Showing 81001 words to 84000 words out of 201974 words
Chapter 28 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
ruwan gora ta dawa palo, tana ci tana kallon, kwana casa'in, a tashar areaw 24.
Koda ta gama cin abincin saida ta jira aka gama shirin sannan ta kwashi plate da cup ɗin da ta bata ta kai kitchen ta wanke su.
Dawowa falon tayi ta kwanta a 3 sitter ta kunna data, ta shiga WhatsApp tana dan chart a groups, wani program ake gabatarwa a wani group , mata saida ado, da take ciki, program ne akan yadda mata zasu kula da tsabtar jikinsu, shirin ya dauki hankalinta sosai, gaba daya ta tattara hankalinta da nutsuwarta ta mayar kan wayarta, domin kuwa abin karuwa ake gabatar wa.
Murda handle din kofar yayi a hankali ya buɗe ya shiga bakin shi ɗauke da sallama kasa kasa , yana shiga, wani daddaɗan kamshi hade da sanyin ac yamai salama , baisan sanda ya lumshe idanun shiba, jingina bayan shi yayi da jikin kofar bayan ya mayar ya kullu, har zuwa lokacin idanun shi a lumshe suke yana shakar daddaɗan kamshin dake tashi a falon.
Ganin ya shige yasa Abba dake tsaye jikin motar shi sakin murmushi tare da, komawa cikin motar yayi ya tayar ya shiga ya bar gidan, yana me rakasu da addu'a zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba.
Ya kusa kwashe 10 minutes a haka kafin a hankali ya ware idanun shi a cikin falon yana bin ko' ina da kallo, idanunshi ne ya sauka akanta, gaba daya hankalinta yana kan handset dinta dake hannunta, ji yayi gaban shi ya bada rasss, da sauri ya lumshe idanun shi ya sake budewa still dai ita ya sake gani again, bai yarda ba ya dauka gizon data saba yi mai ne wasu lokutan yauma ta ke mai, kara saka hannu yayi ya murza idanun shi ya kara budewa, sai lokacin ya tabbatar ita ne ba gizo bane.
Karfin bugun zuciyar shi ne ya linku, jikinshi take ya fara wani irin tsuma,me hakan ke nufi, yanzu hakan na nufin itace amaryar da aka aura mai, itace dama zabin da alhaji baba ya mai na biyu, kokuwa dai Abba gidan kamal ya kawo shi, kokuwa dai mai kama da itace.
Wata zuciyar Ce tace Aslam ka nitsu karka ruɗa kanka, wannan gidan ka ne, kuma Abba da kanshi ya kawoka, kasan dai bazai kaika gidan kamal a matsayin naka ba ko? Tambayar zuciyar nashi ya kara yi, to ita kuma husnah mai takeyi a gidana, bayan tana matsayin matar kamal.
Amsa zuciyar shi ta bashi da cewa, tunda ka ganta a gidan ka , to tabass itace zabin da alhaji baba ya maka, tabass dama ta biyu Ce ka sake samu akanta.
Wayyo Allah dadi Aslam rasa ina zai tsoma ransa yayi dan farin ciki, har zuwa lokacin hankalinta nakan wayarta bata san da wanzuwar mutum a kanta ba.
Daidai lokacin aka gama program din da ake gabatarwa a group din, mikewa zaune tayi tana sakin murmushin ta mai kayatarwa, wayar ta ajiye tayi ɗaga hannayenta sama tana miƙa, still fuskar ta a washe dan program din ya fadakar, da ita kuma ya ilimtar da ita ta karu sosai da wasu abubuwan masu muhimmanci.
Sai lokacin ya kara tabbatar da ita ɗince ba mai kama da ita ba, da wani irin doki, azarbabi, shauƙi, ya dira a gabanta, shi kanshi da za'a tambayeshi baisan yadda akayi ya iso gabanta ba, shidai kawai yaji wani irin Abu na janshi gareta kamar magnet.
Ganin mutum a gabatan ta kamar daga sama yasa ta saki wani irin ƙara,kafin ta shiga furta a'uzubi kalmatillahi, ba karamin tsorata tayi ba, hakan yasa ta kasa tantance wanene, mutum ɗinne ma ko aljan.
Ganin haka yasa Aslam da shauƙi ke dibanshi ya tashi ya rungumota jikin shi, ya kamkame ta.
Luf kuwa tayi a faffaɗan kirjin shi, tana shakar kamshin daddaɗan turarenshi mai kwantar da hankali, idanunta a rintse sai sauke ajiyar zuciya takeyi, shi kuwa a hankali ya miƙa hannu ya shiga shafa bayanta, yana dan bubbugawa, alamar yana rarrashinta,ita dai batasan a ina take ba, dan gaba daya hankalinta baya jikin ta
Zuciyar shi kamar ta fito daga kirjin shi, tsabar azalzalan shi da takeyi, wai yau shine rungume da husnah a jikin shi, wayyo dadi kashe shi, ji yayi tunda yake a duniya bai taba riskar wani yanayi mai dadin da yakai Wanda ya riski kanshi a ciki yauba.
Saida suka kwashe minti biyar a haka kafin ta samu nutsuwa hankalinta ya dawo jikinta, jinta tayi dare dare a rungume jikin mutum, yana shafa bayanta, a hankali ta dago fuskarta daga kan kirjin shi, ta kai kallonta a fuskarshi, zaro manyan idanunta waje tayi, kafin ta zabura ta mai wani irin kyakkyawan hankaɗa, daya zo mishi bagatatan, ba shiri ya saketa tare da hantsilawa da baya kamar zai fadi,Allah ya taimakeshi bai fadin ba, dan gaba daya jikin shi ba kwari.
Mikewa tayi a zafafe tana binshi da wani irin kallo, gashi nan shi ba harara ba amma mutum zai gwammace dama hararan shi akeyi akan wannan irin kallo.
Duk da tariga tasan Aslam shine kaddaran ta ,wannan karon ma shine mijin da aka aura mata a karo na biyu sabanin zaɓin zuciyar ta kamal, ta kuma yi kukan hakan kamar hawayenta zasu kare, tayi baki ckin hakan kamar ta hadiyi zuciya ta mutu ta huta, tayi zazzafan zazzabi akan hakan kamar bazata kara lahiya ba, amma daga karshe ta fawwalawa Allah komai ta amshi kaddaranta da hannu bibbiyu.
Amma yau ganin shi a gabanta har yana wani sakata acikin jikin shi yasa taji gaba daya mikin da tayi kokarin dannewa kwanaki biyu da suka wuce ya dawo sabo dal, ji tayi kamar a lokacin, ake sanar da ita , Aslam ne mijinta ba kamal ba, ta tsani Aslam tun bata San kanta ba, bata sonshi bata kaunar shi daidai da kwayar zarra a zuciyar ta.
Ganin tana jifan shi da wani irin kallo yaji gaba daya jikin shi yayi sanyin, bazai iya juran irin wannan kallon daga gareta ba, zuciyar shi tarwatsewa zatayi,a hankali ya shiga takawa zuwa gabanta.
Ganin yana nufota yasa ta juya da wani irin sauri sauri gudu gudu, ta haura upstairs ta shige dakinta ta banko kofa da karfi.
Ganin haka yasa ya zube guwowin shi a kasa, cike da tsantsar farin ciki, rasa ma me zaiyi,yayi ji yake kamar ya daddage ya kurma ihu tsabar farin ciki, yesssssss ya furta da karfi yana dunkule hannayenshi kamar zai kai naushi, na sameta na mallaketa Allah na gode maka, goshin shi yakai kasa yayi sujud, ya shiga rerowa ubangiji kirari da godiya, yana dagowa kuwa, ya fashe da wani irin dariya kamar sabon kamu, take duk wani kulle mai nauyi da yakeji a zuciyar shi ya kau, komawa yayi da baya ya kwanta rigingine akan titles yayi filo da hannunshi yana kallon pop din falon yana sakin murmushi.
(Tabdijan jama'a Asmah a gidan Aslam, tayaya akayi hakan ta kasance ,tayaya akayi matankadi ya shiga gora ne wai,? Shin ina kamal din mu ne wai, aikam dai banga ta zama ba, gidan kamal nayi yanzu, na dauko mana rahoto)
~GIDAN KAMAL~
Zaune yake a main parlour, akan daya daga cikin kujerun da sukayi wa kyakkyawan katon falon kewanya, system ne akan kafar shi ya tattara dukkan hankalin shi akai da alama wani aiki yakeyi mai muhimmanci, sanye yake da singlet, da kuma wando 3 quarter, yana aiki amma fuskar shi dauke da kyakkyawan murmushi kamar wani sabon ango.
(au na manta Ashe shine ma😅)
Wani daddaɗan kamshi turare ne yamai sallama a hancinsa, lumshe idanu yayi yana kara faɗaɗa murmushin fuskar sa, kafin yakai ga bude idanu yaji tausasan tafukan hannunta akan idanun shi,ta rufe mishi ido dasu, tana tsaye daga bayan shi, daukar laptop din shi yayi ya lalubi table din dake gaban shi ya daura tukun, sannan ya mika hannu ya zagayo da ita gabanshi, bai mata masauki a ko'ina ba sai kan cinyàr shi, sai lokacin ta bude mishi idanu.
Wowww ya furta yana zaro idanu waje ganin irin wankan data dauka, cikin ƙananan kaya masu shegen kyau da suka bi lafiyar jikinta suka bayyana wasu sassa na jikinta, kai gaskiya deeja yar gayu ce, irin sosai dinnan.
Kiss ya shiga kai mata a ko'ina ya samu bakin shi ya sauka, dariya ta shiga kwasa, bayan ta cusa hannayenta cikin lafiyayyar suman kanshi daya sha gyara sai kamshi yake yi, Saida yayi mai isar sa, ya dago ya kalli kyakkyawan fuskarta kalan na Asmah sak, saidai ita ma'abociya kwalliyace ba kamar Asmah ba, da bata cika caba ado a fuska ba.
Yace "my deejah wannan irin wanka haka, Ai saiki karkare susutani, ammin na safe ammin na rana, yanzu kuma gana dare, gsky ni dan gata ne," fari tamai da idanu, tana sakin murmushi, ci gaba yayi da cewa, "gsky wannan wankan ya wanku kuma kwalliya ta biya kudin sabulu, ki tashi muje daga ciki na biya wannan wankan , dan bazai tafi a banza ba" gaban ta ne ya fadi jin abinda yake cewa , tsab ta gane inda ya dosa ganin ya fara yawo da hannayenshi a sassan jikinta, marairace fuska tayi take takoma kallan tausayi, harda dàn taro kwalla a idanunta, cikin shagwaba tace"ya kamal dan Allah kayi hakuri har yanzu ban gama warkewa bafa, wurin zaf" bai bari ta karasa ba yayi saurin dakatar da ita ta hanyar, kai mata dan karamin cizo akan lip dinta na kasa, zafi taji, tace"wash ya kam" ai saurin kai tafikan hannunta ta tayi kan bakinta ta kare labbanta, ganin ya sake duƙo dakai, alamar zai kuma cizonta.
Dan bata rai yayi, yace "so nawa zan gaya miki banason jin kamal daga bakin nan naki"sai lokacin ta tuna mai tayi aka cijeta, murmushi tayi tare da kama kunnayenta duka biyu tace "sowy bazan kara ba mantawa nayi" kire mata hannun yayi daga kunne ya lakace mata hanci, dariya ta kwashe dashi, tana cusa kanta a girjin shi, shima murmushi ya saki, tare da Ciro wayar shi ya shiga kashe musu selfie, dan ba karya kwalliyar ta yamai kyau sosai, Khadijah akwai son photo dama , ganin haka yasa tayi ta canja style yana daukansu hotuna kala kala in romantic way, wani hoton ma bazai yuwu wani ya gani ba saidai iya su biyu suga abinsu, suna gamawa yace "oya tashi muje ciki na baki tukwuci," make kafada tayi tace inyin, yar dariya yayi tare da cewa "yarinya Ai baki isa ba, yau fa kwanana biyar ban sake zuwa ba, tunda naje so daya" tace " to da da baka da aure kwana nawa kakeyi baka je ba," yace "da bansan yadda garin yake bane,amma yanzu tunda na sani kullum sai naje ba ɗaga kafa tunda kin warke, oya tashi muje" kin tashi tayi,ganin haka, yasa ya ciccibeta suka karasa bedroom.
Tun ranar da ya bude fuskar amaryan da akace an musanya mishi da Asman shi yaga photo copy dinta Ce,shikenan hankalin shi ya kwanta tunda dai ya tabbatar ya rasa daman shi ta biyu a kanta,gashi kuma ya samu makamanciyar ta, banbancin su kadan ne, a ranar ya kaddamar mata,itama da yake tana so, don tunda aka gaya mata ta hau murna , take ta bada kai bori ya hau, zaman su ɗagwas ɗagwas , zaki dauka wasu tsofaffin masoya ne,cikin kwanaki biyar din da sukayi tare deejah ta mantar dashi komai ciki kuwa harda Asmah, don idan ba'ita ta ambace ta ba sai a kwana a wuni bai tuno ta ba, shi yanzu ji yake da za'a bashi dama ya zaba daya tsakanin Asmah da Khadijah to ba shakka Khadijah zai zaba, don farat daya Allah ya daura mishi kaunarata matsanancin,irin kaunar da baima Asmah ba.
~WAIWAYE~
A ranar da Kamal ya biyo bayan Amir zuwa sashen alhaji baba, har ya saurari tattaunawar da sukayi, wato ranar da akakai Aslam asibiti, hankalin shi ba karamin tashi yayi ba jin halin da Aslam yake ciki, Aslam zai rasa ransa saboda soyayyar Asmah, idan ya bari haka ta faru bai cika dan uwa na gari ba , kuma ya tabbatar tunda yaji alhaji baba ya furta, ba Aslam ba Asmah ko bayan ranshi, ya furta kenan ruwa da iska bazasu iya sauya mai ra'ayi ba, take zuciyar ta cemai saidai mutum daya, tambayar zuciyar tashi yayi waye wannan mutumin, a take ta ba shi amsa da amininsa alhaji mallam take ya fada motar shi ya figeta da mahaukacin gudu bai tsaya ko ina ba kuwa sai gidan Alhaji Mallam.
Tundaga yanayin shi Mallam yasan ba lahiya ba, sallaman kowa yayi suka kebe da Kamal d'in, nan ya shiga zaiyana ma Mallam abinda ke faruwa tun daga A har Z, kwarai ya tausaya ma Aslam kuma yasan tunda Alhaji baba yayi wannan furucin yayi kenan, bazai canja ba kuwa koda Aslam zai mutu ne saboda son Asmah yafi kowa Sani irin kafiya da taurin kan alhaji baba a duniyar nan, amma duk da haka zaiyi wani Abu akai, nan kamal ya sanar dashi shi ya hakira da asmah har zuciyar shi ya barma ɗan uwan shi aslam, domin ya fanshi rayuwar shi, take alhaji mallam ya shiga saka mishi albarka kuma ya mishi alkawarin zai musanya mishi da ƙanwar Asmah indai yana so.
Mallam bai kara tausaya ma Aslam ba saida yaje asibiti ya gan shi kwance rai a hannun Allah ko numfashi saida oxygen yake iya yi,koda ya koma gida, da lamarin ya kwana a ranshi dan cikin dare kasa bacci kirki yayi saboda tausayin Aslam d'in, washe gari kuwa tunda sassafe ya koma asibitin ya kara duba jikin Aslam d'in, haka nan ya ganshi jiya i yau, tambayar Abba yayi ko alhaji baba yazo asibitin nan Abba ya sanar mai baizo ba, haka ya koma gida ranar ma cike da jimami, jikin shi ya kara yin sanyin da lamarin, take ya kudiri aniyar gobe zai samu Alhaji baba su tattauna akan matsalar nan ya zama dole ya tirsasashi ya baiwa Aslam Asmah, kodan suyi ceton rai, duk da yasan hakan abune mai matukar wahala sauya ra,ayin alhaji baba.
Washe gari kuwa da safe ya dira gidan alhaji baba bagatatan ba notice, saidai ganin shi yayi daga sama, bayan sun zauna sun gaisa sun dan taba hira, nan yake tambayar shi yamai biki, daga yanayin yadda yaga Alhaji baba ya asma mishi yasan lallai akwai matsala.
Serious face mallam ya koma, kafin ya dauko mai tattaunawar da sukayi da kamal a shekaran jiya, da kuma sadaukarwan da kamal yace yayi yabar ma dan uwan shi Aslam Asmah, da kuma musanya ma kamal da Khadijah da yake da niyyar yi.
Alhaji baba bai katse mallam ba saida yakai karshen jawaban shi, ya dubi idanunshi yace "ban amince ba ni, idan kamal ya amince ya hakura ya yafe mishi ita ni ban amince ba, sanin kanka ne bana magana biyu" mallam yace tabbas nasan baka magana biyu dan ni zan karass, saidai a wannan karon ya zama dole kayi magana biyu, domin idan har Aslam ya mutu sanadin wannan lamari, kaima kanada alhaki a ciki, saboda ka haramta mai abinda Allah ya halas ta mishi, nan ya shiga mai wa'azi cikin lalama, amma kafiya irinta Alhaji baba , yana nan akan bakanshi, tuni ran mallam ya baci, nan ya shiga mai faɗa, shima gani haka ya shiga mayar mai da martani kowa na kokarin kawo hujja akan bukatar shi, ran mallam yayi kololuwar baci, mikewa yayi a fusace ya kalli alhaji baba yace"Nagode Muhammad yau ka nuna min yadda ka dauke ni , ka nuna min inda ka ajiye matsayin amintarmu, sannan ka nuna min ban isa da ahalinka ba , naji nagode, na Barka kaje kayi duk abinda zakayi amma ka Sani idan Aslam ya rasa ransa akan wannan lamarin to kasani babuni babukai".
Tirkashi , koda suke yara idan Alhaji baba yama mallam ba daidai ba da wannan kalman yake horashi(Ka Sani babu ni babu kai) wannan kalmar fitar ta daga bakin mallam tana matuqar firgita shi, har ciwo yakan kwanta a zamanin suna yara idan mallam ya furta mai wannan kalma, tunda suka mallaki hankalin Kansu hakan bai kara shiga tsakanin su ba sai yau.
Jikin Alhaji baba yayi mugun sanyi hankalin shi yayi mugun tashi, ganin mallam ya juya zai bar fallon, da sauri ya riko hannun shi ta baya yace" ka dawo aminina na amince, kayi hakuri ka isa da ni kaina ma ba iyali na kadai ba" juyowa Alhaji mallam yayi suka rungume juna da Alhaji baba.
Riko hannun shi Alhaji baba yayi suka koma suka zauna,ya dubi mallam yace " na amince ce saboda kai da kuma amintar mu, amma wlh baɗan Aslam ba, kuma zan bashi auren Asmah kamar yadda ka bukata amma harga Allah bada son raina ba, yaci darajar ka da darajar aminta, tunda wancen lamarin ya faru Aslam baisan ya bada hakuri ba, har yanzu zancen da nake maka daga ni har iyayenshi bai ba hakuri, sannan Abu na gaba Asma'u nidai wannan karan bazan iya kallonta nace mata zan baiwa Aslam aurenta ba, bayan nasan sarai tana soyyaya da kamal, gaskiya ina ganin mun shiga hakkinta da yawa tunda dai munsan bata son Aslam kamal take so, kuma a yanzu bamu da ikon zabar mata miji tunda matsayin bazawara take," murmushi Alhaji mallam yayi yace" indai ta Asma'u ne babu wani matsala yarinya Ce mai biyayya , nasan zata min biyayya ta karbi Aslam a karo na biyu, kuma ita kanta baza ta so Aslam ya mutu ta dalilin taba, ni zan sanar mata komai, amma sai bayan daurin auren" Alhaji baba yace "to shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, saidai kafin nan akwai wasu jarabawar da zanwa Aslam, idan ya ketare yayi nasara, amma idan ya fadi kasani ya rasa Asma'u har abada"murmushi mallam yayi a zuciyar shi yace wannan mutum bazai taba canzawa ba , a fili kuwa yace "yace ba damuwa kana iya mai ko wani irin test insha Allah kuma nasan zai ketare" nan ya labarta mai maganar boye ma Aslam asalin gaskiyar magana yace mai wa tace