Showing 48001 words to 51000 words out of 201974 words
Chapter 17 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
ya nemi guri ya zauna, wayar shi ya laluba ya danno lambar Amira da yayi saving da baby,
Suna zaune a dakin kiran ya shigo wayar ta , ganin ya Amir ne ke kira yasa ta daga , cikin magana kasa kasa yadda ko Asmah dake kusa da ita bataji me take cewa ba tayi sallama, magana sukayi na yan sakonni ta ajiye wayar tana murmushi,
Minti uku ta qara kafin ta miƙe tace "sisters ina zuwa, " zahra tace "sai ina " tace "nan waje", ta fice da sauri dan kar su ƙara tambayar ta wani abin,
Samun shi tayi a inda ya mata kwatance nan suka zauna suka shiga firan su na masoya da tsare tsaren bikin su hankali kwance,
Kallo daya zakasan wadannan masoyane da suke cike da tsantsar kaunan juna da shauɗin juna,
A can dakin kam Aslam tun bayan kallo dayan da ya mata ya zame a hankali ya kwanta,zuciyar shi na buguwa , kishi mai tsanani yana taso mai ji yake kamar , ya tashi ya shaƙe kamal har sai ya dena nunfashi, zuciyar shi ce ta dinta tunzura shi, amma cikin ikon Allah ya shiga maimaita innalillahi wainnaialahi rajiun, lamo yayi ya lumshe ido kamar me bacci , da haka har baccin gaske ya kwashe shi kasan cewar yasha magunguna masu ɗarfi,
Fira aka shiga yi a dakin tsakanin kamal da Dr bash sai jefi jefi su Zahra na saka musu baki,
Zee jin sun dameta yasa ta miƙe tare da jan tsaki ta fice daga ɗakin ,
Harara batool ta rakata dashi kafin ita ma ta ja nata tsakin ,
Dr bash da dama duk abinda yakeyi hankalin shi na kanta , a zuciyar shi yace " yawwa dama nasan ko kowa bai tanka ba , ai hajiya masifatu ta tanka,"
CI gaba sukayi da hira, can Dr bash yace "subhanallahi wlh na manta akwai wani allura guda daya da za'amai cikin dare gashi bamu dashi anan sai anje pharmacy a waje an siyo" kamal yace"ayya to kawo na siyo mana"
Rubuta mishi sunan alluran yayi ya miqa mishi, amsa yayi ya miƙe har yakai bakin ƙofa ya juyo ya kalli Asmah, yace asmy ba rakiya, cikin dan jin kunya ta watsa mishi hararan wasa , tana murmushi, hannu ya haɗe mata alamar roƙo yayi fuskar tausayi, saida ta ja mai aji sannan ta miqe tabi bayanshi,
Dakin ya rage daga batool da zahra sai Dr bash, sai aslam dake bacci,
Dr bash ya dubi zahra yace "kanwata zahra ya makaranta ya karatu," cikin murmushi ta amsa da "makaranta alhamdulillahi , karatu kuma akwai wuya ya bashir" bash yayi murmushi yace "karatun ma balle irin namu sai mai ƙoƙari, kuma ke da gani zakiyi ƙoƙari, ganin yadda kike da nutsuwa da hankali , ba kamar wasu yan matan ba da zaki gansu kullun cikin guje guje kamar yan nursery,"
Dagowa batool tayi da sauri ta kalle shi jin abin da take cewa ,ko ba'a fad'a ba tasan da ita yakeyi,
Zahra ko cikin jin dadin yabon da aka mata, tace " nifa ya bashir bani da wani qoqari saidai taimakon Allah kawai, dama batool kace itace mai kokari don duk cikin mu ta fimu ƙoƙari," cikin son ya tsokani batool yace"kai zahra wannan shirmammiyar yarinyar da ganin ta baza tayi wani qoqari ba, irinsu ne fa masu yin espo a class, da ganin idonta na rashin kunya ta kware a iya espo"
Kan uba aiko dai ya taro masifa don dama tun dazu daurewa kawai takeyi amma a cike take fam dashi kamar zata fashi,
Aiko nan ta shiga zazzaga mai ruwan rashin kunya tanayi tana murguda baki, ta inda take shiga ba tanan take fitaba,
Aiko dai Dr bash mutuwar zaune yayi yana kallonta , ɗan bakinta da take masifa tana mugudawa yake bi da kallo , gaba daya masifarta burge shi yakeyi, abin na mishi ɗaɗin kallo yana sakashi nishadi,
Saida tayi mai isar ta tayi shiru, zahra kam tagumi tayi da hannu bibbiyu tana kallon ikon Allah , don tun ɗazu take ce mata ya isa amma taqi kulata , ganin haka yasa ta yi tagumi tana kallonta,
Su kamal ne suka shigo dakin , ganin haka yasa kamal tambayar ba'asi ,nan ta shiga labarta mishi abinda bash yace tana yi, kamal kunshe dariyar shi yayi yace,
"Kai ammafa Dr ka samu kanwata da yawa ita kake kira da me espo a class, to kiyi hakuri wasa yake miki ai,da'ker ya lallabata ta hakura ,"
Daga nan sukayi sallama da Dr bash, a waje suka dauki Amira suka koma gida,
Kwanan Aslam uku jiki yayi sauqi sosai , nan yace shi ya gaji da zaman asibiti a sallame shi , ƙin sallaman shi bashir yayi yace sai yayi sati, tada balli yayi ba shiri Dr bash ya rubuta mai sallama,............
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fi sabilillah🙏
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan littafin ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan mahaifan mu}
Page 63 & 64
Bayan kwana biyu Aslam tuni ya gyagije , kamar bashi bane aka kai asibiti rai a hannun Allah, saidai fa karfin hali kawai yakeyi , bai bari ya saka damuwa a ranshi ba , ƙokari yake ya yakice ta daga zuciyar shi,amma Abu ya gagara, kullum burin shi ya ganta , duk randa bai sakata a idanun shi ba baya iya barcin kirki, zee kam gaba daya ya tattara al'amarinta ya watsar don yanzu bata gaban shi, kullum cikin yawanta take , ita da beebalo, abu daya ya sani, ya saka ana bibiyar mishi ita duk inda kafar ta ta taka a garin minna , akwai masu bibiyarta,idan kuma ta dawo da daddare, idan ta kowo kanta gare shi zai biye mata, saboda fita hakkin ta, idan kuma bata kawo ba , a sauka lafiya kowa na dakin shi , da safe kuma ba lallai suga juna ba , saboda Aslam da sassafe yake fita, zaije can farkon layin shiga family hause yayi parking ya zauna ya jira har bello ko kamal ya dauki su Asmah zuwa school, a nan yake samu ya ganta kullum , duk kuma ranan da bai ganta a nan ba . har school yake binta a boye a boye, dan kawai ya ganta, idan ba haka ba kam ranar ba zaman lfy , da daddare ma saiya manna hotanta akan kirjin shi yake iya samun bacci,
Yau dai daya kama kwana ashirin cif da sallamar sa daga , asibiti ya gaji, muryarta kawai yake son ji, gashi ba daman yaje family hause, a halin yanzu, dana sani ya shiga yi na cewa da yayi bazai kara zuwa gidan ba yanzu gashi yana son zuwa kodan yaji muryarta amma ba hali, zuciyar shi Ce ta shiga bashi shawarwari iri iri na yanda zaiyi ya samu jin muryarta,
Ya yanke shawaran kawai gidan zai tunkara ya fuske ya shiga falon mummy ya zauna , wata zuciyar kuma tace yayi ɓadda kama ya shiga gidan , a mastayin abokin Amir q
Ƙila ya samu ya ganta, wata kuma tace yayi shigar mata yaje, shawarwari dai marasa kan gado iri iri,
Karshe dai yaga ba ta yadda zaiyi ya shiga gidan ba tare da angane shi ba a haka ya ajiye batun zuwa gida ya barshi a zai tare a school kawai ayi wacce za'ayi , imma zagin shi zatayi tayi, shidai kawai yaji muryarta,
A family hause kam shirye shiryen biki ya kankama , ƙannen mahaifin amir sunzo , neman auren amira kuma an basu, abinka da tuwona maina , ba wani bata lokaci aka gama komai, haka ma batun Asmah da kamal, shima dai duk na gida ne ba wani tsatstsayawa ,
Soyayya tsakanin Barr Adam da zahra kam abin ba"a cewa komai kullum suna maqale a waya, cikin kankanin lokaci yayi nasaran sace zuciyata, tun tana jin kunyar shi tana ɗari ɗari dashi har ta zage ta shiga mayar mai da martanin zafafan kalaman soyayyar da yake gaya mata, don Barr Adam ya iya bi da ita sosai, dama kuma can zahra akwai sauƙin kai ba kamar batool bace, suma dai magana tayi karfi don har an shiga gida an gana gemu da gemu,
Matsalar su ɗaya maryama uwar gidan Barr Adam , tana can ta tada balli, ita bata son kishiya ,saidai ya zaba ko ita ko zahra, shi kuma yace duka yana sonsu, har wayar shi ta dauka ta kira zahra ta zageta tass wai ta rabu mata da miji, zahra kam shiru tayi, aiko batool dake gefenta ta fisge wayar ta shiga mayar mata da martani, kaca kaca sukayi a wayan, Wanda na tabbata da a kusa da juna suke ba abinda zai hana a doku,
Kuka zahra ta fashe dashi wai ita ta hakura da auren Barr Adam aiko batool ta mata ca aka tace " tab tunda nake nikam ban taba ganin wawuyar mace irinki ba, dan kawai kishiya ta kiraki ta miki wannan dan barazanar shine zakice kin fasa auren masoyin ki, to wlh sai anyi auren nan kodan mu gyara ma wancen karkatacciyar matar tashi zama, " ƙwafa tayi tace "kai Allah yaga aniyar jaki yasa baiyi shi da kaho ba, da nine a matsayin ki,da saina ci uban wannan wawuyar matar tashi la'ada waje, kema dole ki ƙarfafa zuciyarki inba haka ba zaki sha wahala a hannun kishiya". Zahra cikin kuka tace "wlh batool bana son tashin hankali ko kaɗan "
Kiran Barr Adam ne ya katse musu maganar da suke, kin dagawa zahra tayi, batool Ce ta daga ta saka shi a hands free , cikin rawar jiki tana dauka ko gaisawa basuyi ba Barr Adam ya shiga bama zahra hakuri cikin lallshi , da kwnatar da kai, tsoran shi ɗaya kar tayi fushi tace ta fasa auren shi , saboda abin da maryama ta mata, don yasanta sarai bata son tashin hankali, don idan ta fasa auren shi shikam ya shiga uku,
Tausayin shi ne ya kama batool ganin yadda ya ruɗe lokaci ɗaya , lallai yana son yar uwarta sosai, tatabbata idan ta shiga gidan baza ta wahala ba, kwandon masifar da tayi niyyara sauke mai ta mayar ta Adana abinta, miƙama zahra wayar tayi ta mata alamar ta amsa mishi,
Amsa tayi ta nuna ba komai ta hakuri nan ya shiga zuba godiya , abin tausayi,
Aiko suna gama wayar ya haura dakin maryama a fusace, kamar wani mayun wacin zaki,
(to nidai nace Allah ya huci zuciyar Mallam adamu,)
Bangaren bash kam ya riga ya gama gane soyyayar batool ta gama mai mugun kamu , har fiye ma da yadda yaji son Asmah, a kwana kin baya,
Saidai kuma shi kaɗai yake kiɗan shi kuma ya taka rawar shi don ita a maƙiyi ma ta ɗauke shi, yanzu gidan ya zame mishi wurin zuwa kullum, haka zaije yata tsokanar ta ita kuma tana zuba mai masifa,
Shima ko a fuska bai taba nuna mata yana sonta ba kullum cikin hade mata rai yakeyi karta raina shi, dan yasan halinta,
tsokananta dashi kullum tayi kwantai bata da farin jini an kawo kudin auren kowa banda nata, kilama ko saurayi bata dashi,
Aiko wadannan kalmomi na fusata batool , nan zata shiga zuba ruwan bala'i , randa mummy kuma ke kusa ta tsawatar mata , to ranar kuwa har kuka sai tayi, tayi tayi ya daina zuwa gidan , ya daina shiga harkarta yaƘi,
Kowa na gidan ya dasa musu ayar❓ gadai su ba wanda zaice soyyaya sukeyi an rasa takamaimai meye a tsakanin su, ko mutum yayi tunanin soyayya suke , idan kuma kaga yanda suke yar tsama sai ka cire wannan mutanin a ranka,
Asmah da Amira kam tsokanan ta sukayi da ta Dr bash , kodai da bash za'ayi, tako ce Allah ya kiyaye wannan dan banzan mutumin, ni wlh ku daina haɗani dashi , don wlh nafi karfin sa ko maza sun kare, Amira tace umumfa batula karfa muzo rashe ya juye da mujiya ,
Ɗan wannan kwana kin da Dr bash ya kwashe yana zarya gidan , ba ƙaramin sabawa batool tayi da, yanayin tsokanar shi ba, a kullum har Allah Allah take yi lokacin zuwan shi yayi , haka zata zarya tana duba agogo,
Yau dai bai samu zuwa ba, luƙuss tayi a kan bed bini Bini ta duba agogo har wurin ƙarfe yadan dare babu shi babu labarin sa ,
Zahra ta dubi Asmah dake gefenta ta nuna mata batool , da zunɗe, kallon batool din tayi suna dariya ƙasa ƙasa, cikin rada zahra tace "yau mutumin ta baizo ba duk ta wahala , in anyi magana tace bata sonsa Allah ya kiyaye," Asmah tace "aiko dai yau zan gwada ta naga karshen karya,"
Tashi tayi ta fita daga ɗakin tadan labe can kuma ta shigo da sauri hankalinta adan tashe, tana cewa" innalillahi wainnailaihi rajiun, Allah sarki Dr bashir " zahra itama cikin pretending, tace "subhanallahi me ya samu Dr din'. tace "yanzu aka bugo ma mummy wai yayi accident,"
Batool da dama tunda Asmah ta shigo ta miqe daga kwance da take , jin kuma abinda akace yasa ta miƙe a zabure , tana dafe kirjinta dake bugawa da karfi kamar zai fado kasa tace " da gaske kike Asmah? Innalillahi wainnailaihi rajiun na shiga uku na lalace " gani sukayi ta zube akan gado dabass, tana wani irin numfashi kamar zata sume,
Cikin dan tsorata Asmah ta kalli zahra suka hada ido aiba shiri Asmah tace"kefa da wasa nake miki, kawai munyi ne muji bakin ki,"
Dagowa tayi ta kalli Asmah tace"da gaske wasa kike" tace "wlh wasa ne kinji na rantse " ajiyar zuciya ta sauke kafin ta koma ta kwanta rigingine,
.aiko dariya suka shiga kwasa suna mata tsiya , wai wannan wane irin gulmammen soyayya ne, gara inza a fito fili tun lokaci bai ƙure musu ba ehee,
Duk rawan kan batool kasa tanka musu tayi , don da gaske maganar ya dake ta sosai, itadai baza tace ga dalilinta na damuwa har haka ba dan kawai ance bash yayi hatsari, dan ita dai tasan bata sonsa shima kuma yasha gaya mata shi me zaiyi da ita,
Amira kam bata ɗakin tana cen wajen Amir dinta suna hira a main falo, saidai ta dawo aka gaya mata ,me zatayi kuwa itama ba dariya ba , haka suka saka ma batool zafi ranan ,ita ko kasancewar jikin ta ya mutu yasa ta kasa tankasu,
Saidai sukayi mai isarsu suka kyaleta, har ummi dake abuja saidai zahra ta kirata ta bata labari, kasancewar sun dauketa kamar kawarsu basa boye mata komai, itama ummi dariya tayi , tace gulmammiyar banza ku kyaleta kawai nan gaba zata gane kuranta,
Shima bash a nashi bangaren kasa sukuni yayi yau gaba daya bai sakata a Ido ba bai ji muryarta ba ,baiga dan cikulin bakinta dake bala'in burgeshi na murgudawa ba , duk sai yake jinshi kamar Mara lfy,
Kasa daurewa yayi dole ya lalubo wayar shi ya danna ma lambarta da ya dauka a wayar Amir kira,
Tana kwance jiki a mace call ɗin ya shigo wayar ta, ganin number mara suna yasa taqi dagawa har ya katse, sake kira yayi dan haka ta daga, danjin wake damunta a tsohon Daren nan,
Shiru tayi batace komai ba kuma bata katse kiran ba ta dai daga ta kara a kunne,
Daga can bangaren Dr bash yayi sallama, tunkan ya karkare sallaman ta gane muryan shi, take wani dadi ya lullubeta, bata San sanda ta saki murmushi akan laɓɓanta ba
Amsawa tayi, tare da tambayar "dan Allah wake magana" shima acan bangaren yace "pls dawa nake magana".
Miqewa tayi daga kwnacen da take ala dole bata gane shi ba tace "Mallam ya zaka kirani kuma kana tambaya wake magana, bakasan wacece ba ka kira," danne dariyar sa yayi ya dake yace "nima gani nayi anmin flashing da wannan number yanzu , shiyasa na kira naji kowa ke damuna cikin wannan Daren,"
Zaro ido tayi waje jin sharrin da zai mata wai tamai flashing, tace " wlh ya bashir kaji tsoran Allah niban kiraka ba banima da lambarka"
Dariya ya kwashe dashi yace"Ashe dai kin gani ne, ni zaki kawowa rashin M kice wani wake magana, to Dr bashir ne yaro mai farin jini san kowa kin Wanda ya rasa, kyakkyawa ajin farko, ba irin wata ba"
Aiko nan ta shiga kushe shi, shi kuma yana wasa kansa yana tsokanan ta , yana kunna ta bai barta ba kuwa saidai ya sakata kuku, su karan Kansu basu San dare ya tsala haka ba saida suka kashe kiran ,
Washe gari da misalin sha biyu na rana Aslam ya isa school ɗin su Asmah, daidai lokacin ta fito daga, canteen ruwa ta siya ta sha dan kishi takeji, zahra kuma taki rakata wai akwai rana,
Tun daga nisa ya hangota , cikin tafiyarta mai jan hankali, shagala yayi da kallonta kafin kuma a hankali ya furta"ya Allah ka mallakamin wanna baiwar taka badan halina ba Allah badan na isa ba," gani zata wuceshi yasa ya tada motar nufanta yayi gadan gadan kamar zai tureta da mota , har ta gama sadaqar wa ta mutu, ya taka burki a gabanta daf da ita, fitowa yayi ya sha kwalliya sosai cikin kananan kaya,sai zuba kamshi yakeyi, don kuwa saida ya tsaya ya mata kwalliya mai sunan kwalliya sannan ya baza turare ya kamo hanya,
.ganin ya Aslam yasa gaban ta yankewa yayi mugun faduwa, nan ta shiga a'uziyya a zuciya ,
Takowa yayi gabanta ya jingina bayanshi da jikin motar, zura hannaye a aljihu ya zuba mata idanu, itama dai ƙuri tamai idanunta cikin nashi babu alamar kunya ko shakkar shi a cikin kwayar idanunta sabanin da ,da idan ta ganshi ko daga kai bata iyayi a gabanshi balle har ta kalli cikin idanunsa,
Ganin kallon kudan yaƙi ƙarewa yasa tace "lafiya Mallam zaka tsaidani a tsakiyar hanya, inada abinyi fa" ta fad'a cikin hade giran