Showing 51001 words to 54000 words out of 201974 words
Chapter 18 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
sama data kasa,
Dadi ne ya lullubeshi shi jin muryarta daya dade yana begen ji,
Murmushi mai ciwo yayi yace"husnah ina sonki"
Idonta kur cikin nashi tace"karya kakeyi Aslam baka sona kuma baka taba sona ba,yaudaran kanka kakeyi da cewa kana sona, bakin da ya furta ki koya zo ya furta so daga baya karya ce kawai, to barin gaya maka ko ka soni ko ka qini Aslam ni bana sonka bana sonka bana sonka , ka fita a hanyata Kamal nakeso domin shine ya soni ya tallafi rayuwata tun bansan kaina, " hade hannayenta tayi alamar roko , tace"dan Allah na roqeka Aslam karka kara shiga sabgata, domin na zama mallakin wani , nan da yan kwana ki , zan zama mallakin farin cikin zuciyata kamaluddeen"
Tana kaiwa nan ta juya a fusace kamar kububuwa ta barshi nan tsaye kamar mutum mutumi,
Ya kusa kwashe twenty minutes a tsaye a wurin bayan wucewarta, kafin ya shiga motar shi ya figeta da wani irin mahaukacin gudu yabar cikin school,
Zaune suke a chicken republic, sunyi order abinci , kowaccensu cikin kwalliya ,da kagansu kaga manyan bebs, ma'aikacin wurin ne ya gabatar musu da abincin da sukayi order, ana ajiye abincin kamshin shi ya bigi hancin zee take taji zuciyata na tashi, amma haka daure ta kai loma daya bakinta,wani irin amai ne ya taso mata, mai karfin kan kace koba ta shiga kelayashi a cikin mayafinta, yawancin mutane dake wurin masu kyama , tashi suka dingayi suna fita da gudu,
Ma'aikatan gurin ne sukayo kanta suna mata sannu, beebalo ma ba'a barta a baya ba , saidai ta amaye abincin da taci ranar kaf, beebalo ta tallabeta , ta kaita toilet ta wanke fuskarta da bakinta,
Mayafinta kam cleaner din gurin ta dauke ta saka a bola ta gyara wurin,
A mota bayan sun fito daga wurin hade kanta da sitiyari , tayi, tana sauke numfashi, beebalo da tun d'azu ta diga mata ayar❓ta kalleta tace "kawata badai ciki kikayi ba," da sauri zee ta dago ta kalleta tace "ci me" beebalo tace "ciki "zee ta girgiza kai tace "ina ba zai yuwu ba ciki adan shekaruna , ke bani da wani ciki " beebalo tace "taya kika tabbatar baki da ciki , yaushe rabonki da al'ada" take gaban zee ya fadi don ita ta manta da wani Abu waishi al'ada,don kan aurenta da Aslam rabonta da shi,
Ganin yanayin rudun da ta shiga hakan ya tabbatar ma da beebalo hasashenta ya tabbata kenan, murmushin mugunta tayi a zuciyata tace"na samu hanya mai sauqi da zan rabaki da aslam har abada , wawuya kawai, kin mutu tunda kia dauki amana kika damƙama beebalo taƙizama"....................
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fisabilillaha🙏
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Page 65 & 66
Beebalo ta kalli zee tace "ke nake saurare ƙawata nace yaushe rabonki da ,period" zee tace"tun kafin bukina yau wata biyu kenan" beebalo tace"tabdijama aikam dai bamuga ta zama ba, dole ne muje a gwada mu gani ko cikin ne, " zee tace" a'ina zamu gwada bayan yanzu dare ne ko wani asibiti mukaje kinsan dai zasuce muje mu dawo gobe ne, kawai mu bari goben sai muje, " murmushi beebalo tayi tace, " ba asibiti zamuje ba kedai kawai kibar komai a hannuna, tabbatar cikin kawai muke da buƙatar ji yanzu, muje pharmacy mu siya P-test mu gwada mu gani,"
Tada mota zee tayi suka gangara na'uzo family pharmacy suka siyo P-test din har guda biyar ,
Gidan su beebalo dake unguwar limawa suka nufa , gida ne da ba kwabo komai yaro yaga dama yayi , toilet suka nufa zee tayi fitsari a wani dan karamin kwalba irin na turaren duri, saka abin gwajin sukayi, minti daya kuwa ya nuna musu layi jajaye guda biyu,
Ciki ya tabbata a jikin zee, ɗaura hannu tayi aka tace "na shiga uku ni zainabu na lalace, wlh bana son cikin nan ban shirya haihuwa yanzu ba , wlh bana son jikina ya lalace, yanzu dana haihu shike nan , nono na zai zube abubuwa da yawa zasu canja a jikina , Aslam zai daina sona, zanyi saurin tsufa, ", beebalo tace baki shiga uku ba ƙawata ni zan tsaya miki mu zubar da cikin nan cikin sirri yanda ba Wanda zai Sani, muyi abin mu mu binne , ajiyar zuciya ta sauke, ta rungume beebalo, tace"nagode ƙawata Allah ya bar kauna," hararan bayanta beebalo tayi sannan ta amsa da "amin amin ƙawata" a zuciyarta kuwa tana aiyana zakici uban ki ne yarinya,
ƙwance yake akan makekan bed dinshi, sai juyi yakeyi, tsakar dare ne don kimanin ƙarfe daya ne na dare,bacci gaba ɗaya yau ya kauracewa idonsa, kalamanta na yau ba karamin matsuguni suka samu a zuciyar shi ba , tunda yake wani magana bai taba tada mai hankali ba kamar yadda kalaman ta na yau suka tada mai hankali, ko wani motsi zaiyi sai kalaman ta sun fado mai a zuciya kamar a lokacin take sanar dashi kamar haka
(karya kakeyi Aslam baka taba sona ba,yaudaran kanka kakeyi da cewa kana sona, bakin da ya furta ki koya zo ya furta so daga baya karya ce kawai, to bari na gaya maka ko ka soni ko ka qini Aslam ni bana sonka bana sonka bana sonka , ka fita a hanyata Kamal nakeso domin shine ya soni ya tallafi rayuwata tun bansan kaina, dan Allah na roqeka Aslam karka kara shiga sabgata, domin na zama mallakin wani , nan da yan kwana ki zan zama mallakin farin cikin zuciyata kamaluddeen")
A fili ya furta "mallakin wani nan da yan kwaniki , ina! wlh baki isa ki zama mallakin wani ba matuƙar ina numfashi, kamal wlh ka rabu da matata kokuma na maka mugun lahani wlh, baka isa ka shiga gonata ba, zanyi maganin kane kamal, ni za,a yaudaya ni za,a munafunta"
Haka yayi ta sambatu kamar wani taɓaɓɓe,
Karshe dai wata zuciyar ta bashi shawara daya tashi yayi alwala yakai kukan shi gurin mahalicin shi,
Haka ko yayi ya miƙe ya dauro alwala yazo yayi nafilfili, yana idarwa ya shiga miqa kukan shi gurin mai duka, baiyi aune ba sai ji yayi ana kiran sallan assalatu,
Tashi yayi , ya shiga toilet yayi alwala ya tafi masallaci, yana dawowa ya biya dakin zee tana nan kwance kamar gawar sababi, har aka gama kiraye kirayen sallah, aka tada sallah aka idar ko motsi batayi ba, tashinta yayi, ta hanyar zuba mata duka a cinya, a firgice ta farka bako addu'a,
Tsaki yaja ya fice daga dakin, cikin sauri ta duro daga kan gadon tunawa da tayi, yau beebalo zata rakata asibiti , a zubar da cikin nan tun kafin ya bayyana, ta yadda kwallon mangoro ta huta da ƙuda, dan itama akan batun cikin nan jiya daƙer tayi bacci , saida ta kira iyayen ta ta gaya musu, dukkansu cewa sukayi taje ta zubar , wai bata isa haihuwa ba,
.yana shiga dakin shi ya zauna yayi azkar , da karatun alkur'ani mai tsarki a karshe ya dukufa yana ta kai kukan shi gurin mahakiccin shi, cikin kaskantar da kai da mika wuya,
Kafin gari yayi haske kuwa , ya samu sauki sosai a cikin ranshi, damuwa da baqin cikin da yake ciki ya ragu fiye da kaso hamsin cikin dari, har yana jin yau zai shiga office Wanda rabonshi da office din har ya manta, sai assistant shi ke tafiyar da komai na kamfanin,
Wanka yayi ya shirya cikin shirin fita office, yana gamawa kuwa ya leka ɗakin zee ya sallameta, dama dai ba batun karyawa a gida,
Shiga motar shi yayi ya nufi gurin da yake zuwa yayi parking kullum dan ganin Asmah ,yau kam taci sa'a ya samu ganin ta, sabanin wataran da ko yazo bazai ganta ba, saboda wani bin lecture rana take dashi ,
Suna wucewa shima ya dauki hanyar zuwa office, message ne ya shigo wayar shi , sharewa yayi dan yasan kila , kamfanin layi ne,
Saida ya isa kamfani ,ya samu shiga office ya zauna tukun , sannan ya dauki wayar shi da niyar kiran P A dinshi ya tuna da message d'in, budewa yayi ya fara karantawa tun kan yakai karshe yaja wani mugun tsaki , indai irin wadanan sakonnin ne ya saba cin karo da su jifa jifa,
Sakone na kalaman soyayya zafafan daga beebalo, delete din sakon yayi ya ci gaba da duba aiyukan dake gabanshi,
Can kuma wani massage din ya sake shigowa, kamar bazai duba ba sai kuma zuciyar shi ya dinga azalzalan shi akan ya bude sakon ya gani, budewa yayi ya fara karntawa, tun kan ya ƙarasa karanta, sakon yaji kanshi na juya mishi, a fili ya furta"whattttt! Impossible, cikin nawa zata zubar tana hauka ne hala," zama yayi daɓass akan kujeran shi mai jujjuyawa,
Can kuma ya zabura ya mike , yasan zee zata aika, yanzu mai zaiyi dan ya dakatar da ita,
Number da aka turo mai sakon ya shiga kira, acan bangaren beebalo ta daga kiran cikin kisisina, tace "amincin Allah ya tabbata a gareka ya kai Aslam tauraron zuciyata," ckin tsawa ya katse ta da cewa"wacece ke me kuma kika sani game da matata," murmushin barikanci tayi"matar ka ko maƙiyarka, lallai aslam har zainab kake kira da mata, to bari na gaya maka zaune kake da kasungumar makiyarka baka sani ba," katseta yayi da cewa "ba abinda na tambayeki kenan ba, kin tabbatar abida kika fad'a min gaskiya ne , don idan nayi bincike na gane wani abu daban rashin ki ya bushe, wlh matuqar kina cikin duniyar nan baki mutu ba ko ina kika shiga sai na lalubo ki," ya karashe maganar cikin wani irin razanannan tsawa tare da dukan table din gabanshi, saida takardun dake kai suka warwatse,
Cikin beebalo ne ya bada wani sauti ,kulululululululululu, alamar zawo na haduwa , dan ba karamin firgitata kalaman aslam da tsawan daya da ka mata yayi ba,
Amma kasancewar ta gogaggan yar duniya yasa ta dake ta fashe da kukan munafurci ,cikin kuka tace "wlh Aslam ni masoyiyarka ce, hakan ne ma yasa na kiraka don bazan so wani abin cutuwa ya sameka ba, ni ƙawar zainab ce mun hadu kimanin wata daya kenan da suka wuce, kuma kullum takan gayamin ita bata kaunar ka ta tsaneka. Dana sanin aurenka takeyi, ita wlh da zata samu dama kasheka zatayi har lahira, ni kuma haka kawai sai Allah ya daura min so da ksunarka na gaskiya , ni nake tausanta na hanata aiwatar da mugun nufinta akan ka, tasha kawo maka farmaki ina kare maka, kwatsam jiya ta same ni da batun cikin ka daya bayyana a jikinta, amma tace ita zubarwa zatayi, baza ta iya hada zuri'a da kaiba,na bata hakuri na bata hakuri taqi hakura, a haka muka rabu, shine d'azu da safe tazo gidan mu wai nazo na rakata ta zubar da ciki , nace baza ni, ba itama na shiga mata nasihar kar tayi haka , amma ta fice ko waiwayena batayiba wai innaga ta fasa zubar da cikin nan yau ranta ne ya fita daga gangar jikinta, tana fita nata kiran ta taqi dagawa, shine na tuna da wani number data taba bani wai number Kane , shine na kiraka ko kai zaka iya dakatar da ita, amma na rantse maka bayan wannan bayanin da na maka bansan komai ba a game da wannan magana," ta karashe maganar cikin fashewa da matsanancin kuka, kamar da gaske
Aslam da gaba daya jiri ke diban shi ya koma da baya ya zauna akan kujeran shi daya tashi, daɓasss, cikin matuqar sanyin jiki yace, "wani asbiti tace miki zata je " cikin sheshsheka tace"bansan wani asibiti zataje ba bata gaya min "
Godiya yama beebalo kafin ya katse kiran , maganar beebalo yayi tasiri sosai a zuciyar shi, kusan minti ashirin ya kwashe zaune a gurin yama rasa ta ina zai fara,
Can kuma kamar an tsikare shi ya dauki wayar shi da sauri ya shiga kiran lambar zee.
Beebalo na gama waya da Aslam ta kwashe da wani irin maketacin dariya, saida tayi mai isarta, sanan ta saisaita kanta , komawa tayi cikin wani karamin asibitin kudi , da sukeje don zubar da cikin,zee nanan zaune a inda beebalo ta barta , tace ta jirata,
Dawowa beebalo tayi gurin zee tace "ƙawa dan Allah kiyi hakuri nadan tsaya gaisawa da wani yayana ne" zee tayi murmushin yaƙe tace "ba komai ƙawa"
Duk jikinta a mace yake ji takeyi kamar ta fasa zubar da cikin nan dan haka kurum takejin gabanta na faduwa, kallon beebalo tayi tace,"kawa ji nakeyi kamar na fasa zubar da cikin nan wlh, haka kawai nakeji a jikina akwai matsala game da wnnan lamari, gara kawai na barshi ,idan ckin ya isa haihuwa sai amin aiki kawai a ciro shi ba sai na haihu da kaina ba, kinga sai a dinga ba babin madaran yara a samo mishi nanny ba shikenan ba"
Beebalo tace "tab wlh karki kuskura kiyi wannan gangancin na barin cikin nan idan har kina so kici
gaba da zama da Aslam, dan wlh yana gane akwai cikin nan ya dinga wulakanta ki kenan, karshe ma ya sake ki a banza akan wani dan qaramin ciki, bakisan maza yanzu basa son mace da anyi aure tayi ciki ba, kuma kinaga zaki iya rainon ciki akwai wahala fa mata da yawa suna mutuwa ta wannan hanyar, kawai tunda mun riga munzo ki zubar da wannan kawai in yaso idan kin samu wani cikin sai ki barshi ,"
Zee dai duk da hankalinta bai kwanta ba haka ta yarda da shawaran beebalo,
Dr din da suke jira ne ya ƙaraso, sun riga sun gama magana da beebalo a waya, ta gayamai harda irin alluran da takeson ama zee,
Binshi office sukayi, beebalo ta kara mai bayani sannan ta fice daga office din ta barshi da zee , dake kawance akan gadon dakin donya gwada ta yasan irin alluran da zai mata,
Tana fita wayar zee dake hannun ya fara qara dubawa tayi taga , lambar Aslam ne murmushi mugunta tayi tare da qin daga kiran
Kira yake yana sake kira a haukace, bata daga ba daga baya ya tura mata da message na karta kuskura tayi gangancin zubar mai da ciki, beebalo na karanta message din tayi delete dinshi a wayar ta kashe wayar gaba daya,
Sake kiranta yayi, yaji wayar a karshe take hankalin shi ya kara tashi, miqewa yayi da wani irin sauri ya fita daga office ya shiga motar shi ya figeta da wani irin mahaukacin gudu,
Dr na gama gwada zee ya kalleta da wani irin tausayawa, alluran da beebalo ta biya shi makudan kudi danya ma zee sun mata karfi da yawa zasu iya hallakata har lahira,
Har ya dakko zai mata yaji tausayin ta ya canza alluran ya mata Wanda bai kaishi karfi ba,
Kiran beebalo yayi yace tazo angama, su wuce gida maza maza, zee kam tuni ta fara ganin jiri jiri, kafin su qarasa mota har ta hada wani uban zuba ,beebalo sai zuba mata sannu takeyi cikin matuqar tausayawa,
Beebalo ne taja motar kasancewar zee bata cikin haiyacin ta, har gidan ta kaita mai gadi wa wangale mata get , tana parking ta tallabo zee har cikin falon kwantar da ita tayi akan dogon kujera, kafin ta juya ta fice daga falon da sauri,
Kaman kar beebalo tabar falon wani irin matsanancin ciwon Mara ya tasowa zee, birgima takeyi tana malelekuwa a cikin falon, tafi minti takatin a haka kafin jini ya balle mata da mugun karfi harda guda guda, kan kace kobo falon yayi faca faca da jini kamar an yanka ƙaramin dabba ,
Aslam saida ya je asibiti ashirin yana Neman zee dana kudi Dana gwamnati amma ko mai kama da ita bai gani ba, gashi wayar ta a kashe , duk da haka bai daina karanta ba,
Sai yamma ya dowa gida a galabaice,tunda ya danno kan motarshi ya hango motar zee fake a parking lot,
Ko gama parking din kirki baiyi, ya balle murfin motar ya fito da gudun tsiya , burin shi yaga bai wuce ace yana shiga ya tarar duk karya ne abinda beebalo ta fad'a mai ba,
saidai kash yana shiga falon ya hangi zee kwance a kasa cikin jini face face, a fili ya furta"ya furta innalillahi wainnailaihi Rajiun, shikenan ta faru ta kara, "
Zee kam hannu ta shiga mika ma aslam numfashinta na wanj irin fusga idonta na lumshewa, lokaci daya ta fede , ta rame ta ƙara fari fat,
Zuciya Ce ta debe shi ya karasa gabanta a fusace ya dagota ya hada ta da bango ya shaqe cikin fitar haiyaci yake cewa" meyasa kika zubar min da gudan jinina , mai na miki zaki sakamin da wannan mummunan sakamako, me jinina ya miki zaki salwantar min da rayuwar shi kika sani ko shi kenan kwaina a duniya, kin cuceni zee tsakani na dake Allah ya isa, ki gayamin wani likitane ya miki wannan aikin ,wa kuma ya baki wannan gurguwar shawaran ,ki fad'a min domin daga ke har duk wani mai hannu a cikin salwantar min da gudan jinina bazan barshi ba na rantse da Wanda raina ke hannun sa "
Zee kam tun taba zazzare ido , har jikinta ya saki numfashinta ya dauke ta sume, yana ganin haka yayi wurgi da ita ya shiga toilet ya ciki ruwan sanyi a katon bokiti ya sheka mata, take ta shiga sauke ajiayar zuciya,
Ganin ta farka yasa ya kara cin kwalarta yace"tambayarki nakeyi keda su waye kuka salwantar min gudan jinina" cikin kuka ta bude baki tana magana amma tsabar azaba maganar ma bata fita sosai,
Ganin taƙi bashi amsa yasa ya ya shiga gwada kanta da bango yana marinta , saida ya mata dukan tsiya ta ƙara sumewa , ya yasar da ita a wajen ya tsallaketa ya wuce,
Dakin shi ya shiga ya hada kayanshi kaf a