Header Ads
Showing 57001 words to 60000 words out of 201974 words

Chapter 20 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1741

Ads at the middle of Article

taso ya buɗe yana tambayar waye,sauran maganan ne ya maƙale ganin Aslam tsaye cikin wani mawuyacin yanayi, da'ker Aslam ya buɗe baki yace, " ka sallami mai keken nan, "
"To yallabai to yallabai" haka me gadi ya dinga maimaitawa jiki na rawa.






Bayan me gadi ya biya kuɗin napep dawowa yayi yana ta jerawa Aslam sannu tare da tambayar shi meya same shi haka, Aslam ya bashi Amsa da cewa"tsautsayi na samu amma da sauki sosai alhamdulillahi"
bayan haka bai ƙara cewa komai ba ya wuce cikin gida.




wanka kawai yake bukata a halin yanzu, don haka yana shiga ya wuce toilet ya hada ruwa mai zafi ya shiga cikin bathtub ya gasa jikin shi da yayi mugun tsami ta ko'ina, saida ya kwashe fiye da awa ɗaya sannan yayi wankan sabulu,ya fito daure da tawul a kugunshi.




Gaban mirror ya tsaya yana karewa jikin shi kallo, yanzu lafiyayyar farar fatarshi mai shegen sulbi da daukar Ido ne ya koma haka cikin kwana uku kacal, duk dabbare dabbare , jaja jaja fari fari, ga wasu wurare sun tattashi saboda cizon sauro, fuskar shi ya kalla, nan take wani kululun baƙin ciki ya tokare mai wuya, ganin yadda halittar fuskar shi ta sauya, gaba daya kamar ba shiba, ƙasan idon shi na dama ya wani kumbura , haka ma labbanshi na kasa shima yayi simtim , goshin sa kuma wani makeken ciwo ne.






ƙwafa yayi a zuciyar shi yana aiyana ta ina zai fara ramakon wannan cin mutuncin da Dad din zee yasa aka mishi, ya lashi takobi ko ba jima ko ba dade ,saiya rama ,ko ba ta hanyar duka ba kuwa,sai ya mishi abin da zaiji zafi kwatan kwacin irin zafin da saka shi ji ,koma fiye da haka, tunda yake a rayuwar shi bai taba zuwa police station da sunan belin din wani ba balan tana kuma ace shi aka rufe, sai gashi yau wai ta dalilin zee shine ya kwana uku a cikin cell, ana dukan shi ana azabtar da shi, zee din daya bijirewa zabin iyayen shi saboda ita,Wanda daga ƙarshe yazo yana nadama da danasani, babu abinda auren zee ya tsinana mai sai asara da wahala, a ƙarshe harda cin mugun duka.




Wata zuciyar ne ta shiga raya mai Aslam baka ga komai a rayuwar ka ba, tukunna matuƙar baza kaje ka nemi gafaran iyayen ka ba, ka tsuguna har kasa ka nemi gafaran alhaji baba ba, Asmah kuma ka sakama zuciyar ka haƙuri da juriya akan lamarin ta , ka zama jarumi , ka dauki rasata da zakayi a matsayin kaddaranka.




Mai me zafi ya dauka ya shafa a inda duk ke mishi ciwo , kaya ya dauka marasa nauyi ya saka, sannan ya sauko ƙasa ya hada tea mai kauri yasha , yasha maganin pain relief, Dana ciwon gabobi, ya nemi waje ya kwanta,.








Saida Aslam ya kwashe sati daya a gida yana jinyar jikin shi , zuwa yanzu ya warke rass duk ciwukan da ke jikin shi sun warke sai abin da baza a rasa ba,fuskar shi ma ta dawo normal kamar bai taba samun wani matsala a wurin ba, baya fita ko ina daga gida sai masallaci, abincima mai gadi yake aika ya siyo mushi.


A gefe guda kuma ya daura damaran yaki da zuciyar shi domin ya cire tunanin Asmah a zuciyar shi , ya tabbata ya rasa ta har a bada, tunda idan lissafin shi daidai ne yau saura wata daya cif ta zama mallakin wanin shi,






Sai dai kuma ko ɗigo bai ragu daga soyayyar da yakema Asmah ba, saima abinda yayi gaba , ba karamin kokawa yakeyi da zuciyar shi ba dan ganin ya yakice ta daga zuciyar shi amma ina,yanzu ta kaiga har gizo take mishi idan yana zaune a daki, shi karan kanshi abin har mamaki da tsoro yake bashi , hotunan ta kuwa yanzu sune komai na wayar shi ko ina ka bude a wayar shi hoton ta ne, hatta password din wayar shi yanzu husnah ne,


Ganin yana azabtar da kanshi a banza yasa ya yanke shawaran da yake ganin shine daidai a gareshi, aikawa yayi mai gadi ya siyo mai sim card na mtn har guda biyu, saka sim din guda ɗaya yayi ya buɗe WhatsApp dashi, da suna M,M ma'an mahaukacin masoyinki, lambarta da take WhatsApp dashi ya dauka , ya yi saving a cikin sabon sim din, ya kunna data, nan take kuwa account dinta yayi applying a wayar shi, shiga yayi ya mata sallama, bata online ,dan haka ya sauka , bini bini ya duba yaga kota hau online amma shiru , har washe gari, sai kusan yamma ta hau online , tana cikin duba message taga message d'in Aslam, bata son number ba, shiga tayi ta duba taga sunan M,M , daurewa tayi ta amsa sallaman, lokacin kuwa yana online don duk bayan minti minti yake kunna data ko zata mai reply, kamar jiya yakeyi, ya shiga jero mata gaisuwa da bangajiya, sannan ya gabatar da kanshi a matsayin yar class dins ce ,a wani group na yan department dinsu ta dauki numberta, jin haka kuma macece ba namiji ba yasa ta saki jiki da shi suka dinga fira , daga karshe har exchanging hotuna sukayi, ya lalubo hotan wata ma,aikaciya a kamfanin su data nace tana sonshi take turo mai hotuna ya tura ma Asmah a mastayin nashi.


Ba karamin dadi wannan lamari yama Aslam ba, har voice takeyi jefi jefi in suna hira, shi kuma bai taba yin voice ba , itakuma bata taba kowa ana iya yin haka ba, don haka tunanin ta bai taba kawowa wai Aslam bane.






A kwana a tashi ba wuya yau saura sati hudu cif bikin su Asmah, ta kowani bangare shirye shirye akeyi ba kama hannun yaro, kowa ka gani a gidan yana cikin shirye shirye ne baga iyayen su ba baga amaren ba, baga angwayen ba, shirye shirye akeyi kamar ba'a tabayin biki a gidan ba , yoo kukuwa amare uku rerass angwaye biyu, don har zuwa lokacin maganar batool da bash bai daidaita ba , a bangaren diraman su ko sai abinda ya karu, har takai da iyaye maza ma sunsan da wannan yar tsaman dake tsakanin su, Abu dai sai gaba gaba yake yi.




Yau da ta kama ranar laraba alhaji baba ya kira daddy da Abba don yaji shirye shiryen me suke yi don shima yasan ta inda zai fara nashi shirin, dan jin wannan bikin yake a ranshi kamar bai taba aurad da ɗa ko jika ba.




Daddy yace "mun gama magana da mummy su zan bada kuɗi aje Dubai ayi musu siyayyar kayan furnitures da kuma kayan kitchen ,da dai sauran duk wani tarkace da ya kamata a sai musu, na bata na gaba daya su hudun ne dukda ita batula har yanzu naga bata fitar da tsayayye ba, amma dai na bada harda nata kasancewar bamusan yanda Allah zaiyi ba,"


Alhaji baba yace"masha Allah komai yayi Allah yayi albarka ya kara budi" gaba dayan su da amin suka amsa.




Alhaji baba ya kalli Abba yake"kai kuma fa yusufa me kake shiryawa".


Abban yace" dama nima munyi magana da maryam akan batun kayan ɗakin dana kitchen d'in amma tunda yaya ya rigani furtawa shike nan, ni zan dauki nauyin duk kayan da amaren zasuyi amfani dashi, na fitan biki dama na kwalliyan amarci, sai kuma batun abincin da za'a ci tun daga satin da aka shiga bukin har zuwa sanda baki zasu gama komawa na dauki nauyi, drinks ruwa nama, kifi , komai ma da za, a ci na dauki nauyi,"
Alhaji baba yace"alhamdulillahi kamai yayi Allah ya muku albarka, to aikun gama kwashe duk manyan hidimomin , to ba damuwa nima baza a barni a baya ba , zan saiwa kowaccen su sabuwar mota , na kuma bata kudi million ɗaya, ta rike a hannunta wacce zatayi sana'a sai taja jari koya kuka gani, lefe dama ko wani ango mun basu dama suje hu hado abinsu da gumin su haka ma sadaki kowannen su ya Ciro daga aljihunshi, gurin zama dama kowannensu ya gama gininsa,me kukace, "


Daddy ne yace"komai yayi alhaji Allah yasaka da alkhairi ya kara girma" shima Abba godiya ya shiga kwararowa wa tare da addu'an Allah ya kara nisan kwana.




Alhaji baba yace"magana ta biyu da yasa na kiraku akan batula ne, har yanzu bata gabatar mana da kowa ba, kuma gashi yau biki saura sati hudu, idan muna da yawan rai, to karku manta dama nace duk wacce bata da tsayayye ni zan zabar mata miji nagari, a kwai wani jikana na wurin abokina alhaji hudu, mai rasuwa Mahmud nasan kunsan yaron , ya gama karatun shi na sojoji, yanzu haka soja ne me mukamin captain, to dashi zan hada ta saurayine baida mata, to amma kuma hajiya ta sameni da wani magana wai tana ganin kamar yaron nan bashiru kamar soyyaya sukeyi da batulan, to nidai nace mata anya kuwa don inda soyyaya sukeyi yanaji anata shirye shiryen aurad da yan,uwanta dole zan yi wani yunkuri shima, to tunda kukaga haka kila zato ne kawai mukeyi, amma duk da haka zankirasu anjima shida batulàn naji ta bakinsu,".


Daddy yace"gaskiya ne nima ina zagin kamar akwai wani Abu a tsakanin su duba da yanayin yadda suke mu'ala a ƴan kwanakin nan, to dana samu mummyn su da maganar tace min ba soyyaya sukayi yi hasalima gani takeyi kamar babu jituwa a tsakanin su."


Alhaji baba yace"koma dai menene yau zan kirasu naji ta bakin su, don kar mu shiga hakkin su , koya kuka gani"


Nan take daddy da Abba sukayi na'am da shawaran alhaji baba, haka suka ci gaba da tattaune muhimman maganganu kafin sukayi sallama da shi suka wuce,




A bangaren Dr bashir kam yana cikin tsaka mai wuya , shi yanzu damuwar shi daya ta yaya zaiyi ya furta wa batool soyyaya, yasan a halin yanzu idan ya furta mata so baza ta saurareshi, shi kuma yana tsoran tace bata sonsa dan bazai iya jurewa ba, kuma bayaso ayi bikin nan ace banda su a ciki, imba haka ba da ya bata lokaci , har zuwa lokacin da itama zata kware mai, to amma bashi da ishashshen lokaci, dan haka ya yanke shawaran , kawai zai turo iyayen shi ne yace ita tace ya turo su , inyaso sai ya toshe kunnen shi daga masifar ta wuyar ta dai a daura idan ta shiga hannun shi zai ladaftar da itane.




Yana tsaka da wannan sake saken ne kira ya shigo wayar shi daga Amir wai alhaji baba na neman shi yau da daddare, sauke ajiyar zuciya yayi a ranshi yana fatan abinda yayi hasashe ya tabbata,




Da daddare bayan ya idar da sallan isha'i yayi wanka ya fesa adon shi kamar yadda ya saba idan zaije tsonaka nan fada, daukar key din motar shi yayi ya fice daga gidan su zuwa gidan alhaji baba,




Daidai wannan lokacin batool na hango zaune a gaban alhaji baba, kallonta yayi yace"batula abinda yasa na kira ki dama naga har yanzu baki gabatar da naki manemin ba kuma gashi naga yau har saura sati hudu biki, ina fatan baki manta da magana na ba na cewa duk wacce bata fitar da miji ba zuwa lokacin dana baku ni zan zabar mata miji da kaina".


Gaban batool ne yayi wani irin faduwa nan take ta shiga haɗa zufa, ita dai a halin yanzu bata da Wanda zata gabatar a matsayin mijin da zata aura , don ko saurayi bata dashi, ita yanzu babban damuwar ta batasan Wanda alhaji baba zai zabar mata a mastayin miji ba , kilama daya daga cikin almajiran wannan abokin nashine alhaji Mallam.




Wani zuciyar ne ta ce mata ya bashir fa, take kuma wata zuciyar tace Allah ya kiyaye ki da auren wannan dan banzan mutumin, wata zuciyar kuma tace, to aiko gara ya bashir d'in akan almajiran alhaji Mallam dan ko ba komai shi dan gayu ne kuma kyakkyawan gaske, wata zuciyar kuma tace kina hauka ne batool idan ke kina iya auren shi to shiya gaya miki yana sonki ne,haka tata saƙe saƙe ta saka wancen ta kwance wancen.


Alhaji baba ganin shirunta yayi yawa yasa yayi gyran murya tare da cewa "ke nake saurare fa batula,".




Dagowa tayi ta kalle shi bayan ta hadiye wani busashen miyau tace"ni bani da wani zabin kaina a halin yanzu, dama dai za'a kara mini lokaci ne zuwa gaba kadan" alhaji baba "yace babu wani lokacin da za'a kara miki nasan kinsan halina sarai bana magana BIYU, yanzu tambayan da zan miki ki bani amsa tsakanin ki da Allah idan kika boye wani Abu kin cuci kanki, menene tsakanin ki ba Dr bashir?" .




Sautin bugun zuciyarta ne ya kara karfi jin an ambaci sunan shi, itako menene tsakanin ta da Dr bashir banda rashin mutunci, ita ko'a fuska bai taba nuna mata alamar yana sonta ba,amma tanaji a zuciyarta da ya furta ba shakka zata iya auren shi, don tana jinshi sosai a ranta,




Cikin kasalalliyar murya tace"babu komai a tsakanin mu , daya danganci soyyaya" murmushi alhaji baba yayi yace "to masha Allah , tashi kije daga nan zuwa ko wani lokaci zaki iya tsinkayar kirana"




Dr bash kam yana isowa part d'in mummy ya fara nufa da nufin ya ganta kafin yaje amsa kiran Alhaji baba, shiga yayi main parlour ba kowa sai katon TV dake kunne yanata aiki , neman guri yayi ya zauna, ko wani daga cikin su zai sakko.




Cikin harde hanya ta fito daga part d'in alhaji baba, innalillahi wainnailaihi rajiun me tayi kenan me hakan ke nufi hakan na nufin za'ayi sarakar ta kenan, ga almajiran alhaji Mallam , tabdijam Ashe akwai kallon rashin M a gidan nan don wlh baza ta yarda ayi sarakarta ba saikace wata kosai,




A haka ta shiga parlourn hankalin ta duk a tashe, jin motsin kofa yasa. Dr bash dake zaune a falon sauri dagowa ya kalli bakin kofar, aikuwa caraf idanun shi ya sauka akanta, wani dadi ne ya lullubeshi shi , take ya saki wani kayataccen murmushi , saidai kwata kwata ita bata ganshi ba, ganin haka yasa , tana zuwa daidai shi zata giftashi ya saka mata kafa.




Tuntube tayi da kafar shi hakan yasa tayi baya zata faɗi, harta rintse idonta don ta sadaƙar ta fadi ta gama, saidai jinta a jikin mutum yasaka ta saurin bude idanun ta, irin rikon nan ya mata kamar suna rawan indiya , karaf idanuwansu ya sarke Dana juna , kallon kuda suka shiga yiwa juna na some seconds.




Hannayenta ta mika ta tunkude shi , ba shiri ya saketa, balla mai harara tayi ta buga tsaki, ita yau bata jin yin surutu don tana da tunanin yi a gabanta, raba shi tayi ta wuce shi, cikin salon takunta na yanga juyawa yayi yana kallonta har ta kama kafar bene zata haye, ta tsinci muryar shi yana cewa" mutum mummuna sai shegen yanga haka, ke ba kyauba amma iyayinki yafi karfin ki, tsabar muni ko saurayi baki dashi duk yan uwanki ankai kudin aurensu banda ke, kibani dama kawai na taimake ki na rufa miki asiri na lallaɓa nace ma su daddy kince kina sona, nayi maneji dake don barinki haka a gida a aurad da yan uwanki, zaki zama abin tausayi ne,".




Wani irin juyowa tayi tana kankance idanu cike da masifa, lip dinta har rawa yakeyi , tsabagen an tabo ta ,tace"Allah ubangiji ka tsare ni,"tuf ta tofar da yawu gefe, kafi ta tako gabanshi cikin wani irin cat walk, dan nisa dashi kadan ta tsaya ta kalle shi a yatsine ta daga yastanta tana nuna kanta daga sama har kasa tace " kalleni frm up to down , wlh nafi karfin ayi maneji dani, kuma da kake batun kyau nasan ko gasar kyau aka saka tsakanin mu kafin mutum dari su jefe maka kuri'a mutum billion sun jefamin, aure ne dai bazan aure ka ba, baka daga cikin tsarin irin mazajen da suke burgeni ka gane ai" ta karashe tare da daga mai gira da murza hannunta ya bada sauti Tass.




Tunda ta fara magana yake binta da wani irin kallon kauna, dan bakinta yake bi da kallon sha'awa ji yake yi kamar ya kamo ta ya shiga kissing dinta madly, har mafarki yakanyi jefi jefi gashinan yana tsotsan bakin ta.


Saida ta juya zata bar wajen ya dawo daga duniyar begen lips dinta, wani irin taku ta shigayi da gayya Wanda yafi na d'azu daukar hankalin shi, daga murya yayi yace"karfa kiyi tunanin sonki nakeyi taimakon ki zanyi kar azo ana kwatance dake a anguwa , wannan wadda tai kwantai dinnan to tunda kuma bakya so kin hutashsheni" ko juyowa batayi ba balle ta tanka shi ,saida ta kule wa ganin shi , sannan ya sauke ajiyar zuciya, wani kyakkyawan murmushi ne ya kufce mai tunawa da gadar zaran da yake shirin daura mata tabi takai, na turo iyayen shi yace injita,kwafa yayi yace yarinya zakiyi bayanine Allah dai yakai damo ga harawa.




Juyawa yayi ya fice daga part d'in zuwa na alhaji baba, yana nan a inda ya gama magana da batool bai kai ga tashi ba, bayan sun gaisa harda dan taba wasa na kaka da jika, alhaji baba ya kalle shi yace "abinda yasa na kiraka bashir tambayar ka nake so nayi tsakanin ka da Allah ka gayamin gaskiya, menene tsakanin ka da batula".




Wani irin farin ciki ne ya lullubeshi , hamdala ya shiga jerowa a zuciyar shi kafin yace" alhaji soyyaya muke yi, inason ta tana sona, amma taƙi bani dama na turo magabatana , nayi nayi taki amince min , wai ita bata da ra'ayin a hada bikinta dana kowa tafi son ayi bikinta ita kadai, wai na bari sai angama bikin yan uwanta saina fito, to dama nima gobe nake son na samu su Abba da zance".




Alhaji baba yace"kai madallah Abu yayi kyau tashi kaje Allah yama albarka gobe kacema alhaji usman ina son ganin shi".




Godiya bashir ya shiga zubawa kamar bakin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads