Showing 45001 words to 48000 words out of 201974 words
Chapter 16 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
ta inda zata bullo, yarinyar da tun gani na farko har yau ya kasa cireta a zuciyarshi daidai da minti daya,
Amsa mata sallaman yayi shigowa tayi cikin natsuwar ta, gabanshi ta nufa ta ajiye tiren hannunta , sannan ta koma baya ta nemi kujera ta zauna,
Sai sannan ta dago kai ta kalleshi, ji tayi gabanta ya yanke ya fadi, da sauri ta dake kai daga kallonshi, don yayi mata kwarjini sosai, gani takeyi kamar tasan fuskar shi amma kuma ta manta inda tasan shi,
Cikin siririyar muryarta tace "ina yini" taja bakin ta tayi shiru,
Tunda ta shigo yake binta da kallo sai yanzu ya tabbatar Ashe rannan ma kallon tsoro ya mata, yanzu ne yake qare mata kallo mai sunan kallo,
Cikin kulawa da maida dukkan hankalin shi gareta ya ̃amsa mata da" ina gajiya faɗeema, ya gida ya makaranta " ta amsa da lfy qlau,
Shiru sukayi dukkansu sai can ya katse shirun da cewa " nasan kin manta ni ko" dagowa tayi ta kara kallonsa a karo na biyu, still bata tunashi ba,
Murmushi yayi yace "dama nasan ni kadai nake kiɗa na da rawa na,"
A karo na biyu tace" kayi hakuri dan Allah ban gane kaba, amma kuma kamar na taba ganin fuskar ka a wani wajen"
Cikin jin ɗaɗi yace"well hakan ma na gode tunda kin tuna kamar kin sanni,naji ɗaɗi kuma nagode, amma kinga ni tun gani na dake na farko ko daidai da second daya ban qara manta ki a cikin zuciyata ba, nine abokin Abban hanifa, nan da muka hadu a gidan kwanaki kika kawo min ruwa "
Cikin mamaki ta dago tace "Ooh sai yanzu na gane ka, dan kayi hakuri ban gàne ka bane da farko, ya hanya ,ya iyalai".
Yace "lafiya qalau sunce ma na gaida ki"
Tace "aiko nagode ina amsawa,"
Dan shiru sukayi kowa da saƙesaƙen da yakeyi cikin ransa,
Can dai brr Adam ya katse shirun ta hanyar cewa"a gaskiya faɗeema wani magana ne mai muhimmanci ya kowa ni gareki, fatan zaki bani aron hankalinki, kuma ki saurareni da kunnen basira, a gaskiya tun ranar dana fara ganinki , kikayi awan gaba da tunani na , na koma gida na kasa samun natsuwa a zuciyata, kaunar ki tayimin kamun farat d'aya, bansamu kwanciyar hankali ba har saida na dangana da mahaifinki, yayi na'am dani kuma shine ya bani daman nazo gareki na nemi yardar ki da soyayyar ki, ina fatan zaki tausaya min ki karɓe ni da hannu bibbiyu a matsayin mijin aurenki "
Sunkuyar da kanta kasa tayi tunda ya fara magana , ta kasa ƙara dagowa ta kalle shi, wani bala'in kunyar shi ne ya lullbeta,
Kallanta yayi ganin bata da niyar cewa wani Abu yasa yaci gaba da cewa" nidai sunana Adamu Aliyu badegi , ni mutumin bidda ne kuma ƙabilar nufawa, nasan kinji hakan a muryata, ko?" ya qarqare maganar yana murmushi,
ƙarayin kasa tayi da kanta , ci gaba yayi da cewa,"inada matata ɗaya maryama, da yara hudu, ni lawyane me zaman kanshi, bayan wadannan ki faɗi duk wani abin da kike son sani game dani sai na faɗa miki,"
Shiru dai ba amsa, kara zama yayi kusan na 20 minute yana zayyano mata kalaman soyyaya, Wanda shi karan kanshi baisan ta yaya akayi suke fitowa daga bakin shi ba,
Ganin dai bazata ce komai ba yasa yace mata zai koma amma taje tayi shawara da zuciyar ta, zai kirata a waya anjima inya isa gida, amma dan Allah ta yanke shawara mai kyau,
Da haka sukayi sallama bayan ya ajiye mata yan dubu dubu guda a shirin, yace ta saka kati.
Saida taji tashin motarshi , sannan ta iya fitowa daga falon, cikin sauri ta qarasa sashen su,
Dr Bash har wajen aikin Amir yaje ya ɗauke shi , suka nufi gidan Aslam har lokacin zee bata dawoba, shiga cikin gidan sukayi, ba kowa falon upstairs suka haura duka sauran ɗakunan a buɗe suke harda na zee,
ɗaki dayan da suka gani a rufe suka shiga knocking, shiru ba amsa,
Daidai wannan lokacin Aslam ya gama sheqa aman shi a nan kan gadon don zuwa yanzu ko tashi matuq'ƙar wuya yake bashi, baga ɗaya, ya fice a hayyacinsa damuwa taima zuciyarshi mugun kamu,
Jin ana knocking yasa ya kasa kunne sosai , muryar Amir dana Dr bash yaji suna sallama , mƙewa yayi daƙer yana layi yana ganin jiri ya nufi ƙofar ya bude musu , yana bude ƙofar ya fada jikin Amir daya fi kusa dashi,
Cikin gigicewa da tashin hankali suka shiga jijjigashi amma ina, daƙer yake bude ido yana lumshewa , kallon Dr bash amir yayi cikin tashin hankali yace " Dr pls do something" bash yace "muje asibiti dashi kawai shi zaifi kaga nan ba wani kayan aiki"
Cikin abinda baifi minti ashirin ba suka isa asibitin da Dr bash ke aiki, ganin su tare da Dr yasa cikin gaggawa aka kawo keken tura marasa lafiya aka shiga da shi ciki, direct emergency akayi dashi
Dr bash ne ya shiga duba shi tare da wasu abokan aikin shi har guda biyu,
Amir kuma yaje bude mai file na asibitin,
Kusan awa ɗaya suka kwashe akan shi kafin su gano taka maiman meke damun sa , ruwa aka daura mai, da alluran bacci masu karfi,
Lokacin da su Dr bash suka fito Amir tuni har ya kira gida ya faɗa mami, da Abba da hajiya mama tuni har sun iso,
Mami ne ta nufi Dr bash tace "Dr bashir ya ake ciki ina my son a wani hali yake ciki"
Dr bash yace "da sauƙi mami mun samu mun shawo kan matsalar, yanzu yana bacci, mum mishi alluran bacci , zaidan jima yana bacci kafin ya farka, ta haka ne zuciyarshi da kwakwalwarshi zasu huta"
Daidai lokacin daddy da mummy da Kamal suka qaraso, daddy yace " bashir meke damun shi ". Dr bash yace "daddy muje office sai na maka bayani"
Office suka rankaya kusan gaba dayan su, zama wasu sukayi wasu na tsaye, daukar file dinshi yayi yayi rubuce rubuce,
Kallon su yayi cike da tausayawa ganin dukkansu yanda suka shiga damuwa,
Yace, " a gaskiya akwai matsala Aslam ya ɗauki damuwa ya saka a zuciyarshi, kuma baya barin kwakwalwar shi ya huta, saboda tunani, ga rashin bacci, ga rashin cin abinci, ulcer shi yayi mummunan tashi, sannan tunanin da damuwar da yasa a rai, yana barazana ga zuciyarshi, idan , badan Allah ya taimaka ba, da yaci gaba da zama a haka tsawon kwana uku komai ma zai iya faruwa dashi, ciki harda bugawar zuciyarshi, kokuma mu rasa shi ma gaba daya"
Tsit dakin yayi kowa da irin abin da yake saqawa a ransa dukkansu basa buqatar sanin abinda ya jefe shi a cikin wannan halin , saboda Abu ne da yake bayyane kowa ya riga ya sani,
Mami ce ta fashe da kuka tana maimaita innalillahi wainnailaihi rajun,mummy ma duk iya dauriyarta da kawaicinta saida ta share hawaye a fakaice,
Dr bash ne ya shiga kwantar musu da hankali matsayin shi na likita , duk da shima cikin tsananin damuwa yake,
Saida komai ya natsa mami ke tambayar ina zainab, nan Amir ya sanar musu abinda megadi ya fada musu na cewa ta fita tun safe gashi har dare bata dawoba,
Daidai lokacin zee na tare da beebalo, fitowa su kenan daga labour kutigi, ana wani biki , ba dangin iya bana , baba beebalo ta jata suka tafi, zama sukayi suma cikin yan biki, suka saje,dangin ango zasu zata dangin amarya ne suma dangin amarya kuma su zata dangin ango ne su,
Haka suka shiga fili suka sha rawa har sunfi wasu dangin ma'auratan zaqewa,
Bayan sun fito ne zee na jansu a mota zata sauke beebalo a gida kafin itama ta koma gida dan dare yayi, karfe takwas ake nema,
Beebalo ta kalli zee tace" kawata kince min kina da aure amma baki taba nunamin mijnki ba koda a hoto ne"dariya zee tayi tace "Abu mai sauki ". Dalleliyar wayarta ta dauka ta nemo hotunan Aslam ta miqama beebalo,
Beebalo na gani ta zazzaro Ido waje a zucyarta ta furata bantan uban can, tabdijan akwai bura'uba kenan dama wannan tsalelen saurayin ne mijin zee, tabdijan wannan shine irin mijin da ta dade tana mafarkin samu, Wanda rashin samun irin shi ya hanata zaman aure, lallai da sake, dole zatasan duk ƙulleƙullen da zatayi ta kara zee ta samu ta maye gurbinta, a gidan Aslam.
Ganin tayi shiru yasa zee tace "yadai naga kinyi shiru ko kinsan shi" cikin murmushin yaƙe tace "wlh ban taba ganin shi ba sai yau gaskiya kawata kinyi dace da miji kyakkyawan gaske ga kudi, masha Allah irin mijin novel muma Allah yasa mu a danshin ku"
Cikin jin dadi zee tace"amin amin kawata" nan ta shiga gaya mata wasu sirrikan Aslam' ita kuma beebalo sai bugun cikin ta takeyi taba nadar abin da zata Nada, kafin su rabo saida ta gama sanin abin da take Neman sani fak akan Aslam, don beebalo akwai shegen wayau, ita kina zee ba wayau sa iya hege😁
Karfe Tara daidai ta iso gida , tun kan tayi parking me gadi ya tare da mummunan labari, nan take hankalinta ya tashi, don duk iya shegenta tana matuqar kaunar Aslam,
Take ta ɗauki hanyar zuwa hospital.......
💖more comment more typing💖
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fi sabilillah🙏
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book ɗin ca duk wscce ta rasa mahaifiya, allah kajiƙan iyayen mu }
page 61 & 62
Koda zee ta isa asibitin duk su mummy sun riga sun wuce sai mami, kawai aka bari da zata kwana da shi,
Da tambaya ta gane ɗakin da aka kwantar dashi , tana shiga ta tarad da mummy zaune a kujera dake gefen gadon , carbi ne hannunta tana ja , sanye take da hijab dinta da alama ma salla tayi don ga pray mat nan a shimfide a ɗakin,
Guri ta samu bakin gadon ta zauna ta miqa hannunta tana shafa fuskar Aslam, gani tayi duk ya koma mata wani iri dan kwana biyu nan da data ganshi, saida ta gama tabe tabenta,
Sannan ta dago ta kalli mami tace"sannu ma "
Mami da mamakin ganin wanga irin rashin kunya na zee ya kasheta , tace " sannu dai aike zanwa sannu"
Cikin ko inkula zee ta ɗauke kanta daga kallon mummy ta mayar kan Aslam,
Nan dakin ya dauki shiru ganin dare yayi yasa mami miƙewa taje ta kwanta , a daya gadon dake ɗakin ta juya musu baya, sai dai tana yi taba farkawa ta duba ko Aslam ya farka don har lokacin bacci yakeyi, bai farka ba,
Zee kam akan kujera ta kwana rike da hannun Aslam, a haka har gari ya waye, har lokacin Aslam bai farka ba,
A can family hause kuwa mummy ne ta shirya breakfast , taba batool tace maza taje bello ya kaita asibiti ta kai musu , daga nan taga jikin Aslam ɗin,
Har ɗakin wata nurse ta kaita bayan tayi tambaya , shiga tayi ta tarad da mami zaune kan bakin gado, zee kuma akan kujera, ta tasa fuskar aslam a gaba tana kallo,
Gaida mami tayi tana tanbayar ta ya mai jikin mami tace"da sauƙi batool ya gida , saidai har yanzu bai farka ba," batool tace "subhanallahi, to Allah yasa dai lafiya " mami tace " insha Allah lafiya alluran da suka mai ne yana da ƙarfi sosai"
Juyowa batool tayi ta kalli zee tace"ina kwana " saida ta kare mata kallon banza ganin kamannin ta da Aslam haka ya tabbatar mata kanwar shi ce, sannan ta amsa da " lafiya "a yatsine,
Batool a kan labbanta ta furta kan uba! Hada ido sukayi da mami , mami ta girgiza mata kai alamar karta tanka , ƙwafa , tayi amma a zuciyarta ta qudiri aniyar , daga yau bata ƙara gaida zee,in anyi duniya dan ma'aiki,
Kwandon abincin ta jawo tace mami ga abinci bari nayi serving ɗinki , hada ma mami tea tayi ta zuba mata , arish da kwai ga kuma bread da butter,
Gdy mami tayi ta amsa ta fara ci, zee na zaune duk kamshi ya gama cika mata ciki, tana jira batool ta gama zuba ma mami ta zubo mata,don yunwa takeji, amma ga mamakin ta sai taga batool ta rufe kuloli ta koma ta zauna ,
Mami na lura da ita sarai ta gane abinda take jira, amma taqi saka musu baki , gara abarta da batool ɗin don dama ance , Karen bama shike maganin zoman bana,
Batool da mami dan fira suka shiga yi jefi jefi, can kuma kaman ance mami ta waiga ta hango Aslam na motsi da idanu alamar zai farka,
Da sauri mami ta miqe tsaye tace " alhamdulillahi batool ya farka" itama zee sai lokacin ta lura dan kallon fuskan shi kawai take amma hankalin ta gaba daya yana kan abincin dake kula a rufe,
Mami tace "batool yi sauri ki kira Dr bashir " da sauri batool ta fice tambayar wata cleaner tayi office din Dr bashir , nuna mata layin da office's din doctoci yake,tace tabi zata ga office din da aka rubuta Dr bashir ta shiga nan ne,
Da sauri ta qarasa ta duba cikin sa'a kuwa ba ko wani patient don haka ta shiga,
Har ta bude baki zata fara gaishe , shi idanun su ya sarqe dana juna cikin gwalalo idanu cike da mamakin ganin mutumin ta, a mastayin Dr bashir,
Shi kuma wani irin farin ciki ne ya lullubeshi , nan take yaji wani nishadi na shigar shi na ganin ta ,jiya daidai da second daya tunanin ta bai barshi ya huta ba, duk kuwa da halin da Aslam ke ciki bai hana shi kwana tunanin ta ba,
Daure fuska yayi kamar bai taba ganin ta ba tunawa da yayi wacece batool , yanzu zata zube mai fitsara
Cikin dakewa yace" madam ya zaki shigo min office haka ba excuse , saikace zaki shiga toilet, ai ko toilet ne naga sai mutum yayi addu'a kafin ya shiga"
Saida ta fakaici idanshi ta watsa mai harara ,sannan tace " patient dinka Aslam ya farka"
Duk harare hararen da takeyi yana kallonta ta gefen Ido amma jin abin da ta faɗa , na cewa Aslam ya farka yasa ya miqe da sauri , yana tattara kayan aikin shi ,yayi waje ,rufamai baya tayi,
Koda suka isa dakin ya buɗe Ido tangararas , yana kallon kowa, fita waje Dr bash yace suyi, sannan ya shiga duba shi,
Alhamdulillahi abinda ake buqata komai ya daidaita bugun zuciyar shi ya dawo normal kwakwalwarta shi ya samu Hutun da ake son ya samu, saidai rashin qarfin jiki da kuma ulcer Wanda waɗannan dama sai a hankali zasu daidai ta,
Nurse Dr bash ya aikata yace tace ma mami a haɗa ma Aslam tea , yasha , don cikin shi ya warware kafin yaci abinci yasha magani,
Mami cewa tayi batool taje ta haɗa, don shakkar cewa zee taje tayi takeyi, ganin tun sannun da ya haɗa su jiya har yanzu wani mahimmin magana bai sake haɗasu ba,
Ɗakin ta shiga ta haɗa mai tea mai kauri yana turiri , ta miƙa ma Dr bash Wanda shi zai bashi , cikin rashin sani wuri karban shayin hannun sun ya tabina juna ,
Da sauri ta saki kofin shayin ta shiga yarfe hannu kamar wacce wuta ya lasar ma hannu kokuma wutar lantarki yaja,
Allah ya kiyaye Dr bash ya riqe kofin da sauri da ba abin da zai hana shayin zubewa,
Murmushi Dr bash yayi a zuciyarshi yace lallai ma yarinyar nan , dan hannu na ya taba nata take wannan yarfe yarfen,? Hmmmm zakiyi bayani ne yarinya,
A fili kuma ya watsa mata harara yace" waike me yasa bakiyin Abu a hankali ne for god sake"
Murguda baki tayi sannan ta fice ɗaga dakin,
Haka Aslam ya wuni a asibiti cikin kulawa , kan dare jiki yayi sauqi alhamdulillahi , don sosai mami take takura mai yana cin abinci, yana shan magani, kan kwabo sai gashi har yana zama da kanshi,
Dangi ana ta zuwa dubashi , alhaji baba dai baizo ba, daddy ma jin ya farka kuma jiki da sauƙi yasa bai koma ba ,don har yanzu bai huce da rashin kunyar da yama mahifinsa rannan ba, mummy ma kawaici ya hanata komawa,
Zee kam ganin har sha biyu ba Wanda ya mata tayin abinci yasa ta fita wajen asibitin ta siya abinci taci, da rana ma koda aka mata tayi ƙinci tayi , wai ita tayi fushi, yanda bata damuwa da lamarin su ,haka ba Wanda ya damu da taci ko bata ciba,
Ƴan matan mummy basu samu zuwa asibitin ba sai dare ya kamal ya kwashe su , suka tafi,
suna shiga suka tarad da ya Amir da Dr bash a ɗakin sai kuma zee, dake gefe tana charting,
Jin motsin shigoya yasa Aslam dago kai yakai duban shi ga ,ƙofa akan fuskarta idanun shi suka sauka, itama kuma hakan ne ta kasance a gareta,
Da sauri suka dauke idanuwansu daga kan juna, tsohon miki ne ya tashi, don ji yayi zuciyar shi na bugawa da ƙarfi fat fat fat,
Qrasowa sukayi cikin dakin , gaidashi suka shiga yi tare da tambayar sa ya jiki,cikin jimla ya amsa musu da,"da sauƙi" hannu kamal ya miƙama su Amir da bash suka gaisa,
Zahra CE ta dubi gefen zee tace "ina wuni anty zee " amira da Asmah ma suka gaishe ta , batool kam dauke kai tayi kamar bata ganta ba ta juya fuskan ta gefe tana tabe baki,
Tun shigowar su sai lokacin ta dago kai daga charting dinta don ganin su wanene ma , idanunta ne ya sauka akan Asmah , aiko ji tayi zuciyarta tayi baƙiƙirin kishi ya motsa , wani mugun kallon sama da qasa ta watsa musu kafin taja wani mugun tsakin da saida ya jowa hankalin kowa na dakin kanta,
Mursisi yayi ta dauke kallonta daga garesu taci gaba da charting dinta,
Jiki ba kwari suka nemi guri suka zazzauna , Amir ne ya tashi ya fita yace musu yana zuwa, can harabar asibiti yaje