Showing 177001 words to 180000 words out of 201974 words
Chapter 60 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
zaman shiru." Sororo ta tsaya can kuma ita ma
ta sakar mata murmushin yaƙe tace "ina kwana." Kama basken ɗin sharan zee tayi tace bari na taya ki zubar wa, saboda tsabar mamaki bata San ta sakar mata kwandon ba. Zee na tafiya ta mai da idon ta kan little da ke tsaye yana kallon ta, wani irin sanyi taji a zuciyar ta ta wahalu da kewar yaron, tsugunawa tayi ta maida tsawan ta dai dai nashi tace " zo my boy." Ta faɗa tana mika mishi hannu, sai da ya kare mata kallo sannan a hankali ya isa gare ta samun kanta tayi da saka shi a jikin ta ta rungume tsam, tana sauke ajiyar zuciya, zee data gama juye sharan kamar ance ta juyo, idanunta ya sauka akan abin da ke faruwa, da sauri ta dauke kanta tana sakin murmushi, abin ya burge ta lallai yarinyar bata da damuwa da alama. Gurin megadi ta ƙarasa ta bashi saƙon daya fito da ita koda ta juyo samun su tayi a gurin suna fira little sai dariya yake yi ko me take ce mishi oho. Tana isowa tace "iyyee mummy and son anata fira to me ake cewa nima a gaya min." Dagowa tayi wannan karon da murmushi gaske bana yaƙe ba ta kalle ta, taji daɗin yadda zee ta kira ta da sunan mummyn yaron, tace "sannu anty zee nagode." Zee tace."Ba komai anty Asmah." Sai kawai suka kwashe da dariya kamar sun saba da juna, zee tace "bari mu karasa ciki." Ta faɗa tana kamo hannun little maƙe kàfada yayi tare da lafewa a jikin Asmah duk dariya suka suka mai zee tace"iyee lallai yaro yaga mummyn shi na asali, to bari na barka a gurin ta zuwa anjima." Ta fada tana kallon Asmah, cikin jin dadi Asmah tace "ai kuwa nagode na samu dan taya hira." Cikin dariya zee tace "kin samu dan saka surutu dai." Kallon shi tayi tace "wai haka my son." Make kafaɗa yayi, zee tace "ai dama bazai ce eh ba sai kunje zaki gane nufi na, nidai nayi nan." Ta fada tana wucewa part din ta, Asmah ma daukar shi tayi suka shige nata part din.
Ranar tayi wunin farin ciki sai wasa take mai ta dafa mai indomie ta bashi a baki ta bashi wannan ta bashi wancen karshe har ya gaji yayi barci ta kaishi dakin ta ta kwantar, har yamma yana gurin ta, gashi ranar Aslam bai dawo da wuri ba, dan tun 2 take ta zuba ido shiru, wanka ta mishi itama tayi da yamma taci kwalliyar ta bata da kayan yara don haka tace bari taje ta amso gurin zee, koda ta fito falo ta samu ana knocking da sauri ta karasa ta bude duk a tunanin ta Aslam ne duk da bata ji diran motar shi ba, sai dai ga mamakin ta zee ta gani a bakin kofar murmushi suka sakar wa juna, Asmah tace "laa anty zee dama gurin ki nake shirin zuwa yanzu na amsar wa my son kaya sai kuma gaki shigo daga ciki mana kin tsaya a waje." Ta fada tana kauce wa ta bata hanya, zee tace "A'a anty Asmah ba sai na shigo ba naga yamma yayi nace bari na zo na dauke shi, Allah yasa dai bai miki rigima ba." "Ba wani rigiman da yayi min wasan shi ya dinga yi, yaron yana da saurin sabo ai." "Hmmm make dai kawai yayi ma haka, nima nayi mamaki sosai yadda ya aminta da ke lokaci daya yaron dake da shegen kyuyan tsiya." Murmushi tayi tace"Ki shigo mana anty zee." Zee tace "kin dai dage kar mai gidan yazo ya same ni." Dariya ta kwashe dashi tace "kaji anty zee dai to sai me idan ya ganki a nan ɗin ai abin da yayi kara shi yayi ciyawa."
Zama tayi tana ƙarewa falon Asmah kallo, masha Allah komai yaji dan babu abin da nata zai nuna ma wannan ɗin ita sai take ga kamar wannan ɗin ma yafi nata tsaruwa, ruwa da darinks ta gabatar mata, sannan ta zo ta zauna, kan kace kobo fira ya barke a tsakanin su, kamar wasu wadan da suka daɗe da sanin juna, duk rabin firan dai a kan little ne, hankalin su ya tafi har basu ji Duran motar Aslam ba sai karan doorbell suka ji, gaban zee ne ya yanke ya fadi, take ta zazzaro ido waje kamar wata mara gaskiya, yayin da Asmah ta saki wani kayataccen murmushi, mikewa tayi da sauri ta nufi kofar fuskar ta dauke da madaukakin farin ciki. Tana bude kofar ya shigo baiko lura da su zee ba ya jawota ya rungume, lumshe idanu yayi yana sauke ajiyar zuciya kicin kicin kwacewar data shiga yi ne yasa shi saurin bude ido jin wani sabon abu yau, kasancewar shike facing cikin falon hakan yasa idanun shi suka sauka akan little kafin ya gama tunanin wani abu kuma ya hango zee zaune tayi kasa da kanta, sake ta yayi tare da hade rai yayi kicin kicin kamar bai taba dariya ba, duk walwala da anashuwar daya shigo dashi kan fuskarta shi take ta bace fat, ita kanta Asmah sai da ta firgita gani yadda ya juye lokaci guda, raɓa ta yayi ya haye sama abin shi ya bar ta anan sake da baki.
Tunda ta ji dirar mota hankalin ta ya bata shine ya dawo, cike da dauki na san ganin kyakkyawar fuskar shi ta dago kai tana kallon kofar sai dai abin da ta gani ya matukar dukar zuciyar ta, har sai da taji kamar zuciyar ta zai zillo kasa ya faɗo, da sauri ta dukar da kanta ta shiga kokarin komawa da zuciyar ta, tana maimai ta innalillahi wainnailaihi rajiun, kallon ta Asmah tayi, gaskiya taji babu dadi don ko ita ne baza taji dadi ba duk da dai baisan suna falon ba, kuma ji yadda ya wuce kamar bai ganta ba, kawai sai taji zee ta bata tausayi, nufar ta tayi tana kirkiran murmushi tana magana ta shiga ta mata amma bata san tana yi ba da alama tayi nisa sosai cikin tunani sai da ta ce "Anty zee!" Da karfi sannan tayi firgigit ta dago ganin ta yasa ta saki murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo amma fa na ciki na ciki. Tace " kin gani ba kin tsai dani gashi oga ya zo ya tarad dani gaskiya naji kunya kuma duk laifin kine." Ta fada tana mike wa da nufin daukar little su tafi sai dai ga mamakin su wayam ba yaro ba dalilin shi, zaro idon da tayi ne yasa Asmah saurin juyawa, itama abin ya daure mata kai to ina little din yake, abu kamar almara babu shi a falon babu alamar shi, Asmah tace ina zuwa ko yabi "honey sama ne." Da sauri ta haura tabar zee nan gaban ta na faduwa.
Samun shi tayi zaune a bakin bed ya rage kayan jikin shi ya bar dogon wandon suit da singlet little na kamkame a kirgin shi ya rungume yaron kamar zai mai da shi jikin shi, sauke ajiyar zuciya tayi ganin yaron a nan, fitowa tayi da sauri dan ta gaya wa zee ga ya cen gurin Aslam sai dai ga mamakin ta wayam taga falon, ko shakka babu ta wuce, wannan abu bai mata dadi ba gaskiya, zama tayi na kusan mintin goma tana tunane tanane lamarin Aslam ya mugun daure mata kai, yana son danta amma yace ita baya son ta to ko shakka babu wagga batu karya ce , jiki a sanyaye ta mike ta nufi upstairs tun kafin ta tura kofar dakin ta ringa jiyo dariyar shi shida yaron kamar zasu tada dakin, da sauri ta karasa ciki a kan gado ta hango su Aslam na kwance ya daura little akan kafarshi ya daga shi sama yana mishi lilo shi kuma yana ta kwasan dariya, ikon Allah tace a ranta, wannan lamarin da daure kai yake. Karasa wa ciki tayi ya dago yana kallon ta, rasa abin cewa yasa tace "sannu da dawowa." Sauke little yayi ya mike zaune yace mata "me ya kawo ta part din nan." Tace "kamar yaya." Hararan wasa ya watsa mata tare da cewa "kamar yayo." Dariya ta kwashe da shi tace "hira tazo muyi ko haramun ne kishiyoyi suyi hira a tare." Yace "bazan hana ki ba amma wlh kibi a hankali dan da kike ganin ta haka shalau shalau ba kanwar lasa bace." Dariya ya bata wai shalau shalau ta kuwa dara sosai tare da cewa " kai dai ka sani, koma ya take ai dai zabin ka ce, kuma sai na gaya mata." "Kin daɗe." Ya fada yana mikewa "muje ni da Allah ki bani abinci naci na kwaso yunwa da gajiyar aiki."
Ranar dai a part dinsu little ya wuni, a tsakanin su sai ji dashi suke yi suna wasa dashi, cikin kankanin lokaci yaron ya saba dasu, ko tunanin su maida mata ɗanta basu yi ba har gurin karfe taran dare, Asmah ce tayi hankalin cewa "Baza mu mayar mata da shi ba, kaga dare yayi kuma ita kaidai ce a part din ta nasan tana cen tana jira." Share ta yayi, sai da ta sake maimai tawa sannan ya kalle ta yace "A nan zai kwana." Bata rai yayi ya mike tare da daukar little suka wuce sama dan ma kar ta samu daman yi mai wani magana, baya jin zai iya rabuwa da yaron koda na minti daya ne ba tare da wani kwakwarar dalili ba, zama tayi tayi shiru tana tunani, gaskiya basu kyauta wa zee ba idan suka yi haka, to amma ya ta iya, yanzu yanda ya haɗe ran nan tana magana cibi zai zama kari, a tsakiyar su yaron ya kwana ranan dan tsabar gata.
A bangaren zee kuwa hakan bai dame ta ba, sai ma dadi da ya mata, domin duk wanda ke kaunar danka ai masoyin ka ne, ko iya haka suka tsaya wlh sun nuna mata soyayya, a bangare daya kuma abin da ya faru dazu yana tsungulin ta a rai, sai dai tana danne wa , duk yadda sheɗan yaso yasa ta taga bakin Asmah taƙi yarda duk yadda zuciya ta hasaso mata sai ta kauce, ta daukar ma kanta alkawari tun da Asmah bata nuna mata wani mugun hali ba to kuwa ita baza ta nuna mata komai ba zata jata a jikin ta su zama kamar yan uwa hakan ma wani mata ki ne da zata samu kusanci da burin ranta.
Washe gari daker ya tafi aiki karshe ma cewa yayi zai tafi da yaron, daka tsallen albarka tayi ta hana, dan tasan idan har ta kuskura ta bashi wannan daman so daya ya dinga yi kenan kuma bazai maida hankali kan aikin shi ba. Yana tafiya ta dauke shi suka tafi part din zee dama sun riga sunyi wankan su sun karya. Da fara'a ta tare su babu alamun damuwa a fuskar ta, bayan sun gaisa Asmah tace "sai kika jimu shiru jiya ko." Murmushi tayi tace "ba komai ai yaro ya koma wajen Asalin mummy shi." Hakan data fada yama Asmah dadi take ita ma ta fara bata labarin yadda Aslam ya karbi yaron da yadda ya dinga mai harda cewa da yayi zai tafi dashi office, dariya zee ta ringa yi zuciyar ta wasai, Asmah ta bata wannan labarin ne dan ta faran ta mata rai kuma ta kwantar mata da hankali , aiko dai kwalliya ta biyu kudin sabulu, ranar a part din zee ta wuni tuni wani irin sabo da shaƙuwa ya shiga tsakanin su kamar ba kishiyoyi ba tare sukayi girki anan Asmah taga basu da kayan abinci sai wanda ta siya ta kuma kudiri aniyar yiwa Aslam magana, sai gurin karfe ukun rana ta koma shiyar ta ta daura ma Aslam girki, tuwon shinkafa tayi lafiyayye kuma gaba daya ta girka harda zee, tako ji dadi ta amsa tana ta mata godiya.
Cikin abinda baifi sati daya ba sun gama fahimtar juna, duk da kowacce zuciyar ta cunkushe yake da kishi musammam ma zee dan ita Asmah har yanzu bata San dawan garin ba tunda kullum tana tare da miji, zee na matuaƙar kokarin danne wa amma fa kullum Daren duniya sai tasha kuka ta gode Allah, Aslam gaba daya bata gaban shi kasancewar yanzu tana yawan zuwa part din Asmah dan tare ma suke hada dinner kullum duk idan ranar tayi rashin sa'a suka hadu takan gaishe shi, a dake yake amsa mata kuma kallo daya yake mata babu kari wannan abin shi yafi komai kona mata rai, bata da matsala ko kaɗan da Asmah sai wanda ba'aka rasa ba, little kam zuwa yanzu ya zama mai uwaye biyu yau ya kwana a nan gobe ya kwana a nan duk dai inda yaga dama.
Yau ma kamar kullum tare suka gama haɗa dinner, sunayi suna hira, Asmah ce ta fara kawo zancen Aslam cikin firan nasu, da sauri zee ta kauda maganar ta canza wata hiran Asmah ta lura sau da yawa haka take mata da ta dauko zancen Aslam zata doje, tausayi take bata sosai na yadda Aslam ya wofintar da ita, sau da yawa takan auna kanta a matsayin zee taga idan ita ake wa haka zata iya jura kuwa, duk sanda tayi wannan tunanin takan jinjina wa zee da hannu bibbiyu. Bayan sun kammala hada mata nata a basket Asmah tayi kamar yadda take yi kullum, dauka tayi ta tashi dan lokacin dawowar Aslam yayi daf, cikin tsokana tace ma little "muje." noƙe kafada yayi alamar bazai bita ba dariya suka zaka mai tace "dama tsokanar nake yi zaman ka wurin mummyn ka." Har takai kofa yace "Mummah." Ta juyo yace "kar kiyi kuka yau kinji." Kallon juna sukayi da Asmah, Asmah tace "kuka kuma?" Murmushin yaƙe tayi tace "shirmen little ne kawai rabu dashi." Tana gama fadin haka ta sa kai tabar part. Kuka kuka haka tayi ta maimaita kalman, tabbas yaro baya karya, to meke saka ta kuka ne, da sauri ta kalli little dake ta wasan shi tace "my boy Mummah ka na kuka kace." Yace "eh mana mummy kullum sai tayi kuka da daddare, ta ringa cewa Allah ya dawo mata da hankalin mijin ta,Allah yasa ya yafe mata, zuciyar ta zata fashe." Zama tayi dabass tana maimaita innalillahi wainnailaihi rajiun, lallai suna shiaga hakkin zee, baiwar Allah a she tana cikin damuwa har haka amma ko a fuska bata taba nunawa ba, kila ma tana jin haushin ta , kila ma ta ringa ganin kamar ita ta hana Aslam dawowa gare ta, tasan ba abinda baza ta ayya na ba tun da dai ita zuciya ai bata da ƙashi lallai Aslam yau ya dawo zata same shi suyi magana ta fahimtar juna.
Bayan sunyi shirin kwanciya yana zaune bakin bed yana wasa da little, zuwa tayi ta zauna a gefen shi, ta kalli little tace "my boy." Yace "na'am." Tace mema "Mummah ka ke cewa kullum idan tana kuka." Cike da rashin wayau yaron ya shiga jero wa harda wadan da bai fada dazu ba, kallon kallo suka shiga yi a tsakanin su, tace "to kaji daga bakin da bai san karya ba." Shiru yayi baice mata komai ba shi karan kanshi yasan abin da yake yi bai kyautu ba, amma bawai dan wani manufa yayi haka ba gwada ta yake yi yaga shin da gaske tayi hankalin kamar yadda ta sanar ko a'a kuma alhmdllh ya samu gamsuwa sosai da tuban nata, ya tabbatar tayi taubatan nasuhan kamar yadda ta fala kuma shima yana shirin ya koma gare ta amma shakkar Asmah yake yi, yana so ya koma gare ta,kodan fita haƙƙin ta,duk da dai har yanzu bawai yana jinta a ranshi bane kamar yadda yake jin Asmah, sai dai ya bata wani matsayi mai girma a ranshi ko ba komai ta ciri tuta domin ta kawo mishi farin cikin ruhin shi wato little......
Oum Ummeetarh
07041130088t
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALDO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu.}
Page 128
Ganin yayi shiru ya tsaya yana kallon ta alamar ya faɗa tunani, yasa tace "dan Allah ya Aslam duk abin da zaka yanke ya zama adalci, kada ka dube ni ko wani, ubangiji zaka duba ka dubu haƙƙin ta dake wuyan ka, tana zaune ne a gidan saboda kai saboda soyayyar da take maka, nasan tayi maka laifi mai girma kuma alhmdllh daga baya ta gane kurenta ta nemi yafiya, dan Allah da manzon sa ka yafe mata haka, taci koda albarkacin little ne da ta haifa maka, ka duba halaccin da ta maka, ta rainar maka cikin da ka cire rai dashi a jikin ta na tsawon watanni tara ta haife shi ba tare da sanin ka ba, ta shayar da shi ta raine shi, duk baka da masaniya ta kawo shi gareka a lokacin da kake tsananin bukatar shi, anty zee tana kaunar ka ya Aslam dan Allah ka tashi kaje gare ta ka share mata hawayen ta." Tsura mata idanun yana kallon ta har kai karshen zancen ta, ganin bai amsa ta ba,yasa ta mike ta isa gaban shi ta kama hannun shi ta shiga janshi da niyyar ta miƙar dashi tsaye, kasa wa tayi dan bai bata wannan daman ba, sai ma shi daya jawo ta ta faɗo jikin shi, dago da kanta yayi suna kallon cikin idanun juna, a hankali ya furta "ba kya kishi na ko husnah, kin dena sona ko?" Da sauri ta shiga girgiza mai kai cikin rawar murya tace "wlh ina son ka ya Aslam kuma ina tsananin kishin ka, son da nake maka ne yasa nake kwadaitar da kai kayi adalci a tsakanin matan ka domin bana so ka tashi da shanyayyen rabin jiki ranar gobe." Tana magana hawaye na taran mata a ido kamar kar ya ambaci kishi, ai sai taji hankalin ta ya fara tashi, ƙokarin