Header Ads
Showing 132001 words to 135000 words out of 201974 words

Chapter 45 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1727

Ads at the middle of Article

yar haka ne, wani daɗi kika samune, kike ci ke kadai, to kowa yaci shi ɗaya ya mutu shi ɗaya" zaro ido Khadijah tayi jin Asmah daga zuwa zata tona mata asiri tun dazu take Ballan abinta babu Wanda ya lura sai ita, Amira tace"haba shiyasa tun dazu nakejin kamshi na buso ni to a sammana, tunda sai mun roƙa " ta faɗa tana mika hannu zata dauki pos dinta dake ita ke kusa da ita, aiko saurin tayi wuf zata kamkame abinta, saidai cikin sa'a Amira ta rigata fisgewa, cakumota tayi zata amsa da sauri ta wurgawa ya Rabi'ah, aiko tana caɓewa ta balle botir ɗin pos ɗin ta saka hannu a ciki, saiga farin kasa cike da Santana.




Daga ledar tayi tana nuna musa tare da cewa"Lalalalaaa kice abin yazo inji mai tsoron wanka, masha Allah naga biyu, kice gaba nan gaba inada suyan rago kashi kashi, saura su O'o da O'o, Allah ya raba lafiyar mrs kamaludden " tuni Khadijah ta saka kanta a cikin cinyoyinta ta dunkule wuri daya, duka dariya suka saka mata, suna tsokananta ta kasa dagowa saboda ummi, ummi kam dake musu dariya ganin abin zaiyi yawa sun sakata gaba karma batool da tafi zakewa yasa tace"kyale su oh Khadijah, ai bake kadai nabe naga kema batool ai cikin ne dake ko?" da sauri batool ta dago tana kallon umminsu, zaro mata ido ummi tayi tace"eh haka nace kema cikin ne dake ko nayi karya," kasa bata amsa batool tayi, ta maida kallonta kan zahra tace "dakema zahra" aiko dai zahra tayi tsuru tsuru Ashe duk boyon banza takeyi tun ɗazu, ummi taci gaba da cewa "a toh naga gara ayi tone tonen tunda haka kuma zaɓa, ga Abu a jikinku kuma, amma kun take kun saka min ƴa a gaba" shiru kakeji batool baki ya mutu, ya Rabi'ah kam guɗa ta daddage ta rangaɗa iya karfinta, kafin tace "masha Allah alhmdllh, waiko mummy Nada wannan labarin kokuma ni zan fara mata albishir," ummi tace "ta ina zata sani nima duk yanzu na gansu da abubuwan su" ya Rabi'ah tace"to ummi banji kinyi lissafi da madam misisi ba matar oga" kallon Asmah ummi tayi tace "kai ita naga kamar babu ko?" ta fada tana kallon Asmah alamar ita take tambaya, ya Rabi'ah kuwa kallon Asmah tayi ta rike haba tare da cewa "ke ko ma'ulle me kika tsaya jira haka, ake neman a barki a baya," ummi tace "barni da ita, zata gaya min bayani ne anjima" ta faɗa tana dan haharan Asmah, Wanda ita kaɗai ta fahimci hararan me ummi ke mata, duk tasha jinin jikinta dama tun da taji kowa nada ciki banda ita jikinta yayi sanyi.




Zahra kam silalewa tayi ta shiga kitchen, ta samu abinci a nan ta zauna ta shake flate ta hau ci, koda ta fito duk sun shiga ciki don yin sallan la'asar da, aketa kira, itama cikin ta nufa, a dakin da ummi ta sauka ta samesu suna sallah.




Bayan sun idar zahra tambayar ya Rabi'ah tayi ko akwai aikin da Za'ayi ne, ya Rabi'ah tace "ba wani aiki duk ayyukan ba'anan za'àyi ba a can family hause dinsu za'ayi raɗin suna, duk abinda ya shafi raɗin sunan a cen za'ayi, ni kuma nawa abinci yourbawa zasuyi,saidai ko ku jera drinks da ruwan da aka kawo dazu a fridge kubi duka fridge din da kuka sani a gidan nan ku cikashi da ruwa da drinks harda na dakunan bakin cen dake rufe Na waje, bari Na Baku keys " ta faɗa tana mikewa ta dauko keys din a cikin side drower ta mikawa Amira, amsa tayi tace "to kumuje mu gama ko kafin fira ya barke mu kasa tashi" zahra tace "aikuwa dai muje" miƙewa sukayi zasu wuce Ummi Na zaune kan pray mat tana addu'a, gyaran murya ta musu duk suka juyo suna kallonta,nuna Asmah tayi sannan ta mata alamar ta tsaya ita, cikin sanyi jiki ta dawo ta zauna a bakin bed, gaba ɗaya walwalarta ya ragu, haka kurum takeji kamar ta aikata wani zunibi ne, ganin duk yan uwanta da aka musu aure tare suna da juna biyu amma ita har yanzu tana nan matsayin virgin bama akai ga maganar ciki ba tukunna, su batool kuwa tafiya sukayi suka kama aikin da zasuyi.






Bayan ummi ta idar ta shafa addu'an bata rai tayi sannan ta juyo ta kalli Asmah, ganin yanayin fuskar ummi saida gabanta ya faɗi, da gani tasan babu wasa a fuskarta, umminsu kenan Zuma ga zaki ga harbi, ita kuma ummi tayi haka ne dan ta samu Asmah ta faɗa mata gaskiyar abinda take son sani don idan ta sake mata fuska zata iya mata karya duk da ba halinta bane karya, zataji kunyar gaya mata wasu abubuwan idan taga dariya a fuskarta.






Cikin dakakkiyar murya tace "wato bakiji maganar dana gaya miki rannan ba ko, wai yaushe kika zama mai kunnen kashi ne Asmah, bansanki da wanna halin bafa" take idanun Asmah suka Tara kwalla, ummi bata saurareta ba taci gaba da cewa "wato ke baza'a miki magana kiji ba ko, kin tsaya shashanci da sunan baki son miji kin manta da abinda ke gabanki ko, waya gaya miki ana wannan yayin yanzu, ko mutanen da, da suke da duhun kai basuyi wannan kauyancin ba balle ku yaran yanzu da kuke a waye, Na gaya miki rannan namiji duk sonda yake ma mace idan bai samu kulawarta ba wlh soyayyar nan bacewa takeyi bat a zuciyar shi, take zakiga ya fara hangen wata, to balle naki ma da yake da wata matar a gefe, wlh idan ya gaji ajiyeki zaiyi a gefe ya dawo da matar shi, shikenan kin shiga uku, keda mijinki saidai hange daga nisa" nan fa ummi ta rufeta da fada ta inda take shiga bata nan take fita ba, don ita duk a tunaninta har yanzu Asmah bata ba Aslam dama bane, tunda gashi har yanzu auren nasu bai cika ba.




Tuni Asmah ta duƙar da kai kasa ta fara kuka harda sheshsheka, jikinta ya ƙara yin sanyi musamman da ummi ta tuna mata da zee, saida taji ummi tayi shiru sannan ta dago kai idanu gaja gaja da hawaye, cikin muryarta mai dauke da amon kuka tace "umminmu wallahi tallahi abinda kike tunani ba haka bane, wallahi ummi tun daga ranar da kikamin magana, komai ya fara daidaita a tsakanin mu" katseta ummi tayi da cewa "rufe min baki karya kikeyi, idan komai ya daidaita mai yasa har yanzu babu abida ya shiga tsakaninku ta fannin auratayya" cikin kuka tace "wallahi ummi ba laifina bane , ba daga gurina bane matsalar wallahi ba daga ni bane" ummi jin ta fara kamo bakin zaren yasa ta kara bata rai tace "to daga waye" ganin ba wasa a fuskar ummi yasa batayi tunanin wani batun kunya ba tace "shine bai taba nuna yanaso ya kusanceni ba" ummi cikin zaro ido jin abinda Asmah tace dan ta ji tsoro kar ace baida isashen lafiya ne tace "ban gane ba kina nufin kodan romance haka dasu dan kiss bai taba yi miki ba" Asmah tace "yana duk wannan amma bai taba wuce haka ba, koni abin Na damuna umminmu"




Gyara zama ummi tayi a bakin bed, tufka takeyi tana warwarewa,a zuciyarta, ta yarda da batun Asmah Na cewa sun daidaita, tun daga yanayin yadda Asmah keta zuba mata rantsuwa, kuma ta gamsu Aslam kalau yake tunda yana da sha'awa, tunda gashi har yana iya wasanni da ita, to daga ina matsalar take ne? Jin amsar da zuciyar ta ya bata yasa ta juyo da sauri ta kalli Asmah tare da tsatsare ta da idanunta masu kaifi a kansu tace,"ya taɓa nuna yana bukatar kusantarki koda so ɗaya ne kin hana" da sauri Asmah ta girgiza mata kai, a fili ummi tace "A'a to meke damun son ne wai" shiru tayi ta dafe kai, cen kuma tace "to ko yana nufin cewa ke zaki fara neman shi" shiru Asmah tayi don bata San amsar da zata bata ba, ganin bata bata amsa ba hakan ya tabbatar mata da cewa bata San amsar da zata bata bane, tace "aiko dai idan ma hakan yake nufi to kuwa yayi wauta dan kuwa hakan bazai taba saɓuwa ba wai bindiga a ruwa inji hausawa, dole shizai fara nemanki don wannan ba tarbiyar mu ta Mallam bahaushe bane, sai kace wasu ƙabilu,zamuyi maganin shi, inyasan wata ai baisan wata ba"




"Ki bani hankalinki da kyau, ki amsamin tambayata, idan kuna wasannin kina mayar mai damartani ne?, girgiza kai Asmah tayi kafin tace "A'a ummi bana iyawa kunya nakeji" ummi tace "OK hakan ma yayi, to kina jin alamar abinshi ya miƙe idan kuna wasan" dagowa tayi bata gane me ummi ke nufi ba hakan yasa tayi shiru"ki bani amsa nace kinajin alamar abinshi yana miƙewa so nake Na tabbatar kalau yake dan insane irin matakin da zan dauka" Asmah cikin rashin fahimta tace"ummi wani Abu" daƙuwa ummi ta mata tare da cewa "gidanku Asmah, kibani amsa ba wasa nakeyi dake ba, nace kina ji ko ganin abin shi Na maza abin fitsarin shi nake nufi, kinaji yana yin karfi idan kuna wasa" sai lokacin Asmah ta fahimci ummi, take wani irin kunya ya lulluɓeta ba shiri takai tafukan hannayenta ta rufe fuskarta ganin haka yasa ummi cewa aɗan kausashe "zanci gidanku fa ki bani amsa, ko kinga wasa a idona" girgiza kai tayi still idanunta na rufe, ta tuna sometimes takanji abin ya miƙe ya zama ƙato yayi karfi kamar katako, har taji yana zungurinta wani bin, duk da dai bawai ta taɓa taɓawa bane, ,takanyi mamaki, har ta tambayi kanta to dama haka nasu yake da karfi ko kuwa nashine haka, da'ker ta daure tace "umminmu ban sani ba amma shidai nashi abin yana da karfi sosai kamar katako " tafa hannu ummi tayi tare da cewa "to wlh garau yake wulakanci ne so yake ya ƙure ki, to kuwa saidai ke ki ƙure shi, ina fatan set din kayan da addawiyya ta haɗa miki suna nan baki kyautar ba" Asmah tace "eh ummi suna nan banma taba buɗe kwalin ba" ummi tace "yawwa to yau inkin koma gida ki kulle kofarki, dakyau ki farke kwalin duka kayan ki daukomin hotonsu a wayarki gobe kizo dasu zan nuna miki waɗanda zakiyi amfani dasu, sanna zan buga ma anty maryar muktar yar zamfara ta aiko min da turaren (kokaƙi Allah) dashi zamu yi amfani ta ruwan sanyi duk taurin kanshi, saiya sauke shi, ke ko aljanu ne ke hanashi sai sun sake shi a lokacin, yanzu bari na baki tsarabar dana zo muku dashi, tunda naga sauran duk suna da kunshi, kene me bukatar su a yanzu, wani ƙaton jaka ta dauko ta buɗe take ta shiga fito da magunguna, magungunane masu kyau da inganci Wanda tayi orden su a gurin anty maryam muktar ana saura kwana biyu zata zo, amma ba bata lokaci har kayanta ya iso cikin sauƙi, nan ta ba Asmah waɗanda tasan ya kamata tayi amfani dasu tace taje ta fara sha kafin goben tazo da hotunan waɗancen na gurin ta,amsa tayi tana yamutsa fuska ganin haka yasa ummi cewa "bani nan da ganin yadda kike yamutsa fuska ba abin arziki Zakiyi ba", da kaina zan dinga baki, waɗanda zata iya sha a nan take ummi ta ritsata tasha sauran da sai anjima kuma ta saka mata a jaka tare da ja mata kunnen akan ta tabbatar tasha a gida .






Daidai nan su zahra suka dawo, batool tace tana bin kayan magungunan dake barbaje a ɗakin da kallo "wai ummi ƙusƙus din me kukeyi ne tun dazu fiyye da awa ɗaya" ya Rabi'ah kam cewa tayi"ayya ummi wato tunda kinfi ɗasawa da ya Aslam shine kika ware tashi matar kike gyara mashi ita mu kuma ko oho ko" dariya Rabi'ah ta bata, ummi tace "eh mana ai zamanin kowa kanshi ya sani nima ɗana kawai na sani," kallon Amira da Khadijah tayi tace "ku kuje gurin mummy ta gyaraku, itace sirikarku" batool tace "to mu gurin wa zamuje umminmu" ya Rabi'ah cikin dariya tace kowa taje gurin uwar mijinta, daƙuwa ummi tama ya Rabi'ah, sannan ta kalli su batool tace " daughters ni zan gyaraku, to kuma naga kowacce taci wake ta koshi, ya za'ayi kenan, amma dai bari na gani ko akwai irin naku" wani ummi ta dauko a roba anyi sillin din bakinshi ta mikawa batool, zahra tace "ummi nifa" ummi tace ke bazan baki shi ba saboda bake kaɗai bane gurin Barr in nabaki zamu shiga hakkin maryama, kukan shagwaba zahra tasa tana diddira ƙafa tace "ummi don Allah ki bani sai Musha tare da ita ai" tafa hannu ummi tayi tare da cewa "iyyee yaran mummy fa angirma" batool dake dudduba robar maganin da ummi ta bata cak ta tsaya tare da dagowa ta kalli zahra dake kukan abata itama tace"wait zahra naji kamar kince a baki magani kuje kusha da kishiyar ki?" Zahra ta harareta tare da cewa "haka nace what is ur problem" dariya batool ta kwashe dashi tana nuna zahra cikin dariya take cewa "kuji wani ɗiɗiɗi, yau naga zallar iyayi da neman suna,lallai zahra baki da hankali kishiya zaki ba kayan mata ta sha" su Amira da Khadijah kam batool ce ta basu dariya, nan suka shiga yi, ummi ma saida ta gama cin dariyarta sannan tace "to ina ruwanki batool, zaman lafiya ne ya kawo haka, koba haka ba zahra " ummi ta karkare maganar tana kallon zahra data cika fal tana aunawa batool harara, nan kuma aka koma caftar kishiya da kishi, batool na basu labarin budurwar Dr bash, data nace tana sonshi wai ita Dr basira, nan ta shiga basu labarin diraman da suke kwasa da Dr bash akan basira suna ta shan dariya gwanin sha'awa, ummi na jinsu kawacce na kawo nata firan da abinda ya shafi nata gidan, ummi na jinsu duk in taji abinda zata gyara masu ta gyara musu , tana yi tana kara koyar dasu dabarun zama da miji da yadda zasu samu rabo duniya da lahira, a haka aka kira mangariba suka tashi domin zuwa su gabatar da sallah.






Bayan ya ajiye Asmah bai zame ko ina ba sai asibiti gurin Dr bash, saida ya shiga harabar asibitin yayi parking sannan ya daga waya ya kira shi, yana dagawa yace "gani na kawo maka ziyara asibiti" Dr bash dake zaune a office ɗinshi ɗaga kai yayi ya kalli harabar asibitin, inda ake parking motoci, aiko idanunshi ya sauka kan motar Aslam, sai lokacin ya yarda, don da jinshi kawai yayi, aiko cikin son ya jashi yace, "aiko dai ka makaro, dan yanzu nabar asibiti, kaima, kayi ganganci kasan yau weekend ne ba kowani time zaka sameni a asibiti ba" Aslam da idon shi kekan motar Dr dake fake a kusa da shi yace"to shi kuma motar nan na uban waye, Mallam karka raina min hankali mana" dariya bashir ya kwashe dashi yana cewa "ta kaima irin wannan ziyara haka ba notice" Aslam yace "to ko na koma ne" da sauri bashir yace "ni na isa nace ka koma yi hakuri ka karaso babban yayan mu" kashe wayar yayi batare da ya amsa mashi ba, ya fito ya kulle motar shi tare da nufar cikin asibitin.........














Oum Ummeetarh
07041130088












Share
And
Comment
Fisabilillah🙏.
💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~




FREE BOOk






{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}








112






Yana shiga office ɗin Dr bash ya taso da sauri hannun shi rike da hanky ya shiga kakkaɓe mai kujeran dake gaban table ɗinshi, yanayi yana faɗin "sannu da zuwa babban yayan mu, sannu da zuwa sannu da zuwa maraba maraba lale lale" da jin ma yadda yake maganar kasan harda shaƙiyanci a cikin lamarin, yana gama kakkaɓewa yace "bismillah yaya ga gurin zama" Aslam bai tanka shi ba ya nemi guri ya zauna, fridge Dr bash ya nufa ya ɗauko mai ruwa da lemon kwalba da cup ya ajiye mai, sannan ya nemi guri ya tsuguna ta gefen Aslam, harda wani duƙar da kai, irin dai yadda ake gaisar da sirikai, cike da ladabi kamar da gaske yace "barka da yamma yaya, an wuni lafiya ya aiki ya iyalai, ya ɗoƙari" Aslam kam shiru yayi ya kasa amsawa a ranshi yana jinjina shaƙiyancin bashir, jin shiru Aslam bai amsa shi ba yasa ya dogo ya kalle shi tare da cewa "yaya a dai ta hakuri damu bansan laifin da nayi ba baka amsa gaisuwata ba," share shi Aslam yayi bai tanka ba saima wayar shi da ya zaro a aljihu ya shiga lalubar lambar Asmah, bashir ƙin tashi yayi a tsugunen,kallo fuskar Aslam yakeyi yana karantar shi, sai yake ga kamar akwai damuwa a tattare da shi, Aslam kuwa share shi yayi, ganin haka yasa bashir miƙewa tare da cewa "wlh Aslam kai mugun dan air ne, " kallon shi yayi ya watsamai harara tare da cewa "har nakai ka, ai baka cika babban dan iska ba tunda ka tashi ai na ɗauka a wurin zaka kwana" dariya Dr bash ya kwashe dashi, yana zagayawa ya zauna a nashi kujeran irin mai jujjuyawa da mutum ɗin nan, yace "to yane meye labari kwana biyu saduwa tayi wuya" Aslam yace "wlh Abubuwan ne yanzu sai a slow" Dr bash yace "wlh fa sai a hankali, to ya amarya ya Amarci, fatan dai anci Amarci lafiya" kallon shi Aslam yayi "tare da cewa ina ruwanka, tunda kai kaci naka ai shikenan" dariya Dr bash yayi tare da cewa "faɗi ka kara naci sosai kuwa inama tsakiyar cine yanzu haka, kaii aure da daɗi wlh nake gaya maka ma Mallam, abin sai wanda yayi, my teema duniya ce" hararan da Aslam ya watsamai yasa yayi sauri daura hannu a baki,

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads