Header Ads
Showing 162001 words to 165000 words out of 201974 words

Chapter 55 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1728

Ads at the middle of Article

hmmm kunsan me ya same ta kuwa." Har suna haɗa baki wurin cewa "A'a mummy." Tace "to haukacewa tayi" batool cikin ta shin hankali tace "haukacewa fa kika ce mummy." Amira kam tuni ta kafa kofin kunun kanwa abaki ta fara kwankwaɗa, mummy tace "kwarai kuwa hauka tuburan, tana zaune kawai sai a ga tana zabure zabure kamar ta ɓaɓɓiya aka rasa mai ke damun ta, karshe miji ya koreta Gidan su ya dallo amarya." Asmah da duk tafi su ruɗewa tace "ta yaya aka gane rashin yin jego da kyau ne ya saka ta hauka." Mummy tace " labarin Nada tsowo kudai bari na barku a nan, dare nayi kuma zanwa yaro wanka." Ta amshi babyn a hannun Asmah ta fice dashi.


Zama Asmah tayi a bakin bed jiki a sanyaye tace "Allah mun gode maka, abubuwa iri iri daga wannan a shiga wancen,Allah dai ya raba ku dashi lafiya kuma." Ta faɗa tana kallon batool, "ke kuma Amira wlh ki tsaya kiyi wanka nan da kyau kin dai ji abin da mummy tace idan ba'ayi da kyau ba haukacewa akeyi ni wlh duk jiki na yayi sanyi, gashi haihuwar ma ba karamin azaba bane dashi aka ce." Zaro ido Amira tayi tare da cewa "kaiii azaban ma, in kinji azaba kara mashi S." Batool da duk ta ƙara tsurewa tace "dan Allah sisters mu bar wannan zance kar kusa na kasa barci yau."dariya suka saka mata Amira tace "yar banza ga tsoro ga mugun aiki." Itama dariyar ta kama yi tace "wlh Allah jikiña yayi sanyi, ga kuma wancen mutumin sai harara na yake yi, tunda ya shigo falon nan yake ta auna min harara, duk hankali ya tashi wlh."Amira tace "wa kenan" tace "wa kika sani banda yaya babba" Asmah ta kwashe da dariya tare da cewa "Zakiyi bayani ne, duk rashin M din da kika gama zazzaga mishi a waya ɗazu a kunnen shi." Dafe kirjinta da yayi wani irin buga wa tayi tare da cewa "dan girman Allah." Asmah tace "wlh kuwa" daura hannu tayi aka tare da cewa "na shiga uku na ni batula." Duk dariya suka shiga yi mata Asmah naba Amira labarin yadda abin ya wakana.


Guri ta samu ta zauna a bakin gado tare da cewa"kinga tunda na zauna a nan nida fita a ɗakin nan sai yabar Gidan nan kokuma in Dr yazo nabi ta kofar kitchen ɗin mummy na same shi a parking lot, dan Allah Asmah idan ya tambaye ki ina nake kice na tafi gida." Haka suka zauna a dakin Amira suna ta fira suna shan dariyar batool, mummy ta dawo da baby tayi mai wanka ta shirya shi tsaf, sai tsoston hannu yake yi, ganin haka yasa mummy tace Amira ta bashi nono, da'ker ta bashi wai kunya, yana kamawa kuwa taji zafi ta tsallara ihu, tana kiran Amir, mummy tace "kice Allah yaso mu dai da muka yo gida dake." Kan ta rufe baki saiga Amir ɗin ya shigo dakin a ruɗe ko ta kan su batool bai yi ba ya nufi matar shi zai tallabo sai cewa yake "baby me ya sameki meke faruwa meke miki ciwo." Mummy ce ta daka mai tsawa "kai Amir." Dakatawa yayi yana Sosa keya tace "fice ka bani guri" ta faɗa tana nuna mishi hanyar kofa saɗaf saɗaf ya fice daga dakin.


Tunda aka samu yadan tsotsa duk da ba ruwa Asmah ta karɓe shi ta hana kowa, duk mai son ganin shi ya gan shi a hannun ta, zahra ta kira waya sun gaisa an dauki hotunan babyn an tura mata sai murna take yi, tana cewa zata zo suna.


Nan Gidan suka karkare wuni ranar sai gurin Karfe taran dare suka bar Gidan lokacin tuni su ya Rabi'ah da Khadijah sun wurwuce, batool ma sun tafi amma fa kamar yadda ta faɗa ta kofar kitchen tabi dan kar ta haɗu da ya Aslam.


Tunda Amira ta haihu kullum Asmah da Aslam sai sunje gida ganin babyn haka zasu ta rigen rigen ɗaukar shi, idan Asmah ta samu ta dauke shi kuwa duk Wanda yazo sai dai ya kalle shi a hannunta, idan zasu tafi kuwa da'ker take tafiya, ranar ma cewa tayi a bata babyn ta tafi dashi da safe zata dawo dashi da safe, dariya su Mami suka fara mata, ita ko bilhakki da gaske take, sai daker mummy ta lallaɓa ta, ta tafi harda hawayen ta kuwa.


Ana gobe suna ummi ta iso, zahra kam Barr ya hana dan itama tayi nauyi, tako sha kuka, haka ta kira ummi a waya tana gaya mata tana kuka da'ker ummi ta lallaɓa ta ta kwantar mata da hankali.


Ranar suna ansha shagali yaro yaci sunan daddy Abdallah za'a kira shi da Ayman, ƴan dama ta biyu fans basu samu zuwa ba wannan karan saboda matsalar rashin jirgin kasa da suka samu, dan har sun shishshirya sun hadu a tashar jirki aka ce musu ba jirgin da zaije minna a ranar, su zainaba har da kuka.


Bayan sunan Amira da kwana 7 Khadijah ma ta haihu, ita ma namiji, wohoho, kar kuso kuga murna gurin wannan ahli, ba'a magana, abin sai Wanda ya gani, ita ma dai gida su mummy suka daukota amma ita a part din Mami ta sauka, wannan karan ma dai Zahra bata zo ba oga ya hana, Asmah kam liyafa taci gaba yaran ta sun zama biyu, kullum sai taje gida, idan bata je da rana ba koda daddare ne sai Aslam ya kaita taga babies.


Ranar suna yaro yaci sunan Abba, yusuf za'a kira shi da na'eem, haka taron suna ya watse lafiya lafiya, aka bar masu jego a family hause inda suke samun kulawa sosai a gurin iyayen su, ummi ma tuni ta koma Abuja.


Yau data kama sati biyu da haihuwar Khadijah, daidai kuma da sun gama shan maganin da Dr Aysha ta rubuta musu na 1mnth yau kuma suke saka ran komawa asbiti, cike kuma da fatan samun dacewa, dan tun last week suka ta saka ran zuwan period dinta shiru gashi har yau da suke shirin komawa hospital babu shi babu labarin shi, da wuri ta tashi ta gama duk wasu aikin dake gabanta har da hada breakfast Aslam na gefen ta yana taya ta ɗan miƙo wancen dauraye wancen, bayan sun shirya dining, wanka suka shiga a tare dan dama tunda komai ya daidata a tsakanin su tare suke wanka muddin zaiyi wanka to dole ne tayi koda kuwà fitowar ta kenan daga toilet sai ta koma sunyi tare, tun tana yi har itama ta saba indai ba taren suka yi ba bata jin daɗi.


Sun bata lokaci sosai wajen wankan suna wasanni dan karshen ta saida aka kashe boss a toilet ɗin sannan suka fito maƙale da juna daure da tawul, zaunar da ita yayi gaban mirror ya shiga busar mata da gashi ta dake jike, sunayi suna hira, yace "my hussy ina ji a jikina kamar wannan karon mun dace da maganin nan, saboda kinga gashi har yau date 15 bamuga period dinki ba." Tace "Allah kuwa honey nima haka nake ji a jikina har mafarki na yi jiya wai gani dauke da babyn ka babba har ya kai 1ysr amma kuma banga sanda nake da ciki ba banga sanda na haife shi." Cike da zakuwa Yace "da gaske hussy." tace "wlh kuwa, ai dana farka saida nayi sujudul shukur." Yace "shine baki gaya min ba nima nayi, aini da har saraka sai nayi duk da ko yanzu ba bata baci, bari ma nayi sauri na gama miki, mu shirya wlh har naji na matsu muje asibitin nan, badan p- test ɗinmu ya kare ba da sai mu gyada tun yanzu ma." A haka ya gama mata ya shafa mata mayukan ta da take amfani dasu ya taje mata shi yayi mata parking ɗin shi, tsaf ta fito kamar wacce taje saloon, Aslam ya gware sosai gurin gyaran gashi, don yana matukar son gashi, wata ran ma har kitso yake mata ya kwance.


Mai ya shiga shafa mata yau har makeup shiya mata, ya Ciro mata kayan da yake son ta saka, tana zaune tana gyara fuskar ta duk inda bai mata ba, tashin da zata yi gaban mirror da nufin ta saka kaya, saiga jini a bayan tawel din dake daure a jikin fari, ita bata ma kula ba, shine ya fara gani sai da gaban shi ya yanke ya faɗi. cikin zaro ido yace "meye wannan husnah." Cikin rashin fahimta tace "A' ina." Yace "a bayan ki."waigawa bayan ta tayi da sauri, ganin bata fahimci inda yake nuna mata ba yasa ya kamo tawel din ya janyo wurin ya nuna mata, a tsora ce ta ƙara ware idanunta a kan abinda yake nuna mata baki na rawa tace "honey kamar jini fa." Shima cikin tashin hankali yace "husnah ba kama bane jinin ne.Inna lil lahi wa inna ilaihi raji un." Ya shiga maimai tawa, yayinda ita kuma tuni ta fara hawaye , kwarai da gaske sun saka rai wannan karan sosai ganin Dr aysha ta basu magani sunsha har na 1mnth bugu da ƙari kuma rashin ganin jinin da basu yi akan lokaci ba, abin ka da mai nema duk sai suka saka rai da cewa lallai cikin ne.


Ranar gaba ɗayan su haka suka wuni kamar wa inda kama mutuwa, asibitin ma fasa zuwa sukayi, karshe Aslam yace baza ma su sake zuwa wani Asibiti ba daga yau, zasu zauna su zuba wa sarautar Allah ido, sannan suyi ta addu'a Allah ya basu masu albarka dan shine mai bayar wa.


Haka ko akayi tun ranar basu kara zuwa asibiti ba,sai dai fa kusan kullum suna hanyar family hause, don babu abinda ya ragu a zukatan su game da kawazucin son babies saima abin da ya ƙaru, mummy Mami da su daddy,kai duk sauran mutanen Gidan suna matukar tausaya musu, kowa fata da addu'a yake musu akan Allah ya basu nasu suma, hajiya mama har yan jike jiken su tayi na mutanen da taba Asmah amma shiru kake ji wai mallam yaci shirya yasha ruwa.


A haka su Amira suka yi arba'in ko kwana daya kuwa basu kara ba mummy ta tattara ta tace ta su tafi Allah ya raya don ta gaji da rashin mutuncin Amir, kullum sai ta mai Jan ido yake tafiya, badan ma tayi kaffa kaffa ba, da kila tun jini bai tsaya ba zai haike mata, Tasha kama shi yana lalube ta, rannan ma badan Allah ya kawo ta ba da bata San me zafi faru ba, aiko tana ganin su ta koma da baya da sauri Allah yasa su basu ganta ba sun yi nissa,komawa bakin kofa tayi ta rafka sallama tuni suka shiga dawurwura daga shi har Amiran to ba gaskiya. Korar shi a dakin mummy tayi, ta rufe Amira da faɗa, tun lokacin ta kara saka ido sosai akan su, jini kuma na yanke mata, ta shiga yi mata gyara na gani na faɗa gyaran da ko da za'a aurad dasu basu samu irin shi ba, shiya sa suna cika 40 days ta tattara su tace suje Allah ya raya.


Sati daya da wucewar Amira itama Khadijah ta wuce, Aslam da Aslam sunji matukar kewa sosai wucewar su Amira, sai dai ba'a rufe sati ba suje gida jensu suna yaran ba.


A cikin wannan yanayin Zahra ma ta sauka,itama dai namiji, murna gurin Asmah kamar ita ta haihu, Barr kememe ya hana ta zuwa wanka gida wai sai dai azo a zauna da ita a mata, ba yadda suka iya, shike da iko da ita don haka aka tsayar ummi zata je ta zauna da ita, tun washe garin haihuwa Asmah tace ita bidda zata tafi, sai anyi suna, Aslam ko yace baza ta ba, nan fa ta shiga zuba mishi rigima kullum kuka karshe har ƴararta ya kai gurin ummi, da'ker ummi ta samu ta sasantasu bayan ta mata nasiha mai rasta jiki, ana gobe suna duk suka dauki hanyar bidda ya Rabi'ah,Asmah,Amira, Khadijah, ummi,hajiya mama, banda batool da ake saka ran haihuwa ko yau ko gobe, Dr shima hanawa yayi aiko dai hauka ne kawai ba yi ba dan bai gaya mata baza taje ba saida ta gama shirya kaya, taci kuka harda su hawa iskan karya, aiko tun daga lokacin ta tasar ma da kanta nakuda.


Wannan karon dai dama ta biyu fans an samu halarta, aiko dai da yawan su sukaje, dan wannan karan harda wadan da basu samu zuwa biki ba.sai ga su inna habee a bidda, su zainaba wannan karon dai babu kuka bakin nan har kunne, su sweetie an sako na kasan akwati, ranar gani ga daughter na sai shagwaba take zubamin, maryama uwar gida ce ta amshe mu da fara'ar ta, ta kaimu falon ta, su O'O sai zunlen ta akeyi ana dariya, nace ba rabi baza kiji tsoron Allah ba ko ina sai kin nuna hali, nan take ta shiga jigilar gabatar mana da abinci, kala kala harda su tuwon shinkafa miyar wake abincin nufawa, aiko dai duk shi suka rufar wa,ana shan miyan wake ana santi, nidai nace musu asha miyar wake a sannu,kakus ko dake cikin ta bai da kwari tun a gidan ta fara zawo, zainaba tsabar santi memo ta dauko wai dan Allah a gwada mata yadda ake miyar nan in ta koma garin su ta ringa yi, oum Aneesarh dake duk itama irin zahra ne banufe take aure ta gware a iya miyar wake, ita ta dinga koya mata yadda akeyi, sai ga inna habee ma ta dauko nata memon tana rubutawa teema kam data fara lashe plate saida ya koma kamar an wanke, anty mahmaa kuwa anga yan uwa sai yare take ta zuba wa ba kama hannun yaro.


Haka aka shiga gabatar da suna cikin farin ciki da annashuwa, yaro yaci sunan mahaifinta Barr, za'a kira shi da sultan.ana tsaka da shan suna mummy ta kira su batool ta haihu mace, nan fa aka shiga wani sabon farin ciki. Mami tace "ita kuma batula ana yayin samari sai ta tashi ta haifo kishiya ,to tunda dama bana gari ta haihu na bar ma mummy." Dariya suka saka mata ya Rabi'ah tace "Mami ya da saurin karaya haka tun baki ga kishiyar ba." Haka suka shiga wasa da dariya cike da farin ciki.


Lokacin da su O'o akayi arba da zahra duk rudewa sukayi, ta kara wani kyau tayi fresh duk yadda suke hasashen ta ta wuce nan, nan fa su zee da su rabi aka shiga kashe selfie nima dan kar a barni a Baya shiga nayi muka dinga dauka na samu na daurawa a status.


Washe garin suna su Asmah dasu mami suka dauko hanyar minna yayin da aka bar ummi akan sai ran suna zata zo ta koma ranar saboda ita ke kula da zahra a nan.


Batool anji maza wurin naƙuda abinka da mai baki, sai surutai kala kala take yi, ita karan kanta Dr dake amsar haihuwar duk tausayin ta saida batool ta saka ta dariya, Dr bash dama cewa yayi bazai iya karbar taba, dan koda ta fara a gida kasa tabuka mata komai yayi kamar ba likita ba, sai da ya kira maah kenan ta dauko wata likita makwabciyar su suka zo kenan, aiko yasha faɗa gurin maah kamar zata mare shi.


Bayan an mata wanka da babynta an kimtsa su, zuwa dare maah tace oya maza ya haɗa mata kayan batool zasu tafi, zaro ido yayi yace "maah me kika ce." Tace "gidan ku bashir abinda kunnayen ka suka jiyo maka shi kace." Gyada kai yayi a zuciyar shi yace akwai ƙura kuwa, ba yadda ya iya haka ya haɗa musu kayan ya kai mota ya zuba musu, sannan ya gaya musu ya gama suka fito suka tafi, ɗakin bash nada maah ta sauki batool kusan da nata ɗakin.


Bayan ya kaisu komawa yayi shima ya jido kayan shi sai gashi da katon a kwati mai taya yana ja, lokacin da ya shigo duk suna falo banda batool dake can kwance tana baccin huce gajiya. Su afifah sun zagaye maah suna kallon ta na gasawa yarinya cibi, an kashe fanka an kashe Ac falon ya dauki dumi sosai, duk idanu suka kwalalo mai, maah tace"ka manta ne da sauran kayan su batulan?" Yace "maah ba kayan su bane nawa ne?" Tace "naka kamar yaya, ko ka amso guga ne" yace cikin babbata rai dan ma kar tace A'a "maah nima na dawo nan Gidan da zama ne har san da zasu komo mu koma tare." Sallallami maah ta shiga, tare da cewa ",yau ni zuwaira naga karshen rashin kunyar yayan zamani, wato biyo matar ka kayi bashiru." Da sauri yace "A'a fa maah." Tace "to idan A'a ne ɓace min da gani kafin na sassaɓa maka." ta faɗa tana nuna mishi hanyar fita magiya ya shigo mata, har da cewa wai tsoron Gidan yake ji bazai iya zama shi kadai ba, harara maah ta watsa mai tare da cewa "to wlh sai dai in a baskwata zaka zauna don nan dai babu ɗakin zaman ka." Ba irin nacin da baiyi ba maah ta kafe kai da fata, dole haka ya amince zai zauna a BQ din ko ba komai kullum zai samu ya dinga ganin batool kafin ya fita da idan ya dawo.


A washe garin ranar da su Asmah suka dawo kowacce ta hallara agidan maah, don yima batool barka, nan fa suka ga baby kyakkyawa da ita kamar afnan sak, Asmah kamar ta hadiye babyn ko yan barka da'ker take basu sai anyi magana ma take mikawa, da kayi minti biyar kuwa zata amsa.


A haka sati ya zagayo akasha suna mai ƙaya tarwa yarinya taci sunan maah juwairiyya, z'ake kiran ta da Ummeetarh, saboda sunan uwar miji taci.


Duk wani gata da kulawa da mai jego ta zata biɗa batool ta samu fiyye da haka a gurin maah, ta tsaya kai da fata tana kula da ita fiyye da yadda zata ma su amrat. Tsakanin ta da Allah take mata komai, gafe guda Kuma.ga wani irin so da take nunawa baby Ummeetarh, daga ita

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads