Header Ads
Showing 129001 words to 132000 words out of 201974 words

Chapter 44 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1717

Ads at the middle of Article

itama ta ɓata rai ta daina kula shi ta fita sabgarshi, ta daina kwana tare dashi, kwana biyu suka kwashe a haka gaba dayan su sunji jiki, ba shiri yace mata yaji ya yarda zai koma aiki, amma sai inzasu dinga yin waya duk bayan awa ɗaya, ba yacce ta iya haka ta amice, amma da sharidin duk kira ɗaya bazai wuce 5 minutes ba, shima haka ya amince, da haka ta samu ya koma office.


Har zuwa wannan lokacin babu abinda ya shiga tsananin su, ta bangaren auratayya saidai zuwa yanzu an samu ci gaba sosai dan sukan sha romance dinsu na fitar hankali, saidai fa iyakar ta nan, ita kanta tana mamakin yadda akayi ya kasa nemanta har yanzu tun abin bai damunta har ya fara dan damunta, har take tunanin anya ma sonda yace yana mata da gaskene kuwa, dan indai akwai soyayyan dole zaiso su zama Abu guda ai, Allah sarki Asmah bata San Aslam yama fita bukatar hakan ba, saidai yana nan akan bakanshi, na cewa saita nemi hakan da kanta tukunna.




Gaba daya Aslam ya manta da wata zee a babin rayuwarsa, Asmah ce kawai a gabanshi a halin yanzu.










Yau gaba daya familin sun tashi da tsantsar farin cike, ba komai bane kuwa face haihuwan da akayi musu gagarumi, yayansu Rabi'a ce ta haihu maman hanifa, ta samu ɗa namiji wannan karon, da safiyar yau mami ta kira su dukkansu daya bayan daya tana gaya musu, duk wacce ta kira ,sai taji ta daka tsalle tana murna tare da tambayarta dama tana da ciki ne, tasan duk abinda sukema wannan tsallen murnan koba komai zasu zo gida zasu haɗu da juna, to ai dole, wata biyar fa ba kwana biyar ba, duk da suna waya da juna, da kuma iyayen nasu......










Oum Ummeetarh
07041130088










Share
And
Comment
Fisabilillah🙏.


💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~




FREE BOOK




{Nasadaukar da wannan littafin ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}






Page 110








Ƴan matan mummy dukkansu sunje sunga babyn ya Rabi'ah sunyi barka, kowaccen mijinta ya kaita saidai cikin rashin sa'a a mabanbantan lokuta suke zuwa, ranar da batool taje ma tana isa Asmah na wucewa, dan Aslam bai barta ta zauna ba, tare suka shiga kuma ko minti talatin basuyi ba yace tazo su wuce, Rabi'ah kam bakin ta sake take kallon ikon god yadda suke wani nannan da juna dan ko da zai zauna saida ya bari ta zauna sannan ya zauna a kusa da ita ya riƙo hannayenta, bakinta cike fal da gulma amma ba daman yi, saboda Aslam daya kasa ya tsare, saidai insuyi su kalli juna ita da abban hanifa dayake shima yana gida lokacin hakan ne ma yasa aslam ɗin shiga gidan,aiko suna tafiya rabi'a ta shiga gulman aslam tana ba abban hanifa labaran diraman da a kasha waɗanda baisan dasu ba, dariya ya dinga yi tare da cewa "ina ruwan baban yaya"zahra ne kawai bata samu zuwa barka ba itama dan tana da nisa ne, kuma ga karamin ciki, Barr tsoro yakeji, hanyar bidda to minna bashi da kyau, yadai mata alkawarin zai kaita da kanshi idan ana gobe suna kuma zai barta har washe garin suna sañan yazo ya dauketa, takoyi murna take ta kira su batool ta gaya musu, nan suke yanke shawaran suma sai ranar da zata zo zasu ƙara komawa tunda zai kama ran aikin suna gashi kuma ranar ummin su zata iso itama.






~ASMAH~








Ranar da ta kama ranar aikin suna, wato ranar asabar, tunda ta tashi da asuba bata ƙara komawa ta kwanta ba saboda ganɗoki, bayan tayi sallah kitchen ta shiga ta fara haɗa breakfast, Aslam na masallaci, koda ya dawo maimaikon ya sameta tana karatun alkur'ani kamar yadda yasaba tarar wa kullum sai yaga ɗakin wayam, fitowa yayi ya shiga nemanta ɗaki ɗaki amma shiru, can ya zo gilmawa ta wurin kitchen yaji ɓuruntun kwanuka, mamaki ne ya kamashi bai taɓa tunanin ganin ta a kitchen a dai dai wannan lokacin ba, balle ma yau da take asabar ba aiki zaije ba, kara sawa yayi da sauri yana mata alamar lafiya me take yi a kitchen yanzu da hannu, don lazimi yakeyi bai da daman yin magana, da fara'ar ta tace" breakfast nake hadawa da wuri, kasan yaune aikin suna inason kafin takwas da rabi na isa cen" bata rai yayi shifa maganar zuwa aikin sunan nan ya fara bashi haushi, ko jiya bata da magana sai zancen zuwa aikin suna har dare, shi har zancen ya gundureshi ma, yaga sai wani rawar kai takeyi zata fita, wai wani takwas da rabi ya mata acen.




Baice mata komai ba saida ya gama lazimin shi ya shafa, sannan yace "karfe nawa kikace zakije aikin sunan ma?" tace "wai da nace ko takwas da rabi ya min a cen, koya ka gani,ko kana ganin yayi latti da yawa" hararan ya wurga mata sannan yace "wato yayi latti ko, to ni nama soke batun zuwa aiki suna, na fasa, matata ba baiwar kowa bace ba wacce zakije kima aiki" jin haka bata San sanda ta iso gaban shi ba, shima sai kawai ganinta yayi, kafin ya ƙara faɗan wata kalma ta haɗe bakinta da nashi, jin haka sai ya kara tallaɓe fuskarta kawai shima, tayi hakane dan karma maganar tayi nisa ya kaishi ga rantsuwa dan yanzu maganar nan daya faɗa gabanta saida ya yanke yayi mummunan faɗuwa,tasan sarai zai aika dan baya kaunar abinda zai rabashi da ita kona minti ɗaya ne, itako baza ta iya jure ya hanata fita aikin sunan nan yau ba, dan tsabar sa abin da tayi a rai har mafarki tayi gata ga yan uwanta ƙawayenta, shiyasa ma yau ta tashi da ganɗokin abin fiyye da yadda takeji jiya.




Saida suka kwashe mintuna masu ɗan yawa suna kissing din juna kafin, ta kwace kanta dan taga alamar baida niyyar saketa, dan Aslam mayen kiss ne baiki suyi awa haka ba, bata kai kanta ba ma ya ta kare balle, dukkansu sauke ajiyar zuciya suka shigayi kamar waɗanda sukayi wasan tsere, yana kallonta da idanunshi da suka canja launi, ya buɗe baki zaiyi magana tayi wuff ta rigashi da dace "dan Allah da manzon sa ya Aslam kayi hakuri kar kace zaka hanani zuwa aikin nan, wlh in ka hanani zazzabi zai iya kamani" yana kallon cikin idanunta ya mika hannu ya dungure mata goshi cikin sigar wasa, tare da cewa "nace baza kije ba koh" aiko inda kuka san ya wanka mata mari, ta fashe da kuka amma daga jin kukan kasan na zallàr shagwane, tsayawa yayi yana kallonta, cikin muryar kukanta da takeyi na shagwaba tanayi tana bubbuga kafa a kasa kamar ƴar yaye, tace "nidai dan Allah dan Allah dan Allah fa nace yayana plsssssssssss" ta kare da jan pls din sosai cikin wani irin siga najan hankali Wanda ita kanta bata San tayi ba.






Wani irin yarr yarr yake ji a jikinshi, gaɓobin jikinshi gaba daya sun amsa gayyatar da take musu, ba shiri ya juya da nufin barin mata kitchen ɗin, don bai gama lazumum shi duka ba yanzu ma karatun alkur'ani yake son yaje yayi, aiko da sauri ta bishi ta cukuikuiyeshi ta baya tare da kwantar da kanta a bayanshi, hannayenta kuma ta zagayeshi dashi, ta daurasu daidai marar shi, kasancewar ya fita tsawo sosai, ba shiri har bakin shi na rawa wurin cewa "naji naji na amince zan kaiki amma tare zamu kafata kafarki kin yarda" jin haka yasa ta shiga tsallen murna tana cewa"yess! Nagode nagode ya Aslam ɗina" aiko tsallen da takeyi sai ta ƙarkare birkita shi, zagayo da ita yayi gabanshi ya daga ta sama cak ya karasa main parlour da ita, girkin da ba'a karasa ba kenan.




Dan suna zuwa falon kan 3 sitter ya direta ya bita ya danne, a zafafe ya shiga aika mata da zafafan romance, duk da ba mayar mai da martani takeyi ba dama, don bata iyawa sai takega kamar zaiga rashin kunyarta, hakan bai dameshi ba, sai da ya rage zafi sosai ya rabu da ita, duk da bawai ya samu yadda yake so bane, gaba daya jikinta ya matu, ita fa ba iya haka taso wasan ya tsaya ba, ji tayi kamar ta kamo shi ta dawo dashi ya sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi amma baza ta iya ba, sai binshi tayi da idanu har ya ƙule ma ganin ta, ji tayi kamar ta tsala ihu,i tafa wannan lamarin ya fara isar ta.




Ɗakin shi ya shiga ya faɗa toilet ya sakarwa kanshi ruwan sanyi, idanunshi a runtse, hannun ya kai yana yamutsa suman kanshi, shi karan kanshi ya gaji a halin yanzu matar shi kawai yake bukata, yana bukatar ƴaƴa shima, yana matukar kauna ya ga kwanshi, kamar daga sama yaji zuciyar na, cewa "duk kai ka jawo wa, kanta wannan bata lokacin, ta yaya zakace kana jiran abinda kasan bazai taba yuwuwa ba, to inzaka yunkara ka yunkura, idan ba haka ba kuwa zaku shekara a haka" da haka ya karkare wankan da zaiyi ya shirya ya fito, koda ya fito falon bata nan, hakan yasa ya nufi ɗakinta a kudundune ya ganta cikin bargo, shima bargon ya ja ya shiga tare da jawota jikin shi, babu Wanda yace ma dan uwansa ƙala kowa da abinda yake saƙawa a ransgi, a haka barci ya dauketa yayinda shi kuma ko alamar gyangyadi baya ji haka ya cinye lokacin barcin safen da tunane tunane, Wanda a karshe ya Samar ma kanshi mafitar da yake ganin zata bulle mai.






Sai gurin sha ɗaya ta farka, lokacin Aslam tuni ya Dade da tashi,lalubashi tayi taji baya kusa da ita, kallonta takai kan agogon bangon dake dakin, sha biyu saura ta gani, salati ta rafka, tare da dirowa daga kan bed din, ta nufo falo, bata gashi ba kawai sai ta nufi kitchen da nufin ta haɗa musu breakfast mai sauki tunda lokaci ya kure har haka, yanzu fa kamata yayi ace tana shirye shirye daura abincin rana, tana shan kwanan hanyar da zai kaita kitchen ɗin tunkan ta karasa taji wani azababen kamshin na mata sallama da sauri ta karasa, ya juya baya hakan yasa baisan da isowarta ba, saiji yayi an rungume shi ta baya, murmushi yayi tare da cewa "kin tashi kenan" amsa ta bashi da "shine baka tasheni ba ko" ta faɗa kamar zatayi kuka yace "sorry bana son na katse miki barcin ki ne" tace "nidai ba wani wayo kawai kamin ɗan ka shirya breakfast ɗin kai kaɗai, kuma dai Allah ya tashe ni, sai ka barmin na karkare,mai gurin yazo mai tabarma ya nade" dariya ya kwashe dashi tare da cewa "kin makaro yarinyar saidai na gobe dan na riga na gama komai sai ci kawai ya rage" taya shi tayi suka kai abicin dining, nan suka zauna zaman ci yace shi zai bata a baki haka sukai ta cin abincin suna wasa kafin su Ankara karfe ɗaya, Aslam da gangan ya dinga mata wayau yana mata mata lokaci dan da gaske baya son fitar nan nata, amma ba yadda ya iya ne kawai.




Haka suka tayin komai a shiririce, basu suka shirya ba sai karfe uku, shima da'ker ta samu yayi wanka, dan da cewa barci zaiyi, gashi kuma su batool da Amira sai kiranta sukeyi anjita shiru, saida ta saka mai kuka, sannan ya mike kenan.




Koda yayi parking a kofar gidan ya Rabi'ah, da'ker ya bari ta shiga ciki, da cewa yayi ma zai jirata harta gama ta fito su tafi, saida tayi ta roƙonsa ya yarda zaije ya dawo, amma saita mai kiss, zaro ido tayi tana bin inda suke da kallo, ga mutane na gilmawa jefi jefi wasu a ƙafa wasu a mota, ga glass ɗin motar su farine ana iya ganin mutum kuma a sauke yake ma, ganin tayi shiru yace "uhummm ke nake saurare" wani dabara ne ya fado mata tace "na yarda amma nima da sharadi, zaka rufe idanunka tukum" bai kawo komai a ranshi ba ya rufe ido tare da cewa "oya bismillah" hannun ta takai saitin idanun shi tayi weaving taga bai motsa ba alamar dai ya rufe idon da gaske, miƙa hannu tayi ta buɗe kofar da sauri ta fice daga motar tana mai dariya, jin haka yasa ya bude ido, shima dai dariyar ya shigayi kafin cikin ɗan daga murya yadda zataji shi yace, "zakiyi bayani ne yarinya gobe ma ranace," gwalo tamai tare da shigewa get din gidan, saida yaga ta maida kofar ta rufe, sannan ya tada motar shi, yabar kofar gidan direct kuwa asibiti ya nufa gurin Dr bash dan sun kwana biyu basu hadu ba saidai a waya.




Gaba dayansu suna zaune a falon zagaye da umminsu da batayi awa daya da isowa ba, Asmah ce kawai babu a cikin su, fira akeyi cike da zakuwa da farin ciki da marmarin ganin juna.


Tun kafin ta karasa bakin kofar shiga main parlourn ya Rabi'ah takejin hayaniya da surutunsu na tashi, cike da zakuwa ta karasa baking kofar da sauri har tana dan haɗawa da gudu, gani tayi kofar a bude yake hakan yasa bata tsaya wahalar yin knocking ba ta faɗa falon bakinta dauke da sallama, daidai lokacin da ummi ke cewa Rabi'ah mikomin wayata na kira Aslam ɗin naji ko lafiya har yanzu bata iso ba, saijin sallamanta sukayi kamar daga sama.......






Oum Ummeetarh
07041130088














Share
Comment
Fisabilillah🙏.


💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~




FREE BOOK






{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}










Page 111






Cike da tsananin zaƙuwa dukkansu suka mike tare da rige rigen yi mata oyoyo, ƙamƙame juna sukayi gaba ɗayansu, suna tsalle kamar wasu ƙananan yara, ko nauyin jikin su basaji.


Sauran yan tsurarrin mutane dake falon tuni suka bar abinda sukeyi suka shiga kallonsu, sake juna sukayi kafin kuma ta shiga binsu ɗaya Bayan ɗaya tana rungumewa, lokacin data rungume Amira kam tsayawa tayi jin tudun Abu ya tokareta, dagowa tayi ta matsar da ita baya kaɗan tana ƙare mata kallo, tun daga sama har ƙasa, gane abinda take kallo yasa Amira saurin kai duka tafukan hannayenta ta rufe fuskarta,Asmah ta bata kunya, kuma ga ummi a wajen, dariya ta kwashe dashi, tare da cewa "kaiii masha Allah Abu yayi kyau aure yayi albarka"






Ummi dake kallonsu tana murmushin ganin abin nasu bana ƙarewa bane yasa tace "to ya isa haka ku kyalemin ƴa tazo ta gaisa da umminta," sai lokacin Asmah ta lura da ummi aikam dai kwasa da gudu tayi ta faɗa jikin ummi dake zaune kan kujera, ta ƙamƙame, tana tsallen murna, ummi kam cewa take "yi a hankali Asma' u karki kada umminki" ina ko sauraren ummi batayi ba, saida taji muryar ya Rabi'ah a bayanta tana mata magana sannan ta sake ummin ta dago fuskarta fal farin ciki, duk sunyi cirko cirko a tsaye suna kallonta kowacce cikin matuƙar farin ciki.




Ya Rabi'ah tace, "yayi kyau wato ta ƙawayenki da umminki kawai kikeyi ko" ƙarasawa tayi ta rungumeta itama tana cewa "sorry yayana kema ai zan dawo gareki" ummi kam sai binta takeyi da kallo kuri, i tafa ta hanga ta hango bataga wani alamar cikin a jikin Asmah ba, idan idanunta ba karya suke mata bama sai tace taga kamar har yarzu a virgin dinta take, dan daga yanayin tafiyarta kawai ta gane hakan, dan ummi Allah ya mata wani baiwa irinsu ne matan da da summa mace kallon ɗaya suke gane yanayin da take ciki, shiyasa kallon ɗaɗɗaya tama su zahra ta gane kowacce nada kunshi, gabanta ne ya faɗi, jin tunanin daya faɗo mata arai na cewa to kodai har yanzu basu sasanta bane, tabdijam aiko da sake, bari dai ta natsu koma meke ciki zantaji.




Zama sukayi nan gaban ummi aka shiga firan yaushe gamo kowa na fadin irin yadda yayi missing din sauran ana dariya, batool ce ta kalli zahra ganin, yadda taketa zare idanu, yunwa takeji dan tunda ta samu cikin nan da taci abinci ko awa bata iya kaiwa zataji cikinta kamar anyi yasa, gashi daga zuwanta aka bata abinci taci, bai wani daɗe ba, gashi bata son tace zataci abinci kar suyi zargin wani Abu,dan kuwa a irin tulin abincin data narka ɗazu, idan tace tana, jin yunwa yanzu dole su saka mata alamar tambaya, itako baza taso haka ba, son kunya takeji , tunda tazo taketa muku muku da abinta, tunda cikin bawai ya fito bane, na Amira ne kawai ya fito sosai saiko na Khadijah wanda shima idan mutum ya kura ido zai iya gani, saidai fa ta makaro don tuni ummi ta gane kaf ciki ne dasu saidai bata nuna ma ta gani ba, batool tace "kekuma lafiya, kiketa muzurai kamar me jin kashi" hararanta tayi tare da cewa"A'a maijin zawo dai" dariya su Amira suka kwashe dashi, ummi tace "oh Allah na gode maka ni Amina, anyi aure, yau watan ku biyar rabonku da ganin juna amma hakan baisa kun fasa wannan hali naku ba ko, kullum kamar masu ganin hanjin juna minti biyu shiri minti biyu faɗa"batool cikin dariya tace "ummi kalla fa yadda take yamutsa fuska tana muzurai kuma kawai dan na tambaya sai ya zama laifi" ummi tace "to aikena bakiyi tambayar a mutunceba, ya zakice mata kamar maijin kashi" batool tace "wlh ummi nayi missing ɗinta ne sosai so nake mudan tuna baya" dariya suka sa dukkansu ummi tace "to kin kyauta" Zahra kuma tace "kedai wlh baza ki canza ba"Khadijah ce ta faki idanunsu ta saka hannu cikin dan pos ɗinta da tunda tazo yake kamkame a hannunta ta ballo farin kasarta(kalba) ta afa a baki tana tsotsa a hankali,Asmah data lura tace "sisto abin kuma

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads