Header Ads
Showing 96001 words to 99000 words out of 201974 words

Chapter 33 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1730

Ads at the middle of Article

wannan sake saken ne taji ana buga mata kofa kamar za'a balla.




Allah sarki baiwar Allah kamar baza ta bude ba sai kuma tayi tunanin kosu hanan ne suka dawo ajiye abincin ta tayi ta tashi ta isa wurin kofar ta bude, gabanta ne ya yanke ya fadi ganin Maryama, da wasu watsatstsun mata biyu tare da ita, suna binta da mugun kallo suna huci, kafin takai ga tambayar su lafiya , farida ta sauke mata mari a fuskarta kau , tare da hankada ta cikin falon, baya tayi ta fadi saboda bata shiryama hakan ba, kuma ba karamin hankada ta mata ba, kafin ta kai ga mikewa, sun rufeta da duka ta ko'ina baji ba gani kamar Allah ne ya aikosu.




Wayyo zahra sunfi karfinta sarkin yawa yafi sarki karfi itadai kokari take ta kare fuskarta kar suji mata a fuska, Maryama hawa kanta tayi ta zauna a ruwan cikin ta, tana tumurmusa.






Daidai lokacin motor barr ya shigo harabar gidan da mahaukacin gudu, waya ya samu daga hanan tana kuka take gaya mai ga mummyn su ta kira anty farida da anty atika sunje dakin anty amarya wai zasu mata duka, iya abinda ya iya tsayawa ya saurara kenan,ya katse kiran ya shigo motar shi da mahaukacin gudu ya nufo gida...........








Yauma dai kumin hakuri mutane na bani da isasshen caji again🙏








Oum ummeetarh
07041130088










Share
And
Comment
Fisabillilah🙏


💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~






FREE BOOK








DAMA TA BIYU💖 ƘIRƘIRARREN LABARINE MALLAKINANE BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYAMIN LABARI TA KOWACCE SIGA BADA IZININA BA❌❌❌❌


(In👂👂👂yaji! gangar jiki ya tsira👌 a kiyaye pls)






{Nasadaukar da wannan book d'in ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}








Page 97






Ko parking d'in kirki bai tsaya yi ba ya balle murfin motar ya fito da wani irin sauri sauri gudu gudu ya tunkari part d'in zahra tunkan ya ƙarasa yakejin hayaniya da hargowa na tashi , hakan yasa ya karasa a guje, idanun shine ya hango mai maryama zaune ɗare ɗare a ruwan cikin babynsa tana dukà ga kuma ga farida da atika nan suma ba'a barsu a baya ba.




Jin zuciyar shi yayi kamar an watsa mata fetir an cinna ashàna, wani irin zafi da kuna ta ɗauka, take ya shiga fidda wani irin huce, Barr irin mutanen na ne da idan ransu ya baci , idanunsu ke rufewa komai ma sukan iya aikatawa a lokacin, yana da matukar zuciya idan aka taboshi.




Dukkansu sunyi nisa babu wacce ta lura da shigowar shi falon, dunkule hannu yayi ya kaima atika naushi a gefen fuska dayake ita ke kusa dashi, take baki ya fashe jini yayi tsartuwa saiga hakora uku a kasa.




Kafa yasa ya tokari Maryama sai gata a gefe a share share a kasa, baibi ta kan wannan ba yasa kafa ya dinga ball da ita a falon ganin haka yasa farida rugawa da gudu ta shige kitchen d'in zahra ta bamo ɗofa, itama atika lallabawa tayi zata fece ya ankare da ita figo ta yayi ya hada da Maryama ya cigaba da kwallo dasu a falon idanun shi gaba daya ya rufe, baibarsu ba saida yaga kamar sun mutu, ya koma kan zahra ya dagota ya rungume gam, ta daku ko hannunta bata iya dagawa, da'ker take sauke numfashi a wahalce,ciccibanta yayi ya kaita bedroom dinta ya kwanta, dawowa yayi ya tarad da su Maryama a yadda ya barsu, wani baƙin ciki ne ya kara tirnike shi, wucesu yayi fuuu, har yakai bakin kofar fita ya sake juyowa a fusace take atika dake da sauran kwari ta fara ja baya, ita Maryama ba halin gudu dan kamar ma tayi targade a kafa takeji.




Gabanta ya tsaya ya nuna ta da yatsa ciki kausassar murya mai cike da amon bacin rai, yace "maryama! na baki nan da 10 minutes ki tattara kibar min gidana ki je gida ki koyo hankali saina nameki, karki kuskura na dawo gidan nan na tarad dake , idan kuma hakan ta faru na rantse miki da Allah na lahira saiya fiki jin dadi," dawo da kallonshi yayi kan atika yace "ke kuma shari'a daga nan har kotun koli nidake ,saikin gayamin dalilin da yasa kika bi matata har cikin dakin ta kika daketa, saina sa an daureki dan ubanki, inga uban daya daure miki gindi a Niger state" fuuu ya juya ya fita yana huci kamar wani mayun wacin zaki.




Jin tashin motar shi yasa farida fitowa daga maboyarta tana zazzare ido kamar na ƙwaɗi, cikin yarfe hannaye take cewa "mun shiga uku yaya Maryama yanzu ya zamuyi yace minti goma ya bamu" atika cikin muryar kuka tace "dan Allah Maryama ki tashi mu tafi karki bari mahaukacin mijin nan baki ya dawo ya taradda mu a gidan nan, na tabbata kashemu zaiyi har lahira" Maryama cikin wahalallalliyar murya take cewa"bazan iya tashi ba atika ya karya mun kafa ya gama dani" jin haka yasa farida cewa"bari na taro mana napep ko kama kama muyi dake yaya kibar gidan nan, shawaran da zan baki kenan, kar kice zakiyi taurin kai ki tsaya kin dai ji abinda yace" fice wa tayi a guje ta nufi get ta fece kiran napep, cikin sa'a tana fita babu bata lokaci ta samu, har cikin harabar gidan ta shigo da napep d'in tara in tara sukayi da maryama suka kawota napep d'in kafa yai tsami bai takuwa atika kam tuni baki yayi sintumtum, amma ita a yanzu wannan bai dameta ba burinta taga tabar gidan kan Barr ya dawo, har farida zata shiga napep d'in ta tsinci muryar Maryama a wahalce tana cewa"farida yarana wlh bazan bar ma maƙiyata ƴaƴana ba ki kwaso su dasu zan tafi," farida tace"kedai anty ki barsu daga baya kyau dawo ki kwashe su,kar yaya Adam ya dawo wlh a tsorace nake kar nima na samu rabona, ke ƙafa atika baki kila ni kuma ido zai ƙwaƙwulemin" ciki zafin ciwo maryama tace"dan uban ki farida ki kwaso min yarana nace" jin haka yasa farida kwasa da gudu part din maryama , a falo ta same su a rakuɓe abun tausayi hanan ta hada Kansu sun dunƙule waje daya sai kuka sukeyi, cikin tsawa farida tace"hanan tashi dan ubanki ki hado kan kannenki mu tafi" hanan cikin muryar kuka tace "anty farida ina zamu tafi" "tsaya kina tambayata karki taso dai" "anty gsky mu baza muje ko ina ba daddyn mu yace mu jira shi yana zuwa yanzu" bata tsaya jin karshen zancen ba ta finciko Ahmad da anisa, ta kama Jan hannunsu zatayi waje dasu, take hanan da suhail suka bita suna jan yan uwansu, kin sakesu tayi a haka suka fito har coumpound d'in gidan daidai nan kuma motar Barr ya shigo gidan.




Gaba dayan su saida hantar cikin su ta kada, atika hannu ta daura aka tace"mun shiga uku yau shikenan mun mutu sai gawa, mai napep dan Muhammadu rasulullahi kaja mu tafi" mai napep kam dayake irina na ne akwai son ganin kwan zomo gyara zama yayi abinshi zai ba ido hakkinsa😅.




farida kam saida fitsari ya fara kufce mata a wando tsabar razana.




Parking yayi ya fito a fusace hango yadda farida ke jamai ƴaƴa kamar wasu ukuyoyi, gadan gadan ita ya nufa.


(dama dazu bai samu ya sassaɓeta ba ita😁)




Ganin haka yasa ta saki hannun yaran ta fara ja da bawa, tana matsawa yana matsota saida suka ƙule a bango,kafa mata idanunshi da suka rine sukayi jajur yayi kafin cikin razananniyar murya mai firgitarwa, "ina zaki kaimin ƴaƴana" shiru tayi tana kara mannewa da bango kamar zatabi ta cikin bangon ta wuce, gani taki bashi amsa yasa ranshi ya kara ɓaci ware hannu yayi ya wanka mata mari, sannan cikin daka tsawa ya kara cewa"nace ina zaki kaimun ƴaƴana" still shiru kara kai mata wani Marin yayi Wanda yafi na farkon gigi tata, take ta saki sauran fitsarin da ya fara kufce mata ɗazu, ganin ta kara mai shiru yasa ya kara kai mata wani, tare da cewa cikin tsawa "baza kiyi magana ina zaki kaisu nace" tuni nunfashin farida ya fara sizing, bai damu ba kara kai mata wani marin yayi saidai yanzu kafin ya sauka a fuskarta yaji an cebe mai hannu ta baya, ganin haka yasa farida kwasa da mugun gudu ta nufi napep d'in su, tana shiga atika tace "dan kutumar uban ka mai napep kaja mu tafi, kar ya juyi kanmu wlh baida hankali idan yazo nan har kai zai hada" jin baida hankali yasa mai napep , shiga taitayin shi, ya tada napep din suka bar gidan, dan shima yaga alamar mutumin kamar baya cikin hayyacinsa.




Kallon kanin shi Dr Ali daya rike mai hannu yayi, girgiza mai kai Dr yayi yace"ya isa haka yaya kayi hakuri" bai iya amsawa Ali ba sai idanshi daya mayar kansu hanan dake ta faman risgan kuka , kamo su yayi ya rungume,yana sauke ajiyar zuciya ya dade a haka kafin suka dunguma zuwa part din zahra, har dakinta suka shiga dukkan su har Dr dan kuwa shakikin shi ne, koma ba wannan ba lafiya ya wuce wasa.






Tana kwance yadda ya kwantar da ita, hawaye na zuba a idanunta wani kan wani, abin tausayi, duk hayaniyar da akeyi a kunnenta , saidai bata jin zata iya motsa koda dan yatsa a halin da take ciki.




Cike da tausaya wa Ali yace"sannu anty zahra" jin haka yasa hanan itama tace"sorry anty zahra" su Ahmad ma suka dauka, karfin gudun hawayenta ne ya karu, Barr kam gaba daya tausayin ta ya gama cika shi saida ya fakaici idanun su ma ya share hawaye, yanzu duk akan shine zahra ta shiga wannan halin, ya rabota da garinta ya kawota inda bata da kowa sai Allah sai shi, gashi kuma ya kasa kareta daga shiga irin wannan yanayin gaba daya sai ya dauki laifin ya daura ma kanshi.




Cikin sanyin murya yace "kiyi hakuri faɗima, duk abinda ya faru lefi nane, amma na miki alkawarin zanyiwar tufkar hanci, Abu makamancin hakan bazai kara faruwa ba, ga Ali nan zai duba ki"wani kallo tabi shi da shi Wanda mai wuyar fassaruwa Wanda ita kadai tasan ma'anar kayanta.




Dubata Dr Ali yayi kuma alhmdllh ba wani babban Marsala saidai tsamin jiki, nan ya rubuta mata maganin da zai warwrar mata dashi, yace tayi wanka da ruwan dumi sosai zuwa gobe zataji garau.




Ranar kwana sukayi Barr yana jigilar kula da ita motsi kwakwkwara tayi saiya taso a zabure yana mata sannu, har saida ya far ba zahra tausayi, ta tabbatar ba karamin so Barr yake mata ba, abinci abaki ya dinga bata wanka ma shiyaso yi mata amma taki yarda badon yaso ba ya kyaleta ganin ta dage, dakin dake kusa da nata ya nuna masu hanan a kwai makeken bed a cikin dakin,kai suka hau suka kwanta ita da yan kannenta, bayan ya musu takeaway sunci sunyi nak, dan ya hana zahra shiga kitchen duk da taso tayi musu ko jellop din spaghetti ne ya hana.




Kwanan ta biyu ta ware ta dawo daidai kamar ba abinda ya faru, su hanan kuwa a iya kwanaki biyu dinnan sunyi wani irin mugun sabawa da ita saboda sakewar da tayi da su da yadda take mu'amalantar su ko mummyn su bata masu haka, ba wanda ya tuna da wata maryama a cikin su sai Ahmad da yake shi karamine, yakan ambaceta jefi jefi, dan yanzu yadda ya saki jiki da zahra ko maman shi bai saki jiki da ita haka ba, bacci kawai ke rabasu, shima a jikinta yake yi, idan yayi nisa take daukar sa ta kaishi dakin su da aka ware musu shida yan uwan shi, tamaso ya dinga kwana a wurin ta Barr ya hana.




Tsakanin ta da barrister kuwa yanzu duniya sabuwa, soyyaya suke sha na bugawa a jarida, ya sangartata sosai da salon shi, gaba daya ta gama mika wuya, shi karan kanshi ya lura da haka, amma ya bari ta kara warware da kyau, duk da ta gaya mai ta warware sosai, shi karan kanshi a matukar takure yake, dan wasannin basa mishi, amma haka yake daurewa, don gani yake yi har yanzu bata gama warware ba.




Maryama kam mai napep bai dire su ko inaba sai kofar wani karamin gida , a wani unguwa na yaku bayi, yana tsayawa suka sauka ita da farida, atika kam cewa tayi mai napep ya kaita general hospital, ko kallon su Maryama batayi ba mai napep yaja suka wuce.




Maryama kafa yaki takuwa fah jama'a, ga farida itama ta kanta take balle ta taimaka mata su shiga gida, Allah ne ya turo wani kaninta namiji, irin yan oyya dinan da ganin shi ma yana bushe bushe, zai shiga gida ya ganta yace"A'a hajiya Mairo kece, sannu da zuwa, zan samu na sigari nan " cikin muryar azaba tace "gali dan Allah taimakeni ka kama ni na shiga gida" sai lokacin ya lura da kafarta yadda ya kumbura, dariya ya kwashe dashi, tare da cewa "ke kuma wa miki eyane a kafa haka," tace "bansan surutu gali dan Allah ka kamani" yace"zan taimaka miki amma a nawa dan kinsan yanzu gwamnati ta hana aikin banza, zaki bani dari biyu in samu na korawa anjima" ba yadda ta iya dole haka ta ciro dubu daya ta bashi ya dawo mata da canji, sannan ya taimaka mata ta shiga, farida dama tuni ta shige, a tsaye suka tarad da mahaifiyar su sai sallallami takeyi ita kuma farida na zaune kan wani tsohon tabarma tana kuka, tana hango maryama ta kara karfin salatinta tana direwa tace "shike nan kin kaso auren kinji dadi sai kizo ki zauna ai ga duwawuna ga naki" tana gama fadin haka ta shige dakinta dake nan ciki daya bata kara fitowa ba kuwa saida mahaifin su Maryama Wanda suke kira da Dada ya dawo, yayi mallakin ganin Maryama a gida har war haka dan bata taba kaiwa ba in tazo inta dade awa biyu, kuma ko ruwan gidan bata iya sha, balle abinci, mamakinshi bai girmamaba saida yaga kafarta a kumbure ita kuma farida ido daya a kumbure yana Neman likewa.




Mahaifiyar su wanda suke kira da mama ta fito ta tare shi bayan ya huta yake tambayar lafiya mai ya samu Maryama da farida mai Maryama keyi a gida har yanzu bata koma ba, labarta mai abinda farida ta gaya mata " ashsha " yace tare da girgiza kai daga haka kuma bai kara cewa komai ba.


Bayan Dada ya fita sallan isha'i ne ya shigo tare da wani dan unguwar su surajo mai gyaran targade, surajo na ganin Maryama za'a ma gyara ya cije baki yana girgiza kai, surajo irin mutanan nan ne masu shegen ruko,dan tun Maryama na budurwa wani sabani ya taba hadasu, har kanin ta gali ya kira yan kaura suka mai duka, duk da a lokacin ya rama dukan da su gali suka mai dan kwana su kusan goma a cell, amma duk da haka yana nan kullace da maryama, yau kuwa gani zai mata gyara yasa ya kudiri aniyar ramawa.




Dada yace "Maryama ki gyara ga surajo na kira ya duba miki kafar nan taki, da alama targade ne" ba yacce ta iya da'ker ta mike kaɗan, surajo na tabawa ta tsallara ihu, dagowa yayi yacema Dada "wannan fa baza ta tsaya ba a samo katti su riketa " karaf a kunnen gali da abokin shi baure da suka zo daukar tuwon dare, gali yace "gamu nan mune nan kattin mu zamu daddaneta inta kamama mu ɗaɗɗaureta Allah wlh, kai shege baure matso tanan operation ya samu" magana yakeyi cikin muryar su ta shiryayyu, banace ba shiryayyu.




Baure yace "A'a'ah mairo sannu mairamu" ba tausayi haka suka rirriketa, tana ta zabga ihu ga kannenta ta nan rututu kusan rai goma maza da mata don itace ta farida gidan daga ita sai gali sai farida, Allah ne ya taimaketa ya tsamota ya hada ta da Barr ya aure ta,surajo ko tunda ya duke ya damki kafar saida ya gama luguguce shi tana ihu na kusan minti goma sannan ya fara mata gyaran tsakani da Allah.




Wayyo maryama dan azaba harda su fitsari a wando, su baure kuwa sai dariyar keta suke mata, saida aka gama gyaran, suka sake ta tare da lalemata yar wayar ta da dan kudinta da tazo dasu har ATM card dinta don pos din gaba daya suka dauke.






Bayan mama ta gama tuwo ta zubo mata miyyar kukan nan Kore shar yako ji daddawa sai kamshin shi ke tashi, da tuwan jan dawanta da aka tukashi tun wurin azahar duk ya sassandare.


Ko kallon abincin maryama batayi ba, haka ta hakura zata kwana da yunwa, bata raina kanta ba saida suka zo kwanciya, innalillahi daki daya dan karami ita da kannenta mata su kusan bakwai, gashi mutum hudu a cikin su na fitsarin kwance, wani yagalgalallan katifa ne a dakin Wanda farida dame bi mata suke kwana akai sauran kuma suyi shimfida a kasa su kwanta, da'ker farida da hansai suka sauka suka bata katifar, hansai kuwa datafi farida tsiwa sai yaɓa mata magana takeyi a kaikaice kamar zata zageta dama basu ɗasawa saboda rashin kunyarta sunfi shiri da farida.








Washe gari Dada ya nemi ganin Barr donji ta bakin shi, don baice ma Maryama komai ba tukun sai yaji ta bakin Barr da yake Dada tsohon karki ne kuma yasan mutunci sosai.




Brr bai bata lokaci ba ya same shi har shagonshi a sabon kasuwa, don nan hace yaje ya sameshi, bayan sun gaisa Dada yace"Adam abinda yasa na kiraka nan, in son miyi magana a sirrance, ka gayamin gsky tsakanin ka da Allah mai ya hada ka da matarka Maryama har kace taje gida saika neme ta"sauke kai Adam yayi komai na dawo mai fresh a ido kamar lokacin abin ke faruwa, bai boyema Dada komai ba kuwa ya zayyane mai abinda ke faruwa tun daga lokacin daya fara Neman aure har zuwa abinda ya faru jiya.




Jinjina kai Dada yayi yace"sannu Adam da hakuri Ashe haka kata fama da rashin hankalin wannan yarinya maryama, Allah ya maka

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads