Showing 18001 words to 21000 words out of 201974 words
Chapter 7 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
Amira tace"ni Allah yasa ma kafin lokacin mun fara attending class , da ko bani da lecture ranar sai naje school "
Asmah tayi murmushi ta fahimci duk wannan abin da sukeyi , sunayi ne don tayata jin haushin wulaqancin da d'an uwansu ya mata ne, tace " duk kallon ku nakeyi ai wlh baku isa ba, bikin ya Aslam sukutum kuce wani ba ruwanku da shi , harda me cewa zata je school ranan ko, akan me to na fahimci ni kuke tayawa jin haushi ko , to wlh na yafe , aini wannan abinda da ya faru gaba ta kaini , ba gashi yanzu xanyi karatuna hankali kwance ba, da bai sakeni ba da yanzu inacan Allah kadai yasan halin da nake ciki" ai ni in kuna sona da gaske har haka kamata yayi ku taya ni murna, don haka ku manta da wannan caftar ku dauka kamar ba'abayi ba, har ankon yini dana dinner na zabar mana a wurin anty ummi,wani atamfa da wani material na gani a status dinta masu kyau sababbin shigowa , anjima bello zai karbo mana gobe sai mu mukai dinki daga nan mu biya gidan ya rabi'ah.
Haka ko akayi washe gari tunda safe bello yaje gidan anty ummi a unguwan darussalm ya amso musu atamfar da material din da Asmah ta zabar musu a matsayin ankon bikin, mummy ce ta biya musu kudin kayan da kyar don da tace ba wani ankon da zasuyi saida suka ta roqonta ta amince,
Wuraren sha daya da rabi suka cikin shirinsu na zuwa kai d'inki daga nan kuma zasuje gidan ya rabi'ah, kamar yadda suka tsara. part din mummy suka biya don gaisheta kamar yadda suka saba kullum, mami bata falo tana ciki don haka suka nemi guri a falon suka zauna jiranta, zamansu ba jimawa mami ta fito cikin shirin fita anguwa, ganinsu yasa ta fadada fara'arta, nan suka shiga gaisheta tana amsawa cikin kulawa
Mami tace"sai ina kuma haka naga anci wannan kwalliya ". Zahra ne ta amsa"mami zamuje mukai dinki ankon mu ne daga nan zamu biya gidan ya rabi'ah kullum complain take mana bama son zuwa gidan ta " mami tace"lallai yaran mummy kunaji da wannan yayar taku harda wani anko kukayi"
Batool tace "eh mami Asmah ce ma ta nace sai munyi ankon, itace ma ta zabar mana atamfar ta yini data dinner ' mami ta kalli Asmah tana mata hararan wasa tace"wato shine mu baza'a nuna mana ankon bako" a ranta kuma tana mamakin sauqin hali irin na Asmah , ace duk wannan wulaqancin da Aslam ya mata har tana wani fitar da anko dan zaiyi aure"
Asmah ce ta katse mata tunaninta da cewa "mami AI ankon fa na yan mata ne ba naku bane " mami tace "ba namu ba mu suwa". Asmah tace "tsofaffi mana". Mami ta zaro ido tare da cewa "ja'ira nice tsohuwa ".
Dukkansu dariya suka sa mata , inda suka tashi suna cewa mami sai mun dawo , tace"to Allah ya tsare, ku gaida min da Rabin da wannan mummunan yarinyar nata mai kwace miji " Asmah da zahra suka amsa mata da to mami, batool tace" kai mami kodai kina kishi ne ta fiki kyau, ta kwace miki miji " mami tace wanna beran tama isa ta kwace min miji ne da wani hancinta kamar Biro, dariya suka saka suna fita falon tare da ce mata mami sai mun dawo.
Asmah ce gaba suna fitowan part din mummy suna kwasan dariyan da mami ta basu hankalinta , kwata kwata baya kan kofar sai ji kawai tayi ta gwabza karo da mutum, da sauri tayi baya tana riqe goshinta tare da cewa wasshh subhanallah...
Shima Aslam dan baya yaja don ganin da wa yayi karo haka, idanunsu ya sarqe cikin na juna , da sauri ta dauke kanta daga kallon shi tare da furta "sorry " a hankali yadda bama lallai yaji ba, amma yajin,
Suma su batool dake binta a baya ganin abinda ya faru , yasa suka shiga firgici da tsoro duk a tunaninsu mari zai kai mata kamar yadda ya saba marin ta a baya. Amma sai sukaga akasin hakan,
Bi tayi ta gefenshi ta wuce suma ganin haka yasa da sauri suka bi bayanta. Mota suka shiga bello yajasu suka bar compound din gidan,
A tsaye yake a inda ta barshi ko qafanshi ya qasa dagawa daga wajen, tunda idanun su ya sarqe da juna ya tsinci kanshi cikin wani yanayi mai wuyan fassaruwa ga kuma faduwan gaban da muddin zai hadu da ita sai ya tsinci kanshi acikin shi, ya tasar mai wannan dalinlin yasa yake kiranta mayya, yoo imba maita ba ace kullum idan ka hada ido da mutum sai faduwan gaba, abinda ya bashi mamaki har yasa ya kasa motsawa kuwa ba komai bane sai ganin yadda yarinyar ta canza gaba daya ,a lokaci daya, ya tabbata inda Dane yadda sukayi karonnan da tuni ta zube a kasa tana kuka tana bashi haquri cike da tsoran shi, amma yanzu ji yadda ta kalle shi a wulaqnce tace mishi wani sorry ta gifta shi ta wuce ba wani damuwa a tare da ita , qwafa yayi ganin mami ta fito.ganin shi nan tsaye yasa tace "yawwa Aslam muje ko" shima sausauta fuskar shi yayi tare da cewa "to mami " , parking lot suka nufa suka shiga mota ko ina zasu ohoo.....
Wani babban shagon dinki inda suka kai dinki sukaje, bada dinku nan sukayi telan ya nuna musu style a wayanshi suka zazzaba sanna suka bashi rabin kudin dinkin suka fito, direct gidan ya rabi'ah bello ya kaisu inda ya barsu said a yamma zai koma ya daukosu......
Sun tarad da ya rabi'ah tana tsaka da aiki kace kace , abokin mijinta barrister Adam zaizo kuma ba qaramin ji dashi mijin ta keyiba don abokin shi ne tun na yarinta, a secondary school suka hadu Wanda yake boarding ne , Allah ya hada jininsu shikenan abota mai karfi ya qullu a tsakanin su , Wanda ya kaiga har iyayen su suma suka zama abokai sanadiyar su.
Barrister Adam ba yaro bane don a kalla zaikai shekara arba'in da biyar ko hamsin, amma abinka da dan gayu dan boko , ba kowa ke gane ya kai wadannan shekarun ba zaka dauka baifi 35 zuwa 38 ba yanada mata daya maryam da yaya hudu, banufen bidda ne iyayen shi gaba da baya nufawa ne amma kuma wayyayyun yan book ne,.
Kama mata aikin sukayi nan da nan kuwa suka kammala, daidai lokacin kuma uncle nura mijinta ya kira waya yace mata
barrister Adam din ya iso, ta kawo mishi abin mosta baki daganan su gaisa, yana falon baqi,
OK tace mishi tana ajiye wayar, ta kalle su tace" kunji ba wai ya iso yana falon abban hanifa gashi ni kuma ko wanka banyi ba sai warin kitchen nakeyi". Zahra tace "to yaya ki kai mishi abin motsa baki daga nan ki gaishe shi , sai kizo kiyi wanka ki koma ' shiru tayi alamar tunani sai kuma tace" no zahra ba haka za'ayi , barin had,a miki abin tabawan a tire kije ki kai mishi, ni kuma nayi wankan sai inje mu gaisa " OK kawai zahra tace mata,...
Kitchen ta shiga ta hado komai data shirya domin taran barrister Adam a tire ta miqawa zahra tace takai palon Abba hanifa ita kuma ta shigab room dinta donyin wanka, ..
Tiren zahra ta dauka ta nufi falon uncle nura da sallama a bakin ta kutsa kai cikin falon, dagawo dukkan su sukayi suna kallonta tare da amsa mata sallamarta ,
A hankali cikin nitsuwa ta qarasa stakiyar falon ta jawo wani dan table dake gefen kushin ta daura tiren akai ta dan matso dashi gaban gaban Barr Adam , dagowa tayi fuskanta sake tace "ya nura ina wuni" Abba hanifa ya amsa da "lpy qlau , yau yan biyun mummy ne agidan namu"murmushi yayi tace "eh yau mun kawu muku ziyara' yace "to madalla munko gode, ina sauran yan'uwanki"tace "suna ciki"yace "ok" juyowa tayi ta kalli barrister Adam da tun shigowarta ya kamata da ido baiko qeftawa tace "ina wuni " shiru yayi don baima jitaba , hankalinshi yayi nisa , gashi dai yana kallonta amma baijita ba said a abban hanifa yace "barrister ana gaishe ka " dan firgigit yayi yace "oh sister ya kike "tace "lpya qlau ya hanya "yace "alhamdulillahi mun sameku lfy tace "lpy qlau " yace"masha Allah"...
Miqewa tayi ta fice daga falon , da kallo barrister Adam ya rakata harta qurema ganin shi , saida abban hanifa yayi gyaran murya , sannan ya juyo da sauri ya kalle shi, d'age mai gira daya Abba hanifa yayi tare da cewa "yane" ajiyar zuciya barrister Adam yayi tare da cewa"finally yau Allah ya hada ni da ita , a cikin garin minna " Abban hanifa yace "ita wa kenan"
"Amaryata da naketa mafarkin na aura"abban hanifa yace"bangane amaryanka ta mafarki ba me kake nufi"barrister Adam yace"kona maka bayani yanzu bazaka taba ganewa ba, yanzu dai bari na tambayeka don Allah ". Abban hanifa yace "ina saurarenka ". Kasa yayi da murya kamar wani zai jisu yace "wannan beautiful young lady dinnan da ta fita yanzu wacece ita" murmushi abban hanifa yayi don ya gano abokin nashi kamar ya zurma yace "kanwar madam ce yan biyu ne ma suke bi mata a haihuwa" barristers Adam yace" wonderful Ashe shiyasa yau tunda na tashibacci naji kamar magnet na Jana zuwa minna a she abinda zan samu babba ne"abban hanifa yace"kamar yaya banfa gane abinda kake nufi ba Mallam" barrister Adam yace "ina nufin ina sonta, ina son aurenta, inason ta zama matata kuma amaryata " bata rai Abban hanifa yayi na wasa yace "kaga Mallam ayi haka dani ba kaima kasan nida maryam 5&6ne bazan bada goyan bayan a mata kishiya ba", Barr Adam kai dai ka Sani tunda ka fara wannan maganar nasan bazakamin abin arziki ba don haka ta hannun rabi'ah zan bi, "oho nidai ba ruwana kaida maryam,". Yace" eh din dama Vance da ruwanka ba ai"
Ranar su Asmah a gidan ya rabi'ah suka wuni sai magrin bello yazo ya daukesu.
Washe gari Monday suka fara shiga school don fara yin registration dinsu.........
Finally zahra ma ta samu nata rabon๐๐๐๐๐๐๐
Date: Oct 13, 2022
๐DAMA TA BIYU๐
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wanna book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Page 33 & 34
A kwana a tashi ba wuya yau gashi saura kwana uku daurin auren Aslam da zee , tun ranar Monday aka fara program ba kama hannun yaro ,
Ta bangaren zee biki akeyi gagarumi yayinda ta bangaren Aslam abin dai gashi nan kadaran kada han, don mummy ma cewa tayi bazata gaiyace kowa ba,yoo ta gayyaci mutane ta ce musu me , bayan ko wata uku ba'a rufa ba data gayyato su bikin Aslam, yanzu kuma ta sake ce musu suzo bikin Aslam again, gsky baza ta iyaba.
Biki dai ba wani bare daya zo duka dai yan gida ne wadan da zuwa bikin ya zame ma dole,
Yau ne akayi kumbo kuma yaune ango ya fara halartan program daya daga cikin ukun daya zaba zaije,
A babban hole din dake mai jama'a hotel akayi 4:pm aka fara aka tash70:pm, daga dangin ango kam ba wanda yaje. Sai shi kadai da abokansa sai ko kamal, su zahra dama sukayi niyyan zuwa kuma mummy tace bazasuje ba, haka suka haqura,
Misalin qarfe takwas da rabi na dare, Aslam ne da wasu daga cikin abokan shi zaune a palon shi suna fira, su niyara ne Aslam, amir, Dr bash, sai wasu baqin fuska su biyu,
Fira sukeyi suna dan rahan su irinta abokai suna dariya, kamal ne yayi sallama ya shigo , ganin su a palon yasa shima ya zauna akaci gaba da hiran da shi ,
Amir ya dubi Dr bash yace"bash kasan ni ban iya boye, boye ba arayuwa ko mutum zaiji haushi na saina fadi abinda ke raina" Dr bash yace"kwata kuwa nasan da haka " amir yace "a gaskiya ina taya abokina kuma dan uwana jaje" duka sauran abokan nasu da shi kan shi Aslam din maida hankali sukayi kan shi don jin me zai fada,Dr bash yace "jajen mefa" amir yace "na rashin kyakkyawa kuma natsatsiyar yarinya kamar Asmah mana" hade rai Aslam yayi ganin amir na naman yaci mai mutunci, bash dake kunshe dariyar shi ganin yadda lokaci daya fuskar Aslam din ta koma, yace, "amir me kake nufi kana nufin kace ita zainab bats da kyau da nastuwa ne " amir yace"a a nifa bance ba ta da nutsuwa ba tanada nutsuwarta dai dai gwargwado, amma batun kyau kam abarshi, mace a tsaye sambal sai kace bigun katako " dariya sauran abokan suka saka, anas yace "gaskiya amir baka da mutunci wlh".
Aslam kam qara hade fuska yayi tamau iya kunnuwa kuwa ya kunnu sosai , ji yake kamar ya tashi ya rude amir da duka, amma ya fuska ya qyaleshi,
Amir ya amsa ma Anas da cewa "nida shi wayafi wani rashinmutunci , ai tunda ya wulagantamin qanwa akan wannan figaggiyar yarinyar mai zubin tabarya , wlh daga shi har ita sun shiga uku dani, kuma wlh asaran shi don nayi imanin bazai taba samun kamar taba balle wacce ta fita, tun yanzu AI gashi nan Allah ya fara kamashi, kaga bashir na daya Asmah akwai natsuwa, hankali, ladabi, biyayya kunya , ilimin addini Dana book tarbiya, uwa uba gata da wani irin kyau mai fisgar duk wani lafiyayyen namiji, asalin figure 8 nake gaya maka mallam, komai yaji " miqa mai hannu bash yayi suka fata suna dariya , yaci gaba da cewa "wlh badadon nayima kaina wani tanadaiba da ba abinda zai hanani yin wuff da ita kuma ko yanzu ma bata baci ba "
a fusace Aslam ya miqe kamar wani mayunwacin zaki ya kaima amir wawura, amir da tun dazu yake ankare da Aslam din sanin da yayi hakan zai iya faruwa, yayi wuff ya miqe yayi hanyar qofa, tsayawa Aslam yayi yana huci ganin bai samu nasaran damqarsaba yace"banza dan iska kawai" juyawa yayi ya wuce sama fuuuu daki ya shiga ya buga kofa da qarfi ji kake bamm, don ranshi ba qaramin baci yayi ba inyace zai tsaya yin magana lokacin bazai fadi alheri ba,
Amir daya gama tikar dariya ,ya dubi su bashir yace ku tashi na rakaku ku tafi, yayi qwafa tare da cewa "ai wlh dani kake zance Aslam duk wula qancin da kamin a lokacin wancen bikin saina rama" tashi sukayi suka fice suka bar kamal shi kadai,
Kamal da yayi mutuwar ......
Manage pls
Date: Oct 14, 2022
๐DAMA TA BIYU๐
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wanna book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Page35 & 36
Kamal da yayi mutuwar zaune tun lokacin da amir ya fara magana akan Asma'unshi, jiki ba kwari ya miqe ya shige room d'inshi, ba abinda yafi tsaya mai arai irin cewa da amir yayi , (wlh bada don nayiwa kaina wani tanadi ba. da ba abinda zai hana nayi wuff da ita kuma ko yanzu ma bata baci ba") ya maimaita wannan kalman a fili da zuciyarshi yafi sau hamsin
Me hakan ke nufi karfa ya tsaya sanya ya sake rasa Asmah a karo na biyu , karfa yayi saken da zai kuma rasa second Chance d'inshi,
Tunawa yayi har yanzu fa Asmah bata bashi gamsasshiyar amsa game da maganar su ta rannan ba , a fili ya furta "ya zama dole ki bani amsata a gobe goben nan, ya zama dole nasan matsayi na a gareki, ya zama dole manyan mu Susan da maganar nan, Susan da zamana kar na zauna kallon ruwa kwado yamun qafa, a haka ya kwanta barci yanata tuna ni da'ker bacci barawo ya dauke shi...
Asmah anata bangaren ta riga ta gama shawara tsakanin ta da zuciyarta , ta karbi soyayyar ya kamal da hannu bibbiyu ko dan kyauta tawanshi gareta, ina laifin masoyinka. Ita kam dai ta amince da kamal indai har zai mata alfarmar barinta tayi karatun ta lpy ba tare da manya sunsan da maganar ba ,
Washe gari ummi ta iso daga abuja ita da yan biyun ta maza kannan amir, wadan da qanana ne baza su wuce shekara takwas ba, don bayan haihuwar amir ta dade kafin ta sake haihuwa har an cire rai ma, ta sauka a d'akinta dake part din hajiya mama Wanda in tazo anan take sauka , yau yan matan mummy ummin su tazo, suna can part din hajiya mama acan suka wuni sai surutu suke zuba mata , ita kuma tana biye musu taji mastalolinsu, tana basu shawarwari inna bada shawaran ne , don tun basu kai haka ba ta basu wannna daman na duk abinda ke damun susanar mata , kar su yarda su sanar ma wani a waje damuwarasu,ta jasu a jiki sosai ta maida su tamkar qawayenta,
Ranar yan matan mummy part din hajiya mama suka wuni kwana ne kawai basuyi can ba , don sai wuraren goma suka dawo part dinsu lokacin na mummy na sashen daddy,don haka dakinsu suka wuce suka kwanta sai bacci.
Washe gari juma'a ma haka suka tashi cikin hada hada don gida yadan cika, duk da ba'ayi gayyata ba saida mutane suka zo,
Zahra da Asmah sallama suka wa mummy zasuje amso dinkin su don tailorn ya kirasu ya gama , su biyu zasuje don amira da batool na sashen mami suna taya ta wasu aiyukan, cikon kud'in d'inkin mummy ta basu suka nufo parking lot da niyyar bello ya kaisu, nan suka tarar bello naya nan wai Aslam ya aike shi , juyawa sukayi da niyyar komawa ciki su