Showing 183001 words to 186000 words out of 201974 words
Chapter 62 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
sha'awa, girgiza mai kai tayi , a hankili tace "yau fa ba kwana na bane kwanan anty zee ne." kamar ta caka mishi wuka haka yaji maganar ta ta daki zuciyar shi, cikin zaro ido yace "waye ya gaya miki kwanan ta ne yau." Tace "ba sai an gaya min ba, kwana 2-2 zamu din ga yi kayi daya saura da..." Bai bari ta kara sa ba ya katse ta da ɗan ƙarfi "ban amince ba ni kwana 1-1 zaku ringa yi nama riga na sanar mata, dan bazan iya jure yin har kwana biyu ba tare da ke ba." Tace "saboda me naga duk abin da zaka samu gare ni zaka same shi gurin anty zee har ma fiye da yadda zaka samu gare ni." Numfashi ya sauke "hmmm baza ki gane bane husnah ta." Mika ɗayan hannun yayi da nufin ya ci gaba da abin da yake so , sake rike dayan hannun tayi tare da cewa "to ai ba yanzu zan karɓe ka ba sai dare, har yanzu kana dakin ta ne, idan kana da bukatuwa ne kaje gare ta dan Allah." Kwace hannun shi yayi ya tashi yazauna bakin bed tare da dafe kai, ganin haka yasa ta dauka ko fushi yayi, hankalin ta yaɗan tashi, amma a ranta ta ayyana, wlh bazan baka daman da zaka faɗa halaka ba, in sha Allah bazan zama silar da zaka tashi da barin jiki a shanye ba ranar alkiyama kamar yadda mata da yawa a zamanin nan suke yi suna sane miji ba daidai yake aikatawa ba amma baza su taba hana shi ba su a ganin su hakan so ne, to wlh cuta ne tunde kema da aka haɗa kai dake aka zalinci wata Allah bazai barki haka ba.
Daga bayan shi ta tsaya ta fara shehshekan kuka irin wanda tasan zai tada mishi hankali, ai kuwa a sukwane ya juyo ya jawo ta ya shiga rarrashi, cikin shehsheka tace "dan Allah kar kayi fushi dani ya Aslam, wlh ba wai na hana ka kaina da gangan bane, idan na bari ka aikata hakan mun shiga hakkin anty zee kuma Allah bazai barmu ba,bana son ka zama mara adalci a tsananin mu tun kafin tafiyar tayi nisa." Tana maganar tana kara matsar kwallah, take yaji babu dadi a zuciyar shi cikin muryar rarrashin yace "ya isa haka my hussy, na fahimce ki, kuma in sha Allah zan dage sosai nayi abin da kike nusar dani, ke ta dabam ce a cikin mata husnah ta, Allah ubangiji ya miki albarka." Rungume shi tayi sosai ta kwantar da kanta a jikin shi.
A part ɗin ta yayi shirin zuwa aiki tunda a nan kayan shi suke, har falo ta rako shi tana rike da jakar laptop din shi, a falo ta mika mishi ba yadda baiyi ba ta raka shi wurin mota ta ki, a cewar ta zee zata hango su kuma baza taji dadi ba tun da ba kwanan ta bane, sai da ya biya part din zee ya sallame ta ita ma sannan ya dauki hanya.
Yadda suka saba gudanar da harkokin su haka suka gudanar babu wani canji a tare da su, sai dai yau Asmah ta dage a part ɗin zee za'a shirya dinner tunda a nan Aslam din yake,in yaso idan ya gama zai kwanta sai ya dawo nata dakin har zuwa wani daren tun da ya ce kwana 1-1 zasu yi, koda ya dawa ɗakin Asmah ya fara biya wa ko zama bata bari yayi ba ta kora shi wajen zee, da da daddare kuma da zai yi dinner ya saka zee ta kira ta suka yi tare, ya kuma ce kullum tare zasu dinga yi duk wacce keda miji a je part din ta ayi. Da daddare Bayan ya sallami zee guraren karfe 9 ya dawo part din ta yadda ya din ga rawan jiki a kanta sai da abin ya daure mata kai, zaka rantse irin kamar wanda yayi wata da watanni bai kusance ta bane, sai sambatu yake yi, yana saka mata albarka tare da yabo yana cewa ita ta dabam ce a cikin matan duniya dan Allah duk rintsi kar ta rabu dashi, kaza kaza haka yaita yi kamar zautattce wani abin ma bai San yana fada ba, ita dai mamaki ya ne ya cika fal, bayan sun nutsu yadda ya ringa tattalin ta kamar wani daren farko abin har dariya ya din ga bata, hakan ya faran ta mata ko ba komai ta ji dadi duk da ya dandani wata macen bai wofintar da ita ba, shikam ai sai lokacin ya ƙara tabbatar da darajar ta da kimar ta lallai ya tabbatar yayi sake a baya, daya bari ta subuce mishi, badan Allah yaso shi ba da duk wannan romon lagwalan daɗin bazai San akwai su a duniya ba.
Bayan wasu satittika gidan Aslam ya gama daidai ta, idan kaga yadda Asmah da zee suke gudanar da rayuwar su sai kayi rantsuwa ba kishiyoyi bane, sun maida juna kamar wasu yan uwa, suna girmama juna anty sama anty ƙasa basu taba bari wani sabani ya shiga tsananin su ba, sun haɗe Kansu ban da tattalin abin da zasuyi su faran ta ran Aslam babu abin da suke yi. Sai dai fa Asmah tana shan fama sosai da Aslam,kullum cikin taro shi take a kan hanya madaidai ciya idan ya bauɗe, tana namijin kokari wajen ganin cewa yayi adalci a tsananin su, sau da yawa har faɗa suke yi idan yayi wani abin daba daidai ba ta nuna mishi bai kyauta, amma faɗan baya nisa dan a take suke shirya wa, tana tausayin zee sosai dan takan ce, lallai Allah ya sota da rahama daya sa ita ce ta kasance abokiyar zaman ta idan da ta samu muguwa da wlh zaman gidan Aslam sai ya gagare ta, a dai yadda yake nuna yafi son ta karara a bayyane, kuma ko a gaban waye, sai dai itama zainab yana iya bakin kokarin shi wajen sauke duk wani hakki nata dake kanshi kuma yana bata kulawa kamar yadda yake ba Asmah, yana kuka matukar respecting dinta ganin yadda ta tsare girman ta ko a fuska bata taba nuna tana da muwa da wasu abubuwan da yake yi ba wata ran ma har yakan ji babu dadi shi karan kanshi, a gefe guda kuma ga kambun daya bata na uwar gida kuma wacce ta fara bashi farin cikin daya kasa samu a tare da Asmah wato haihuwa. Duk abin da Aslam yake yi zee bata taɓa nuna damuwa ba koda kuwa akan fuskar ta ne, takan kauda idanun ta idan yayi wani abin, ta riga ta sani takuma sadaƙar cewa Asmah ta yi mata fintinkau a zuciyar Aslam, tana tsananin kishi da Asmah sosai, amma kishi irin na matan annabin rahma, don duk abin da taga tayi na kwarai har Aslam ya yaba koda kuwa kwalliya ce ko girki kokari take ita ma ta takwatan irin shi kokuma wanda ya fishi koma wanda bai kai shi ba, a bangaren iyayen ta kuwa tana da labarin duk halin da suke ciki a wajen wan mahaifin ta Alhaji Abdur-rahman wanda dama shine ya shirya mata komai na tahowar ta Nigeria yana a Malaysia jirgin ta ya daga zuwa Nigeria hasalima shine yayi mata komai na barin kasar ita da ɗanta ba tare da sanin ƙanin nashi ba, jirgin ta ya daga da daddare da safe ya nufi gidan ƙanin nashi da nufin ya sanar dashi abin da ke faruwa kuna ya nusar da shi gaskiya shine fa ya tarrar ana tsaka dawan nan tataburzar.
Iyayen shi sunyi matuƙar farin ciki da wanan lamarin kuma hankalin su ya matukar kwanta wa ganin yadda suka haɗe Kansu abinda basu taɓa zaton zai zo da sauki ba, dama bata Asmah suke to ji ba don ita sun riga sunsan wacece ita su suka raine ta sunsan abin da zata iya da wanda baza ta iya ba, zee suke ji duk da kuwa ta ce masu ta shiryu, basu gaskata hakan ba sai da suka gani zahiran muraran, dan duk ran da zata je family hause tare suke zuwa, kowa a gidan ya shaida lallai Kansu a haɗe yake kuma suna gudanar da tsabtataccen kishi wanda da wuya a samu irin shi a zamanin nan na matan yanzu.
Duk wanda yaga Aslam yasan ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali dan har wani dan kiɓa yayi mai ban sha'awa, haka suma matan Asmah kam ta murje ta ƙara haske itama da dan kiɓa ta kara cika cif cif kamar yadda yake so, sai dai abin da ke bata haushi tumbi da taga yana son fito mata, haka kurum taga cikin ta na tasa wa alamar tumbi zata yi, tuni ta dena cin duk wani abu da tasan yana saka kiɓa da tumbi amma a banza abu sai ƙara gaba yake yi tun ba wanda ya kula har ta kai Aslam ma ya kula, aikuwa ya din ga mata dariya yana tsokanar ta ganin da gaske ba so take yi din ba. Cikin haka zee ta fara zazzabi koda akaje asibiti wai ciki ne dan sati biyu, zo kuga murna gurin Aslam da Asmah tuni suka fara buge bugen waya duk wanda suka kira yaji abin da ke faruwa sai yama Asmah kwallah dan tausayi tare da fatan itama Allah ya bata nata, yadda take farin ciki har taso tafi Aslam din zee kanta abin na matukar bata mamaki lallai Asmah daya ce tamkar dubu a cikin alumma samun kanta tayi da saka ta a addu'a itama Allah ya bata nata na kanta.
A can Malaysia kuwa a daidai wananan lokaci, ankai ruwa rana sosai da Dad lokacin daya farko ya ganshi a asibiti ciwon shi ne ya motsa sosai wanda rabon daya tashi yafi shekara ashirin tun zee na yar ƙarama, tun da ya farka bashi da wani abin fada sai daughter shifa a nemo mishi ɗiyar shi, ya ki kwantar da hankalin shi bare a samu ciwon ya kwanta,sai alluran barci ake ta ɗirka mashi, likitoci ma da suka ga abin yaki ci yaki cinyewa suka tambayi su mom wacece daughter ɗinnan ne dan Allah idan tana nan su kowa mishi ita, sai lokacin Alhaji Abdur-rahman yake sanar wa mom cewa shine ya fitar da zee da ɗanta zuwa Nigeria kuma yanzu haka tana ɗakin mijin ta, mom bata yi wani mamaki ba sanin halin Alhaji Abdur-rahman na ƴanci da son ƴaƴa, shifa duk abin ɗa yake so ko daidai ne ko akasin hakan baya taba hana wa, shi kuma kalar nashi jarabtar kenan, ta tuna lokacin auren zee da Aslam shine dai yayi uwa yayi makarɓiya, hankalin ta yadan kwanta tun da yanzu tasan inda zee take, duk da dama tayi zargin hakan.
Dabara ne ya fado mom nan ta samu Alhaji Abdur-rahman sanar dashi take suka haɗa baki yama Dad daɗin baki cewa anga zee ta dawo gida amma tace baza ta iya zuwa asibitin ta duba shi ba sabo da baza ta iya jure ganin shi a kwance babu lafiya ba yanzu dai ya daure a karfaffa jikin shi ya samu yaji sauki a samu a sallame shi yaje gida yaga zee, kamar wani ƙaramin yaro haka ya yarda da zancen su, dan da gaske zee ta kasance ita ce raunin nashi na farko a duniya kamar yadda yake faɗa.
Cikin kankanin lokaci ya wartsake aka sallame, dama Alhaji Abdur-rahman ya riga ya gama tsara yadda zai sanar dashi komai ya gayyato manyan malamai har su biyu da zasu mai wa'azi, tun kan akai karshen maganar da dai ya fahimci in da suka dosa ya birkice musu abin ka da jahilci zagi ta uwa ta uba, ya kuma lashi takobin zaije ya dauko yar shi koda da jan ciki ne kuma sai ya wulaƙan ta Aslam wulaƙanci mai tsanani,lamarin da yasa sukayi kaca kaca da ɗan uwan nashi ya gaggaya mai magana ya kuma ce yayi hankali dai da shiga lamarin aure da ma'aurata domin wani rabon tabbas yana kisa, ranar ya tattara ya dawo Nigeria rai a bace, yana dawo wa kuwa ya samu daddaɗan labari wai zee nada ciki, yayi murna sosai dan shima akwai son yara.
Anyi haka kamar da kwana biyar Dad ya dira a Nigeria shi kaidai dan ko mom bai gayawa zai zo ba, direct a Niger state ya sauka, ko huta baiyi ba ya dauki shatar taxi yayi ma gidan Aslam diran mikiya, part ɗin ta daya sani tun farko ya nufa mai gadi na tare shi ya wanka mishi mari, suna zaune a falon ta kamar yadda suka saba suna hira, cikin nishaɗi zee nata tsokanar Asmah dake ta mata complain akan maganar tumbi,zee na cewa to kodai ciki ne, Asmah tace cikin lafiya ban fa Dade da gama period ba sai dai idan wani ciwon ne nidai wlh asibitin zani, kafin zee ta samu daman bata amsa , suka ji an shiga bubbuga ƙofa ba kaukau tawa duk sun tsorata musamman Asmah da take da saurin tsora ta har sai da taji wani abu yayi zillo a cikin ta, zee da yake ta ɗan fita karfin hali, ita ce ta tun kari kofar ta buɗe, gaban ta ne yayi wani irin mummunar faɗuwa har sai da ta yi saurin dafe shi, take kuma marar ta yayi wani irin murdawa, wanda ta gani a bakin kofar yana huci kamar mayuncin zaki tabbas ba kowa bane face Dad ɗin ta take ta duke a wajen tare da kama marar ta duk da haka kuma tana karfin hali ja da baya dan ta tsere mishi, duk da Asmah bata San shi ba ta tsora ta ainun da ganin shi hakan yasa itama ta fara da ja baya tana yarfe hannu, shigowa falon yayi ya tunkari zee da ke daga kafa daker daker tana rintse idanu numfashin ta na seizing baiyi wata wata ba ya dauke ta da wani irin mahaukacin lafiyayyen mari, abin da bai taba shiga tsanin su ba a tarihin rayuwar ta wai Dad ya mare ta, ko lura da yanayin da take ciki bai yi ba idanun shi sun rufe fisgar hannun ta yayi ga shiga janta, tana daga duƙe dafe da marar ta, ta shiga dan kokarin coge wa amma ina bata da wannan karfin ganin haka yasa Asmah kwasowa da mugun gudu ta biyo su ta rike ta da karfi tana kuka tana canja, tun da dai ita ba sanin Dad tayi ba, baza taba bari ya tafi da zee a gaban ta sai dai ko ya haɗa su, su biyu ya tafi da su, ganin Asmah ta na jan zee yasa ranshi ya ƙara ɓaci da wani irin karfi ya fusge su gaba daya dukan su sai da suka watse a kasa, Asmah ta bugu da kujera bai bi takan hakan ba ya fisgi hannun zee da karfi gaske yayi waje da ida, daidai sun iso tsakiyar compound din gidan cikin hukunci ubangiji motar Aslam ta shigo gidan duk da lokacin dawowar shi bai yi ba, akan abin dake faruwa direct idanun shi suka dira, wani irin burki ya taka tun daga bakin get da wani mahaukacin gudu ya fito daga motar ya nufosu, baiyi wata wata ba yasa hannu ya fisge zee daga hannun Dad take ta zube a wurin yaraf ba numfashi tsugunawa yayi akan ta yana jijjigata da karfi yana ambaton sunan ta hankali tashe, muryar Dad ne ya katse shi,a fusace cikin kaukausar murya yace kai tsinanne dan matsiya ta ka kyale min ƴa ta dan uban ka." Jajayen idanun shi ya dago ya zuba a fuskar dad, zuciyar shi yaji yana tafasa tsabar fusata har wani rawa labenshi yake yi baki ya bude zai yi magana amma ya kasa, kuma hakan ya taimaka dan duk abin da zai faɗa a lokacin bazai zama alkhairi ba , wani irin tafasa zuciyar shi ta shiga yi, tun daya kafe Dad da ido bai ko kefta ba , kawai hasaso ta ina zai kai mai makura yake yi.......
Idan naga ruwan comment akwai update anjima
Oum Ummeetarh
07041130088
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}
Page 130
Ganin yadda Aslam ya kafe shi da jajayen idanun shi yana huci kamar wani mayunwacin zaki, sai da ya firgita , amma dake riƙƙeƙen ɗan duniya ne daure wa yayi ko a fuska bai nuna ya razana ba sai ma ci gaba yayi da cewa"Ba da kai nake magana ba fitsararre ka zuba min wasu kwala kwalan idanun ka makar na kwadi, nace dan uban uban ka ka kyale min ɗiya ta." Bai dauke idanu akan shi ba kuma bai kyale tan ba, "OK baza ka kyale ta ba ko? To ina zuwa a kwai wadanda zasu shiga tsakani na da kai, zaka gane ƙaramin ɗan iska ne kai." Yana gama faɗin haka ya juya da sauri fuuu kamar zai tashi sama ya fice daga gidan, abu biyu ne ya saka shi fice wa ba tare da zee ba, na farko dan ya gujewa wannan kallon da Aslam ke mishi dan har ga Allah ya tsora ta da yanayin shi, yasan bai da ƙarfi yin dambe da Aslam koda hakan ta kama sai dai a nakasa shi a banza, na biyu kuwa dan ya kwaso police suzo su tafi da Aslam, dan wannan karon yayi alkawarin sai ya wulakan ta shi, don idan ya kulle shi a wannan karon, in ba wani ikon Allah ba sai dai ya kare rayuwar shi a gidan maza. Har ya fice daga get ɗin Aslam bai ɗauke kanshi daga kallon shiba , ba komai ne ya hana shi haɗa ma Dad jini da majina ba, sai dan darajar mutum biyu masu daraja a gareshi na farko little na biyu