Showing 15001 words to 18000 words out of 201974 words
Chapter 6 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
da zata raka ya kamal, ...hoda ta shafa tare da zizara kwalli a idanunta , sai maskara data qara ma dogon eyelashes dinta,jambaki ta dauka pink ta shafa kadan akan pink lips dinta , sai gira da tayi amfani da brush na tage gira ta gyara , kallon kyakkyawan fuskarta tayi a madubi, ita karan kanta tasan cewa ita kyakkyawa ce koda kuwa ba Wanda ya taba fada mata hakan , balle kuma tasha jin hakan a bakin daruruwan mutane,...fari tayi da kyawawan idanunta da sukafi komai fusgan mutum idan yana kallonta ,murmushi ta sakarwa kanta tare da cewa "idon mayu",a hankali yadda ita kadai taji meta fad'a, batool ce ta dago ta kalleta jin kamshin turarenta ya cika mata hanci tace"waike malama Ina zakije ne da yamman nan kike wani kwalliya "kasancewar batool bata nan sanda kamal yace zata rakashi shopping yasa bata San da maganar ba , amsa tayi da "zan raka ya kamal shopping ne wai zaije yama budurwa shopping ". miqewa batool tayi zaune tare da cewa "kutumelesi shine bazakice nazo mujeba kiketa shiri ke kadai, bari kiga na watsa ruwa nima muje" ta fada tana shirin miqewa ,Asmah tace "kinga malama koma ki kwanta kici gaba da karata novel dinki, don su O,O ma dazu ba yadda basuyiba zasu yace bazai je da su ba sun fiye rawan kai"ta fad'a tana kallon side d',insu zahra ,Allah yasa basu jitaba , hankalinsu yayi nisa , komawa batool tayi ta kwanta tana cewa "nayi shiru"taci baba da karanta novel dinta ,.....wani dogon rigan atamfa chiganvy mai kyau ta zura, bayan ta saka inner wear dinta , rigan irin mai pocket dinnan da ake yayine ya kamata daga sama daga qasa kumaya bude sosai, wani fashion Dan kunne da abun wuya ta saka, parking din gashinta mai tsayi da laushi baqi sidik tayi, ta kashe daurinta zahra bihari bayan ta saka abin daurin dankwali a ciki ,mayafi golden color ta dauka qaramin kasancewar akwai golden color a jikin atamfar, ta yafa , pos ta dauka mai siririn hannun cen da takalminshi , suma gold color ne sunji Stone sai shining sukeyi ,qara fesa turare tayi a jikinta , sannan tace yan mata sai na dawo mai zan siyo muku, zahra ce ta dago kai ta watsa mata harara taci gaba da chatting dinta , don har yanzu haushi takeji ance baza,aje dasu ba sun fiye rawan kai ,batool ce tace ki siyomin rufaida yoghurt mai banana pls sis, karki damu tace mata tare da ficewa daga dakin ganin call din
ya kamal na sake shigowa wayarta.......
Zaune suke a compound din gidan a wani Dan rumfar bunu mai dauke da kujeru da table na katako mai kyau, Aslam ne tare da abokinshi Dr bashir , abokin shine tun na yarinta Wanda sukayi karatun boka Dana islamiyya tare a Jami,a suka raba jaha kasancewar shi Dr bashir pharmacy ya karanta shi kuma Aslam ya karanci businesses, Dr bashir baya qasar jiya ya dawo tunda ya tafi karatu qasar waje koda ya gama saiya kama aiki acan yakan zo ganin gida jefi jefi
fira sukeyi inda Aslam ke sanar dashi ran Sunday gobe kenan, su Abba zasuje nema masa auren zee, a gurin wan babanta alhaji abdurrahim, kasancewar yasan komai game da soyyanshi da zee din,
Zaro ido Dr bashir yayi yace"kace wallahi ". Harara aslam ya watsa masa tare da cewa "kasan na saba maka qarya, ai dole kace na rantse". Dariya dr bashir yayi, tare da cewa"ai abun ne da mamaki, ban taba zaton su Abba zasu sakko da wuri haka ba " tabe baki Aslam yayi tare da cewa" zasu sakko mana tunda wancen kinibabben tsohon yasa baki",Dr bash yace "amma baka da mutunci alhaji baba ne kibabbe" yace "kwarai ma kuwa, ko zaka je ka gayamai ne " bash yace "a,a ni bashi zan gayama ba daddy zan gayama", zaro ido Aslam yayi yace"ka rufamin asiri na samu daddy ya fara amsa gaisuwata da'ker" ......
Dai dai lokacin Asmah ta fito daga part din mummy ,cikin takunta mai Jan hankali , sai zuba kamshi takeyi, direct parking lot ta nufa inda ta hango motar ya kamal , ta bude gefen shi ta shiga tazauna , kamal ne yace "sister barka da yamma " a kunyace ganin ita ya kamata ta fara gaishe tace"yawwa ya kamal , sorry na shanyaka a mota ko, wlh naje yima mummy sallama ne ta aike ni kitchen, shiyasa na dade"murmushi kamal yayi tare da cewa "ba komai sister bari muje yamma naqara yi" ya fada tare da tada motar yayi ribass ya fice daga gidan,
Sai lokacin lokacin Dr bash da yayi mutuwar zaune tun fitowar Asmah ya sauke wani wawan ajiyar zuciya tare da juyowa ya kalli Aslam,....
Aslam Wanda kanshi ke duqe yana lallatsa phone dinsh, sai lokacin ya dago kanshi, tun fitowarta daga part din mummy kallon daya ya mata ya dauke kai, ganin ta shiga motar kamal, ta'be baki yayi ya daga kafadunshi alamar I don't care dinnan,,
Dr bashi yace"yace Aslam kardai kace min su yan biyu ne suka girma haka " girgiza mai kai yayi yace"no nasu bane". "To amira ce "Dr bash ya sake tambaya "ba ita bace" ya bashi amsa Dr bash ya sake "cewa to wacece wannan mai kyau din". Hade rai Aslam yayi jin Dr bash ya kirata da mai kyau haka kawai ya tsinci zuciyarshi dajin haushin Kalmar, cikin dan hasala yace"kai dalla wani bin kai banza ne wlh,kan wannan qaramar mara kunyan rayinyar duk ka wani rude kanata jeromin tambaya kamar wani sabon dan jarida, maimakon Dr bash yaji haushin ihun da Aslam ya masa , amma sai ya kasa,qara qasa yayi da murya tare da cewa "Aslam Dan Allah wannan din itama yar gidan nan ce"
share shi Aslam yayi bai bashi amsaba , murmushi Dr bash yayi yana shafa girjinshi dai dai gefen heart dinshi yace"ta sace zuciyata a gani na farko , kyawunta, nutsuwarta , kamalanta , masu Jan hankali ne ,kuma insha Allah naga matar aure"
.
qara hada rai Aslam yayi yana watsawa bashir wani banzan kallon,zuciyarshi ta dauke zafi sai tafasa takeyi haka kawai, shi karan kanshi bazaice ga abinda ya tunzira shi ba, cikin bacin rai yace "amma wlh ka bani mamaki kuma kaji kunya bashir " miqewa yayi yana tartare wayoyin shi manya guda biyu dake ajiye kan table din wajen ,juyawa yayi ya nufi hanyar part dinsu, ko qala bai qara cema Dr bash ba,
Shima bashir bai damu ba don yasan halin abokin nashi , yanzu haka zaice zai jawo mai raini ne gurin qannen shi , shiyasa ya hasala haka , miqewa yayi ya nufi motar sa ya shige ya bar gidan da qudirin gobe zai dawo ya samu mummy Dan jin wacece wannan mai kyau din,age da wannan yau banda chaji sosai
Date: Oct 11, 2022
đź’–DAMA TA BIYUđź’–
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Page 29 & 30
Wani babban shopping mall sukaje , shopping sukayi sosai na kayan kwalliya da turaruka masu kyau da tsada , sai kayan kwalama dangin su chocolate, sweet, biscuit,dadai suransu,
Juyowa tayi ta kalli ya kamal dake tura mata Dan kwandon da take zuba siyayyarta a ciki, tace
"Ya kamal mu barshi haka , wad'an nan ma nasan zasu birgeta. "
Kamal yace"kin tabbatar sun isa kuwa" tace "eh" yace "kodai mu hada mata da suttura haka". Tace"eh to saidai ko abaya" ok yace "muje shagon da ake saida abayas din saiki zabar mata"....
Kai kayan da suka saya suka yi akayi musu packaging dinshi kamal ya biya suka bar mall din,
R.U all store sukaje dake nan kan titin bosso road. Babu kalan abayan da babu a wajen,
Har tasa hannu ta fara dubawa dai kuma ta juyo ta kalle shi tace "ya kamal zo ka zabar mata kaga ni bansan size dinta ba , tunda ban taba ganinta ba "
Murmushi yayi yace "ki daukar mata size dinki, don inaga a tsayi da jiki zata kaiki"
Dan Jim tayi tuna dazuma data tambayeshi colourn skin d'inta dan ta zavar mata mai da powder, cewa yayi ta daukar mata irin wanda take amfani dashi Dan haskensu zaizo daya, yanzu kuma yace size din jikin su daya.
Kawar da wannan tunanin tayi tare da zaban wasu ubansun abaya's masu shegen kyau da tsada , kala biyar dai dai jikinta nuna mai tayi yace "sunyi kyau kuma daga gani ba qaramin kyau zasu mata ba" murmushi kawai tayi cewa yayi itama ta dauki abinda take so, girgiza kai tayi tare da cewa"ni babu abinda nakeso saidai naga irin turaren alhaji baba zan daukar mishi " "OK" yace,
Turaren ta dauka guda biyu ta daukar ma hajiya mama ma nata,yoghurt da ice cream din rufaida ta daukar musu ita da kawayenta, kamal ya biya suka fito,
Daidai parking lot wani mutum da dukkansu suka lura da bibiyarsu da yakeyi tun dazu , ya musu sallama ,
Amsa mishi sukayi kamal ya miqa mishi hannu sukayi musabaha, tare da tambayarshi lafiya dai ko,
Murmushi mutumin yayi yace"lafiyarce ta kawo ni, ni suna na Ali m Ali, inason nayi magana da sisterka ne inba damuwa "hade rai kamal yayi jin abinda Ali m Ali ya fad'a, yace "haba bawan Allah ya daga ganin mutane zaka tsare su haka akan titi baka San ko su waye ba , to wannan da kake gani matar aure ce kuma tare take da mijn ta" .
Murmushi Ali yayi yace "Mallam wannan ba matar aure bace kuma kai ba saurayinta bane, don naji da ya kamal take kiranka, don haka nake roqonka ka bani dama numbar wayarta kawai zan amsa , ya fada yana hade hannu alamar roqo🙏 pls ya kamal"
Qara hade rai kamal yayi yace "nan ba shine wajen daya dace kayi magana da ita ba, in kana son yin magana da ita gida zakabita,"
Kallonta tayi yace "muje" ba musu ta bude mota ta shiga ko kallon ali dake binta da mayen kallo batayi ba, kamal ya figi mota da karfi, furkar nan a hade kamar bai taba dariya ba, a zuciyarshi yace "haka kawai yazo ya batamin mood d'ina na farin ciki , a fili kuma yayi tsaki ,Wanda yasa Asmah saurin kallon shi,
ganin kamar ransa ya back sosai akan abinda ya faru, yasa tace "kayi hakuri ya kaml wlh nima koda baka wajen bazan kulashi ba, don ni yanzu babu batun soyayya a gabana karatu nake sonyi"
Ajiyar zuciya kamal ya sauke tare da cewa cikin sanyin murya "da gaske kikeyi Asmah" gyad'a mai kai kawai tayi alamar eh ,
maida kanshi yayi yaci gaba da tuqi kamar bazai qara cewa komai ba, sai can ya kira sunanta
"Asmah " "naam ya kamal" ta amsa shi , yace "akwai wata magana da nakeso nayi dake in bazaki damu ba" , bai bata daman amsawaba yaci gaba da cewa "amma bansan ya zaki kar'bi batun ba Wanda tuna hakan na matuqar tsinkar min da zuciya, nakan shiga tashin hankali idan na tuna daga ni. sai mahaliccina mukasan halin da zuciyata take ciki a kanki, Asmah zuciyata ta makance ta kurmance bata gani da ji si naki, naso in danne bugatarta har sai kin kammala karatunki na bayyana miki, amma bazan iyaba Asmah ina tsoran abinda ya faru dani a wancen karon ya sake faruwa dani, Wanda na tabbata idan wancen karon na dauki dangana wannan karan zuciyata bazata iya dauka ba, nauyin bakin da nayi a baya yasa na kusa yin babban rashi a rayuwa ta, sai kuma ubangijin taliqai ya sake aramin dama ta biyu akanki "
Dai dai lokacin ya parka motar tare da fuskantarta sosai yace "Asma'uu..I love u. ina sonki Asmah ina qaunarki qauna Mara iyaka, don Allah Asmah nima kisoni karkice A'a ya fad'a yana hade hannayenshi alamar roqo🙏🏻"
Kamar wawuya haka ta tsaya tana kallonshi, bata taba tsammanin hakan daga gare shi ba , duk da kuwa irin tarin kulawarshi gareta,
Ta dauka tausayi da sanin darajar Dan Adam da yake dashine yasa yake bata kulawa fiyye da yadda yake ba qannen shi kulawa , Ashe abin ba anan ya tsaya ba,
Tabbas kamal ya cancanci ta soshi domin ya hada duk wani Abu da mace ta gari zataso mijinta ya kasance dasu ta ko ina, saidai bata jin shi a ranta ko kadan, amma duk da haka baza ta taba watsa mai qasa a ido ba, kodan ta quntatawa Aslam kuma ta cika burin kakaninta, zatayi soyayya da kamal kuma ta aure shi, indai har zai iya jiranta ta kammala karatunta Wanda a yanzu shine babban burinta....
Ganin shirunta yayi yawa ne yasa kamal cewa ya bata kwana biyu taje tayi tunani, abinda ta yanke zai saurareta, haka ya tada motar suka qarasa gida,dai dai ana kiran magriba, don haka yana sauketa yayi masallaci bayan ya bada dukkan shopping da sukayi an shigo mata dashi ciki,
Koda ta shiga ba kowa a falon qasa don haka dakinsu ta wuce,da lelodin shopping dinta niqi niqi a hannu,
Sallah ta taras su zahra nayi don haka itama alwalata dauro ta tada nata sallan.
bayan sun idar karatun alkur,ani mai girma sukayi har zuwa isha'i sukayi sallah , nan ta fito musu kayan kwalaman suka ci suka ture, bayan sun gama suka shiga tambayarta dame dame ta zabarma budurwar ya kamal din, shiru ta musu ganin zasu dameta tace musu kanta na ciwo su kyaleta , ganin haka yasa suka kyaleta suka shiga wani hirar daban.
Kwanciya tayi bayan ta cire kayanta ta sakana bacci ta fad'a duniyar tunanin gobenta ,a haka bacci ya kwasheta ko abinci bataci ba, tunda sun riga sunyi ciye ciye d'azu.
Washe gari Abba da wasu abokan daddy guda biyu sukaje nema ma Aslam auren zainab, saida aka shanya su na kusan awoyi biyu lafiyayyu ba ko ruwa , alhaji badamasi daya daga cikin abokan Abba da bashi da haquri ya fara fad'a yace su tashi su tafi wannan ai wulaqanci ne su ba yan iska bane da za'a a shanyasu kamar wasu marasa aikin yi, Abba ne ya shiga tausar sa da
qar ya haqura ya zauna, yana fuffuka , sai fad'i yake a ina Aslam ya had'u da wannan yar gidan marasa mutuncin ne..
Sai chan mom da dad da alhaji abdurrahim suka fito suka zauna, mom ta daura qafa d'aya kan d'aya tana hura hanci bako gaisuwa, shima dad hade rai yayi shi a dole bada son ranshi zai bada yar shiba,alhaji abdurrahim nema, mai Dan dama dama ,
Su Abba kam sunga ikon Allah yau, tunda suke basu taba gani N wannan lamari ba , amsan gaisuwa harda uwar amarya,
Alhaji badamasi da bai bari ta kwana ya dubi mom dake cika tana batsewa yace"madam kidan bamu guri maganar maza da maza zamuyi " dad yayi caraf yace "ku fad'i abin da. zaku fad'a a gabanta ba damuwa,
Alhaji badamasi zai qara magana Abba ya dakatar dashi
Gabatar da abinda ya kawosu sukayi, na buqatar hada zuri'a da su ,
Dad sharesu yayi yana daddana waya Alhaji abdurrahim ne ke amsa su , nan dai yace ya basu ya fadi dukiyar aure suka bayar a take , maqudan kudi kuwa bana wasa ba , a nan aka tsayar da lokacin biki nan da wata daya
Haka suka taso kowa ranshi a dagule , ba mai bakin magana cikin su kowa da abinda yake saqawa a ranshi ..........
Oum ummeetarh
07041130088
Share & comment🙏
Date: Oct 12, 2022
đź’–DAMA TA BIYUđź’–
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Page 31 & 32
Gaba daya gidan ba wani mai farin ciki da wannan auren na Aslam, mummy kam ma fakewa tayi da matsayin sa na d'an fari, tace ita ba ruwanta da batun aurensa, su mami ne uwayen shi ita ba d'anta bane, da haka ta zame hannayenta cikin lamarin ta bar su mami da ummi a ciki.
Su suka had'a lefe bayan Aslam ya basu card d'inshi, yace su cire ko nawa zai isa,
Sunko cire Dan lefe na gani na fad'a suka hada ba algus ko baqin ciki a ciki,
Ta bangaren zainab kam shirye shirye sukeyi ba kama hannun yaro, daga ita har iyayen ta abunka da wayayyu yan boko partyn da suka shirya ya kai kala bakwai, don tun ana saura sati d'aya daurin aure zasu fara program, ta nan bangaren ma Aslam ba qaramin kud'i ya sake musu ba , kamar bai San zafinsu ba
Shiko anashi bangaren shi kadai yaketa shirye shiryen shi, ya qara qyara gidan shi na London road dan can zasu zauna _ part dinshi ba part din da aka kai Asmah ba.
;
Dole ya nemo amir ya bashi hakuri akan abinda ya mishi a wancen lokacin, don yasan duk wani zirga zirga bazai iya shi kadai ba,saida mataimaki, kuma amir d'inne, kadai zai iya tsaya mai yamai komai tsakani da Allah, abinka da 'yan uwa kuma aminai, take amir ya manta da komai na baya suka shiga zirga zirga tare...
Yau yan matan mummy suna cike da farin ciki kasancewar admission d'insu ya fito kuma alhmdllh dukansu sun samu abinda suke so, Asmah da batool masscom, zahra da amira pharmacy , duk university daya suka samu babban university na minna, ranar Monday kuma zasuje su fara registration,
Zaune suke a d'akin su, suna fira batool tace "biki fa na qaratowa inaga yau saura 2 week fa ;". Zahra ta ta'be tace "nifa ko akaina bana kawo wannan bikin, da ayi da kar ayi duk uwarsu daya".