Showing 87001 words to 90000 words out of 201974 words
Chapter 30 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
tunanin anya abun da tayi ya dace kenan, ko ba komai Aslam mijinta ne kuma miji yafi gaban wasa, don yana sonta bai kamata ta ringa mai haka ba, gaskiya ya bata tausayi, ya Aslam d'in da ta sani giant baya wasa baya son raini dan gayu dan kwalisa, wanda da ko kallon ta yayi ada sai taji kamar ta saki fitsari a wando tsabar kamewan shi da rashin daukar wargi shine ya dawo haka a hannunta, hmmmm lallai duniya juyi juyi, take shedaniyar zuciya ta shiga ce mata, wai kina nufin har kin karaya kin fara jin tausayin shi, kin manta abubuwan da ya miki a baya kenan, to wlh karki kuskura kiji tausayin shi yanzu saiya kara gasuwa, Allah ne ya kama miki shi ya kuma baki dama akan shi kema ki rama musgunawan da ya miki a baya, shima yaji a jikin shi.
Da haka shedan yayi tasiri akanta ɗan tausayin shi data faraji nan ya wuce.
Minti arba'in ya kwashe yana faman aikin girka sakwara da miyan taushe, harda farfesu, gas biyu yayi don ya yi sauri ya gama kar ranta ya baci ta fasa ci,lokacin da ya fara daka taji kamar taje ta ce ya barshi kawai , amma ta dake, tana nan zaune ya gama ya jera a dinning, zuwa yayi ya shaida mata ya gama,yana dining, kallon shi tayi, ganin duk ya hada zufa, gashi duk ya wani rarrame, yasa taji ya ba'il baya tausayi, tsintar bakin ta tayi da cewa "sannu da aiki ngd" wani dadi ne ya lullubeshi jin abinda tace,kenan ta yaba tunda gashi har da gdy, ya fahimci tana da raguwar zuciya, ta farajin tausayin shi,murmushi ya sakar mata, a zuciyar shi yace na samu logonki yarinya, saura kiris nayi nasara a kanki , zan jure koma meye, har zuwa sanda zaki shiga hannun, zakiyibayanine, saina birkita miki kwakwalwa ta yanda zakiji inba Aslam ba sai rijiya rijiyar ma mai kwalabe.
Ganin ya tsaya kanta yana kallonta yana sakar mata kyakkyawan murmushin shi, yasa tace "pls ka zubomin zuwa nan bazan iya zuwa dinning dinnan ba" yace "angama babyna" juyawa yayi da niyyar zuwa ya zubo mata, tace "wait Aslam" juyowa yayi yace "na'am sweetie" tace " pls daga yanzu baba sonjin baby, ko sweetie ko husnah or whatever, kawai ka kirani ni Asma'u na yafimin" yace "to shikenan an gama mrs Asmah".
Zuwa yayi ya zubo mata sakwaran katon malmala, ya zuba miya a gefe
ya zubo farfesun a wani plate din dabam, ya dauko ruwa da juice ya hado a tray ya kawo mata.
Ajiye mata yayi ya koma garin zaman shi data nuna mai ɗazu, daukan sakwaran tayi ta kai loma daya baki, so yummy ta fada a zuciyar ta, gaskiya yayi dadi, ware wa tayi taci gaba cin sakwwaranta hankali kwance tana Santi, ji tayi idanun shi sun mata yawa akai har tana neman kware wa, ɗagowa tayi ta kalle shi, shima ganin zata dago kai take ya koma fuskar tausayi, aiko dai ya bata tausayin.
Tace "kai baza kaci sakwaran bane" yace "babu saura ai duka na zubo miki" dage kafaɗa tayi taci gaba da cin abincin ta, can dai ta kasa jurewa, tace "ka wanko hannu kazo muci tare to" cikin zumudi yace "da gaske" tace "eh kobaza kaci bane?" yace "A'a zanci" wanko hannun yayi yazo ya zauna kusa da ita yasa hannu sunaci tare, sai kallonta yake yana murmushi, can kuma dan samun guri ya guziro sakwaran wai zai bata a baki, hararan shi tayi, ba shiri ya maida hannunshi bakin shi, haka suka gama, zai kwashe kwanukan tace ya barshi, ita ta kwashe ta kai kitchen ta shiga wankewa, tana ciki yi ya shigo yace ta barshi, itama tace ya barshi haka suka haɗa hannu suka wanke tanayi yana dauraya, har suka gama, ta share kitchen d'in yayi mopping, haka dai suke aikin kadaran kadahan ba wani fira a tsakanin su, ta daure fuska shi kuma sai murmushi yake mata.
Bayan sun gama tsab ta kama hanyar dakinta zata je ta dan huta binta ya shigayi a baya batare da ta sani ba, saida ta buɗe ƙofa zata shige juyowan da zatayi taga mutum a bayanta, gabanta ne ya faɗi don ya bata tsoro, kallon shi tayi tace "lafiya" cikin alaman rashin gaskiya ya shiga Sosa ƙeya kafin karya da zai mata ya faɗo mai, yace" ji nayi kamar kince nazo muje na miki tausa" harara ta wurga mai kafin ta shige dakinta, ta banko kofa tana Jan karamin tsaki.
Murmushi ya sake wani irin nishadi na musamman yake ji yau, jinshi yake makar an bashi kyuatar ticket ɗin shiga Aljanna, a fili ya furta"tausayin na takeji, tausayi kuma alama ce ta soyyaya, zan biki yadda kikeso,zan miki duk abinda kikeso zan maida kaina ba kowan komai ba a gabanki har sai na wanke kaina da dukkan tarin laifuka na a gareki, zan dasa miki soyyaya ta a zuciyarki, ba tare da kin shirya ma hakan ba, zan sakaki ki soni irin soyayyar da baki taba yima wani mahaluki a duniya ba,nayi miki alkawari" ya karashe maganar yana dunkule hannayenshi alamar maganar daga zuciyar shi take fitowa kai tsaye.
~BATOOL~
Yau kimanin wata daya kenan da auren su, kuma har zuwa wannan lokacin babu jituwa a tsakanin su kullum cikin rigima suke da juna,soyyaya ce zazzafa ke dawainiya da zuciyar ko wannan su, amma sun kasa ganewa balle su tsaya suyi rayuwar aure mai ma'ana, Dr bashi da matsala don shi tun ba yauba ya riga ya gane sonta yakeyi bana wasa ba, matsalar daga gare tane, taki ta gaskata zuciyarta dake azalzalan ta kullum akan lamarin Dr d'in.
Kowa zaman kanshi yakeyi a gidan, kowa shi zai neman ma kanshi abinda zaici, batool girkinta takeyi lafiyayye ta zauna taci a gaban shi, yana haɗiyan yàwu, amma ko siɗi saidai yaje yayi takeaway a waje yazo gida yaci kokuma yaje gidan hajiyan shi yaci, kullum cikin fada suke kamar wasu tom and jerry, duk wannan yanayi da suke ciki basu taba raba makwanci ba, ɗaki ɗaya suke amfani toilet daya komai daya duk da akwai wasu dakuna a gidan amma Dr bai yarda da hakan ba, duk fadan da zasuyi kuwa, ba yadda batool batayi ya bar mata dakin ba ya koma wani amma fir yaqi tayi naci tayi mita harta gaji, saidai insunzo kwanciya ta jera pillows a tsakanin su,ta juya mai baya, gata da birgima ta gama jere jeren pillows d'in karshe wataran a kirgin shi take kwana, shiko da ta birgimo jikinshi ya kara rungume ta susha baccin su,inta farka ta ganta a nan kuwa ta hau bala'i tace shine ya matsota dama dan haka yaki canja ɗaki.
Yau ta kama lahadi babu aiki kuma yaune ya saka rana zai dauke ta suje ta gaida hajiyan shi, don tunda akayi bikin bata fita ba, hajiyan da kanta ne tace karta fara fita yanzu ta bari ta dan kwana biyu sai ya kawota, kannen shi kuwa yammata zuwan su uku, kuma ba laifi tadan saki jiki dasu, dan kwata kwata basu da matsala ƙauna suke nuna mata sosai, anty sama anty ƙasa, duk da sun girmeta a shekaru ƙaramar su ce kawai zasu iya zuwa sa'anni, ashmat da amrah ma sun dawo so d'aya.
Misalin karfi takwas na safiyar ranar lahadi, kwance take a gadon ɗakinsu tayi daddaya abinta , don tunda ta idar da sallah, tayi azkar da addu'o'in ta ta koma ta kwanta bacci mai nauyi ya kwasheta, cikin baccin taji ana yayyafa mata ruwa a fuska , ba shiri ta ware idanunta cike da masifa,dan tasan aikin wanene wannan, wannan Ai wulakanci ne.
Maganar da zatayi ne ta makale hango shi da tayi tsaye gaban mirror daure da tawul a kugu ya juya baya, da alama daga wanka ya fito, lallausar farar fatan jikinshi mai sulbi dauke yake da dotdot naruwan wankan dayayi, mataji ne a hannun shi yana sharce jikaken gashin kanshi da gangan kuma yake yarfa mata ruwan a fuska, don tsokana, yanayi yana kallonta ta mirror ganin ta bude ido yasa yayi sauri dauke kallonshi a kanta.
Duk tsiwar batool idan ta ganshi a cikin irin wannan yanayi ,lukus tajeyi duk kunya ya cikata bata iya kallon shi a haka, gashi shi kuma ɗan duniyan kanshi ne, duk in yayi wanka haka yake fitowa abinshi kullum yazo yayi share shafen shi a gabanta ya shirya a gabanta, itako taita sunne sunnen kai, bata iya dagowa har sai ya fita, yaukam ganin ya juya baya ne baya kallonta yasa ta kurama bayanshi ido bako keftawa tana kisima tsaruwa da haduwar surassa.
Duk kallon kurillan da take mai yana kallonta ta mirror, yana murmushi, saida ya gama duk abinda zaiyi ya juyo da sauri auko tayi saurin maida idonta ta rufe kamar bata farka ba, dariya ya kwashe dashi a fili ya shiga rera wakar "muna furci dodo maiyi baza yaci riba ba, haka" tana jin shi bata kanta ba, yana gama wake waken shi na habaici yace " ni bana son munafurci kince bakya sona bana burge ki wacece wacece yanzu kuma kinzu kina satar kallon min jiki kinga haɗaɗɗiyar sura me kyau, irin wanda baki taba gani ba ko'a tv, to wannan haɗaɗɗiyar surar na nana faɗima ne, amma tunda an ƙaƙaba min ke zan iya sammiki kafin mai guri yazo mai tabarma ya naɗe" jin kalaman son ranshi da yake faɗa yasa ba ta San sanda ta buɗe ido warass ba ta manta ma baccin karya takeyi, tashi tayi zaune ta rafka wata uwar shewa tana tafa hannaye, kafin ta kwashe da dariyar rainin hankali,cikin dariya tana nuna shi tace"ina haɗaɗɗiyar surar take a nan, dallah mallam ware cen, in ana maganar haɗaɗɗu ka daina saka kanka a cika, jibe ka fa" ta karashe tana kwasar dariyar ta, haushi yaji yace "ni kike cewa ma bani da haɗaɗɗiyar sura to kalli nan kiga" wani irin bubbuɗewa ya fara yi yana baza kwanji yana daga kirji sama da kasa, sannan yayi wata irin tsayuwa na aftoci, take taga ya rikiɗe mata ya koma mata kamar wani barden soja ba Dr ba,dunkule hannun hagun shi yayi ya tara Pawern shi guri daya yana bubbgawa gurin da daya hannun, nan take damatsen hannun shi suka koma kamar na wani dan wrestling, da sauri ta dauke kanta daga kallon shi dan gaba daya wani yamyam take ji a jiki ta, duk yana lura da yanayinta tsaf, taɓe baki tayi tana kawar da kai gefe tace"to na gani kana da naman kirji da hannaye ba shike nan ba" dariya ta bashi wai naman kirji, aiko ya shiga darawa, yace"kwanji ake cewa ba naman kirji ba" tace "oho dai koma menene ni bai wani burge ni, bari kaga na tashi na samawa ciki na abinci" mikewa tayi ta nufi hanyar fita daga dakin yace "ke kazama ina zakije a haka ki dawo kiyi wanka tukun " bata kula shi ba ta wuce kitchen abinta, shima ganin ta wuce yasa ya shiga shirya wa don hatta kayan sawan shi rabi na dakin.
Kitchen ta shiga ta hada lafiyayyar breakfast mai rai da motsi, tuni kamshi ya bade lungu da sako na part d'in, Dr yana gama shiryawa cikin kananan kaya bakin wando da riga red colour, masu mugun kyau da tsadar gaske, ya fito yana baza kamshi yayi kyau kuwa ba kadan ba, tunda ya sako kafarshi waje daddadan kamshin girkinta ya nurnike mai hanci, shaka yayi yana lumshe ido take miyan shi ya tsinke,gsky koma meye wannan take girkawa yayi alkawarin yau sai yaci shi saidai ayi duk bura'uban da za'ayi, falo ya nufa ya zauna yana lallatsa faskeken wayar shi.
Saida ta gama tsab ta kwashe a kula ta jere a dining,sannan ta fito a kitchen din tana miƙa, ganin shi tayi zaune, yana ganin ta yace "sannu da aiki, " harara ta watsa mai tare da cewa "ban sannu ba ina ruwanka da aiki na" ta karashe tana murguda baki, yace "to naji je ki zubo muci yunwa nake ji wlh," tace "yau naji wani sabon salo hammata a diraya, na saba dafa abinci da Kaine dama" yace "to yau dai dani kika dafa dan wlh sai naci" tace "aikodai baza kaci shiba in ciki gara yau saidai ya zube, bari kaga naje nayi wanka nazo naci abincin na oh" ta karashe maganar tana miƙewa zuwa dakin su, don ragon azanci anan tabar kulolin abincin ta wuce.
Tana bada baya ya saki wani murmushin keta a fili yace"yarinya man kaza, in bakiyi sharar masallaci ba kyayi ta kasuwa ai" mikewa yayi tsam ya shiga kitchen ya dauko plate ya nufi dining bude kulan abinci yayi dan kadan kuwa tayi daidai cin mutum daya, murmushi yayi yace "kin ma kanki da kinyi da yawa da saina diba na bar miki, amma wannan ba wani isana ma zaiyi ba balle na rage miki" juye abincin yayi tas a plate din har yana karkade kulan, ya dauki kofi daya ya hada kakkauran tea , ya dauki plate dinshi da kofin shayin shi ya nufi daya extra bedroom din ya bamo kofa...............
Tabɗijam Dr ka taro mach😳
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fisabillilah🙏
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
DAMA TA BIYU 💖 KƘIRƘIRARREN LABARINE MALLAKINANE BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYA MIN LABARI TA KOWACCE SIGA BADA IZI
NINA BA❌❌❌❌
(In👂👂👂yaji gangar jiki ya tsira👌a kiyaye pls)
{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}
Page 93 & 94
Mintuna talatin batool ta dauka kafin ta fito a shirye tsab cikin Riga da skirt na atamfa, ta kashe daurinta ture kaga tsiya, sai baza kamshi yakeyi, cike da takama zatazo tama Dr shegantaka, bata ganshi a falo ba hakan yasa ta nufi dinning taja kujera ta zauna zatayi ɗa'amun, saidai tana jawo kula taji ya biyota ba nauyi, da sauri kuwa ta ƙarƙare buɗe kullan wayam.
Cikin zaro idanu ta furta "kutumelesi" mikewa tsaye tayi ta rike kwankwaso tana girgiza kai, kafin ta taƙarkare tace"basharrrrr" da ƙarfi saida ko'ina na gidan ya amsa , zuwa lokacin kam Dr ya gama tanɗe abincin tas ya suɗe plate, jin ihun muryarta tana kwaɗa mai kira yasa shi tasowa da plate din a hannu ya buɗo ƙofa yana lasar hannu da jan yaji, ga plate da cup empty a hannun shi, tsayawa yayi a gabanta yace "lafiya naji kina ta kwala min kira kamar naci miki bashi"yanayi yana suɗar yatsu tsut tsut.
Takaici kan takaici ina wuta batool ta jefe Dr bash, ba ta san sanda ta karasa gabansa taci kwalar shi ba cikin tsiwa tace"bashar ina abincina"
Ajiye plate d'in hannunshi yayi ya shiga tafa hannaye yace "la'iha'illallahu! yarinya wuyarki ya isa yanka ni kike çima kwala kike kira na da bashar gatse gatse, lallai na fahimçi kina so mu cire raini a tsakanin mu, kinaso aba hammata iska, karki damu nasan meke damuki, zaki samu dont worry" jijjigashi tayi da yake ya sake mata jiki, tace "ni ba wannan na tambayeka ba, nace ina abinci na" buɗe mata baki yayi yana nuna mata cikin bakin shi ma'ana ya lamushe.
Tsabar takaici da bakin ciki sake shi tayi ta zube a gurin ta b
ɓare baki tana risgan kuka, shiko dariya ya hauyi mata yace "kuma yarinya daga yau kika karayin girki ke keɗai a gidan nan muddin inanan to ba rabonki bane, Allah kinji na rantse" sautin kukanta ta kara tanayi tana shushura kafa kamar wata sabuwar ƴar yaye, kai da kaga kukan kasan na zallan shakiyanci ne.
Saida tayi ma'ishi duk yana zaune yana kallonta da taga ba sarki sai Allah, ta tashi tana gungumi tana hararan shi, baiji mai take cewa ba yace"inba tsoro ba ayi da karfi naji mana" bata tanka shi ba ta wuce daki abinta ta kwanta.
Bayan kamar 10 minutes ya shigo idan ta biyu ya wuce ta ya shiga toilet ya rage cikin shi, yana fitowa ta kalle shi kasakasa tace"anci abincin Allah ya isa ba dole ata kashi ba" tayi maganar ne kasa sosai yadda bazai jiba amma cikin ikon Allah karaf a kunnensa, haura wa yayi kan gadon hawa kanta yayi ya zauna ya danne mata kafa, haɗe hannayenta yayi duka biyu ya rikesu gam da hannu daya yadda baza ta iya kwacewa ba, dayan hannunshi kuwa ya mika ya hade leɓenta na sama dana ƙasa ya matse da karfi, azaban zafi taji sai mutsu mustu takeyi ta kasa kwacewa, yace "wannan wannan ɗan bakin naki ya iya rashin kunya manya manya duk randa na samu dama ta biyu a kanshi sai na kusa cinyeshi" batool dai ba baki azaba ya isheta sai hawaye tajeyi, ganin haka yasa ya saketa ya tashi a kanta, aiko ta rushe da kukan gaske ba irin na ɗazu na shakiyanci ba, don ba karya taji zafi sosai,sai Allah ya isa take jero mai amma a zuciya dan kar yaji ya ƙara mata.
Fita yayi ya bar mata dakin ya koma falo yana kallo, ita kuma daga wannan kukan bacci yayi awon gaba da ita, wani American film akeyi mai kyau a mbc 2, saida aka gama ya mike yana kallon agogo, ganin sha biyu harya dan gota yasa ya nufi dakin, bacci yaga tanayi ga layin hawaye nan daya bubbushe mata a fuska, kawai sai yaji ta bashi tausayi, hawa gadan yayi a hankali ya shiga shafa mata fuska yana hura mata iskar bakin shi a fuska, bude idanu tayi akan shi, murmushi ya sakar mata kamin yakai hannu ya rike kunnayenshi yace"sorry batulan bashir, nine na saka ki kuka ko?"jin haka yasa ta kara narkewa idanunta suka ciko da kwalla, cikin shagwaba ta gyada mai kai alamar eh shine, yace "to hi hakuri bazan ƙara ba kinji, ki tashi ki samu wani abu kici ki shirya muje gidan hajiyata ki gaisheta" aiko a ɗokance tace to , dan ta gaji