Showing 90001 words to 93000 words out of 201974 words
Chapter 31 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
da zaman gida tana bukatar ta fita taga gari, tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka koda ta fito bai dakin dan haka ta saki jiki ta shirya tsab abinta ciki dogon rigar lace, ta kashe dauri nan ta fito shar da ita saidai dan kumburin da idanunta yayi saboda kukan da tasha, a falo ta same shi zaune yana jiranta, tana fitowa yace"inyeee kinyi kyau gaskiya zo muyi selfie" murmushi tayi jin yau shida kanshi yace tayi kyau, ba ta gama murmushin ba ta tsinci muryarshi yana cewa ,"saidai ko kaɗan baki kama kafar faɗima na a kyau ba" take murmushin fuskarta ya bace bat, itafa ko wacece faɗiman nan tashi ta mata mugun tsana wlh, ji take da zasu hadu zata iya shaketa har sai ta daina numfashinta.
Haka suka fito suka shiga mota yajasu sai gidan hajiyan shi,(batool a gidan surukai a dawo lafiya,nidai fatana Allah yasa karsu yada hali a can😕)
~AMIR~
Zaune yake a falon gidan shi ya rafka uban tagumi da hannu bibbiyu, abin duniya gaba ɗaya yasha mai kai, gama wayar shi kenan da ummi, amma kwata kwata bata saurareshi ba, tace kar ya kuskura ya tako kafar shi Abuja idan kuma ba haka ba zai fuakanci bacin ranta mai tsanani.
Tun ranar da ummi tazo ta tarad da aika aikar daya aikata, ta shiga fushi dashi, a gidan ta kwata tana kula da Amira da shan maganinta da shiga ruwan zafinta, Amir kam tun ranar bai kara saka amira a idanun shi ba don ummi ta kasa ta tsare, kwananta biyu a gidan Amira ta wartsake saboda kulan da take samu sosai gurin ummi , a ranar kuwa Ummi ta tattara ko family hause bata koma ba don ma karsu daddy su hanata tafiya da Amira, direbanta da zai maida ta gida ta kira,yazo har cikin gidan ya ɗaukesu sai abuja, a lokacin Amir baya gidan yana dawowa ya tarad da wannan mummunan lamari, ummi ta wuce da Amira abuja, tashin hankali.(hmmmm kujimin Hadiza da kokari,kekuma ummi haka akeyi hisabillilahi😁)
Tun ranar yake kiran wayar ta taki dagawa saida aka kwana aka wuni sannan ta daga, magiya ya fara zuba mata da ban hakuri tuni ta dakatar dashi,tare da mai kyakkyawan warning akan kar ya sake kiranta indai akan wannan maganar ne Amira zata riƙeta hartayi gud five months tukun na zata dawo da ita punishment dinshi kenan akan abida yayi.
Amir ya shiga tashin hankali ba kadan ba , har wani rama ya fara yi a tsaye, gashi yana jin kunyan yakai karanta, yasan asirin shine zai tonu sai kowa yaji abinda ya aikata, haka yaci gaba da boye magana a can family hause kuwa ba Wanda yasan abinda ke faruwa.
Yau da Amira ta cika wata daya acan kuma yau hakurin shi ya kare ya kudiri aniyar zuwa Abuja ko ganin tane ya yasa mu yayi, tun safe yake kiran ummi saida tagama jamai rai ta dauka, yace zaizo tace karya kuskura, amma bayajin zai iya hakura dan haka ya tashi ya shirya ya dauki hanya.
A bangaren Amira kam tasananin kewa da kaunar mijinta ke damunta, amma tsananin kunyar ummi yasa ta kasa, nunawa, gashi ba waya sukeyi ba sai a kwana a wuni basu gaisa ba da yake wayarta ya lalace gabanin biki dana ummi suke gaisawa, daki guda ummi ta ware mata suna zaman su qalau dan koda wasa bata taba nunama Ummi alamar ta gaji da zaman ba gidan angonta takeso.
Da wuraren karfe biyar na yamma suna zaune a falo ita da ummi twins sunje islamiyya, abban Amir ne ya shigo dan haka Ummi ta tashi ta bishi dakin shi domin ya kimtsa, zama tayi ita kadai tana kallon faskeken plasma dake manne a bangon falon a zahiri zàka zata shirin da ake haskawa take kallo amma a baɗini ta lula duniyar tunanin mijinta ne, yau kwanan su biyar rabon da suji muryar juna, ganin tunanin bazai fishsheta ba yasa ta mike ta nufi hanyar dakinta domin tayi wankan yamma.
Daidai nan kuma Amir ya shigo cikin falon a darare bakin shi dauke da sallama kasa kasa fatan shi ace Abban shi na gida , idan yananan duk hukuncin da ummi zata mai nakin jin maganar ta dayayi zaizo da sauki, ganin gilmawanta yayi ta shiga dakin bakin dake nan kusa dana su twins, waige waige ya shiga yi a falon ganin alamar ba kowa yasa cikin sanɗa ya lallaba yabita dakin data shiga, koda ya shiga ta riga ta shiga toilet dan haka zama yayi a baki gado yana jiran fitowarta, minti 10 kacal tayi ta fito abinta daure da tawel.
Turuss ta tsaya ganin ya Amir ɗinta zaune a bakin bed yana sakar mata murmushi, tsayawa tayi tana kallonshi itama cike da kewar shi,ware mata hannayenshi yayi alamar tazo gareshi, kasawa tayi, da sauri ta juyamai baya , kunyar shi takeji, basuyi irin wannan sabonba ,dan tunda wannan lamarin ya shiga tsakaninsu basu kara ganin juna ba sai yau.
Wani irin kewanta yake ji bana wasa ba, da sauri ya tashi yayi hugging dinta ta baya, yana sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri, cikin tsananin farin cikin ganin ta ya shiga cewa " I miss u so much babyna, nayi kewarki sosai wlh, kema kinyi kewata ko" gyada mai kai tayi, yace"in babynmu na farko macece baza musa sunan ummi ba kinji" ta sake gyada mai kai, sake ta yayi ya ruko hannunta suka dawo bakin gado zama yayi sannan ya zaunar da ita akan cinyarshi,lafewa tayi a jikinshi ta manna kanta a kirjinshi,tayi shiru, tana sauraren bugun zuciyarshi,shikuma ya mika hannu ya kewaye ta ya lumshe idanu, haka suka zauna shiru abin tausayi kamar wasu sababbin marayu.
Ummi kam tana gamawa da Abban Amir, tace bari taje falo tabar Amira ita kadai, koda ta fito falon bata ba labarin ta, a fili tace "ta wuce ɗaki kenan, yanzu zata je ta kama bacci,bari na kirata ta farayin dinner tukunna, inba haka ba inta kwanta, baza ta samu taci abinci ba kenan" tana maganar tana karasawa kofar dakin Amira, tura kofar tayi ta shiga, ganin su tayi makale da juna ayadda bama susan ta shigo ba saɗaf saɗaf ummi ta sake kofar ta koma da baya, mamaki fal ranta yaushe Amir ya shigo gidan nan har ya tsallake faluka ya shiga bedroom din Amira bata da labari, komawa tayi dakin Abban Amir jiki a sanyaye, ganinta haka yasa yace"lafiya naganki haka ina Amiran take" rike baki tayi tace "hmmmm Abban amir kaidai bari yau naga abinda yafi karfina" zama yayi kusa da ita yace"mekefaruwa ne gayamin pls kin sakani cikin zulumi" labarta mishi abinda ta gani yanzu tayi, aiko Abba amir maizaiyi ba dariya ba, nan ya shiga yi mata dariya, yace"kece bakijin magana na gaya miki ki mayar mai da matarsa kinki, waike kina kwatar mata enci, waya gaya miki yaran yanzu ana musu haka,to wlh in baki tattarssu kin bashi matarsa ba, gobe abinda zaki gani saiya hanaki bacci ma," sauke ajiyar zuciya tayi tace ""hmmm aiko naga kwatar enci, ja'ira bakaga yadda ta lafe a jikin shi ba fah, yanzu Allah kadai yasan da wani ido take kallona Oh ni Aminatu naga ta kaina" Abban Amir yace"to ai sai gobe ki tattara masa matarsa ya tafi da ita inba so kike ayi cikin ɗan luv a a gadon ki" tace "aiko bakace be Abban amir, Allah dai ya kaimu goben".
Amir kam saida yaji ana shirin kiran magriba ya salalo ya fito cikin amincin Allah ba kowa a falon, ya fice da sauri ya nufi masallaci, ummi dake hangenshi tana daga kitchen, ta sauke ajiyar zuciya kamin taci gaba da aikinta, ita yanzuma kunyar Amira takeji bata san wani irin kallo take mata ba, daga yadda ta ganta kwance jikin amir tasan tayi kewar mijinta sosai, sai yanzu take ganin wautar abinda tayi.
A can masallaci amir ya hadu da Abban shi nuna mai yayi kamar saukar shi kenan ko gidan ma bai shiga ba yace bari yayi sallah, Abba yace "Allah sarki haka nefa" shidai bai gane nufin Abban ba haka suka runtumo zuwa gida, yayin mamakin yadda ummi ta tarbeshi a sake ba wani nuna alamar tana jin haushin shi, take wayar da sukayi ɗazu ya shiga fado mai arai, a zuciyar shi yace kamar ba ita bace keta min masifa dazu a waya, to kodai Allah ya karbi addu'a nane dana ke tayi akan ya daurani akanta.
Tunanin shi ya katse jin ummi na cewa "aiko dai kazo akan gaɓa dama gobe nakeson nakiraka kazo ka dauki matar ka, sai gashi Allah ya kawo kama," wayyo Allah dad'i amir ya furta a ranshi bai zaci abin zai zomai da sauki haka ba, Allah maji rokon bawa.
Nan ya shiga rerowa ummi godiya kamar ya ari baki, har tausayi ya bata yadda taga ya susuce, bai nemi ganin Amira ba don kar ummi taga ya cika azarbabi tace ta fasa, dakinshi da yake sauka idan yazo gidan ya sauka,washe gari a wurin breakfast ne yaga Amira, iya dauriya yayi ya samu suka gama ckin abincin nan lafiya baiyi wani abinda zaiji kunya agaban iyayen shi ba, don ba karamin kyau yaga ta kara mai ba , balle ma kwalliyan da yaga tayi, sai yakeji kamar ya zauna yata kallonta, kamar tv, duk a kage yake dasu keɓe, ya samu yadan rage zafi.
Ana gama breakfast , cikin azarbabi yace ma ummi da Abba shi zai koma, ummi duk ta gane azarbabi yake yi ya dauki matar shi, shi yasa yace zai tafi tun yanzu,cikin son ta gwada shi tace "aiko gashi Amira bata gama ba ko zaka tafi inyaso next week ka dawo ka dauketa" har bakin shi na rawa wurin cewa "A'a ummi zan jirata mu tafi taren ko nan da zuwa yamma ne" Ummi tace "wai da nace kar ka bata lokaci tunda naga Sauri kakeyi" yace "A'a ummi ba damuwa ta gama mu tafi kawai zan jirata" Abban amir na zaune sai kumshe dariyar shi yake yanajin diramin uwa da ɗanta.
Kiran Amira ɗaki tayi ta bata wani babban leda cike da kayan mata ingantattu tace kowanne akwai bayanin yadda zatayi amfani dashi ajiki ta rubuta mata, hada kayanta ta tayata dama kayan ba wasu masu yawa bane, ja mata kunne tayi akan karta kara zama ya mata irin damkar da ya mata wancen karon, intaga abin zaiyi yawa, har ya mata illah ta gudu, itakam Amira kunya kamar tace kasa ta tsage ta shige.
Har mota ta rakata ta shiga suka dauki hanyar minna twins kuwa harda kwallah na kewan anty Amiran su
To amarya da ango safe journey, asha amarci lafiya💋
Gidan Aslam haka rayuwar su yaci gaba da tafiya, kullum cikin bauta ma Asmah yakeyi da abinda ta saka shi da Wanda bata sakashi ba duk yi yakeyi, girki kafin ta tashi da safe ya gama breakfast, ya gyara gida ko ina yadau kanshi,ita dai baza tace mai sannu ba bare na gode, abinci kam zama takeyi taci hani'an idan ya girka, aikin gida kam duk ta sakar mai saidai tayi wanka taci kwalliya na fitar hankali ta kame a falo tana charting haka zaita kallonta yayta lasar laɓɓa, kamar tsohon maye, wanki da gugan kayanta duk ya dauke mata, batun zuwa office kuwa tuni ya jingine shi gefe sai assistant dinshi ne ke tafiyar da komai.
Asmah kam zuwa yanzu ta rage mugun tsanar da tamai ada yanzu dai kadaran kadahan takejin shi, itadai bayajin tsanar shi kamar da kuma bata jin sonshi a ranta ko kaɗan, tasan dai yana mugun bata tausayi,
Yau data kama ranar Sunday da misalin karfe takwas da rabi na safe taji ana mata knocking, ko bata tambaya ba tasan Aslam ne tashi tayi ta bude kofar ganin shi tayi dauke da tsintsiya da moppa a hannu, fuskar shi dauke da murmushi yace"gud morning mrs Asmah" amsawa tayi da "morning" yace "dama nace yau bari na share miki dakinki ne" har zatace ya barshi, don duk share sharen shi bai taba share mata dakinta ba, wata zuciyar tace ,barshi yayi Allah ne ya kama miki shi ya zama bawanki, cemai tayi"bismillah" tana kuacemai a hanya ya shiga, wow ya furta aranshi dakinta ya hadu sosai gashi a gyare tsab ba wani tarkace komai kimtse a muhallin sa, uwa uba kuma daddaɗan kamshi dake tashi mai saka nutsuwa dayake tashi hade da zabar Ac, kai gaskiya ita tanada tsabta ba kamar zee ba komai nata tsab stab, irin wannan wayewar yake nema yaje yayi lalube cikin duhu a baya.
Toilet dinta ya shiga ya fara wanke wa shima fess yake kara dai daurayewa yayi sama Sama, sannan ya dawo bedroom din nanma ya gyare shi tsab, ya ko iya gyara gado kamar wani klinan hotel, yana gamawa ya kunna heater ya hada mata ruwan wanka don yaga alamar batayi wanka ba ko.
A falo ya sameta yace "mrs Asmah nace na gama gyara dakin, saura wanka ko zaki tashi muje na taya ki na riga ma na sirka ruwan" harara ta watsamai, nan yayi fuskar tausayi tare da cewa "pls mrs Asmah wlh zan cuɗa ki da kyau" dariya ma ya bata, aiko ta shiga darawa, nan ya shagala yana kwallonta kamar yasa harshe ya lashe ta haka yakeji don so...........
Naceba wai baza ku tambayeni ina babyn Adam bane😤
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fisabillilah🙏
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
DAMA TA BIYU💖 ƘIRƘIRARREN LABARINE MALLAKINANE BAN YARDA WATA KO WANI SU JUYAMIN LABARI TA KO WACCE SIGA BADA IZININA BA❌❌❌❌❌
(In👂👂👂yaji, gangar jiki ya tsira👌 a kiyaye pls)
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}
Page 95
~BABYN ADAM~
Har Barr ya gama kwanaki bakwai daya kamata miji mai mata yayi a dakin amaryarsa budurwa,babu abinda ya shiga tsakanin su, na auratayya, saidai a yan kwanakin nan ba karamin sabo sukayi da juna ba, ta riga ta gama sakin jiki da shi duk dari darin da takeyi dashi da yanzu ta dena,yakan dan taba wasa da ita amma iyakanshi kenan bai taba nuna yana son wuce hakan ba, wannan yasa hankalinta ya kwanta, ta saki jiki da shi tunda abinda take ma tsoron, taga baida alamar yi, da amala dai ita nata miji ba dan air bane.😛
Har yayi kwana bakwai a dakinta bata fara girki da kanta ba daga gidan su ake aikowa, dan maryama cewa tayi baza tayi ba,
Duk motsinsu akan idon maryama, ta sanya musu ido sosai sometimes har labe take musu, ta fahimmci babu abinda ya shiga tsakanin su har yanzu, hakan kuwa ba karamin daɗi ya mata ba.
Tsakanin ta da Barr kuwa babu zaman lafiya kwata kwata, kullum cikin tayar mai da hankali take, gaba daya lamarin ta ya isheshi, kawai daurewa yakeyi yana kai zuciya nesa.
Yau ta kama zai koma ɗakin uwar gida ya gama kwanakin shi bakwai a dakin amarya, zahra harda kukanta shaɓe shaɓe haka yasa ta a jikin shi yana lallashi kamar wata jinjira, da'ker ya samu tayi shiru, tashi yayi ya shiga toilet ya haɗa mata ruwan wanke, yace tayi wanka ta same shi a dakin shi zai hada ta da maryama ya musu nasiha daga nan kuma yaji ra'ayin su,yanayin kwanakin da zasu raba.
Bayan fitar sa ta tashi ta shiga toilet d'in ta sheka wankanta da sabulanta masu kamshi na gyaran jiki, ta wanke dogon gashinta ta fito, zama tayi kan kujeran gaban mirror tayi shafe shafen ta, na mayukanta da turarukanta haɗaɗɗun gaske, tsantsararren makeup ta ɓata lokaci tayi a fuskarta, lokaci ɗaya ta dauki wani irin mugun kyau kamar wata balarabiya, dama ko batayi kwalliya ba mai kyauce balle kuma, lace ta ciro tsantsararre maroon color sai ratsin peach, ɗinki riga da skirt, dinki ya dan kamata haka yasa ya fito mata da shape sosai, dass ta fito kamar wata yar tsana, dauri ta kashe mai kyau na yayi, mayafinta karamin ta dauka peach ta ratayeshi a kafaɗa, turare ta dauka ta kara fesawa a kayanta, ta zura takalmanta mai tsini mahadin mayafinta ta dauki handset dinta ta nufi sashen Barr.
Bayan shigan shi daki wayar shi ya dauka ya danna ma Maryama kira, ringing wayar keyi tana kallo taki dagawa, har ya katse kara kira yayi saida ya kusa yankewa ta daga, ta kara a kunne batace ƙala ba, jin haka yasan baza tayi magana bane,don wani bin ji take da izza kamar wata jinin sarauta, da kausasheshen murya yace"na baki nan da 10 ki kimtsa ki sameni a part ɗina" kit ya kashe wayar sa, yanayin yadda taji muryarsa tasan ba wasa a maganar shi yasa ta tashi ba wani kimtswan da tayi kayan bacci ne a jikinta riga da wando da hulla haka ta taho abinta, Maryama ba kazama bace, amma tunda akayi mata kishiya ta dauki wahalallan kishi ta daura ma kanta shikenan komai nata yaja baya, har a gurin miji kimarta ya ragu, saboda wannan haukan da tajeyi da sunan kishi, saiyaji duk ta fice mai a rai, duk ta sukurkuta kanta a banza a wofi, tunda gashi dai duk tsiyar ta bai hana shi aure ba kuma bai hanashi kawo amaryar cikin gidanta ba,
( pls mata a kiyaye asan irin kishin da za'a dingayi ba kishin da zaki zubar ma kanki mutunci a gurin miji ba, duk sonki da miji idan ya tashi aure, kiyi hakuri ki danne kishinki, ba'ace karkiyi kishin mijinki ba amma kisan irin Wanda zakiyi, idan kika kama girmanki sai kiga duk wani abinda zai gudanar a lamarin aurenshi saida yardan ki, kece zaki zama bai bashi shawara komai zaiyi saiya gaya miki saiya nimi shawaran ki, tunda yaga kin bashi goyan baya, anan saiki yagi abinda kika yaga,amma in kika yi hauka zaki tashi a tutar babu ne, wasu ne can zasuci moriyar lamarin, idan kikayi kishin hauka kika tayar mai da hankali, kimar ki zaki zubar a