Header Ads
Showing 186001 words to 189000 words out of 201974 words

Chapter 63 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1737

Ads at the middle of Article

kuwa ita ce zee, duk lalacewar Dad mahaifin ta ne, Kuma su iyaye komai munin halin su ba'a kin su tana son uban ta sosai kamar yadda shima yake son ta, idan ya mishi wani abu makamancin duka ko zagi tabbas idan ta farka baza ta ji daɗi ba, ga kuma little da sauran ƴaƴan da zasu haifa nan gaba tare da ita, idan har ya duki Dad zai zama abin gori ne a gare su kuma ma ai shi yana da ilmi idan ya biye mishi sun zama ɗaya kenan.


Da'ker ta samu ta lallaba ta lalubi jikin kujera ta dafa ta mike, tana jin ta tsaye kan ƙafafun ta take duk abin da ke faruwa ya shiga dawo mata da gudu ta nufi waje tana kwala kiran anty zee hango sun da tayi yasa ta nufo su, ganin zee kwance a hannun Aslam bata numfashi yasa ta sauri duƙewa cikin tashin hankalin da tsinkewar zuciya ta shiga jijjjgata tana kiran sunan ta, shiru babu ko alamar zata motsa, dago hannun ta da zata yi da nufin ta tashi taje ta kawo ruwa a yayyafa mata sai ganin hannun tayi caɓal da jini, hankalin ta ne ya kara tashi cikin kuka tace "innalillahi wainnailaihi rajiun,shike nan ya Aslam ya kashe mana ita." Sai lokacin ya lura da hannun Asmah shima hankalin shi ba karamin tashi yayi ba yunkurawa yayi ya miƙe da ita sai ga jina faca faca ya na bin jikin ta, a guje ya nufi mota da ita ya buɗe bayan ya kwantar da ita, itama Asmah rufa mai baya tayi ta buɗe gefen me zaman banza ta shi a haukace ya figi motar ya fice daga gidan, sunzo dai dai fita kwanar gidan wanda zai hau da su babban titi suka ga cincirundon mutanen a tsatstsaye tun daga nisa ya din ga danna horn, ganin yadda yake mugun gudu yana danna horn yasa tun kofin su karaso wajen mutanen suka dare suka basu hanya, bai tsaya bi ko tambayar meke faruwa ba ya harba kan babban titi ya dauki hanyar wani babban private hospital, yana shiga aka karbe ta akayi emergency room da ita, likitoci kusan uku suka rufa akan ta domin ceto rayuwar ta abin ka da asibitin masu kumbar susa


A fusace Dad ya bar gidan Aslam da nufin ya nufi police headquarter ya debo ƴan sanda ya biya manyan su kudi dan suzo suci mutumin Aslam sumai dukan tsiya sannu su tafi dashi su kulle shi kuma ya dauki yar shi ya tafi da ita, yana tafe yana sambatu yana zage zage kamar wani taɓɓaɓe gaba daya hankalin shi baya jikin shi burin shi kawai ya ganshi a police station, yazo tsalleke titin domin ya koma hannu da zai samu taxi cikin rashin sani wani tsohon Sharon ya shararo da gudu birke ya tsinke mai tun daga nesa yake ta danna ma Dad horn amma ina baiji ba hankalin shi baya jikin shi idanunshi sun rufe kunnuwan shi sun ɗoɗe tsabar bala'in dake cin zuciyar, aikuwa cikin hukuncin ubangiji mai Sharon ɗinnan yayi sama da Dad kuma ganin ba kowa abin ka da unguwan yan gayu yasa mai Sharon dinnan fece wa ya bar Dad nan kwance rai a hannun Allah, me gadin dake farkon Layin ne ya fito da nufin yin wani uzirin sai ganin mutum yayi kwance cikin jini shine fa yayi kururuwa mutane suka dan fiffito yawancin su ma masu gadin gidajen unguwan ne, koda suka fiffito tsayawa suka yinyi cirko cirko ana shawara an rasa wa zai taimaka mai zuwa asibiti, suna cikin wannan tsayuwar ne motar Aslam tazo ta wuce su da mugun gudu, kasancewar cikin tashin hankali yake yasa bai kula da abin da ke faruwa ba, wani he ya bada shawara a shiga gidajen dake kusa a gaya musu suzo su duba ko dan uwan su ne moto ya buge dan ga dukkan alamu daga cikin wannan unguwar ya fito, da wannan shawaran suka fara bi gidanjen da ke kusa cikin haka ne suka zo gidan Aslam, me gadi dake nan duk cikin shi ya duri ruwa ya kasa zaune ya kasa tsaye don duk abin da ke faruwa akan idanun shi ne abin da yafi daga mai hankalin shine yadda yaga Aslam ya figi mota a tsiya ce , ya tarbi mutum biyu da suka yi sallama a kofar gidan , jin abin da ke tafe dasu kuwa baiyi kasa a gwuiwa ba yace suje ya gani duk da ko kusa bai kawo tunanin Dad bane yama fi ba cewa to ko Aslam ne ya buge mutumin tunda yaga ba cikin hayyacin shi ya figi motar ba. Ko da suka je kawai sai yaga mutum da ya fita a gidan su mintuna ƙalilin da suka wuce mutumin da ya mare shi yanzu yanzu ba tare da ya mishi komai ba, "Allahu Akbar." ya furta lallai dan Adam ba'a bakin komai yake ba yanzu wannan bawan Allah idan da yasan zai shiga cikin wannan mawuayacin halin nan da yan mintuna me zai kai shi aikata abin daya gama aika ta wa yanzu yanzu. Zuciyar musulumci take yaji tausayin Dad ya kama shi, dan kuwa duk wani mai imana idan yaga Dad dole ya tausaya mishi bai yi kasa a gwuiwa ba wurin cewa bai san shi b, amma ya bada shawaran a taro napep akai shi asibiti in yaso su likitocin saji dashi, take fa yawa suka amince da zance, ya samo me napep akayi general hospital da Dad kafafuwa na lilo alama


Likitoci sun sha matukar fama sosai kafin su samu su tsaida jinin daya barke mata da'ker suka ceto rayuwar ta, Aslam da Asmah kam sunan nan a kofar emergency room din Asmah sai kuka take yi Aslam yayi rarrashi har ya gaji ya kyale ta, shi karan kanshi karfin hali kawai yake yi, dan ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai safa da marwa yake yi, lokacin da daya daga cikin likitocin dake duƙufe akan zee ya fito har rice rige sukeyi da Asmah wajen tambayar shi halin da take ciki, be basu amsa anan ba sai cewa da yayi su biyo shi office, bayan sun zauna file din ta ya bude ya shiga dan rubuce rubuce, Asmah kam ta kosa taji wani hali zee ke ciki hakan yasa tace "Dr pls wani hali take cike meya samu yar uwata." kallon su yayi tare da gyara zaman siririn farin glass din dake idanun shi yace "patient din da kuka kawo mana wato zainab Abdus-salam, ta samu miscarriage sakamokon wani tashin hankali da firgici data shiga na lokaci daya." Kamar saukar aradu haka Aslam yaji saukar maganar Dr a zuciyar shi Asmah kam tuni ta rushe da wani irin kuka kwace ce mata akayi zee din ta rasu, Aslam kam innalillahi wainnailaihi rajiun ya shiga furtawa a zuciyar shi, Dr ne y shiga rarrashin ta yana kwantar mata da hankali, dan Aslam bashi da karfin halin iya rarrashin ta a halin da yake ciki, ji yayi zuciyar ta kara daukar zafi,rintse idanu yayi yana jin tsanar Dad na kara baibaiye lungu da sako na zuciya shi, alkawari ya dauka tare da lasar takobin wannan karon bazai bari mahaifin zee ya shashi silla ba shari'a zai yi dashi bakin rai bakin fama daga nan har kotun koli na duniya sai anbi mishi hakkin shi akan Dad koda duk abin da ya mallaka zasu kare, jajayen idanu shi bude akan Dr cikin murya mai dauke da tsananin bacin rai yace "Dr wani hali matata take." Shi karan kanshi Dr abin ya bashi mamaki amma ya dauka duk bakin cikin rasa cikin ne yasa yake mai magana a haka, cikin muryar rarrashi Dr yace " matar ka tana lafiya munyi duk abin da ya kama ta muyi, harta wankin ciki duka munyi mata, yanzu haka barci take yi allura muka mata nan da awa 4 zata farka, ku kwantar da hankalin ku, babu wani wani matsala zata farka lafiya insha Allah." Rubutu ya ɗanyi a jikin wani dan paper ya mika wa Aslam gashi wannan magunguna ne zaka siyo mata na jini sunfi yawa aciki wanda zata din ga sha ba sai mun mata Karin jini ba idan tasha wadannan magungunan amsa Aslam yayi suka yi ma Dr godiya sannan suka fito Asmah ta shiga dakin da aka kwantar da zee shi kuma ya tafi pharmacy dan siyo magunguna.


Bayan ya dawo ya samu Asmah zaune a kan kujera hannunta cikin na zee dake ta sharar barci, ajiyar zuciya ya sauke ganin ta dawo daga suman da tayi yanzu barci take sai lokacin tunanin kiran su mummy ya fado mai, take kuwa ya lalubi waya ya kira Mami, kan kace kwabo asibiti ya cika da yan uwa, sai bayan isha'e zee ta farka kuma alhmdllh jikin da sauki sai dai Dr yace bazai sallame ta ba sai zuwa gobe, Mami da Asmah ne suka kwana a Asibiti, shi kuma Aslam ya tafi gida a gurin mai gadi ya samu little har ma yayi barci abin shi cikin net a kan dan karamin gadon dake dakin mai gadi, me gadi kamar ya gaya mai halin da dad ke ciki sai kuma kawai ya share,


A cen general hospital kuwa bayan sun kai Dad asibiti, cikin gaggawa a kayi cikin emergency dashi aka bashi gado,wadan da suka kawo shi wucewa suka yi bayan sun sanar wa likitocin cewa tsintar shi suka yi yayi accident a bakin hanya da alama mota ce ta buge shi kuma mai motar ya gudu.jin haka yasa akayi banza dashi tun da babu wanda zai tsaya mishi, sai bayan isha'e daker dai aka samu wani likita mai dan tausayi ya kula shi, jikin shi aka duba cikin sa'a aka samu wayar shi, a kulle wayar take hakan yasa aka cire daya daga cikin sim uku dake wayar aka saka a wani wayar take lambobi guda uku suka bayyana. Daughter, wife, Brother, ganin, haka yasa suka San duk wadannan makusantan shi ne, wani je ya bada shawaran a kira Brother saboda shi namiji ne zaifi matan saurin fahimtar lamari, Alhaji Abdur-rahman na zaune a falon shi yana hutawa shida matar shi kira ya shigo wayar shi, sunan daya gani ya matukar bashi mamaki kwarai sanin irin bakin zuciya na kanin nashi yasan sarai a yadda suka yi rabuwan baran baran karya ne ya neme shi nan kusa sai dai idan shine ya gaji ya neme shi, ajiye mamakin shi a gefe yayi ya daga wayar, maimakon ya tsinkayi muryar ƙanin nashi kamar yadda ya sakankance zai ji sai ya tsinkayi muryar wannan Dr , a gurguje ya sanar dashi abin da ke faruwa da me wannan lambar Alhaji Abdur-rahman yasha mamakin jin cewa a Nigeria ne ƙanin nashi yayi hatsari har ake neman shi a general hospital, jiki a sanyaye ya amsa wa Dr da cewa gashi nan zuwa nan da 20 minutes, suna ajiye wayar Mom ya kira yake tambayar ta ina Dad nan take ce mashi rabon da shi tun jiya, take ya sanar mata da abinda ke faruwa aiko dai hankali ba karamin tashi yayi ba nan ta fashe mashi da kuka a waya, daker ya dan rarrashe ta sama sama ya tashi ya kamo hanyar asibiti, sai da Alhaji Abdur-rahman ya iso ya bude ma Dad file yayi duk abin da ya kamata yayi sannan Dr din suka taba shi.


Dad ya nakasa iya nasaka dan gaba daya kafafun shi sun samu karaya bibbiyu ga kuma hannun shi na dama, banda uban ciwukan daya jijji ga kanshi daya fashe , fuskar shi ta canja kamanni lokaci guda haƙora ukun sama dana kasa duk sun zube sai wawakeken giɓi, su karan Kansu litocin sun tausaya mai kuma sun jinjina ma taurin ranshi da bai mutu ba duk da tarin ciwukan daya ji. Abinka da harkar nera suna gaya wa Alhaji Abdur-rahman akwai karaya za'ayi gyara yace a bashi Dad ya zai canza mai asibitin ba bata lokaci kuwa akayi cike ciken komai aka saka shi a. Ambulance sai asibitin da zee ke kwance.A cikin daren aka yi ma Dad ɗauri dan tsananin azaba harda su kashi a wando suma kuwa yayi yafi so uku yana farfaɗowa, gashi baisan ya kira Allah ba, sai tsala ihu yake yi kamar wani Arne, ranar gaba ɗaya asibitin sai da akasan da zaman Dad masu tausayi nayi masu dariya nayi, su Asmah da Mami ma sun sami labari duk da basu san ko wanene bane kwarai sun tausaya mai, Alhaji Abdur-rahman ne kaiɗai yake ta kai kawo akan shi har zuwa safe, sai da yaga komai ya daidai ta har barcin azaba ya kwashe Dad sannan ya yi sallama da likitoci da niyar zai je gida ya huta, zuwa anjima zai dawo, da safe wuraren karfe 7 Aslam ya iso asibiti,kusa da motar Alhaji Abdur-rahman yayi fakin ba tare da sani cewa motar shi bace, fito wa yayi ya zagayo ya buɗe ɗaya gefen ya dauki little juyowan da zai yi daidai lokacin Alhaji Abdur-rahman ya iso wajen fakin din domin shiga ɗaukar motarshi, kallon mamaki suka shiga bin juna da shi, Aslam na tunanin to waya gaya mishi zee na asibiti don shi a tunanin shi zee yazo dubawa, shi kuma yana tunanin ya akayi Aslam yasan Dad na asibitin nan to ko shima Dr ya kira shi, Aslam ya ƙarasa ya bashi hannu sukayi musabaha, Dad yace "Ya mukaji da wannan iftila'il kuma." Ba tare da ya fahimci komai ba yace "Sai godiyan Allah, amma jikin da sauƙi sosai Alhaji don Dr ma yace yau zai bamu sallama." Alhaji Abdur-rahman cikin mamaki "sallama Kuma! wa za'a ba sallama?" Aslam yace "Ita mana." "Ita wa?" Ya tambaya, Aslam shima abin ya fara ɗaure mishi kai dan haka yace " Ita Zainab ɗin." Zaro ido Alhaji Abdur-rahman yayi cikin kaɗuwa yace "kana nufin kace min Zainab na kwance a wannan asibitin ita ma?" Aslam yace "eh Alhaji ai na dauka ma ita kazo duba wa." Maimakon ya bashi amsa sai "innalillahi wainnailaihi rajiun ya shiga maimaita wa." Can kuma yace "Muje ka kaini wajen ta na duba ta meye ya same ta." Suna tafe Aslam ke gaya mishi ai ta samu miscarriage ne, Alhaji yace "subhanallahi garin yaya." Shiru ya danyi kamar bazai gaya mishi ba sai kuma wata zuciyar ta umarce shi daya faɗa domin barin kashi a ciki baya maganin yunwa, tuno kawai abin da ya faru don faɗawa Alhaji sai da yaji zuciyar shi ta dauki zafi dan sanyin data ɗan yi tuni ya gushe. Bai yi ƙasa a gwuiwa ya kwashe komai ya shiga gaya mishi, tunkan Aslam ya kai karshe Alhaji wata uwar burki ya taka tare da juyowa hankali tashe yace "Kana nufin Abdus-salam yaje gidan ka ajiya har yayi sanadin zubewar cikin jikin Zainab." Kasa bashi amsa Aslam yayi dan wani irin tukukin bakin ciki yake ji a ranshi. "Innalillahi wainnailaihi rajiun, Allah wadaran naka ya lalace, gaskiya Abdus-salam baiyi wa kanshi adalci ba dama na gaya mishi wani rabon karfi gareshi kisa yake, to shi Allah ma yaso shi bai mutu ba amma kuma da wannan halin daya shiga ai gara mutuwa." Kallon rashin fahimta Aslam ya shiga binshi dashi, ganin haka yasa ya kwashe duk abin da ke faruwa tun da ga daren jiya da aka kira shi a waya daga general hospital zuwa wayewar garin yau, ko ɗar Aslam baiji a ranshi sai ma cewa da yayi "Allah kyauta Allah ya kiyaye na gaba." Sun tarad da su jugum jugum kamar wa'inda aka aikowa da saƙon mutuwa, Asmah da Mami na zaune a bakin daya extra bed ɗin dake ɗakin, zee kuma na zaune a bakin nata bed din rike da cup din tea a hannun ta idanunta sunyi jajur alamar taci kuka ta ba uku lada, ganin wan mahaifin nata yasa ta sake fashewa da kukan da da'ker su Mami suka samu tayi shiru, shima direct gareta ya isa ya zauna a kusan da ita tare da kamo hannayenta ya rike cikin nashi, yana bin ta da wani irin kallon tausaya wa, cikin tsananin kuka tace "Abba dan Allah ka gaya min gaskiya da gaske Dad shine mahaifina shiya haifeni, Abba Dad kullum ikirarin shi yana sona yafi kowa sona a duniya amma wlh ni soyayyar shi ni batai mini rana ba, tun da har ya kasa bani farin ciki, ya kasa barina na zauna da mijina domin na sami Aljannahta aƙarƙashinsa, Abba Dad yayi sanadin da cikin jiki na ya fita, shin wannan wane irin sone?." Ta karashe da wani irin matsanancin kuka, jikinshi ya jawota ya rungume, Asmah da Mami tuni zuciyar su ta daɗa karyewa ji suka kamar su taya ta kuka, Aslam kam taɓe baki yayi ya dauke idanunshi daga garesu, daker Alhaji Abdur-rahman ya samu ya lallɓa zee ya samu ta tsagaita kukan ta, cikin kwantar da hankali yace "Kiyi hakuri Zainab ko wani bawa da kalar jarabtar da ubangiji yake mishi a rayuwar shi ta duniya, ke da mahaifin ki jarabtar ku iri ɗaya ne, shi kece jarabtarshi, kema shine jarabtar ki, kiyi hakuri ki daina jin kamar cewa ba shi ya haife ki ba, tabbas shi ya haifeki, amma Allah ya jarabce shi da wani irin makauniyar soyayya akan ki, wanda a karshe shine yayi sanadin nakasan shi." Nan kuma ya kwashe duk abin da ke faruwa da Dad ya sanar mata, kan kace kwabo ta kara birkicewa, sai kuka take tana kiran dadin ta, karshe ma ta tsige Karin ruwan dake hannunta tace ita gurin dadin ta zata tafi, wai a haka ma Alhaji Abdur-rahman bai gaya musu irin raunukar daya samu ba daga ita har Aslam ɗin kawai ce musu yayi, yayi hatsari, ba shiri Alhaji yasa aka kira Dr ya duba ta, a take ya rubuta mata sallama ma gaba ɗaya kawai, Alhaji Abdur-rahman yace Aslam ya kaita gida, aiko

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads