Showing 66001 words to 69000 words out of 201974 words
Chapter 23 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
mahaifansa akwai yayyi da kannen sa kai harma da kakanin sa ko",amsawa wasun su sukayi yayinda wasu suka gyda kai,.
Dr James yaci gaba da cewa"dan Allah idan kunsan abinda patient dina yake so da har ya saka shi a rai ya haifar mai da wannan mummunan ciwo ku bashi ko kumu shi abinda yake so, idan kuka mai haka ina mai tabbatar muku zaku nemi ciwon nan ku rasa gaba ɗaya a jikin sa, domin shi ya haifar da cutan, kunga kenan shine original maganin da zai warkar da shi gaba ɗaya don wannan aikin ba yana nufin ya rabu da ciwon kwata kwata bane,yadai kwantar da ciwon ne kuma zai iya tashi akoda yaushe, so ina rokon ku pls and pls ku mai abinda ya keso" Abu na biyu patient ɗina yana da bukatar ganin, mummy da Daddy da kuma Alhaji baba, to idan suna nan zamu Baku dama ku shiga gare shi , amma banda hayaniya da yawa kuma banda fada mai maganganun da suka shafi ciwon shi, ma'ana abin da zai iya tayar mai da ciwon shi,.
Abba yace ta "Dr mun gode amma inda hali ka Bari mu shiga gaba ɗayan mu domin dukkan mu nan muna bukatar ganin sa , ko dan hankalin mu ya kwanta"
Dan shiru Dr yayi kafin yace"zaku iya shiga amma, dan Allah banda hayaniya , banda kuma maganar da zata tayar mai da hankali, amma ku bamu minti biyar mu canja mai daki tukunna, " juyawa Dr James yayi ya koma dakin kamar da minti uku sai gashi an fito da Aslam daga wannan dakin da mutane basa shiga zuwa na kusa dashi, Wanda anan ake ajiye duk Wanda ya fito daga wancen dakin,
Har cikin dakin ya Dr James ya musu jagora, yana kwance akan gadon marasa lafiya na ɗakin, karin ruwa ɗaure a hannun shi, dukkansu da kallon tausayi suke binsa , ya rame ya jeme ya ƙara fari fat, idanun shi sun zurma sunyi zuru zuru, abin gwanin tausayi.
Ware idanu yayi yana bin mutanen dakin gaba daya da kallo, akan Alhaji baba ya tsaida kallon shi, buɗe baki yayi a hankali , idanunshi sun cicciko da ruwan hawaye idanun shi cikin na Alhaji baba yace"na Sani ni mai laifi ne a gareka, laifi kuma mai girma, na tuna ranar da kake cemin, wata rana zanyi nadamar abinda na aikata ,ranar da nadamar baza ta amfaneni ba, yau ga ranar tazo, kuma as u say a lokacin da danamar bazata amfaneni ba,", haɗe Hanna yenshi yayi muryar shi ta fara rawa, idanun shi still akan alhaji baba ya cigaba da cewa "dan girman Allah Alhaji baba, dan darajer annabin rahama( S a w) ka yafemin abinda na aika ta a gareka ina rokon ka gafara, bazan iya tashi daga kan gadon ba balle na duƙa maka, nayi babban kuskure a rayuwa ta, kuma na gane kuskurena, na Sani wannan ciwon da nakeyi shine ajali na, inaji a jiki na bazan tashi daga kan gadon nan ba, don Allah kace ka yafe min ko na kwanta kabari na cikin salama," daidai lokacin wani kuka ya kufce mai , mai ban tausayi,.
Tuni daki ya kacame da koke koke masu ruwan hawaye kuwa tuni ya wanke musu fuskoki , babu abinda ke tashi a ɗakin sai sheshshe ƙan kuka, mazan ne ma masu taurin zuciya , suma ko wanne ka kalla cikin su idanu yayi jajur kamar garwashi,.
Idanun shi ya mayar kan Daddy da Mummy, cikin muryar shi dake fita a wahalce yaci gaba da cewa "iyaye na daddy mummy ,kuma kuyi hakuri akan duk laifin da na aikata muku, duk bacin ran dana sanyaku tun daga haihuwata har zuwa yau, ku dubi girman Allah ku yafe min, idan da fushin ku ko kannani a tare da ni bazan ji ɗaɗin kwanciyar kabari na ba", sauran mutane dakin yake bi da kallo yana kiran sunan kowannen su yana cewa su yafe shi shidai yana ji a jikin shi karshen shi yazo ,.
Lokacin da idanun shi suka sauka akanta, idanunta sunyi jajur fuskarta kuwa ta cabe da majina da hawaye, sai sheshsheka takeyi tana ajiyar zuciya, saida ya kureta da kallo na kusan mintuna biyar, kafin ya buɗe baki idanunshi a kanta yace"ki dena kukan nan haka husnah ta , kukan ki yana taba min zuciya ,digar hawayen ki daidai yake da digar, ruwan dalma a zuciyata, bana so na koma ga mahaliccina na barki kina kuka, share min hawayenki kinji my husnah" abin kamar almara samun kanta tayi da bin umarnin sa wato ta shiga share hawayenta da hijabin ta, kallon shi ya mayar kan kamal, dake tsaye kusa da Daddy, yace"dan uwa kamal wasiyyar da zan bar maka itace, dan Allah ga amanar husnah ta nan a hannunka, zan mutu zan koma ga mahalicci na saboda rashinta, ka rike min amanarta karka bari hayawe su kwaranya daga idanunta , itace rayuwata farin cikina sanyin idaniyata,bayan raina ka kula min da ita ka wanzar da farin ciki a cikin duniyar ta, kowani bawa da kalan kaddaransa ni nawa kaddaran rayuwar, itace husnah, ina son husnah so mai tsanani Wanda na tabbata, soyyayar ta itace ajalina , nayi wasa da damata ta farko Dana samu akanta, gashi kuma har yanzu Allah bai bani dama ta biyu akanta ba, kai Allah yaba dama ta biyu akanta soda haka ka riƙe daman ka da kyau ɗan uwana".
Girgiza kai kamal ya shiga yi idanun shi jajur cikin tsananin tashin hankali, kasa tsaya wa yayi, da sauri ya karasa gaban gadon ya rungume Aslam a jikinsa dukansu suka fashe da wani wani irin kuka mai ban tausayi, cikin muryar kuka kamal yake cewa,"A'a ya Aslam dan Allah ka dena fadin irin wadanan kalaman marasa ɗaɗin ji a kunnuwan mu, insha Allah baza ka mutu ba zaka rayu, zaka rayu tare da husnan ka , kuyi aure ku hayayyafan ma su Abba jikoki, indai har saboda Asmah ne ka shiga wannan halin wallahi na hakura da Asmah na bar maka ita duniya da lahira, dama matarka Ce nima karanbani nayi nake Neman shiga gonar da ba tawa ba nayi kiwo," kamkame shi Aslam yayi, a hankali ya shiga furta"A'a ɗan uwana ban cancanci haka ba kada ka sadaukar da farin cikin ka akaina,domin nima ban sadaukar da farin cikina akan na iyayen mu ba". kamal yace "A'a yaya Aslam kafini bukarta ta a halin yanzu na sadaukar maka da soyyaya ta domin rayuwar ka ya Aslam"
Daga bayan su suka tsinci muryar Alhaji baba , yana cewa"ban amince ba, na riga na faɗa ko bayan raina ban amince Aslam ya auri Asma'u ba dan haka ina nan akan bakata , idan kai ka hakura ka janye ka bar masa ni ban janye ba,maganar yafiya kuma daya nema zan yafe masa amma da sharaɗi zan kuma yi masa zabi a karo na biyu, idan har ka amince da zabi na na yafe maka Aslam, Allah ya yafe mana baki daya, kuma kowa ma a nan ina son ya dubi girman Allan daya hada mu dashi ya yafe masa, amma maganar auren Asma'u kam babu shi, na fada na kara, zabina na biyu kuma za'a hada bikin tare da nasu kamalu ne, iya alfarman da zan iya maka kenan" Sakai yayi ya fice daga dakin abin shi ko jiran Alhaji Mallam da suka zo tare baiyi ba,.
Shiru falon ya dauka kowa da irin tunanin da yake sakawa a zuciyar shi, Alhaji Mallam ne yayi gyaran murya, dukkansu suka maida hankalin su a kanshi , Cikin muryar shi ta dattijan da tsantsar ilimin addini ya ratsasu ya soma cewa"a gaskiya Aslam ka aikata babban kuskure a baya amma alhamdulillahi tunda har ka gane gaskiya kuma ka nemi yafiyar wadanda ka bata wa, saidai abinda zan fada maka shine kayi hakuri da Asma'u, tunda kaga haka watakila ita ba alkhairi bace a gare ka , maganar zabin da Alhaji baba yace zai maka ina mai baka shawara da ka karba da hannu bibbiyu , na tabbata zata zame maka farin ciki, kuma ta sakaka ka manta da cewa ka taba son Asmah a rayuwar ka,"
Aslam ya sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya yace"Alhaji a halin yanzu na Riga na cire rai da rayuwata, tunda har na rasa Asmah, domin kuwa itace rayuwata, amma duk da haka nayi farin ciki da zabin ku kuma na karba da hannu bibbiyu , kuma insha Allah zakuyi alfahari da ni a karo na biyu, nasan baza ku taba zabar min abinda zai cutar dani ba wancen karan ma , kuruciya da wauta ne ya sakani aikata aikin danasani,"
Alhaji baba dake laɓe a bakin kofa yana sauraran komai sauke ajiyar zuciya yayi sanna yasa kai ya wuce abinshi bai jira Mallam ba don fushi yake yi da shi ko mai ya hada su ohoo nan gaba zamuji.
~MALAYSIA~
Yau kimanin sati uku kenan da barowarta 9ja , tunda ta saka kafarta a cikin gidan bata kara lafiya ba, hoton yanayi da ta baro Aslam a ciki a police station ya ki fita daga kwakwalwarta, kullum Daren duniya kuka take kwana , ji takeyi da da hali da ta koma 9ja gurin mjinta ta rungume abinta da hannu bibbiyu, amma ina lokaci ya kure mata domin iyayenta babu abinda suka tsana sama da Aslam a duniya wayar ta ma tuni Dad ya amsa ya canja mata wani da wasu layukan, yanzu bata da buri daya wuce ta samu lambar beebalo ta kirata tasan beebalo mai kaunarta Ce zata iya mata duk abinda ta saka ta, mom ne ta turo kafar dakinta ta shigo hannun ta dauke da plat shake da kayan marmari yankakku, masu sanyi, zama tayi a bakin gadon da take ta mika hannun ta taba wuyanta, jikin na nan da zafin kau kamar ko yaushe , tunda ta dawo Malaysia bata kara lafiya ba ga kukan da ta aura tanayi kullum dare ,ga kuma rashin cin abinci,ko ruwa bata iya sha saita amayar fruit kadai take iya CI ta zauna lafiya shima idan taci da yawa sai sun dawo, ga kuma wani tsinkakken miyau dake addabarta, wannan lamari ya matukar daga hankalin iyayen zee, sunje asibiti ance fever ne,.
Yau dai sukayi da wani babban likitan mata Dr habu sarki, kan cewa zaizo har gida ya dubata, kwararren likita ne da samun ganin shi ko Malaysia sai wane da wane, yasan aikinsa sosai ba karamin wuya Dad yasha ba kafin ya samu Dr habu sarki ya amsa gayyatar shi, saida ya zube makudan kudade bana wasa ba,.
Tasar da ita mom tayi tana bata fruit din abaki tana sha kadan kadan , suna cikin haka dad ya shigo dakin , ya sanar dasu isowar Dr, mom tace saidai ya shigo nan ya dubata kaga jikin ba karfi baza ta iya sauka kasa ba ,
Haka ko akayi Dr ya shiga har dakin zee, babu kayan kirki a jikinta kayan bacci ne mai shara shara kanta babu dankwali amma iyayen ta ko a jikin su, dauke kai Dr yayi daga kallonta domin shidai musulmine dan 9ja kuma ba fasiki bane hasalima tare yake da iyalinsa suke zaune anan Malaysia,
Tambayoyi ya shiga mata akan abinda ke damunta tana bashi amsa, yana rubutawa,akan yanayin da take ji ajikinta, bayan ya gama ya bukaci miyanta da fitsari ba bata lokaci aka bashi na'urorin daya zo dashi ya dauka ya shiga gwaje gwaje akan miyau da fistarinta , yana gamawa bayan ya samu amsar abinda yake nema ya kalli Dad yace"Alhaji abdussalam, daughter ka tana dauke da juna biyu ne karami, Wanda ke bata wahala ,duk wadannan abubuwan da takeji a jikinta saboda ciki ne laulayi takeyi"
Cikin tsnananin tashin hankali da kiɗami dad da mom har suna hada baki wurin cewa ciki kuma Dr, Dr yace" yes tana da ciki tabbas" mom tace"Dr wani irin ciki kuma kadai sake gwadawa dakyau"nanta labarta mishi batun zubar da cikin da zee tayi, Dr yace "ana samun haka Ai alluran da wancen likitan ya mata bamai karfi bane kuma ba'ayi wankin ciki ba , to cikin na nan baiyi komai ba saidai yadan koma baya ,ma'ana ya zuba, watannin shi sun ragu,".
Dad da mamaki ya gama kashe shi yace to Dr yanzu abinda nake so dakai"allura zaka mata Wanda zai wanke shegen cikin nan , domin ni bana bukatar hada zuri'a da wannan dan iskan yaron,da daughter ta haife wannan cikin gara taje ta yo cikin shege a waje ta haifa, yafi min alheri akan ta haifi cikin wannan tsinanan yaron Aslam".
Zee tunda Dr ya ambaci cikin jikin ta nanan wani irin farin ciki ya lullubeta , ta shiga yiwa Allah godiya, amma jin kalaman dake fitowa daga bakin Dad yasa ta saurin dagowa ta kalle shi,.
Dr mamakin dad ne ya cika shi kicin mamaki yace"ba cikin aure bane, ma'ana cikin sunnah" dad yace "eh" Dr yace "meyasa make son a zubar ku barshi mana , idan aka kara mata wani alluran zubar da ciki akan Wanda akayi da mahaifarta baida kwari zai iya samun matsala" dad yace" ba komai ayi ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba, na gwammace ta rasa mahaifar ma gaba daya da ta haifi wannan la'a nannen cikin" Dr yace "A'a fa Alhaji rabo yana kisa fa , tunda kaga cikin nan duk gwagwar mayar da yasha bai fita ba Allah ya kaddara rayayye ne idan ka matsa akan a fitar dashi akwai matsala" Dad cikin rufewar ido yace" kayi abinda na umarce ka Dr ko nawane zan biya ka," daga kafada Dr yayi alamar l don't care tunda na gaya maka gaskiya kaki ji ɗinan,.
Wani ruwan allura ya zuka a sirinji, ya saita daidai adadin yawan da ake so na alluran ya nufo zee dashi........... ..
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fisabillilah🙏.
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Page 79 & 80
Wani uban tsalle zee ta daka, nan take sai gata a bakin kofar toilet, kamar ba ita bace kwance shame shame ba lafiya, da kallon mamaki duk suka bita, Dad yace"meye haka daughter ki tsaya ya miki allura mana, ki rabu da wanna cikin da ke wahalar min dake" girgiza kai tayi tace"no Dad bana so kar a zubar inason abuna, zan haifeshi inason cikina" sanƙare wa Dad yayi yama kasa furta ko kalma ɗaya tsabagen mamakin, yace "daughter pls kar muyi haka dake, ki taimakeni a cire cikin nan kinfi kowa sanin yadda na tsani mahaifin cikin nan , bazan iya jurar haɗa zuri'a dashi ba," maƙe kafaɗa tayi kamar wata karamar yarinya yar two years, mom Ce ta kara da cewa"haba daughter kizo mana kinga munbar Dr a tsaye fa " still kin zuwa tayi haka suka shiga rarrashinta da tsoratar da ita akan maganar haihuwa da irin azabar da zata sha, amma ta.musu ƙememe, ta gwammace ta sha ko wacce irin azaba Ce indai baza ta mutu ba akan ta sha azabar rabuwa da Aslam, tasan idan Allah ya taimaketa ko ta dalilin wannan cikin na jikinta dole wata rana zata sake haɗuwa da Aslam ɗinta.
Dr kam ganin sunata lallshinta ta ki yarda , ya ajiye sirinjin ya zare safar dake hannun shi, ya shiga haɗa kayan shi don yana da gurin zuwa da yawa.
~9ja~
Yau Aslam ya cika kwana uku da farkawa, jiki alhamdulillahi yana samun sauki sosai, dan zuwa yanzu yakan mike tsaye da kanshi ya shiga toilet, yana samun kulawa sosai gurin likitoci da kuma yan uwanshi,.
A gida kuwa shirye shiryen biki ake tayi ba kama hannun yaro , tuni baƙi sun fara sauka daga garuruwa mabanbanta, ranar asabar da karfe goma ne za'ayi daurin aure a babban masallacin juma'a dake minna.
Gayyata kam ko ta ina yinsa ake gaba ɗaya gari ya dauka da maganar wannan daurin aure na amare biyar ya gama baibaye garin minna da kewaye , hatta gidajen radio maganar da suke yi kenan a yan kwanakin na, haka gidan TV. NTA minna, duk wata kafar sada zumunta , saida maganar bikin nan ya leka,.
Ba wani program za'ayi sosai ba, saboda matsalar rashin lafiyan Aslam badan haka kam , program din da suka shirya yi yakai bakwai, yanzu kam ummi ta shirya mother's day , sai walima, sai kumbo, sai kuma kidan kwarya da za'ayi ranar yinin biki.
Amir kam baiji dadi ba da alhaji bana yace baza ayi dinner ba , sai cizon yasta yakeyi, dan dinner nan ba karamin shiri ya mishi ba, rashin kunyar daya tanada buhu buhu zaiyi a wurin dinner nan yawa ne dasu, dan duk cikin angwayen Amir ya fisu rawan kafa, hatta pre wedding pictures ba Wanda sukayi, sai shi baban rawan kai, har asibiti yaje kamar abin arziki, ya samu Aslam ya wanke tass, wai ciwon son shi bai tashi tashi ba saida ya bari bikin shi ya zo ya gama tsara bikin shi da irin rawar da zai sha a wurin dinner, gashi yanzu ya rusa mai shiri.
Dariya Aslam ya shiga yi mai dan yafi kowa sanin yanda Amir yaci burin yin abubuwa sosai a bikin shi, suna haka Dr bash ya shigo ɗakin, haduwa sukayi suna tama Aslam tsiya, harda tuna mai lokacin da yake cewa su daina neman ƙana nan yara zasu jamai raini a wajen ƙannen shi, sai gashi shi saboda soyyayar ƙaramar yarinya ya kwanta ciwo harda cewa shiya sadaukar da rayuwa husnah Ce ajalin shi, nan Amir ya tashi yana kwada ma Dr bash abinda ya faruwa ranar da su Alhaji baba sukazo yana kwaikwayan muryan Aslam, dayake bash din baya wurin, aiko dai bashir yasha dariya harda rike ciki,.
Amare sai shan gyara sukeyi ta ko'ina,