Showing 111001 words to 114000 words out of 201974 words
Chapter 38 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
mu}
💖Tallah!💖 Tallah!!💖
💖Tallah!!!💖
💖
Albishirinku manyan mata! ma'abota kwalliya da
_Rantsattsun lesussuka💃,
_Atamfofi manya da k'anana💃
_Galla gallan shaddodi manya da k'anana muna da su kowani iri💃
_Akwai kuma yadiddikan maza kamarsu koranza,plan yard dadai sauransu💃
_Munada mayafai, takalman maza da mata,sarqoqi, awarwaraye,da duk sauran nau'ikan kayan ado na maza da mata muna dasu 💃
Akanfaninmu na""R & U""Global Enterprise Dake Nan Garin Minna Niger State, saikunzu..........
Ga numbern mu kamar haka👇
08062160424
08066891424.....
Sayan day'a ko sari acikin farashi mai sauqi👌
Kubamu odern ku,danshine aikimmu akoda yaushe da yardar Allah........👌
Sai an gwada akansan na kwaraiiii💃💃💃.....
Page 102
~BATOOL~
Yau kimanin sati biyu kenan da mai afkuwa ta afku tsakaninta da Dr bash, tsaye take a kitchen gaban gas, sanye take da zumbulelen hijabi dogo har ƙasa breakfast take haɗawa domin kuwa safiyace, daga inda take tsaye ta juyawa kofar shigowa kitchen din baya.
Takun shi ta fara ji daga bayanta alamar yana kusan to kitchen d'in, take gabanta ya fara faÉ—uwa, jikinta ya dauki karkarwa, har saida Cokalin miyar dake hannunta ya subuce ya faÉ—i.
Daga bakin kofar kitchen É—in ya tsaya ya harÉ—e hannu a kirji yana kallonta, koda wasa batayi gigin juyowa ba, tsayuwar kusan minti biyar yayi kafin ya juya ya bar kofar kitchen.
Ajiyar zuciya ta sauke jin ya bar kofar kitchen d'in, dukawa tayi ta dauki cokalinta ta daureye, taci gaba da girkinta, cikin sauri sauri ta karkare , ta zuba mai nashi a kula ta ajiye mai a gurin data saba ajiye mai a kitchen d'in nata kuma ta zuba a plate, ta dauka ta kamo hanyar fitowa daga kitchen d'in saida ta fara lekowa taga ko yana falon, yana nan kuwa saidai ya juyawa hanyar kitchen d'in baya, cikin sanɗa ta lallaba ta haye sama, tana samu ta haye ta ƙarkare da gudu ta shige dakinta ta banko kofa.
Dr bash yana zaune a falo ya juyawa hanyar fitowa kitchen baya amma duk abinda takeyi yana kallonta ta jikin glass din tv kasancewar tv a kashe yake, girgiza kai yayi cike da damuwa ya mike ya shiga kitchen din ya dauki nashi abincin ya shige sabon bedroom d'in shi dake nan a kasa.
Abinda ke faruwa shine tun ranar da Dr bash yayi nasaran raba ta da budurcinta, gaba daya batool tayi wani irin laushi, tsoran shi takeji kamar wani malaikan daukar rai, saboda ba karamin azaba tasha a hannunshi ba, tayi dana sanin rashin mutuncin da ta dinga mai tuntuni, da tasan haka aure yake da wallahi, saidai in gawarta za'a aurar,ta kai kusan 3 days ko taka kasa bata iyawa da kyau, wani irin tsoran shi hade da kunyar shi ne ya darsu a zuciyar ta tun daga ranar, tun ranar har yau taki bari idanunta da nashi su haÉ—u, idan kuwa yazo kusa da ita tsorata takeyi jikinta ya kama karkarwa, wasan buya take yi dashi sosai, Dr bash tun yana daukar abin wasa yana mata dariya yana tsokanarta har dai lamarin ya fara bashi tsoro, dan ranar da ya gaji ya kara nuna alamar son ya sake kusantar ta duk da rawan da jikinta keyi tana kuka bai saurare ta, tubeta yayi ganin da gaske yakeyi, yasa take numfashinta ya fara sizing kan ya farga ta sume mai.
Hankalin shi yayi matukar tashi, rasa yaya zaiyi da ita yayi,kamar ba likita ba, can dai ya debo ruwa ya yayyafa mata, tana farkowa kuwa kuwa da kuka ta fara tana rokon shi dan Allah yayi hakuri, karya ya sakeyi mutuwa zatayi, a take bash ya yarda lallai ba, iskanci bane da gaske ta tsorata da shi, dole dan kar ya dinga firgitata yasa ya tattara ya bar mata dakin hakan kuwa ya mata dadi,tun daga lokacin kuma ganinta ya nemi yimai wuya a cikin gidan, sai ya kwanta ya wuni bai ganta ba, dan bata fitowa sai ta tabbatar yabar gidan, zata fito ta shiga kitchen sauri sauri tayi girki, duk abinda ta girka kuwa saita ajiye mai, yau ma gajiya yayi da rashin ganin ta dan kusan kwana biyu kenan a Jere ko motsinta baiji ba, hakan yasa yayi dabara ya shiga mota ya fita da sassafe yabar gidan, jin haka yasa ta fito da sauri ta fada kitchen donta haÉ—a breakfast, parking d'in motar shi yayi a kofar gidan ya lallaba ya dawo shinefa ya sameta a kitchen, wannan rayuwar shi suke fuskanta a gidan tun daga wannan ranar da mai afkuwa ya afku, abudai kamar shafan aljanai, bashir kam ya shiga damuwa abin har ya fara shafar aiki da lafiyar shi.
(Allah sarki bash kai kuma taka ta sameka, Allah ya taro maka ita da gaggawa)
~MR & MRs-AS~
Tsawan sati daya kenan da fara rashin lafiyar Aslam, har zuwa wannan lokacin kuwa jikin dai gashi nan ba sauki, abun na matukar damun Asmah, duk tabi ta damu kanta, inka ganta duk tayi zuru zuru kamar itace a kwance, yayinda Aslam tuni ya gyagije yanzu haka da za'a dubu su sai an samu ya fita lafiya ya samu kwanciyar hankali yayi wani fresh dashi ya kara haske harda dan kiba.
Yana daga kwance komai ita kemai, abinci saiya zaba wanda yakeso zata girka ta shakare mai plate ta bashi a baki yana mata yanga yana walata a haka zai tanÉ—e tass, da zarar anyi sallah ishs'e kuma ya kama rawar sanyi karya yace ta rungume shi sanyi zai kasheshi, haka nan tana hawaye saboda tausayin shi yata rungume shi, a haka har barci ya kwashe ta.
Tsananin tausayin ta yasa ta kasa gane karya yakeyi lafiyar shi lau, bata taba lura da cewa jikinshi ba zafi ba, haka idan yana rawar sanyin shi na karya tace bari ta kashe Ac bai taba yarda, cewa yakeyi ta barshi, duk da haka bata taba harbo jirgin karyan shi ba,zuwa yanzu ita kanta tayi wani irin sabo da shi, jin shi tajeyi har cikin zuciyarta, takan shagala da kallonshi musamman idan yana mata shagwaba, sai ta tsinci kanta da biye mishi ta dinga lallashin shi kamar wani dan yaye.
Yanzu haka tsaye take a kitchen tana ta faman dama mai kunun gyada da kosai dan yau shi yace yana so na breakfast, tana aikin amma zuciyarta cike da tunane tunane, idan lissafinta dai dai ne yau ya kama Aslam zai gama shan maganin sa duka , don idan yasha na dare yau shike nan mugungunan sun kare, kuma ita ta duba ta dubo bata ga wani saukin da ya samu ba gashi har magani ya kare yanke shawara tayi, zata tuntube shi su je asibiti, kokuma ta kara kiran Dr James, da wannan tunanin ta kammala hada lafiyayyar kunun gyadanta da yaji madara da kuma kosai mai hanata da kwai a ciki, jerawa tayi a tray ta dauka ta nufi dakin.
Aslam na zaune bakin bed waya yake yi da Amir, sai kwasan dariya yakeyi , Amir na bashi labarin tsiyar da ummi ta mashi da irin wuyan da yasha da kuma yadda ummi ta mayar mai da matar shi cikin sauki ba tare da wani tashin hankali ba, Aslam kam sai dariya yake ma Amir d'in harda su kwanciya, yana rike ciki, hankalinshi yayi nisa baiji sallamar Asmah ba.
Sallama tayi har kusan so uku ba'a amsa mata ba hakan yasa ta kutsa kai don duk tuananin ta ya koma barci kokuma yana toilet shiyasa bai jita ba, saidai ga mamakin ta sautin dariyar shi taji, kafin ta kai kallonta kanshi ya Ankara da shigowarta, dif yayi da dariyar da yakeyi, tare da yamutsa fuska,take ya maida muryar shi na marasa lafiya, hannunshi kuma dake tallabe da cikin shi tsabar dariya, ya kara dannan shi akan cikin kamar dai gurin namai ciwo, a wahalce ya shiga cewa "ba damuwa bross na gane na fahimceka ba komai bari zan kira ka letter, bana É—an jin dadi ne" mamaki ne ya nemi kashe Amir a daya bangaren, saida ya cire wayar a kunnen shi ya duba sunan da kyau ya sake mayar wa kafin yace wani Abu kit yaji Aslam ya katse kira, da sauri ya sake kira amma Aslam ya danna mishi busy, har so biyu dole ya hakura , a ranshi yana aiyana lallai akwai lauje cikin nadi, dan shidai ya san ruwa baya tsami banza amma koma meke ciki yayi alkawarin bincikowa.
Daskarewa Asmah tayi take ta shiga tunanin to kodai kunnayenta ne suka jiyo mata sautin dariyar shi, dan dai ita ko kur'ani aka bata zata rantse taji dariyar shi, sai dai kuma a yadda ta ganshe sai ta rantse bai taba dariya a duniya ba, kawar da wannan tunanin tayi ta karasa ciki ta ajiye tiren ta akan table din datake ajiye wa, ta fara serving dinshi tanayi tana bashi hakuri bisa dan bata lokacin da tayi, kallonta yayi yace "ba komai yar Aljannah, nagode da dawainiyar da kikeyi dani Allah ya saka miki da gidan Aljannah madaukakiya, Allah kuma ya baki ƴaƴan da zasu miki fiye da yadda kika min" dadi da kunya ne suka lullubeta a lokaci guda dadin addu'o'in da ya mata da kuma kunya maganar shi ta karshe da yace Allah ya bata ƴaƴa, ganin ta kawar da idonta gefe cike da kunya yasa ya fakaici idanta ya mata gwalo, sannan yaci gaba da cewa "insha Allah zamu haifar ma su daddy jikoki kyawawa masu kama dake, kina so" kunya ya ya kara lullubetata ta lura shidai Aslam kwata kwata babu wani Abu wai shi kunya a lamuran shi, yana ta wani magana akan haihuwa haihuwa, ta yaya zasu haihu, ita dai tasan ko anyi aure akwai wasu abubuwa dake faruwa kafin akai ga samun ciki har a haihu, take ta ƙara yin kasa da kai tuno ta yaya akeyi a samu cikin ma har a kai ga haihuwa, tanada wannan muradin itama kuma tana sha'awar ta haihu amma fa da Kamal kawai take da wannan sha'war bada kowa ba.
Aslam ganin tayi kasa da kai tayi shiru kamar ta Lula wani tunani yasa ya katseta da cewa "kinyi shiru Mrs Asmah ko baki son mu haihu ne" firgigit tayi jin maganar shi kamar daga sama, bata bashi amsar wannan tambayar ba sai cewa da tayi" oh sorry ga abincin na zuba maka" tana magana tana karasawa gaban sa da plate da cup d'in kunun data zuba mai, bata tsaya bata ma kanta lokaci ba ta shiga diba tana kaiwa bakin shi, karba ya dingayi yana ci yana kallon fuskarta yana sakin murmushi, wani irin dad'i yake ji a zuciyar shi, inama ace bawai saboda bashi da lafiya bane take mai wadanan duk abubuwan da take mai inama ace dai soyyaya ce tayi sanadin da take bashi abinci haka a baki ba tausayi ba.
A haka ta gama ciyar dashi, ta mike zata bar gurin komar da ita yayi ya zaunar, sannan ta mike a hankali ya dauki plate da cup din ya isa inda sauran abincin suke a kula, ita dai binshi takeyi da kallon mamaki, mai zaiyi da abinci kuma bayan yace mata ya koshi, mamakin ta bai ƙaru ba saida taga ya ciko plate da cup da kunu da kosai ya zauna gabanta ya dibo yakai bakin ta, kin bude baki tayi ta tsaya kallon shi, katseta yayi da cewa "umhumm ke nake jiya oya haaa" girgiza kai tayi ta bude baki zatayi magana, katseta yayi ta hanyar daura dan yatsar shi akan labban shi yace "shiiii bana son musu kawai kiyi haaa" yadda ya bata rai sai taga ya koma mata asalin ya Aslam data Sani a baya ba wannan Aslam d'in ba dake binta sau da kafa kamar wata uwar shi, bata San sanda ta bude ɗan bakin ba kuwa ya shiga bata a hankali tana karba, gaba dayansu wani irin nishadi suka tsinci kansu a ciki a daidai wannan lokacin, ji suke kamar su tabbata a haka, har saida ya tabbatar ta koshi sannan ya barta, kwashe kwanukan tayi ta kai kitchen ta wanke, sannan ta dawo ta bashi magani yasha,ta wuce kuma toilet ta hada mishi ruwan wanka.
Kamar kullum yauma mika mata hannu yayi ta dagashi, tsayawa tayi tana kallon shi tunawa da dazu daya mike yaje ya dibo mata abinci ai bata dagashi ba kuma taga ya iya tashi da kanshi, muryar shi ta tsinta yana cewa cikin shagwaba "pls mana Mrs Asmah tunanin me kikeyi" jiki a mace ta mika hannu dan É—aga shi, saidai ji tayi ya fisgota ta fado jikinshi, komawa da baya sukayi kan bed d'in,tana a sama shi kuma yana a kasa ya mutsa fuska yayi yana cewa"wash Allah kirgina kin fado min a kirji zaki karyamin kashin hakarkari, gaki da nauyi, kamar buhun siminti, wash kirjina zai balle" jin abinda yake cewa yasa tayi maza ta sauka akanshi, ta shiga bashi hakuri a rude kan bata San yanda akayi ta fado kanshi ba, dago kai yayi ya kalleta ganin duk yadda ta rude tana ta faman bashi hakuri, yasa ya saki murmushi a zuciyar shi a fili kuma fakan idanta yayi ya mata gwola, saidai cikin ikon Allah karaf a kan idanunta, turuss tayi ta tsaya daga ban hakurin da take mai tana kallonshi ganin haka yasa, ya shiga pretending yana zaro harsher waje yana mayarwa, yana jan yaji, cikin rasa madafa ya shiga cewa "wash harshena yaji, kai gsky yau kosan nan naki yayi yaji sosai wlh hala tarugu guda goma kika zuba"Asmah kam tsabar mamaki daskarewa tayi a tsaye a gurin, kosan da yaci kusan 30minute da suka wuce duk baiji yaji ba sai yanzu, ita dai ganin idanunta ta kamashi yana mata gwalo, sharewa tayi amma a ranta ta sakama lamarin ? mark, na biyu kenan dazu ta kamashi yana tikar dariya yanzu kuma gashi yana mata gwalo, amma ya fake da wani abinda hankali ba bazai dauka ba wai yaji.
Bata dai nuna damuwar komai ba ta tallabo shi zuwa toilet d'in kamar yadda ta saba kullum, rabin jikinshi na cikin nata ta kaishi toilet d'in ta fito, ta Ciro mai kayan da zai saka ta bar dakin zuwa falo,zama tayi ta shiga tunanin abubuwa biyu da suka faru yau a kusan lokaci daya da suka matukar bata mamaki, shin da gaske ne abinda idanu da kunnayenta suka gano da juyo mata, kodai karyace kawai sukeyi yi mata, kai gaskiya da gaskene dan tasandai bata da matsalar ji da gani balle tace ciwon su ne ya motsa mata yau, to kodai mr Aslam ya warke kawai pretending yake mata dan ta dunga kulawa dashi, kai anya ya za'ayi mutum da girman sa da hankalinsa yayi kar yar ciwo haka, ajiyar zuciya ta sauke mai karfi kafin a fili tace koma me ke ciki zan Saka ido sosai domin na gano gaskiyar lamarin, inko karya yake min ko hmmmm ta kareshe tare da girgiza kai.
Aslam koda ya gama wankan shi ya daura tawul gyaran murya ya mata alamar ta shigo ta taimaka mai ya fito, dan dama haka sukeyi yanzu har fitowa toilet d'in sai ta taimaka mai yakeyi, jin shiru alamar bata dakin abin ya matukar bashi mamaki, haka ya mike a hankali ya leko ganin da gaske bata dakin yasa ya fito da kanshi, zaman jiranta yayi tazo ta shafa mashi mai da sauransu amma har ya bushe shiru ba amon ta ba labarin ta, take yasha jinin jikinshi, lallabawa yay, yayi shafe shafen da kanshi ya saka kayan, kamar yabi bayanta ya dubo ko lafiya amma sai wata zuciyar ta kwabe shi da cewa muddin kayi haka sai ta zargi wani Abu, dole ya hakura ya koma ya kwanta amma zuciyar shi gaba daya babu dadi, a haka bacci ya kwashe shi Mara dadi mai cike da mafarkai barkatai, harda Wanda Asmah tagane Ashe kalau yake, ta kuwayi mummunan fushi wai harda su gaggauramai mari tayi a makarkin.
Koda ta gama zaman ta a falo lekashi tayi taga yayi bacci dan haka itama ta wuce dakinta ta kwanta, tana son tayi bacci saidai kash baccin yaki zuwa sai juyi tajeyi akan makeken bed dinta,jin ta tajeyi kamar a bude take dukda taja kakkauaran bargonta ta rufa, ji takeyi gadon ya mata wani irin mugun fad'i, karshe dai saida ta lalubi pillow ta rungume sannan ta iya baccin.
Sai bayan azahar ta tashi bata ɓata lokaci ba ta gabatar da sallanta, sannan ta nufi dakin Aslam, ta tarad shima ya tashi da alama ma ya dade da tashi don har yaje masallaci yayi sallan azahar ya dawo, sannu tamai da jiki, nan ya shiga yamutsa fuska yana amsa mata a wahalce kamar gaske, tambayar shi tayi abinda zaici ya fada, ta wuce kitchen taje ta girki ta kawo ta bashi a baki kamar kullum.
Haka dai suka wuni ranar har zuwa dare inda bayan ta gama bashi abinci ta dauko sauran maganin shi Wanda idan yasha wannan shikenan ya kare ta bare mishi tayi ta bashi, bayan ya gama sha ta kalleshi tace" Mr Aslam idan kasha wannan maganin na yanzu ka gama shanye duka magungunan da Dr ya baka gashi kuma ni banga alamar kaji sauki ba , ya zama dole ka yarda muje asibiti kokuma na sake kiran Dr yazo gida ya kara dubaka, ni abinda yafi bani tsoro ma, wannan rawan sanyin dake tashi maka da daddare kaga rannan baka ma Dr complain dashi ba kar azo kuma ba fever d'in bane wani ciwo ne na dabam"tsayawa yayi ya rasa wani amsa zai bata can dai ya daure yace "to Allah ya kaimu goben sai ki kira Dr James din ya canza min wasu magungunan, tunda dai wadanan basuyi ba", kamar kullum yauma haka rawan sanyin nan ya sake kama Aslam, bata jira yace ta rungume shi ba, tana ganin haka ta shige jikinshi