Showing 93001 words to 96000 words out of 201974 words
Chapter 32 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
idanun shi da idanun dangin shi,idan akwai wacce Baku shiri cikin yan uwanshi, ta samu hanyar da zata kuntata miki,saidai kiga ana abubuwa baki da labari, amma kin kama kanki, sai ki kange komai, komai sai anbi ta hannun ki, ya sakar miki ragamar komai, dan Allah a kiyaye kuma duk tsiyar da zakiyi bazai hanashi auren da yayi niyya ba, kijama kanki raini a gurin kishiya may be ma kin girmeta kin fita komai, Allah yasa mu dace).
Samun shi tayi zaune a falo yana amsa call a waya, guri ta samu a kujeran dake facing nashi ta zauna tana cika tana batsewa, ci gaba yayi da wayar shi ko kallonta shima baiyi ba, zaman ta kamar da minti biyar zahra tayi sallama cikin zazzakar muryarta mai dadin amo, daidai lokacin kuma Barr ya gama wayar da yakeyi, kamshinta ne fara musu sallama kafin a natse ta ɗago labulen falon ta shigo, da idanu suka bita yuuuu, kowa da irin kallon da yake mata, maryama ganin zahar da irin wankan data dauka ga wani zazzafan kamshi dake tashi a jikinta, saida gabanta ya yanke ya fadi rasss, take ta raina kanta a wurin ji tayi duk ta muzanta, kishi da ƙyashi da baƙin ciki suka mata kawanya a lokaci daya, take ta shiga aunawa zahra wani irin mugun kallo mai cike da tsantsar tsana.
Shiko Barr wani irin kallon so da tsananin ƙauna yake binta dashi, ji yake kamar ya tashi ya taro ta ya saka a kirjinshi, ko zaiji saukin zillon da zuciyar shi take mai akanta, yana tsananin son uwar gidan shi sosai amma sonda yakema zahra special ne.
Murmushi ya shiga jifanta dashi, hakan yasa itama ta shiga mayar mai da martani, matsawa yayi daga tsakiyar kujeran da yake zaune 2 sitter ya koma gefe, ganin haka zahra direct kusa dashi ta zauna a daya gefe.
Har ta zauna Maryama nabinta da wannan mugun kallon, cikin sakin fuska ta kalleta tace"yaya Maryama ina kwana" wani mugun tsaki taja kamar bakin ta zai tsinke, a madadin ta amsa gaisuwar ta sai cewa tayi"wlh kaji kunya Adam yanzu ɗan wannan abun ka iya cire kudinka ka bada sadaki da sunan kana so, kazo ka ajiye kana kwanciya da ita, yarinyace fa ƙarama Wanda na tabbata da kayi auren wuri da ka haifeta, wannan abin kunyar dame yayi kama, na tabbata wannan yarinyar idan ta girmi hanan(yar su ta fari)da nisa ta bata shekara biyar, yanzu kai baka jin kunyar ka tube zindir a gaban yar cikin ka, kalli kanka ka fa har furfura kake dashi" tsaki taja kafin taci gaba da cewa "suma iyayenta ne basu da hankali wannan ai child abuse ne".
Wani gigitaccen tsawa Barr ya daka mata wanda saida hantar cikinta ya kada, amma ta dake tana huhhura hanci, zahra kam zaro ido tayi waje maganar Maryama na karshe yayi mugun dakar mata zuciya, iyayenta ne basu da hankalin, tabdijam aikam baza ta kyaleta taci bulus ba, itama fa ta iya masifar nan da rashin kunya kawai dai batayi ne saboda Allah yayi ta da sanyin hali, yoooo ita da takema yar uwar batool danja har a gwada mata masifa da fitsara da rashin kunya, buɗe baki tayi da niyar yaba mata maganar da har ta mutu baza ta manta dashi ba, fahimtar hakan yasa Barr ya damki hannunta dake kusa dashi da karfi dagowa tayi ta kalle shi ya girgiza mata kai alamar kar tace komai, zahra a kwai biyayya kamar dai Asmah😅.
Sauke kanta kasa tayi sai hawaye sharrr, kamar an bude famfo, a zuciyar ta tace maryama kinyi da meyi zan nuna miki aiki karamar yarinya a aikace, amma kafin nan saina mallakama mijina kai na mun dawo g-g dake, sai kinyi nadamar zagin iyayena da kikayi.
Barr kam fada yahau Maryama dashi karshe ya koma nasiha yana dasa aya tace "oho dai andaiji kunya wlh girma ya fadi" bai tanka ta ba yace "yanzu ki fadi kwanakin da kikeson ku dingayi ma'ana ku raba girki," budar bakinta sai cewa tayi "Allah ya kiyaye na raba girki da yar cikina" cikin fushi yace "haka kika Ce ko to shi kenan ni na raba kwana 1-1 zaku dingayi daga yau, kuma kin amshi girki yau, da rana zaki fara zuwa breakfast din gobe, abinci kuma breakfast da dinner tare zamu dinga ci" yana kaiwa nan ya tashi ya bar masu falon , itama Maryama tsaki taja ta mike ta watsa ma zahra harara, tace "wlh ki sake mai jiki ya kwakuleki a banza dan ba zama kika zoyi gidan nan ba, na miki alkawarin saina fitar dake dan bazan yi kishi da yar cikina ba, in zaki rike budurcinki ki rike kyasamu ki kaima asalin mijinki" tana kaiwa nan ta bar falon, a fusace kamar kububuwa.
Lokaci daya taji hawayen dake fita a idonta ya kafe,murmushin takaici ta sake,a zuciyarta tace wato ma saka mani idanu takeyi tana kallon ko wani motsi dake gudana a tsakanina da mijina ko,inba haka ba ya akayi tasan babu abinda ya shiga tsakanin mu, hmmmm to zan shayar dake giyar mamaki Maryama.
Tashi itama tayi ta bar part din ta koma nata, abin daya faru ya tsaya mata a rai sosai, wayar ta ta ciro tana tunanin shawaran wa zata nema, Ummi , zuciyarta ya bata amsa lallai ummi ce tafi cancanta, saboda yadda suke da ita kamar kawaye, zata bata shawara mai kyau a bayyane baza ta rufe mata komai ba, take ta lalubo numbar ummi ta danna mata kira,ummi ta daga bayan sun gaisa, nan ta sanar mata abinda ya faru, da irin maganganun da maryama ta yaɓa mata, da zagin iyayenta da tayi.
Nutsuwa ummi tayi ta bata shawarwari masu kyau wadanda zasu billar da ita, aikam shiru tayi tana recoding d'in abinda ummi ke gaya mata, sun dade kafin sukayi sallama, haka ta wuni a daki ita kadai, ba Wanda yazo gurinta itama bata fita wajen kowa ba, maryama bata kira cin avinciba itama bata nema ba, anam part dinta ta samar ma kanta abinda zataci.
tun da safen nan kuwa bata sake saka Barr a idanunta ba sai bayan isha'i ya shigo ya same ta kwance a kan gadonta, tana ganin shi ta tashi zaune ta shiga mai sannu da zuwa, zama yayi a baking bed d'in, yana kallon ta cikin muryar kwantar da hankali ya shiga lallashinta yana bata hakuri akan abinda ya faru dazu,nuna mai tayi ba komai, komai ya wuce, dadi yaji ya kara gode ma Allah daya mallakamai zahra a matsayin matar sa, yarinyar tanada hankali da hangen nesa sosai, sallama ya mata zai wuce wurin Maryama, har bakin kofa ta rako shi tana sharar kwallah kishi fall zuciyarta, shima ji yakeyi kamar kar ya tafi ya barta, ganin hawaye yaki dauke mata yasa ya jawota jikinshi ya dago fuskarta ya shiga lashe mata hawayen dake fitowa a idanunta, yana gamawa kuma ya hade bakinsu guri daya ya shiga kissing dinta, 5 minutes suka dauka a haka kafin ya saketa yana maida numfashi yace"kiyi hakuri babyn Adam kidena min asarar hawayenki, insha Allah gobe war haka muna tare shiyasa na zaɓi 1-1 days saboda ni kaina bazan iya wuce kwana daya bakya kusa dani ba" murmushi tayi jin abinda yace, tace"gud 9t my hrt bit, ka kulamin da yayata da kyau" ta juya da sauri sauri gudu gudu ta haura dakin fadawa gado tayi tana risgan kuka kishi da kewar mijinta na addabar zuciyarta, ta kudiri aniyar mallaka mishi kanta a gobe idan ya dawo dakin ta wanna kuwa daya daga cikin shawaran ummi ne.
Saida ya kulema ganin ta sannan ya fice daga part d'in da sauri, acan kuma yana zuwa ya tarad da bala'in Maryama, ganin zata hana shi bacci yasa tsakar dare ya korota waje ya bame kofar shi, haka suka cinye daren ba wani armashi ko baccin karki ba Wanda yayi cikin su ukun kowa da abinda ke damunsa.
kuyi manage yau bani da isasshen caji,🙏
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fisabillilah🙏.
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
DAMA TA BIYU💖 ƘIRƘIRARREN LABARINE MALLAKI NANE BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYAMIN LABARI TA KO WACCE SIGA BADA IZININA BA❌❌❌❌❌
(In 👂👂👂 yaji gangar jiki ya tsira👌 a kiyaye pls)
{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}
Page 96
Washe gari zahra koda ta tashi bayan tayi sallar ta na asubahi, komawa baccin ta tayi, wuraren 8 ta tashi, share part ɗinta tayi ta gyare ko ina tsab ta shiga toilet ta fesa wankanta ta zo taci kwalliyar ta kamar yadda ta saba, bata jira breakfast daga Maryama ba, ta shiga kitchen ta Samar ma kanta abinda zataci, tana cikin ci ne Barr yayi sallama ya shigo cikin shirin shi na fita.
Tashi tayi da sauri ta tare shi, ware mata hannayenshi yayi ta faɗa jikinshi ya mayar ya kulle, gaskiya jiya ta wahala da kewan shi da'ker bacci ya dauke, iya sati ɗaya da sukayi tare, ba karamin sabo sukayi da juna ba, haka tayi ta juye juye, sai daga karshe ta gargadi zuciyarta da cewa, wai me akayi ma da har zaki fara damuwa irin haka, kin manta mijin wata kika aura, karki bari ki sabar wa kanki da wannan yanayin, tun wuri dan wahala zakisha, tunda dai kinsan dole hakan zaidinga faruwa daga yau.
Da wannan ta samu ta yakice shi a zuciya tayi bacci, ammafa pillow nanan rungume a jikinta, madadin shi kenan.
Cikin farin cikin ganin shi ta shiga cewa"nayi kewarka sosai mijina jiya da'ker bacci ya daukeni"baice komai ba sai wani wahalallan ajiyar zuciya daya sauke,karasawa sukayi wurin da takecin breakfast dinta, zama taga yayi yaja plate din gabanshi, cikin mamaki tace"A'a ya haka abinci nane wannan fa, inace har breakfast din yau yaya Maryama zatayi" yace "to bataga daman yi ba dani da yara yau horon yunwa take mana , ko jiya wurin anty innagi naci abincin dare, haka ta barmu a gantale" zahra cikin tausayawa tace "yara fa me zasuci su" yace "na bari hanan na dafa musu indomie".
Barin shi tayi yaci gaba da cin abincin shi kaɗai dan kaɗan tayi bazai ishesu su biyu ba, daukar tea din da ta haɗa yayi ya kurba sannan ya kalleta, yace "ya kika tsaya kizo muci mana" girgiza kai tayi tace "kaci kawai ni dama na riga na koshi" bata saba mai karya ba don haka ya yarda.
(Pls mata a dena yima miji karya, komai zaije ya dawo ki fadi gaskiya,karki kuskura mijinki ya miki shaidan karya, heee sister kin bonu, ya dena yarda dake, wlh wanibin ko gaskiyar kika fada bazai taba yarda ba saidai yaji ki kawai, ki gama rantse rantsenki a banza, dan Allah me yafi wannan ciwo da gaskiyar ka amma a ki yarda da kai, amma idan ya shaide ki da gaskiya wlh watara ko ɓacin rana ne yazo kika dan shillo karyarki yarda zaiyi ba ganewa zaiyi ba, tunda yasan ke mai gaskiya, Allah yasa mu dace)
Gama wa yayi ya tashi ya wanke hannun shi a washing basin dake wurin dinner, daukar briefcase dinshi tayi ta rakoshi har bakin kofa, suna zuwa nan ta mika mishi jakar shi, kallonta yayi "yace iya rakiyar kenan" murmushi tayi tace "eh,mana wayo kake son kamin, na raka ka ka wuce ka barni gara dai na tsaya iya nan" amsan jakar shi yaya yace"kinsan dai yau kece da ni ko " fari ta mishi da ido wanda saida yasa gaba ɗaya tsigar jikin shi tashi, tare da cewa "ina sane dan har nama fika zumuɗi don kaji" dadi yaji na furucin ta yace "inyee a she dai ana sona har haka, to me za'a tanadar min " tace "me kake so" don ita duk daukar ta abinci yake nufi, sai gani tayi ya kama kunnenta ya mata raɗa, ai ba shiri ta zaro ido, tare dakai tafukan hannunta rufe fuskar ta, kamin kuma ta kwasa da gudu zuwa ciki tana kwasan dariya, shima dariyar ya shiga yi yana girgiza kai, a ranshi kuwa sake sake ne kala kala.
Yana tsaye ya shagala da kallon haryar da tabi, yaji wani irin mahaukacin knocking na tashin hankalin, kamar za,a balla kofar , ba shiri ya dawo hayyacinsa, bude kofar yayi da sauri dan ganin wane mahaukacine wannan, arba yayi da uwar gida tana wani irin huci, ranta a bace, tana ganin shi tace"to alagumgumi maci amana, har yanzu dai lokaci na bai wuce ba da ka shiga dakin yar yarinya karama ka taushe ta, wlh adamu ranar lahira da shanyayyen barin jiki zaka tashi insha Allahu, tunda gashi tun ba'aje koina ba ka fara nuna rashin adalci a tsakanin mu, insha Allahu sai wutar Allah ta cika,azzalumi kawai, mak" sauran zance ne ya katse jin saukar biyar dinshi a fuskarta, mari ya mata bana wasa ba don saida ya daidaici idanunta sun rufe ruf da masifa ya ware yatsu yasauke mata su da hannun hagu ma kuwa.
Wani ihu ta kwarara mai matuqar kara ta duke a gurin dafe da kuncinta, shikan, da ranshi ya gama baci, ko kallonta bai karayi ba yabi ta gefenta ya wuce abinshi, hanan da komai ya faru akan idanunta ne ta karaso da sauri ta kama hannun mamanta da idanta ke rufe bata ma ganin gabanta tayi part dinta da ita.
A falo ta zube tana risgan kuka tare da tsine ma zahra albarka, tanayi tana daukar alwashin rama marinta a jikin zahra saidai in sakin ta zaiyi ya sake ta, amma tayi alkawarin, cin uban zahra la'ada waje, take ta dauka wayarta ta kira wata kawarta Mara mutunci, da wannan Mara kunyar kanwar tata wacce tama su ummi tsaki ranan nan.
Take dukkansu suke Ce ta basu nan da ƴan awanni gasunan zuwa, share hawayen ta tayi, tayi kwafa, tace wlh yau saikin gwammace da baki taba sanin mijina ba a duniya.
Allah sarki zahra sha ɗaya nayi ta shiga kitchen cike da ɗoki , yau zata fara girki a gidan aurenta.
Tunanin me zata girka ta shiga yi, da'ker ta samu ta tsaida abinda zata girka, a nutse cike da kwarewa ta fara aikinta, kafin 2 ta kammala abinka da gas, mai kai takwas😝
White rice tayi da stew, da yaji naman kaza, ta hada pineapple juice , da farfesun cat fish, sai coslow, dayaji dafaffiyar kwai da hanta.😋
Sababbin kula mai kyau ta dauka ta zuba abincin a ciki, tunani ta shigayi, ta ina zata samu ta Sanar ma Maryama ta gama lunch, ita dai baza taje part dinta ba,ita ba saboda maryama tayi girkin ba tasan ba lallai taci ba don yara tayi, tausayin su ya kamata tun daga lokacin da Barr ya gaya mata, maryama bata basu abinci ba tun jiya sai hanan ne ke jagwalgwal musu, tana wannan sake saken taji ana knocking zuwa tayi ta bude, hanan ta gani tsaye rike da hannun karamin kanin su Ahmad, murmushi hanan ta sakar mata tare da cewa"anty ina wuni" itama zahra mayar mata da martanin murmushin tayi tace "A'a yaya hanan ina gajiya ya gida" da yake ta Riga tasan su tun kafin suyi aure tasan hotunan su da sunan kowanne su, zahra tace "ku shigo mana hanan" kin shigowa sukayi sai ma dan wayge wayge da taga hanan d'in nayi kafin a hankali cikin raɗa tace"anty dan Allah kina da abinci kiba ahmad tun ɗazu sai kuka yakeyi yunwa yakeji mummy bata bamu abinci ba tun jiya" tausayin yaran ne ya kara cika zuciyar zahra har taji kamar ta zubar da kwallah, amma ta dake, tace "karki damu hanan ni nayi muku girki mai dadi shigo ki karbar muku kije kuci," tsayawa hanan tayi tana kallonta taki shiga gane kamar yarinyar tsoron shiga dakin take da alamar an mata kyakkyawan gargadi akan shiga lamarin zahra, cewa zahra tayi ta jira ta bari ta , dauko masu, komawa tayi ta dauko kulolin ta samu tire ta jera musu komai akai ta fito ta mika mata, cikin tsananin jin dadi hanan ta mika hannu zata karba, sai ji sukayi an bangaiji tire kamar daga sama, daga zahra har hanan ba Wanda ya lura da tahowar maryama, abincin gaba daya ya zube ko kadan be rage a kullan ba, wani wawan mari maryama takai ma hanan kafin ta mude mata kunne ta figi hannun Ahmad taja su kiyy zuwa part dinsu tana shiga ta rufe hanan da duka da zagi.
Zahra na tsaye a inda suka barta tanajin duk abinda ke faruwa, kwallah ne suka sauka akan kuncinta na tausayin hanan ,dukawa tayi ta tattara kulolinta, ta shige dakinta.
Daidai lokacin kuma kanwar Maryama farida da kawar ta atika suka diro cikin gidan.
Tarar wa sukayi maryama na dukan hanan nan suka hana tare da tambayar ba'asi, kwashe abinda hanan d'in tayi na zuwa tambayar abinci gun zahra tayi ta gaya musu, nan farida ta kara mata da rankwashi da zagi.
Kallon su maryama tayi tace "abinda yasa na kiraku so nake muje ku tayani naci uban wancen karamar yar iskan, so nake in nuna mata ƙwaruru ba tsaran wake bane, wai harni ni Barr zai Mara akan wannan yarinyar, tunda mukayi aure shekar goma sha hudu kenan ko dungurina bai taba yi ba, sai yau dan ya auro wannan figaggiyar, " a zabure farida tace "ma me? mari fa kikace yaya maryam, kuma akanta, lallai yau zamuci uban yarinya, la'ada waje, ta yadda ko ganin ki tayi sai gabanta ya fadi" itama atika kumfar baki ta shiga yi kafin suka rankaya zuwa part d'in zahra.
Hanan na jinsu duk hankalinta ya tashi, ita dai bata son su je su duki anty amaryarsu mai kirki kamar yadda ta lakaba mata, tunanin me zatayi dan dakatar dasu ta shigayi,dan hanan yarinyace mai matukar wayo.
Zahra bayan ta koma dakinta da kwanukanta da maryama ta barar kitchen ta wuce dasu ta wanke abinta, kafin ta zuba nata abincin ta wuto parlour ta zauna tana ci tana tunanin su hanan, Ahmad ma ne yafi bata tausayi shida yake karamin yaro màra wayo ace an barshi da yunwa haka, tana