Header Ads
Showing 201001 words to 201974 words out of 201974 words

Chapter 68 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1726

Ads at the middle of Article

damuwa Kuma hakan bazai zama takurawa ba." Yace "ba komai my luv ki faɗi duk bukatar ki idan bai sabawa Shari'a ba, Kuma baifi karfina ba na miki alkawarin ko menene zan miki, domin na faran ta miki kamar yadda kika faran ta min."sauke jiyar zuciya tayi tace "baifi karfin ka ba insha Allah." Dan shiru suka yi gaba ɗaya shi yana sauraren ta ita Kuma tana tunanin yadda zata faɗi bukatar ta,ta yadda bazai mata wani gurguwar fahimta ba, can dai ta daure tace "Dan Allah da manzon sa, Aslam so nake ka raba nama gida da Asmah." Shiru yayi ya bai bata amsa ba da alama ma ya fada tunanin, dagowa tayi suka tsirawa juna idanu gyada mai kai tayi tace "dan Allah da manzon sa karkace A'a Kuma karka tambaye ni dalili." Ta karashe maganar hawaye na cika mata idanu, tausayin ta taji ya mamaye mishi zuciya take tsohuwar Zuma ta motsa yana son zee sosai itama don ita din zaɓin shi ce, amma fa ko rabin na Asmah baikai ba, yana adalci a tsakani su a komai amma banda gurin nuna soyayya, shi Kuma wannan kadai ne jarabtar shi, ganin hawaye ya fara wanke fuskar ta yasa yace "ya isa haka Zainab ki share hawayen ki zan miki abin da kike so shi kenan zaki koma gida na dake odoye yayi miki." Rungume shi tayi tana gyada kai, take ta shiga jero mai godiya ta kare da cewa dan Allah karya gayawa Asmah sai ranar da zata tare ɗin ya ko yi mata wannan alkawarin, tare da cewa tabar komai nata na nan a kwai komai acan gidan taje ta duba abin da bai mata ba sai a canza mata, wanda babu Kuma a siya a saka mata.


Hakan ce kuwa ta kasance daga ita sai shi suke ta shirye shiryen su na komawan ta odoye ba tare da Asmah ko wani nashi ya sani ba har suka gama kwashe kayan sawan su a gidan Asmah bata sani ba, sai ranar da zata wuce da safe shida zee ɗin suka saka ta a gaba suna bata hakuri tare da gaya mata batun tashin, aiko kamar saukar aradu taji zancen, take ta
daka tsallen albarka tace bata yarda ba, rarrashinta suka shiga yi amma taƙi kula ko daya daga cikin su, wasa wasa fa fushi tayi sosai dasu har su mummy ta kira takai karan su amma ba wanda ya goyi bayan ta sai dai a bata hakuri , tanaji tana gani zee ta bar gidan aranar tare da little koda take sallaman ta kin amsa ta tayi saima ficewa da tayi ta bar mata ɗakin ta shige wani ta ɓamo kofa ta murza key tana hawaye, itama zee jikin ta yayi bala'il sanyi ji take kamar ta fasa amma Kuma inta tuna mafita take neman musu ta yadda zaman lafiyar su zai dore sai taji zuciyar ta ta ƙarfafa, komai idan ana nesa nesa da juna yafi armashi, Kuma duk abin da Aslam zaiyi ma ɗaya, ɗaya baza ta gani ba bare taji haushi ai kazantar da baka gaji ba tsabtace inji hausawa, wannan shine mafarain rabuwar gida tsakanin zee da Asmah Kuma hakan ya taimaka ma zaman su sosai da sosai Asmah tayi fushi Kuma daga karshe da kanta ta sauko har taje taga gidan zee din ta saka mata albarka suka ci gaba da zumuncinsu kamar yan uwa ba kishiyoyi ba, wannan kenan.




BAYAN SHEKARA GOMA


Abubuwa da dama sun faru a cikin waɗan nan shekarun masu daɗi da marasa dadi, kadan daga cikin marasa dadin akwai mutuwar Alhaji baba da hajiya mama, wanda tsakanin su wata biyu ne kacal, cikin masu daɗi akwai haife haife da akayi sosai a cikin ɗan waɗan nan shekarun batool da zahra yayan su hudu hudu, Khadijah uku, Amira shidda, dan yan biyu ta jera har sau biyu bayan haihuwar daddy, kwanciyar hankalin da nutsuwa ya watada a cikin zuciyar Alhaji baba, yan matan mummy zuwa wanan lokacin sun zan manyan mata zumunci da shakuwar su kuwa kullum gaba yakeyi, kowacce ta tara zuri'a tana zaune lafiya a gidanta sai hamdala. Asmah kam zuwa wannan lokaci ta zama Babbar mace ƴaƴa sun baibaiyeta ta ko'ina tun daga haihuwar su mummy kofar haihuwa ta bude mata dan ko wata biyar yaran basu rufa ba wani cikin ya bayyana a jikin ta, ta haifi yan biyu kaza bayan su ta sake yin ƴan daɗɗaya sau uku sai kuma abin ya tsaya tsab kamar anyi ruwa an dauke,a bangaren zee ma zuwa wannan lokacin komai alhmdllh dan itama ta waye ta shigo gari Asmah ce data fahimci kamar batasan komai a bangaren ba ta saura ta akan hanya tare da wayar mata dakai babu hassada ko munafirci a ciki dan ita wlh tausayi zee ke bata kula tsakanin ta da Allah take sonta har zuciya, aiko dai zee ta ga gurin zama kama jiki tayi itama gyara takeyi sosai tunda ta fahimci yana da mahimmanci sosai ga mace musamman mai kishiya dan ta fahimce tashin gyara na daya daga cikin abin da yasa Aslam yafi fifita Asmah akanta, ta ƙara haihuwa itama y'ay'a biyu bayan little duk maza daya Dad da alhaji Abdur-rahman, Aslam ya samu kwanciyar hankali yayi wani ƙiba ya zama babban mutum matan shi kuwa Kansu a haɗe yake kamar yaya da ƙanwa, haka ma ƴaƴan su dan tuni su mummy suka koma hannun zee da zama little kuwa yana wajen Asmah dan shi na wajen ta dama,yaran idan ba ka sani ba baza ka iya tantance wa'inne ne na Asmah ba haka baza ka iya gane su waye na zee ba, zee suna kiranta da mammah kamar yadda sukaji little na kira Asmah suna kiran ta da mummy abin gwanin birgewa sai wanda ya gani masha Allahu lakuwata illaha billah.....






Karshe




Alhmdllh! Alhmdllh!! Alhmdllh!!




Oum Ummeetarh
07041130088

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads