Showing 120001 words to 123000 words out of 201974 words
Chapter 41 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
hankali, ta sani ya kamal ya haramta a gareta, tunda ya kasance a yanzu mijin yar uwa kuma kanwarta,amma yadda ta kwanta tana tunanin shi barci ya kwashe ta yasa har take mafarkin shi, kallon agogon dake manne jikin wall din dakin tayi biyu harda minti 10, lokacin tuni har an idar da sallan azahar a masallatai, alwala ta dauro ta fara gabatar da sallah, bayan ta idar kuma ta koma ta kwanta, Aslam ne ya fado mata a rai, ji tayi gabanta ya yanke ya fadi, samun zuciyarta tayi da son sanin wani hali yake ciki yanzu, take taji zuciyarta na azalzalan ta akan ta tashi ta fita ko ganin shi ne kawai tayi, da'ker ta samu tayi yaki da zuciyarta ta tayi fatali da wannan umarnin da take bata, wayar ta ta dauka ta kunna data ta shiga WhatsApp d'inta Wanda rabonta da shi yafi sati, message na gama shigowa ta fara bi daya bayan daya tana dubawa Wanda zata amsa tayi Wanda zata share ta share, haka har takai kan message d'in Khadijah, budewa tayi, idanunta ne ya sauka akan wasu zafafan hotunan da Khadijah ta turo mata yau kimanin kwana uku kenan, hotunan ta ne ita da kamal masu shegen kyau, kala kala cikin wanin irin yanayin da ita kanta baza ta iya fassarashi ba take bin hotunan da kallo, gasu fess da su sunyi wani fresh shar dasu, kallo daya zakama hotunan kasan ma'abota hotan cike suke da tsantsar so da kaunar junan su, yanayin murmushin dake dauke a fuskokinsu kadai ya ishi mai kallo shaidar hakan balle kuma idan ka kalli yanayin styles d'in hotunan, a kasan hotunan ta rubuta, "komai ya daidaita a tsakanin mu yar uwata fatan kema haka daga naki bangaren"
Bata sanda ruwan hawaye ya fara wanke fuskar ta ba sai gani tayi yana diga akan screen d'in wayar, ta bata lokaci akan kallon hotunan fiye da awa daya, can kuma Kamar wata tabbabiya ta saki wani kayataccen murmushi, a fili ta shiga furta "na taya ki murna yake yar uwata Khadijah, hakika Allah ya baki miji daya tamkar da dubu, Allah ya zaunar daku lafiya,ya Allah wannan soyayyar junan su da na gani kwance akan fuskokin su Allah ka dauwamar musu dashi har abada" reply ta mata da "wow masha Allah, perfect mach, gsky hotuna sunyi matukar kyau yar kanwata, tunda nake ban taba ganin couples d'in da suka yi marching sosai da juna irin wadan nan ba, kyawawan masoyan asali, Allah yabar kauna romeo & Juliet " a karshe ta kawata rubutunta da emoji kala kala, na murna dana murmushi tayi sending, sauka tayi a WhatsApp din ta koma gallery folder daya ta ware na hotunan kamal zallah, take ta shiga folder ta fara deleting d'in duk wani photo da ta Sani na shi dake wayarta, yadda take deleting hotunan shi haka takeji yana fita a zuciyarta, saida tayi deleting duk wani abu daya shafi kamal a wayarta, daidai da app da tasan shi ya saka mata a wayar saida ta goge dan kar ta dinga tunawa da shi, bata bar komai ba hatta da phone number dinshi saida tayi deleting a wayarta, take taji zuciyarta ya samu wani irin space mai girma wanda a da babu shi a zuciyarta ta, lallai kamal ba karamin wawakeken gurbi ya samu a zuciyar ta ba,wasai take jin kanta a yanzu babu kowa a zuciyarta.
Wayar ta da yayi ringing ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, sunan da ta gani na yawo a saman screen d'in wayar yasa bata san sanda ta saki kayataccen murmushi ba, cike da dauki ta daga wayar tare da cewa "Assalamu alaiki yake ummin mu" daga daya bangaren ummi tayi murmushi mai sauti sannan ta amsa mata da "wa'alaikissalam Asma'ul-husnah fatan kuma lafiya ya my son yake da fatan ana kula da shi sosai ko" murmushi tayi cike da jin kunyar maganar ummi tace "yana lafiya umminmu" ummi tace " masha allah yana gida ne ko ya fita don nata kiran wayar shi yanzu kafin na kira naki bai daga ba" Asmah tace "gsky bansan ko yana nan ba ko ya fita" ummi cikin zare ido tace "na shiga uku ni Aminatu, ban gane bakisan ko yana nan ko ya fita ba" Asmah cikin ko in kula tace "wlh umminmu ni rabona da shi tunda safe" ji tayi ummi ta rabka wani uban salati, kafin tace "Asma'u! kardai kice min zaman da kukeyi kanan ke da Aslam d'in wata da watan ni, Ashe baki da wayau ke shashasha ce ban Sani ba" tuni Asmah ta shiga zazzaro ido jin kalmomin dake fitowa daga bakin ummi, take ummi ta rufeta da fada ta inda take shiga bata nan take fita ba, hankalin Asmah bai kara tashi ba saida ta tsinci muryar ummi na cewa "nasani, nasan abinda yasa kika ki bama Aslam dama duk da irin tarin soyayyar daya yake miki, kamal ne ko? To wlh ki kama kanki dan kamalu tuni ya shafe babinki, yanzu haka zancen da nake miki Nana Khadijah ciki ne da ita har na wata biyu, ke kina nan kin tsaya wasa da daman ki " tuni hawaye ya gama wanke fuskar Asmah, cikin muryan kuka ta bude baki tace "ummi wlh b" cikin tsawa ummi ta katseta da cewa "wlh me? ni babu abida zaki gaya min a yanzu, ki Sani shi so da kike gani tamkar tsuntsune dake sauka akan bishiya domin yayi kiwo, idan ya sauka a bishiya ya rasa abin da zai kiwata dole zai fira daga wannan bishiyar ya koma wata, idan kuma ba'ayi a hankali ba bazai sake wai wayar wannan bishiyar ba kenan har abada, idan zaki kama kanki ki kama, Aslam yayi miki laifi mai girma a baya kuma ya gane kurensa, tunda kika ga Allah ya sake hada ku a karo na biyu shi kadai yasan abinda ya boye a tsakanin ku, kiyi hakuri ki rungumi kaddararki da hannu bibbiyu, bari na tuna miki wani abinda kika manta kinsan dai bake kadai bace mace a gurin Aslam ba ko? ina fatan kina tune da zainab" take gabanta yayi wani irin faduwa,jin abinda ummi ta fada tabdijam har ga Allah ta manta da wata zainab matar Aslam, wahayenta ne suka kara karfin gudu, take ta kara yunkurin yin magana dan ta kare kanta, ummi lura da ta yi jikinta ya gama yin sanyi yasa wannan karon ta bata daman cewa wani Abu, baki na rawa tace"wlh umminmu ba abinda kike tunani bane, wlh ummi a halin yanzu babu burbushin soyyayar ya kamal ko digo a zuciyata," take kuma ta shiga bama ummi labarin abinda ya faru yanzu yan mintocin da suka gabata, kasancewar basa iya boye ma ummi komai dake damunsu a rayuwar su.
Sauke ajiyar zuciya ummi tayi yanzu hankalin ta yadan kwanta jin hakan daga bakin Asmah, tasan komai zaizo sa sauki tunda babu kowa yanzu a zuciyarta, kwantar da murya ummi tayi cikin sigar lallashi ta fara cewa" alhmdllh naji dadin jin wannan maganar daga bakin ki Asmah, yanzu kuma lokacin yayi da zakiba Aslam dama domin ya mallaki wani fili daga zuciyar ki, Aslam yayi miki laifi kuma ya gane kurensa a halin yanzu ya kamata ki saurare shi, tunda kikaga haka Allah kadai yasan menene ya boye a tsakanin ku, kuma nasan keme bazakice a yanzu bakijin Aslam ko kadan bane a ranki, ko nayi karya?" Ummi ta tambaya, shiru Asmah tayi ta kasa bata amsa, dan kam idan har tace batajin shi a ranta yanzu tayi ma Allah karya, jin shiru yayi yawa yasa ummi tace "uhummm ke nake saurare fa" cikin sanyin murya tace "umminmu a halin yanzu wlh bana jin kin yaya Aslam a raina kuma kai tsaye bazan iya cewa ina sonsa ba,nasan dai ina jin matsanancin tausayin shi a raina, kuma nakan ji kewan shi idan baya kusa dani bayan wadanan, bazance ga wani Abu da nake ji game da shi ba Ummi" murmushi ummi tayi a daya bangaren a zuciyarta tace ahaf magana ya kare, a fili kuma tace "naji hakan ma wani ci gaba ne da sannu zaki soshi, amma fa sai kin saka ma ranki hakan, nidai yanzu abinda nake so dake, idan har bakyaso nayi mummunan fushi dake, na baki nan da sati guda naji kyakkyawan sauyi, a zaman takewarku, idan kuma ba haka ba wlh zanje na samu Alhaji baba, da mallam na gaya musu, sannan kuma na samu mummyn ku da daddy na gaya musu suma, kinsan dai wanene Aslam a gare su baza suji dadi ba idan sukaji abida kike masa" girgiza kai takeyi kamar a gaban ummi take, ummi nayin shiru ta shiga cewa a firgice "dan Allah ummi kiyi hakuri kar ki gaya musu Wlh zan sauya, insha Allah zan karbi kaddarata da hannu bibbiyu" wani wahalallan ajiyar zuciya Ummi ta sauke sannan tace "alhamdulillahi naji dadin hakan, kuma ina nan ina tsumayen jin daddadan labari, nifa so nake kafin shekara ta zagayo kowaccen ku ta ajiye min jika, inso samu ne ma yan bibbiyu ko uku uku nake so" dariya Asmah ta kwashe dashi, daga nan kuma ummi ta shiga janta da wasa kamar wasu kawaye , karshe kuma ta shiga koyar da ita dabaru kala kala wadan da zasu amfaneta sosai nan gaba , Asmah taji dadin hakan sosai, nan ta bude memory tana ta saving dinsu, suààaààà£
Aàqnfi awa biyu suna waya kafin sukayi sallama.
Komawa tayi da baya ta kwantap akan bed dinta tayi lamo maganganun da sukayi da ummi ya matukar shigar ta , jikinta gaba daya yayi sanyi kalau, musamman kan cewa da ummi tayi zata fadama su mummy abinda ke faruwa,koba komai mummy da daddy sune mutanen da take matukar so bayan iyayenta, kuma baza suji dadi ace taki abinda suka haifa ba, koba komai Aslam jininsu kuma jinin mutum mafi daraja a idanunta Alhaji baba...........
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fisabillilah🙏
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}
Page 106
Haka suka ƙare wannan yinin cike da damuwa a zuciyar kowannen su, a bangaren Asmah Abu biyu ke damunta, maganganun da sukayi da ummi ɗazu, sai kuma, tunani da kewar Aslam daya addabi zuciya da ruhinta, gaba ɗaya jinta take kamar wata Mara lafiya, a haka har lokacin kwanciya barci yayi, koda ta kwanta kasa bacci tayi sai juyi kawai takeyi a makeken bed dinta, karshe ta janyo pillow ta rungume a kirjinta kamar yadda ta saba amma a banza, ji takeyi kamar ta tashi ta fita ta ganshi koda a boye ne,ba tare daya ganta ba,ba karamin dauriya tayi ba da ta hana kanta aikata hakan, daga karshe ta kwabi kanta da cewa, ya kamata ta kama ajinta koba komai ai shiya mata laifi shi ya kamata ya fara nemanta ba ita ya kamata ta fara neman shi ba.
A bangaren Aslam kam ya ma fita shiga damuwa, har karfe goman dare ya kai a falo yana zaman jiran tsamanin fitowarta, amma shiru gashi shi kuma ya kasa zuwa ya tunkareta, ganin goma da kwata yasa ya mike jiki ba kwari ya nufi dakin shi, wanka yayi tare da shirin bacci, kashe wuta yayi ya haye bed dinshi ya kwanta, saidai koda gigin wasa babu alamar bacci a idanun shi, gani yayi ma gadon ya mishi wani irin mugun fadi da girma, kai gaba daya ɗakin ma, ga wani irin sanyi da yakeji yana shigar shi duk da kuwa ƙudundunewa da yayi da katon bargo.
Idanun shi a bude kerr agogo ya buga 12am dai dai, kasa daurewa yayi ya mike ya kunna wutan dakin tare da zura slipas dinshi ya fice daga ɗakinshi ya doshi nata gaban shi Na faduwa, gara yaje ya tunkareta ayi wacce za'ayi komai ta fanjama fanjam, don ya tabbatar idan bai sanyata a idanunshi yau ba lallai bazai iya rintsawa ba.
Saida yayi tsayuwar kusan minti goma a bakin kofar yana tunanin anya kofar ma a bude take ko a kulle, a hankali yakai hannunshi kan handle din kofar ya murda tare da tura kofar a hankali, wani wawan ajiyar zuciya ya sauke jin kofar a bude.
Ware idanunta tayi daga lumshesun da tayi jin motsin ƙarar taba ƙofar dakinta, kafin tayi tunanin wani Abu ta ga ya tura kofar ya shigo dauke da munafukar sallama a bakin shi, ita ba a boye ba kuma baza'a kirata a fili ba ,wani irin mugun dadi ne ya ziyarceta, take ta sauke wani boyayyan ajiyar zuciya, a halin da zuciyarta ke ciki kiriss ya rage ta tashi ta bishi a cikin tsakiyar daren nan, saidai gashi Allah ya kawo mata shi, lamo tayi tana kare mai kallo ta cikin hasken kofar daya bari a buɗe.
Shikam Aslam bai ganta ba kasancewar dakin dimdim yake da duhu, kuma daga haske ya fito,idanunshi baya iya ganin komai sai duhu, jin bata amsa sallaman shi ba, hakan ya Tabbatar masa tayi bacci, wayar shi ya kunnu ya haska dakin ganin haka yasa tayi saurin rintse idanunta ba tare da ya ganta ba, lallabawa yayi a hankali ya kwanta a bayanta, duk abinda yakeyi tana jinsa, shiru sukayi daga ita har shi Na kusan 20 minutes, shi yana tunanin tayi bacci, ita kuma mamakin karfin halin shi na neman kashe ta, tayi shiru tana jiran taga mai yake shirin aikatawa.
A hankali ya dinga matsawa kaɗan kaɗan jikinta, har ya manna kirjin shi da bayanta, jin shiru bata motsaba yasa ya mike hannu a hankali ya rungumota jikin shi sosai, yana sauke ajiyar zuciya.
Kamar daga sama yaji tayi gyaran murya tare da cewa "welldone" ba shiri ya saketa tare da mikewa zaune, itama mikewan tayi tare da lalabur makunnin wutar dakin mai haske ta kunna.
Kallon cikin idanun juna suka shiga yi, kowannensu idanunshi cike da kewa da begen Dan uwanshi, zuciyoyinsu kamar yayi tsalle ta fado kasa tsabar a zalzalan da take musu, yadda ya ganta haka sanye cikin kayan barcinta masu dan kauri riga da dogon wando ga kuma gashin kanta daya barbazu kasancewar bata dauresu ba, sai tashin kamshi take ba karamin hargitsa shi tayi ba ji yake kamar ta wuff ya rungumota amma babu hali.
Marairaice fuska yayi, cikin wata irin marainiyar murya yace,"my husnah dama kema bakiyi bacci ba? " shiru tayi bata amsa ba saima dauke kanta da tayi daga kallon shi, ganin haka yasa ya matsa gabanta ya mika hannunshi ka kamo nata ya rike cikin nashi, a hankali cikin marainiyar muryarshi ya fara cewa"kiyi hakuri Mrs Asmah na San na miki laifi mai girman gaske, amma ina mai baki hakuri kisani wlh ni ba makaryaci bane, hasalima na tsani duk makaryaci, soyayyarki ce ta maidani haka kaunar kice ta rikiɗar dani na koma haka, ina sonki Asmah nasani kema zaki shaida haka, Dan Allah ina rokon ki da kiji ƙaina ki tausaya min ki bani dama na mallaki wani sashe a zuciyarki komin kankantarsa,zuciya ta na daf da kaiwa matakin da baza ta iya juriya akanki ba, hakurina ya kusa karewa a kanki, na miki alkawari husnah zan maki duk wani abin da kike tsammanin samu daga wurin mijinki fiye da yadda kike hasashe, zan nuna miki zallar madarar soyayya mara sirki, fiyye da yadda kike tunani, zan kula dake fiyye da yadda zan kula da kaina da tarin dukiyoyina, zan biya dukkan bukatarki,wanda na sani da Wanda ban sani ba fiyye da tunaninki, zan kare duk wani hakkin ki daya rataya a kaina iya karfina na, zan biya miki bukatar rai da gangar jikin ki yadda baki taba tsammani ba, Dan Allah Mrs Asmah ki bani dama komin kankarta ta, ki yarda dani da abinda nake fada miki wlh baza ki tabayin nadama ba,ina sonki my husnah ina mahaukacin kaunarki, ki tausayamin ki dubeni Dan fiyayyen halitta annabin rahama,sallahu alaihi wasallam"
A zuciyarta tama annabi salati itama, tare da dagowa ta sauke mishi dara daran idanunta a kanshi, shima dama idanun shi nakan fuskarta, kallon idanun juna sukeyi, kowanne da abinda yake karanta a cikin idanunn ɗan uwanshi, ta hangi tsantsar matsanancin soyayyarta a cikin kwayar idanunshi tare da tsantsar gaskiya akan abinda ya fada mata yanzu, yayinda shi kuma ya hangi tausayi, da burbushin soyayya da kaunar shi a idanunta.
Itace ta fara katse kallon ta hanyar zare hannunta cikin nashi, tare da juyawa mai baya ta kwanta, gaban shi ne ya yanke ya fadi me hakan me nufi, yes take nufine kokuma A'a.
Sun kwashe kusan 20 minutes a haka babu Wanda ya sake cewa komai, kundunbale yayi ya, mika hannu a hankali ya daura akan damtsen hannunta, wani irin shock taji a jikinta, lumshe idanunta tayi tare da budesu a hankali.
Ganin tayi shiru bata hanashi hakan ba, yasa a hankali ya shiga shafa hannun yana matsawa a hankali, daga karshe kuma ya koma ya kwanta, tare da janyota jikinshi ya rungume, a tare suka sauke ajiyar zuciya.
A hankali ya shiga cusa kanshi cikin sumar kanta dake nan a kwance Dan Sam bata iya parking din gashinta idan zata kwanta, yana shakar daddar kamshin dake tashi a cikin gashin, yayinda ya mika hannushi, ya dage Dan rigarta na barci ya daura tafukan hannayenshi akan shafaffen cikinta yana shafawa.
Sun kusan kwashe 30 minutes a haka, ko wannensu cike da begen Dan uwansa, a hankali ya farayin sama da hannayenshi yana kokarin kaisu inda zuciyar shi ke muradi,inda tun daga ranar daya gansu har yau hoton su bai taba bace mai a idanun shi ba, jin haka yasa tayi tsam tana zazzare idanu.
Kamar Wanda aka dannawa tsop, haka ya tsaya ƙem da hannayenshi, zuciyarshi ce ta kwabe shi da cewa, kul Aslam me kake shirin aikatawa ne haka, ka cika zalama wlh, kabi komai a hankali ka samu kaɗan raba ta ƙyaleka kuma kana neman ka wuce gona da iri, ka kiyaye ka maida zalamarka ka Adana, ka lallabata ka koya mata yadda zata saki jiki da