Showing 3001 words to 6000 words out of 201974 words
Chapter 2 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
ta, anrasa mai bakin magana acikinsu,
Ganin sun tsaya suna kallonta kaman wasu mutum mutumi yasaka ta nufar kofar ta barsu nan tsaye tayi facewarta , da Sauri batool ta bi bayanta tasha gabanta tace " yanzu da gaske tafiya zakiyi asmah "
Wani kallo ta watsa mata tace "me zan zauna inyi miki" batool tace "dare fa yayi asmah " tace " saime to in dare yayi, Wlh ko qarfe biyu dare ne yanzu bazan kwana agidan nan ba batool " batool zata sake mata wani magana ta daka mata tsawa da cewa " dallah ki matsamin a gaba malama". Hakan yasa batool matsawa a gabanta ta bata hanya ta wuce .
Komawa dakin batool tayi nan ta tarad da sauran, amira na trying number yaya kamal yaqi shiga, sake dialing number tayi cikin sa' a kuwa wayar ya fara ringing saida ya kusa katsewa kamal ya daga kiran tare da sallama ,
Ko amsa sallaman amira batayi ba ta fara magana cikin muryar kuka "yaya kamal kana inane don allah kazo yanzu Dan Allah yaya kazo ka taimakemu " jin abinada amira ke fad'i hankali tashe yasa kamal shima cikin Dan tashin hankali yace " meke faruwa ne amira kina inane yanzu"fisge wayar a hannu amira zahra tayi ta kara a kunne tace" yaya kamal kazo gidan yaya aslam dake London road inda akakai asmah dazu"
"OK Ku jirani ganin nan zuwa yanzu"
Asmah kam koda ta fito wucewarta tayi ko waiwayen su batayi ba,koda tazo get cikin sa'a mai gadi ya kewaya don haka sakata ta zare a qaramin kofa tai ficewarta,
Bayanta suka biyo cikin sassarfa amma ko kafin su fito tayi nisa, suma ganin get a bude yasa su bin bayanta da sauri - sauri gudu - gudu , hongota sukayi tanata zuba Sauri tayi musu nissa sosai, hanyace miqaqqiya babu kwana har zuwa titi, don haka suka shiga binta a baya don karta bace musu.
Kasancewa unguwace ta manyan mutane kuma gashi dare ne yasa babu abun hawa Na haya sai motar gida dake wucesu jefi jefi
Share
And
Comment
Fisabillah🙏
💖DAMA TA BIYU💖
BY
AYSHA NALADO
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Page 9&10
Motar kamal ne ya shigo kwanar gidan a guje sai gudu yakeyi hakan yasa bai lura da asmah ba ya wuceta.......Amira ce ta fara hango motar don haka ta gaya wa sauran ga yaya kamal nan, hannu suka daga mai don ya ganesu ,
Gabansu yayi parking ya fito a rude yana tambayansu lpy meya samesu ina ita asmah? Duk hankalinshi a tashe yake.
Khadijah ce tayi karfin halin amsa masa da "yaya asmah tàna gaba..... yaya kamal muje gida sai amaka bayani wlh akwai matsala"
Shima bai qarayin magana ba ganinsu lafiyar su lay ba wani ciwo ko wani mugun abu a tare dasu, bude motar suka yi suka shiga baya dukkansu yayinda kamal ya zauna a mazaunin shi na direba,,, Rivas yayi suka kama hanyar gida,, hango asmah sukayi daidai ta isa bakin babban titi, parking kamal yayi a gabanta ya bude mata kusa dashi baice mata komai ba, itama ba musu ta shiga ganin kamal ne gashi kuma dare na qarayi.........
Zaune yake a room na hotel daya kama hankalin shi kwance kamar bai aikata komai ba...babu alamar damuwa ko wata nadama at are dashi, baidamu da neman shi da akeyi a gida ba. sarai yasan irin neman shi da amir dasu Abba sukeyi acikin garin minna... Amma ya bace musu bat ba amo ba labarinsa duk inda akasan zai iya zuwa ya anje ba a sameshi ba duk hotel din da akasan zai iya zuwa amir yaje ya bincika baije nan ba... Kasancewan amir yasan halinshi nasan Babar harka yasa iya manyan hotel din dake garin ya duba bai duba qananan ba. Hotel din daya kama ba Wanda zaiyi tunanin zai iya zuwa nan...amir kan ba qaramin kunya yasha ba Na irin gayyatar da yayi na abokansu tun da secondary, Dana aboard inda sukayi karatunsu da abokanan kasuwancinsu, amma aslam ya watsa masa kasa a ido, ko zuwa su gaisa baiyi ba kuma bai halarci wajen daurin auren ba balle ayi maganar zuwa dinner da amir din ya shirya , duk tarin yawan aboka nansu da sukazo haka amir yara jigila dasu shi kadai tun daga abincinsu abin shansu wurin kwana su dadai sauran su sai kamal dake dan taimaka masa haka dai had yasamu aka gama daurin auren ya sallame su , kiran ways kuwa amir ya kira aslam a waya yafi sau Dari bai dagawa massages kuwazed'a magana, amma aslam yayi mursisi dashi ya share shi,
System dinshi ya bude ya shiga gabatar da aikatotin shi Na yau da kullum da yake gudawarwa da suka shafi harkokin business dinsa saida ya gama tsab ya kulle system, wayarsa be ta fara ringing gyara zama yayi da kyau ya dauki wayar yana duba me kiran nashi...
(zee my 💖) ya gani yana yawo akan screen din wayar saida kiran ya kusa katsewa yayi picking tare da sallama... cikin kashe murya da tsabar iyaya zee ta amsa sallamar tare da cewa" da fatan masoyina ya wuni lafiya "
Wani kayataccen murmushi ne Wanda ba kasafai ake ganin irin shi a fuskarshi ba ya subucemai , amma kuma bai amsataba yadai amsa sallamarta a zuciyarshi....
Jin shirun yayi yawa yasa zee cire wayar a kunnenta tana dubawa ko yana kan layi , still dai call din nanan bai katseba, ganin haka yasa tasan yau yan miskilan na kusa, don haka tace "haba my husband to be yau kuma wani laifin na maka kake neman horani da shirunka" dan dakatawa tayi don tasan sarai bai cika son magana da yawaba,
Shiru kamar bazaiyi magana ba can kuma sai yace" lafiya qalau na wuni kuma ina fatan kema hakan take a gareki " murmushi tayi tace"nima qalau na wuni saidai kewarka data hanani sukuni " "dagaske kina kewata"ya tambayeta " sosaima, inkaji kewa daya kenan "
yace "ok to yayi kyau yasu mom"
"Tana lafiya tacema na gaisheka ". "OK" kawai yace mata, Dan shiru sukayi gaba dayansu kowa naji da kanshi har garama zee saboda son da take mishi wani lokacin takan ajiye Jan ajinta ta mishi magana , yanzuma ita ta katse shirun da cewa,"wani labari Mara dadi nake taji abakin mutane wai kayi aure dis week " amsata yayi da cewa "waya gaya miki " tace"friends dina da suke 9ja mana, kusan mutun biyar suka kirani awaya suka gayamin sannan kuma na gani a Media......amma saboda baka gayamin ba ban wani yarda ba, saboda nasan duk duniya inba niba baka kala wata mace ni kadai ce zabinka "lumshe kyawawan idanunshi yayi ya bude a hankali sannan ya ce mata" da gaske ne nayi aure" ya fada mata haka ne kawai don ya gwada ta, domin kuwa dagasken ne kamar yadda ta fada itace zabinshin duk duniya, itace first luv dinshi kuma har yanzu ita yakeso, bashi da wani burin daya wuce ya mallaketa domin ta hada duk abinda yake buqata awurin diya mace musamman matar da zai aura Wanda yake ganin asmah ko RabinRabin shi bada shi
Share and comment
Fisabillillah.
💖DAMA TA BIYU💖
BY
AYSHA NALADO
FREE BOOK
{Nasadaukara da wanna book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Page 11&12
Aiko ya gwadatan Dan wani iri kwance kwance gabanta yayi ya fadi, nan da nan hankalinta ya tashi ta birkice, mom dinta dake zaune kusa da ita tanajin duk abinda suke fad'a ta jawota jikinta ta rungumeta ganin tanason ta fashe da kuka, ita kuma mom bata son tayi kuka a gabanshi akan wanna maganan,
Don acewarta idan yaga ta damu dashi haka sosai zai wulaqantata ne idan sunyi aure, bazai dinga kulawa da baccin ranta ba, don yana ganin tana bala'in sonshi komai zai mata bazata damu ba, wai ta dena nuna mai mahaicinso 'karya raina ta, hannu mom ta saka ta kashe wayar,
Aslam jin shiru yayi yawa yasa ya cire wayar a kunnen shi ya duba gani yayi tayi ending call din , murmushi yayi don ya riga yasan hakan zata faru, yamaga qoqarinta da bata yi mai wani hauka ba, d'on yasan yanda takeson shi idan taji yayi aure ba qaramin tashin hankali zata shiga ba,
Saidai abinda aslam bai saniba ranar da zee ta farajin labarin yayi aure saida tayi dan qaramin hauka, mom dinta ne ta dinga lallashinta sannan ita ta hanata nuna mishi ta damu da auren da yayi, ita ta hanata ta kirashi tun lokacin ta zuba mishi hauka, ta gaya mata ta nuna irin abin bai dameta ba, wai don idan ya gane ta na kishinsa ya samu lagonta kenan, ba a nunama namiji mugun so don ba yan goyo bane,
Zaune take tayi irin zaman nan na tahiya kanta a kasa yayida gabanta kadan wani farin kyakkyawan tsohone hannunsa goye a bayansa sai safa da marwa yakeyi fuskan nan nashi a murtike babu alamar fara'a kai da gani kasan ransa a mugun bace yake,
Sallama daddy da mummy sukayi amsa musu alhaji baba yayi neman guri sukayi daga gefen kafet din dake shimfid'e a tsakiyar parlon suka zauna,
Asmah ce ta gaishe su cikin girmamawa sai lokacin dukkan su suka kula da itace a wurin amsa mata sukayi, zuciyoyinsu cike mamakin ganinta da kuma tarin fargaba, basu taba tsammanin ganin ta a nan a dai dai wannan lokaciba, don koda su zahra suka shigo basu gayawa mummy komai ba, koda ta tambayesu lafiya suka dawo ba sunce zasu kwana bane, ce mata sukayi lafiya qlau sudai sun dawo ne sun fasa kwanan ,
Ita kuma ganin yanayin su wani iri sai ta alaqanta hakan da qila yayansu ne ya korosu,
Sallamar da aka kumayi ne ya katsewa mummy tunaninta, mamice tare da abbah sai kuma ummi dake bayansu, suma guri suka samu suka zauna suna mamakin ganin asmah ,
Dukansu hankalinsu suka mayar kan mahaifin nasu dake ta faman safa da marwa,
Shima ganin duk yayan nashi sun hallara yasa ya juwo ya fuskancesu ransa a matuqar bace ya fara magana "Aisha" ya kira sunan mummy ,
Dago kai mummy tayi tana amsa masa da "na'am baba
Yace" yace inason a matsayinki na mahaifiyar wannan yaro aslam ki kirashi ki bashi umarni nan da minti goma ko a ina yake yazo ina buqatar ganin shi a falon nan"
Nan take gaban mummy ya yake ya fad'i kar aje wani mugun abu aslam yayi fa, don ita hankalinta bai kwanta da wannan kiran gaggawan da alhaji baba ya musuba duk da batasan kiran menene ba, hankalinta bai qara tashiba saida taga asmah a wajen yanzu kuma gashi ance ta kira aslam, haka dai ta daga wayarta don kiran aslam din ,
Yayinda alhaji baba yaci gaba da magana cikin dan danne yanayin da yake ciki na bacin rai ya kira sunan ya yan nashi guda uku da ya mallaka a duniya yace" abdullahi" "na'am baba daddy ya amsa,"
Yace "dakai da qannenka Yusuf da Amina da matayenku da yayanku .....Allah ya muku albarka" har suna hada baki gurin amsa masa da amin baba.
Daidai nan kuma hjiya mama ta shigo dakin, tsohuwace mai kamala cikin shiganta na mutunci idanunta sanye da farin glass na qara karfin gani, tana dan dingisawa alamar kafa nadan matsa mata abinka da jikin tsufa, waidonma su tsufan nasu mai kyau ne angode Allah Neman guri tayi ta zauna a daya daga cikin kujerun falon ..
Magana alhaji baba yaci gaba dayi" tun kuna qanana kuka kasance masu yimin biyayya a dukkan abinda na umurceku, sannan haka kuma horas da yayanku akan bin umarnina, Baku taba saba umarninaba daku da yayan Ku....nagode nagode Allah ya saka muku da alkhairi, kuma insha allahu zaku tsinci ribar biyayya a gaba koda bayan raina ne, sannan kuma Abu na biyu da yasa na kiraku nan shine"
(Kuyi haquri dear fan's jiya banida chaji ne)
Share and comment
Fisabilillah🙏🏻
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
🇳🇬🇳🇬HAPPY INDEPENDENCE🇳🇬🇳🇬
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Page 13 & 14
"Maqasudin abin da yasa na tara ku anan shine "miqama Daddy takardan sakin da asmah ta kawomishi yayi,
Hannu biyu daddy yasa ya karbi pepan amma bai bude ba yana jiran umarni.
CI gaba Allah ji baba yayi da fad'in "wannan shine sakomakon abin da aslam ya sakamin da shi ,
Tunda nake cikin yayana da jikoki na ba'a taba aikatamin abinda aslam ya aikatamin yau ba, amma ba komai rayuwace"
Alhaji baba ya qarashe maganar cike da bacin rai a muryarshi"abdullahi bude takardar Ku gani mana" daddy da duk jikin shi yayi sanyi qalau yayi karfin halin bude pepan da bismillah a bakin shi.....abinda ya gani rubuce cikin pepan ne ya sakashi sakin pepan ba tare da ya shiryaba, abbane ya miqa hannu ya dauki takardar ya duba..... Miqewa shima yayi a zabure ya maimata innalillahi wa innailaihi rajiun kafin ya bude baki yace "wani irin haukane aslam ya aikata haka" Ummi ne ta karbi takardar ta duba itama ta miqa ma mummy da mami , kowa hankalin shi ya tashi a falon nan idan ka cire asmah da alhaji baba....
A zabure daddy ya miqe yayi hanyar waje, Alhaji baba ya dakatar da shi da cewa "abdullahi dawo ka zauna" ba musu daddy ya dawo ya zauna ,
Alhaji baba kallan mummy yayi yace "Aisha kin kiramin shi ?"
Amsawa mummy tayi da "na kirashi bai yi picking ba amma na mai text nasan inya gani zai kira yanzu" gyada mata kai alhaji baba yayi alamar gamsuwa......
Daidai wannan lokacin kuwa aslam ne ya fito wanka daure da towul a qugun shi, yana goge kanshi da karamin tawul d'in dake hannun shi, saida ya gama goge jikin shi ya dauki body lotion dinsa ya shafa da body spray dinsa mai shegen tsada da tsananin dadin kamshi, ya shirya cikin kayan barcinsa farare riga da wando marasa nauyi, pray mat ya shimfida ya gabatar da shafa'i da wutiri yayi addu'o'inshi , so yake ya kwanta barci da wuri , kallon agogo yayi ganin goma da Rabi na dare yasa ya Dane gado ya kwanta ya kashe fitila mai haske yabar dim light, wayar shi ce tayi qara alamar message ya shigo kamar ya share Dan d'azuma yana ji ana kiran shi ya share ko dubawa baiyiba balle yasan waye, shi duk zaton shi zee ce ko yanzuma yana zaton ita ce ta mai message , daukar wayar yayi da niyar kashe wa gaba daya don da gaske bacci yakeson yi da wuri, sai kuma ya tsaya don ganin message din daga mummy ne, ganin abinda ta rubuta ya sakashi saurin lalubo numberta ya kira jiki na rawa, daidai lokacin alhaji baba ke cema mummy ta sake kiran shi,
Ringing wayar mummy ya fara ganin Aslam dinne yasa yasa mummy saurin d'agawa ko amsa sallamarsa batayiba tace a kausashe"kasameni a gida nan da minti goma kuma umarni nake baka ba shawara ba idan har ni na haifeka...... Idan kuma nima zaka bijiremin d'inne to bismillah shege ka fasa" git ta kashe wayarta ta barshi da way a manne a kunne, Nan shima hankalinshi ya tashi jin yadda mahaifiyarshi ta mai magana cikin bacin rai, ga dukkan alamu sakon abinda ya aikata ya iskesu kenan.....hankalinshi ya dan tashi jin muryar mummy cikin bacin rai da tsananin fishi don yasan fishinta ba sauqi har gara fishin daddy yafi sauqi akan nata, amma ko dar baijiba akan abinda ya aikata balle yayi nadama
Tashi yaya ya shiga cikin qananan kaya ya dauki key din mota da wayarshi ya fice daga hotel din zuwa gida minti 15ya kaishi gida , direct sashen alhaji baba ya nufa son yasan sunacan suna jiranshi ,
Da sallama a bakinsa ya shiga parlon Abba da mami da hajiya mama ne kawai suka amsa mishi a fili , samun guri yayi ya zauna kusada abba, kanshi a qasa ya fara gaida mutanen parlon, kamar dazu daddy da mummy basu amsa mishi ba amma alhaji baba ya amsa mishi wannan karon,
Kallon asmah yayi kanta duqe a kasa nan take ya qarajin tsanar yarinyar a ranshi, kamar ya shqeta ta mutu kowa ya huta haka yake ji a ranshi duk ita ta jawo mishi wannan matsalar da yace ciki iyayenshi na fushi dashi akanta,
Kowa ya nutsu a parlon ana jiran hukuncin da alhaji baba zai yake gyaran murya yayi kafin ya fara da fadi "fadin Muhammad naga saqonko kuma na code amma ka Sani ka tabka babban kuskure Wanda zakayi Dana Sani nan gaba , lilokacin da Dana sanin bazai amfaneka da komai ba zakayi nadama loacinda nadaman ka baida amfani, kuma ka rubuta wannan maganar ka ajiye ko bayan raina zaka tina na taba gaya maka shi, "dago kai aslam yayi zai fara bada haquri,,
Dakatar dashi alhaji baba yayi da cewa"banyi fushiba Muhammad kankan ka cuta baniba, wlh kayi babban asara , domin zabin da namaka zabine daya a ciki dubu amma kasa qafa kayi tafali dashi, har kana sakinta ranar da aka daura muku aure waidon ka kunyatani..kanka kama,
ita kuma Asma'u zataci gaba da zama damu anan, Allah zai bata mijin da yafi komai tayi aurenta na aurad da ita kamar yadda nama kakanta aminina alkawari
Yusuf inason idan zaka je yima yan biyu da amira registration ka hada da asmah, tunda auren bai yuwuba karatu zata ci