannan bugun kofa ba, amma haka ya daure ya bude kofar,




Mamakine ya kusa kashe shi ganin mutane har biyu sanye da kakin police abakin kofar dakin shi,


Kallon su yayi yace "malamai lfy , " daya daga cikin su yace"u ar under arrest, munzo mu tafi dakai office ne" yace "saboda me zaku tafi dani office me nayi, zakuzo har cikin gidan ubana kuce zaku tafi dani,"




Dayan ne yanzu ya amsa da"Mallam da Allah kar ka wahalar damu , kazo muje office duk abinda kake son sani kaji daga baya acan"
Shiru ya danyi na some seconds kafin yace"muje to zan biyo ku a baya da mota ta, " kin amincewa sukayi, kasancewar suma ogan yadan san musu wani Abu cikin abin da ya samu akan case din, kuma ya gaya musu no mutunci,




Hannunshi suka kama zasu saka mishi handcuffs yaqi amincewa , dole yana ji yana gani ya shiga motar police suka tafi dashi,


suna fita Abba ya kalli Daddy yace " me yasa ka yi haka yaya," Daddy yayi murmushi yace" idan nace musu baya nan baza su yadda ba , sai sun shiga sun dudduba, haka kawai su tasar ma iyalan mu da hankali suna cikin hutawa ba laifin fari bana baki, gara dai su tafi dashi cikin salama, ai tsunstun daya ja ruwa shi ruwa kan duka" Abba yace "to yanzu zamubi bayan su ne" Daddy yace"A'a nifa baza ni ba idan kai zaka bisu bismillah"


Abba yace "aikam banga ta zama ba bari na shirya nabi bayansu" dage kafadu daddy yayi alarmar, I don't care ya nufi part dinshi ,shima Abba part dinshi ya nufa don ya shirya yabi bayan su zuwa station,




Suna isa station ba'a bashi daman yin wani magana ba aka shiga da shi cell , ogon su ya bada umarnin a mishi dukan tsiya, Aslam na tambayar me yayi ba Wanda ya saurare shi, mutum biyu ne jibga jibga suka shiga dukan shi da kulake baji ba gani,




Ko kafin Abba ya karaso sun hada mishi jini da majina, Abba daya nemi jin ba'asi folder case din Aslam É—in da ka bude aka dauko mishi, mahaifin matar shi ya shigar da kara akan dukan tsiyan da yama Ć´ar shi da karamin ciki Wanda hakan yayi sanadiyyar zubewan cikin, yanzu haka tana asibiti a kwance rai a hannun Allah,






Dukar da kai Abba yayi ya shiga maimata innalillahi wainnailaihi rajiun, dagowa yayi idanun shi sun rine, yace "yanzu oga meye abinyi," oga yace" abinyi shine zamu rike shi anan gurin mu har sai yarinyar ta samu lafiya, sannan mu mikashi kotu a yanke hukunci daidai da laifinsa,"


Abba yace "ko za'a iya bamu bellin shi kafin, komai ya daidaita" ba,
Oga yace "ba zaiyuwu ba"


Abba zai ci gaba da magana oga ya dakatar dashi ta hanya daga mai hannu yace "na gama magana, bana sonjin wani magana data shafi beli"


Abba ganin yadda ya daure fuska alamar yana so yaci mai mutunci, yasa dole yayi shiru da bakin shi , ya mike ya fice daga station din, jiki a sanyaye.




A gida kam ba Wanda yasan abinda ke faruwa, don daddy dama abin ko ajikin shi, bai damu ba, balle har yaje gayawa mummy, Abba kuma kin gayawa mami yayi don karta shiga damuwa,


Koda ya sanar ma daddy abinda oga ya fad'a mai , na cewa Aslam ya daki matar ya zubar mata da ciki. Mahaifinta, ya shigar da kara gurin yan sanda , da yadda sukayi na batun beli, daddy cewa yayi Allah ya kyauta,




Wasa wasa kwanan Aslam uku a station kullum kuma sai am mishi dukan tsiya safe da rana da yamma, Abba kam kullum cikin zarya yake amma oga yaki sauraren shi,


Alhaji baba Abba ya sama da maganar , shima dai Allah ya kyauta kawai yace,


Mami kam ta shiga zullumin don tun ranar da Aslam yazo mata da batun zee ta zubar da ciki take ta saka ran kara ganin shi amma shiru kakeji,ta zuba ido shiru ta kirashi a waya shiru,




Bayan kwana uku zee ta warke ta samu karfin jiki sosai , nan Dr ya sallameta,


Dad É—aukanta yayi sukaje station din da aka rufe Aslam sawa yayi aka fito mai dashi,




Innalillahi karkuso kuga Aslam yanda ya koma abin tausayi, duk jikin shi yayi shedan duka wani gurin ma ya fashe, fuskar shi kam ya kumbura sintim kamar ba Aslam ba kwata kwata ya fice daga haiyacinsa , taso shi gaba yan sandan sukayi, har gaban dad, kallon banza ya watsa mai kafin yace," Aslam kake kowa,kayi babban kuskure da daga hannu ka dukarmin yarinya, koni Dana haifeta ban taba dukanta ba sai kai, don kawai ka mata asiri ka aure ta kuma sai ka hada da duka, so yau asirinka ya karye, daga yau babu kai babu zainab, ko a hanya karka kuskura ka kara nuna ka santa, " kallon oga yayi dake ta washe baki kamar gonar auduga yace a "sake shi haka",


Kallon zee yayi data miqe tsaye ta dafe girjinta , tun fitowar Aslam ganin yadda ya koma yasa tuni hawaye ya fara bin kuma tunta, tana son Aslam sonda ko iyayenta bata yi musu irinshi, koda take cewa ko shine autar maza ta barshi , fad'a kawai takeyi, don ita kanta tasan karya takeyi, kawai bacin Raine ya saka fadar haka ,






Ganin yanda take kuka, yasa dad mikewa a fusace ya figi hannunta suka bar cikin station, daga nan kuma airport suka nufa, basu zame ko inba sai Malaysia,




Aslam kam rigar shi wani kurtun dan sanda ya miko mai ya karba ya saka wasu takaddu ya sassaka hannu kafin suka sallameshi daga station din..............








Oum ummeetarh
07041130088








Share
And
Comment
Fisabilillahi🙏.


đź’–DAMA TA BIYUđź’–


BY


~AYSHA NALADO~


FREE BOOK










{Nasadaukar da wannan page din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}


















Page 69 & 70










Keke napep ya hau zuwa London road, babu ko sisi a aljihun shi, don ƙananan polisawan nan tass suka yashe shi, jiran shi me keken yayi ya ƙwanƙwas get din gidan me gadi ne ya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads