Showing 63001 words to 66000 words out of 201974 words
Chapter 22 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
mummy suna zaune suna tattaaunawa ga akwatina nan a barbaje a gabansu ba'akai ga kwashewa ba, hango zahra sukayi a guje dankwali a hannua, da sauri mami ta tare ta , tana tambayar ta lafiya, nan ta rattaba musu abinda ke faruwa, da sauri suka dunguwa zuwa ɗakin , daidai batool na tsaka da tsula tsiyarta, mami ganin haka hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba mummy kam kallo daya ta mata tasan cewa na karya ne , kasancewar ta San yan matan nata farin Sani, tasan halin kowacce, tasan abinda kowaccen su zata iya aikatawa,.
Ummi karasawa tayi ta tallabota ta shiga tofa mata ayatul kursiyu,mummy kam kwafa taja ta fice daga dakin dakinta ta nufa ta dauko wayar chargi mai kauri ta linka shi biyu, ta dawo ɗakin kallon ummi da mami tayi ta musu signal da Ido akan su kauce, kasancewar idanun batool a rufe yake yasa bata san wainar da ake toyawa ba,ummi ta bude baki zatayi magana mummy ta mata alamar shiiiii da hannun, kaucewa kuwa sukayi,.
Batool jin su mami da suka rirriketa sun saketa yasa taci gaba da birgima tana bige bige, tana cewa "wlh bana sonsa wlh karku aura min shi inba haka ba zan kashe kaina ,wayyo Allah na" takai wannan ayar zata dauki wani taji saukar bulala , a jikin ta , ba shiri ta buɗe idanu, mummy kam ganin haka yasa taci gaba da lafta mata wayar charjin duk inda ta samu a jikin , tana cewa "zaku fita ko baza ku fita ba, kaga shedanu,nace zaku fita" batool da zafin duka ya fara ratsata, ta shiga cewa "munfita mummy munfita wlh munfita kiyi hakuri , Mummy batool ce batool ce," ganin mummy ba ta da niyyar kyaleta yasa ta mike ta saiti hanya ta fice da gudu daga dakin, mummy tace "ja'ira mu zaki kawowa shedanci" biyo bayanta tayi, aiko ta kara kwasa da gudu,.
Daidai su Asmah da Khadijah sun shigo falon , faɗawa jikin Asmah tayi ta kamkameta , mummy kam ta na zuwa ta shiga neman inda zata ci gaba da zuga ma batool charji, aiko ba hanya dan duk inga mummy ta daga bulala ita kuma zata tura Asmah , ganin haka yasa mummy kyaleta don karta je ta zuga ma Asmah bataji ba ba ta ganiba,.
Daidai nan ummi tazo ta janye batool d'in ta rungume ta , suka nufi dakin su, sai sauke ajiyar zuciya takeyi akai akai,.
Kwantar da ita ummi tayi tana share mata hawaye, da haka baccin wahala ya kwasheta sai sauke ajiyar zuciya takeyi , har a cikin baccin,.
Washe gari hajiya addawiyya mai gyaran amare ta dira a gidan kawar ummi ce, ta kware gurin gyaran jikin amare da kayan mata ingantattu, ciki da bai take gyara amare, katon shago gareta, bata bin mutane gida inba mutum ya gayurta ba, wannan ma saboda Ummi ne yasa ta amince ta zo, albarkacin kawance, daki aka bata guda a part din mummy, dakin dake kallon nasu batool,.
Ba bata lokaci hajiya addawiyya shiga gudanar da abinda ya kawota gidan, Asmah zahra da Amira gyara suke amsa na musamman ciki da bai, batool kam cewa tayi ita bata son ko wani gyara ita baza tayi ba, rarrashin duniya ummi ta mata amma taki amincewa saida ta gaji ta hada ta mummy ta mata Jan I do sannan ta yarda anayi tana matsar kwalla ita fa bill haqqi bata so.
Kwana biyu da zuwan addawiyya su Asmah suka fara daukan haske, kowa ya kalle su saiya kara tun ba'aje ko'in da gyaran ba kenan, ganin haka yasa Khadijah yin tsallen albarka ta dire tace itama sai an mata , dole ummi ta saka baki hajiya addawiyya ta aminc ta haɗa da ita.........
Manage pls yau ban wuni a gida bane🙏
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fisabillilah🙏.
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiy ! ea Allah kajiqan iyayen mu}
Page 75 & 76
~ASLAM~
Yau kimanin kwana bakwai kenan yana fama da matsanancin ciwon kirji da zazzafan zazzabi, idan abin ya turnike shi ya kama wani irin tari, a wahalce yana kaki daya tofar jini ne haɗe da majina , abin tun yanayi kadan kadan, har ya rinjaye shi gashi baci ba sha , Dr bashir ne ke zuwa har gida yana kula da shi, yana matukar tausaya ma halin da Aslam yake ciki , yayi yayi suje asibiti a duba shi da kyau don dole wani abin sai Anje asibiti amma Aslam yaki, taurin kan Aslam da kafiyar shi ba karamin Mamaki yake bashi ba, idan ya cika damun shi da magiya akan ya yarda suje hospital, sai yace ya bar shi kawai ya mutu indai bazai samu Asmah ba baiga amfanin ci gaba da Rayuwa ba.
Amir Dr bash ya samu da maganar ganin idan har yayi shiru Aslam ya mutu a wannan halin yana da Alhaki akai , Amir ma abin ya bige shi, hankalin shi bai tashi bama, saida yayi ido biyu da Aslam, wayyo Allah shikam kasa juriya yayi saida ya zubar da hawaye, yana tsugune a gaban shi rike da hannunshi yana hawaye , wani amai ne ya tasowa Aslam d'in kan kace kwabo ya shiga kwara shi,amai ne na jini harda guda guda yana gamawa ya shiga sauke wani irin numfashi kamar zai shiqe a take, kamkame hannun shi Amir yayi yana hawaye da majina, cikin muryar kuka yace"dan Allah dan uwana kar ka mutu ka barni , dan Allah ka tashi , akan Asmah ka saka kanka a ciki wannan halin, " wani murmushi ya saki Wanda da ka kalla kasan na tsananin azabar ciwo ne, ya kara kamkame hannun Amir dake cikin nashi , da'ker ya bude baki yace,"dan uwana Amir rayuwata ba ta da anfani idan har babu Asmah a tare dani, itace rayuwata idan har ban mallaketa ba na tabbata mutuwa zanyi ɗan uwa ka dena wahalar da kanka a kaina, ni nasan tawa ta kare, a duniya" Amir yace "kadena fadin haka ɗan uwa, ka amince akaika asibiti, nikuma na maka alkawarin samo maka Asmah, zata zama mallakin ka , da izinin ubangiji" juyowa yayi ya kalli Amir a wahalce yace"ta yaya zata zama mallaki na,? ta yaya bayan alhaji baba ya riga yayi mummunan furici akan mu, cewa fa yayi ko bayan ransa bai yarda na kara mallakar ta ba, bayan haka kuma ga ɗan uwa na Kamal na tabbata shima yana sonta kwatan kwacin yadda nake sonta,sannan kuma ita karan kanta Asmah bata sona ba ta so na ba ta so na" haka ya ta maimaitawa tun yana fadi dakyau har ya koma faɗi a rarrabe kafin, kuma hannun shi dake cikin na amir ya saki, idanun shi ya kakkafe numfashin shi ya dauke diff.
Innalillahi wainnailaihi rajiun , Amir ya shiga furtawa hankali tashe , dan ya riga ya gama sadakarwa sun rasa Aslam, cikin fitar hayyaci ya mike ya fice daga gidan bai zame ko ina ba kuwa sai tsakiyar falon alhaji baba, .
Alhaji baba na zaune a falon shi yana kallon labarai a tashar BBC , sai gani yayi Amir ya shigo mishi falo afujajan, idanun shi jajur, nil down yayi a gaban Alhaji baba dake zaune akan kujera 3 ya daura kanshi a cinyar alhaji baba, ya mika hannu ya rungume alhaji baba a hakan da suke , kafin ya fashe da wani irin kuka maiban tausayi,.
Tun shigowar shi falon kallo daya alhaji baba yamai gabanshi yaji wani irin mugun faduwa gaba , take ya shigar maimaita innalillahi wainnailaihi rajiun a zuciyrshi, har zuwa sanda ya rungume shi yana kuka abinda yake fadi kenan,bai yi kokarin dakatar dashi ba saida yayi kukan sa ma,ishi, ya shiga sauke ajiyar zuciya ,ganin haka yasa alhaji baba cewa "Amir menene meke faruwa" cikin dasasshiyar murya yace,"alhaji mun rasa shi , mun rasa shi saboda furucin ka , mun rasa shi saboda tsautsauran ayinka, dan uwana Aslam ya bar gidan duniya saboda , kaunar abinda yake halal a gare shi kaikuma ka haramta mai".
Mummunan faduwa gaban Alhaji baba yayi, dajin furucin Amir, koda Aslam yake mara biyayya a gare shi, yana matukar kaunar shi, kaunar ce ma ta sa ya zabe shi a cikin zaratan matasan jikokin nashi har su uku ya bashi auren Asmah,.
Kafin yakai ga furta wani kalma wayar Amir ta dauki ringing dubawa yayi ganin Dr bash ne yasa Amir daga kiran ya kara a kunne cikin sanyin jiki, daga can bangaren Dr bash yace"Amir bai mutu ba suma yayi ,yanzu haka muna asibiti, saika sanar a gida, ka kwantar da hankalin ka amir insha Allahu everything will be alright, yanzu dai ga doctors nan sun rufa a kanshi insha Allah za'a shawo kan matsalar, idan hakan bai yuwu ba dole akwai wani aikin da za,amai wanda muje da tabbacin za,a dace" ajiyar zuciya amir ya sauke a baiyane ,yayinda shi kuma Alhaji baba ya sauke nashi a boye.
Gaskiya wannan lamarin ba karamin tayar mai da hankali yayi ba ,amma da yake namijin gaske ne dakewa yayi , dan kuwa Amir dake tsugune gaban ya kura mishi ido yana so yaga yanayin yadda zai karbi maganar, bai fahimci komai ba, bude bakin shi yayi cike da dattako yace"kul nasake jin wadannan kalmomin na fitowa daga bakin ka Amir kada bacin rai yasa ka tuhumeni da dalilin ciwon dan uwanka , Aslam shiya hallaka kanshi da kanshi , cikin girma da arziki na dauki Asma'u na bashi ita ba tare da ko sisin shi ba , amma daga karshe kaga abinda ya saka min dashi, sakin ta yayi fa ranar da aka kaita gidan shi a mastayin matar sa, wani kiyayyace tafi wanna , ina mai fada baisan ya bani hakuri ba , baisan yaba iyayenshi hakuri ba , don shi gani yakeyi bai aikata wani laifi ba, na barshi da zabin nasa ya aura , to da yake shi Allah kasan kamun sa , ba irin namu bane , cikin ruwan sanyi Allah ya bi mana hakkin walakantamu da yayi , nasan kanada lamarin komai daya faru tsananin shi da zabin nashi, ko wannan bai ishe shi ishara yasa ya dawo da baya ya nemi garafan iyayen shi ba, ina cikin haka kwasam na samu labarin wai yana son Asmah, wlh da farko ban yarda ba saboda nasan inda kunya bai isa ya budi bake yace yana son Asmah ba, koda ace kamal bai Ce yana son Asmah ta bazan yarda Aslam ya kara aurenta ba , sai kuma abin yazo cikin sauki kamalu ya nuna yana da muradi, Allah sarki rashin Sani yafi dare duhu, inda nasan haka zai kasance da kamal din zan aura mata tun. farko da duk abin bai zo da haka na, amma sorry to say ya makaro kaima shaida ne bana magana biyu , Aslam inhar son Asmah zai hallakashi saidai ya mutu indai nine Wanda zansa baki ya aure same ta " da sauri amir ya mika hannu ya daura akan bakin Alhaji baba, alamar yayi shiru karya karasa fadan abin da yake son fada, shi tsoran shi daya ma kar Alhaji baba ya rantse dan idan ya rantse abin zaifi rashin kyau.
Kamal dake labe bakin kofa ja ya dingayi da baya da baya idanun shi sunyi jajur, tun shigowar Amir gidan akan idanun shi ne ganin yanayin da ya shigo kamar ba cikin hayyacinsa yake ba yasa yabi bayan sa , saidai jin kalmomin dake fitowa daga bakin Amir yasa ya ci wani wawan birki daga bakin kofa, yana gama sauraran komai ya juya da wani irin sauri ya bar gurin mortar shi ya fada ya figete da wani irin gudu mai ban tsoro,
A can asibiti kam kusan awa shidda kwarara manyan likitoci suka kwashe akan Aslam kafin su shawo kan matsalar, a kwance yake kamar gawa fuskar shi sanye da na'uran jawo numfashi wato oxygen
A kofar dakin da aka kwantar da Aslam kuwa , kamal, Amir, Abba, Daddy, mummy, ummi, mami, hajiya mama, bello, yam matan mummy, Khadijah, duk zaune suke wasu a tsatstsaye wasu na safa da marwa, kowa ka kalla cikin su fuskarta, ko fuskar shi dauke yake da matsanancin damuwa masu kuka nayi masu hawaye nayi masu addu'a nayi,.
Baifi minti ashirin ba da wani babban likita ya tabbar musu da cewa wannan baccin da Aslam keyi , zai iya daukar kwana uku a haka yana bacci , bayan kwana uku zai iya farkawa a kowannen lokacin, idan ya farka ma ana saka ran Abu daya cikin uku ,either ya farka qlau, asamu nasara ,kokuma ya farka ciwon ya qaru har fiye da nada Wanda hakan zaija sai an fitar dashi kasar waje anmai aiki, shima din aikin cikin kila wa kala don zai iya yuwuwa kafin a fara aikin sai sun nemi a saka hannu akan yarjejeniyar , idan anyi aiki ,dayan biyu zai iya kasancewa, either Rayuwa ko mutuwa, na uku kuwa shine mai gaba daya wato zai iya yuwuwa daga wannan barcin ya zarce kushewa, zuciyar shi Ce ta tabu sakamokan saka mata tunanin wani Abu da kuma yake da tabbacin bazai samu ba , wannan dalilin ya haifar mai da wannan irin tabuwar zuciya mai hadarin gaske.
Wanna jawabin na Dr James shiya kara hargitsa tunanin wadannan family na Alhaji baba, gashi gaba daya an hana su ganin Aslam din don dakin da yake kwance ba mai ikon shiga sai likita da nurse,.
Idan kuna bukatar ganin majinyacin ku saidai a nuna muku shi ta CCTV dake dakin,.
Haka suka karkare wuni a wurin sallah ne kadai ke tada su, abinci kam ranar sun manta da ana cinsa a duniya don ba Wanda yaji yunwa a cikin su , sai wurin karfe goman dare daddy ya tarkata su kowa ya wuce, ummi da mami da kamal da Amir ne suka tsaya suka kwana a asibin tare dashi. Washe gari ma haka suka wuni gwanin tausayi , kamal kam tuhumar kanshi yakeyi da cewa idan Aslam ya mutu dasa hannunshi a ciki domin tun farko daya hakura da Asmah lokacin daya gane Aslam na Santa da duk hakan bata faruba gaba daya ya dauki laifin komai ya daura ma kansa.
Ranar daya cika kwana uku yana barci da misali goma na Safiyar asabar Wanda yayi daidai da sati daya ya rage daurin yan matan mummy, Aslam ya fara motsi alamar zai farka daga daga baccin daya tafi na kwana uku, ma'aikaciyar dake kula da bangaren CCTV na asibitin ne ta farga da farkawar shi ba shiri ta dannawa babban likita dake kula da case din Aslam waya Dr James ,.
Cikin gaggawa ya nufi dakin da Aslam ke kwance oxygen ya cire mai da wasu na'urorin dake jikin shi.
Ja yayi da baya ya hade hannaye ya kulle ido ya shiga jero addu'o'in su nayan choci , far far ya fara yi da idanun shi a hankali kafin daga bisani ya bude su tar, akan fuskar Dr James dake tsaye shi daya kwllin kwal a dakin, daidai shima ya gama jero addu'a ya bude ido,.
Daga yanayin yadda yaga kwayar idanun shi kadai ya tabbatar da insha Allahu aiki yayi kyau, motsa baki Aslam ya shigayi alamar yana magana ne amma rashin karfin jiki yasa maganar bata fitar da karfi, ganin haka yasa Dr James ya matsa kusa da Aslam din ya tasa kunnen shi a wurin bakin shi yana sauraran me yake fada,.
Alhaji baba daddy mummy nake son gani yanzu, sanin irin laruran shi daya shafi matsalar zuciya, gara a bashi dama ya fadi abinda yake son fadi kar ya kara saka shi a zuciya ya dawo musu da aiki baya,.
Dr James fita yayi wurin tarin yan uwan majinyacin da suke matukar bashi tausayi, ganin yadda suka zuba mai idanu yuuuuu yasa tun daga nesa ya fara sakar musu murmushi alamar aiki yayi kyau, Abba ne ya fara tambayar sa yaya ya farka, don tun da aka sanar musu da ya motsa gaba daya suka shiga zulimin , a wani hali zai farka, wanne daga cikin ukun da Dr ya gaya musu ne,..............
Kuyi hakuri yauma dai abin ba yawa ga ba editing🙏
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fisabillilah🙏
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu.}
Page 77 & 78
Dr James ya kalli Abba yace,"ya farka, kuma we thanks God, ga dukkan alamu aiki yayi kyau, saidai kuma akwai wasu abubuwa da ya kamata a kiyaye, wanda kiyaye su shine zaiba patient din daman gama warware da wuri rashin kiyaye su kuwa zai kasance makamashi ne na fama ciwon har fiye da da,".
Daidai lokacin Alhaji baba da Alhaji Mallam suka shigo cikin asibitin, dukkansu fuskokin a haɗe alamar kaman sun samu wata matasala a tsàkaninsu, Alhaji Mallam zuwànshi asibitin na uku kenen yayinda alhaji baba zuwan shi na farko kenan,.
Kusan kowa yayi mamakin ganin Alhaji baba a asibitin, amma kuma ba Wanda keda ikon tambaya akan dalili , Abba ne ma a zuciyar shi yayi hasashen duk yadda akayi Alhaji Mallam ne ya sako shi a gaba zuwa asibitin, domin duk duniya babu Wanda ke iya saka Alhaji baba kuma ya hanashi ya hanu kamar Alhaji Mallam, haka shima Mallam din, Alhaji baba kadai ne kedai iya tursasa shi yin Abu, tun suna yara suka ba junan su wannan daman.
Bayan gaggaisawa Dr James yaci gaba da cewa"kafin na faɗa muku abubuwan daya kamata ku kiyaye a game da patient dina a matsayinku na ƴan ruwan shi, a kwai wani roƙo guda ɗaya da nakeson na maku, nasan nan cikin ku akwai mahaifiya da mahaifin shi akwai ƴan ruwan