Header Ads
Showing 126001 words to 129000 words out of 201974 words

Chapter 43 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1707

Ads at the middle of Article

kamar kunne na zai tsinke" yanzu ma still bata tanka shiba saima kara cuno baki da tayi tare da mikewa tana kimtsa dinning ɗin, tattare kwanika masu datti tayi ta kwasa zuwa kitchen, ba tare da ta tanka shiba, binta yayi a baya zuwa kitchen din yana ta mata magana ta share, sai ma wanke wanke data tsiri hadawa zatayi, ganin alamar zata wàhalar dashi yasa ya shammaceta ta baya tana cikin hada ruwan kumfa taji anyi sama da ita ta baya, wutsil wustil ta fara yi tana son kwacewa amma ba hali donba rikon wasa ya mata ba, ganin dai da gaske bazata iya ba yasa ta hakura tare da yin lamo a hannun shi kamar wata yar jinjira.






Ganin ta nutsu yasa ya fara takawa da ita a hañunshi a hankali, bai diretà ko ina ba kuwa sai tsakiyar bed dinsu,kafin tayi yunkurin tashi ya bita da sauri ya danne , kokarin ture shi ta shiga yi ta kasa, hannunta ya hada duka ya rike tare da cewa cikin muryar lallashi, "haba my baby meke faruwa ne haka, wanene ya taba min ke ne haka yanzu mu fara shari'a dashi daga nan har kotun koli, uhummm, gayamin kinji babyna" kukan shagwaba ta fashe dashi tana matsar kwallah tare da cewa "ba kaibane" zaro ido yayi tare da cewa "subhanallahi ni da kaina?" ta girgiza mai kai alamar eh, yace "um umh amma kuwa ban kyauta ba dana ɓatawa babyna rai, yanzu ki gayamin laifina na hada hakuri" cikin shagwaba tace"ba Kaine nace ka dawo mana da yaya maryama ba kaƙi, kullum inna maka magana baka amsani" shiru yayi ya tsira mata idanu yana kallonta dama ya riga yasani, idan akwai abinda ke haɗa su rigima to wannan maganar ne, ta dage kai da fata itafa sai dawo da uwargidan shi, yayinda shi kuma yake ta doje wa, ya tuna yadda suka rabu yau da safe kafin ya fita aiki, duk dai akan maganar, ya rasa wani irin zuciya kega Zahra, shidai bai taba ganin mace mai kaunar kishiya ba tunda yake sai ita, kishiyar ma irin maryama wacce idan aka bata wuka tsab zata iya daba mata a kahon zuciya.




Sheshshekan kukanta ne ya dawo da shi hayyacinsa baya son bacin ranta ko kadan, rarrashinta ya shiga yi, amma sai kara sautin shashshekanta takeyi, bata bari ba kuwa saida taji yana cewa"naji naji ya isa haka baby zan dawo da ita naji na amince" tsayawa tayi da kukan da take ta kalle shi ido gaje gaje da hawaye tare da cewa "da gaske kake?" ya girgiza mata kai alamar eh, ta sake cewa "kayi alkawari" yace "nayi" tace "to yaushe " yace "yaushe kikeso " cikin zakuwa da jin dadi tace "gobe" yace "an gama amaryar Adam"kamkameshi tayi cike da farin ciki ta shiga zuba mai godiya.




Dakatar da ita yayi tare da cewa "ni wannan godiya gaskiya bata gamshe ni ba, ba irinta nake bukata ba," fuska a washe kamar ba ita bace ta gama fushi yanzu ba tace"ka fadi duk irin Wanda kake so zan maka habibi" murmushi yayi tare da raɗa mata irin Wanda yake so ɗin a kunne, da Sauti ta kai hannu ta rufe fuskarta tana dariya kasa kasa, yace "uhummm ke nake saurare ko baza ki iya bane" a kan labbanta ta "furta zan iya" kafin takai hannu a hankali ta shiga balle mai maballan gaban rigarshi.............








Rashin samun comment da yawa shekaran jiya shiya hanani karfin gwiwar yi muku posting jiya, in kuna son mu gama da wuri mu daura wani to oya naga ruwan comment masoya😍










Oum Ummeetarh
07041130088










Share
And
Comment
Fisabilillah🙏
💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~




FREE BOOK






{Nasadaukar da wannan book ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}






109








~MALAYSIA~
Bayan wata uku






Dad ɗin zee na hango zaune a cikin wani ƙaton falo mai dauke da kujeru sama da guda hamsin, a cikin falon akwai wani ɗaki mai wawakeken kofar glass, zaune yake ya zuba tagumi da hannu bibbiyu yayinda gabanshi kaɗan mum ne sai safa da marwa takeyi ta kasa zaune ta kasa tsaye, basu kaɗai bane a falon a kwai wasu mutanen amma kowa da abinda ya dameshi babu mai shiga harkar kowa,




Daga kaina nayi na kallin sunan da ke rubuce a saman dakin ~labour room~ abunda idanuna suka hango min kenan.




Suna a wannan yanayin bini bini dad kan amsa call a waya yayinda mum kam gaba daya bata cikin hayyacinta, sai yi take tana aza hannu a kai tana saukewa, can bayan kamar 30 minutes sukaga an budo kofar glass din an fito, wani mutumi ne fari sol kamar zabiya sanye da kayan likitoci ya fito daga dakin, da sauri Dad ya zabura ya mike,shida mum har suna rige rigen isa gareshi, a ruɗe. Dad ya fara cewa "Dr ina daughter ta haihun,ko har yanzu?" Mum ma cewa take "pls Dr ina daughter na, wani hali take ciki, Dr idan abin bazai yuwu ba kawai ayi mata theater" Dr kam rasa ma wani amsa zai basu yayi, ganin yadda suka tare shi, gashi shi kuma sauri yakeyi yasa yace musu"excuse me pls" tare da dojewa ya wuce su da sauri, hannu mum ta daura akai tana hawaye tare da ambaton "innalillahi wainnailaihi rajiun" Dad kam bin bayan Dr yayi da sauri saidai kafin ya cin masa ya shige wani office, Wanda babu mai ikon shiga sai likitocin asibitin, dawowa yayi jiki a sanyaye ya nemi gurin shi Nada ya kuma zama.


Tsakanin shida mum an rasa mai jarumtar rarrashin wani, kimanin awa goma kenan da suka kawota asibitin, tun cikin dare naƙuda ya tasar mata gadan gadan, ba shiri kuwa aka shige da ita labour room, saidai har zuwa yanzu karfe goman safe bata haihu ba kuma ba Wanda yace musu wani Abu game da ita, saidai kawai gani sukeyi likitoci da nurses nata zirga zirga a ɗakin.




Hankulansu gaba ɗaya yakai matukar ƙololuwar tashi, tsoron su gaba ɗaya kar su rasa
ta, itace farin ciki su, ita kaɗai suka mallaka suna matukar tsoran rasata.




A wannan yanayin maimakon su tayata da addu'a, amma ina abinka da jahilai, Dad sai zufa yake hadawa idanunshi sun rine jajur,in yayi ya lailayo ashar ya ɗura wa Aslam, yayinda mum ta kasa tsaye ta kasa zaune sai fareti takeyi tana risgan kuka.




Bayan mintunan da basu gaza goma ba wata nurses ta fito daga ɗakin, nan itama suka mata caa aka, kallon mutanen falon tayi fuskarta dauke da murmushi tace,"su wanene iyayen zainab Abdussalam" bakin na rawa Dad yace "yes mune mune" mum ma tace "eh nice mahaifiyar ta, wani hali take ciki" nurse tace "alhmdllh ta sauka lafiya yanzu an samu baby boy," tsabar farin ciki mum batasan sanda ta rungume nurse ba, Dad kuma kallonta yayi yace "nurse wani hali take ciki" cikin murmushi tace," tana lafiya yanzu haka ana gyarasu ita da babyn nan da yan mintoci za'a fito da ita zuwa ɗakin Hutu, sai ku samu ku ganta" dad" ajiyar zuciya Dad ya sauke tare da shiga jero ma nurse ɗin godiya, nan kuma ya ɗauki waya ya shiga kiraye kiraye.




Nurse kam da'ker ta samu ta kwace kanta a hannun mum ta koma ɗakin da ta fito.


Ba'afi 20 ba kuwa aka gunguro zee daga labour room zuwa ɗakin Hutu, sai lokacin su mum suka samu ganinta, tayi fiyaut da ita, ta kara haske, basu Daɗe a ɗakin ba akace su fita su barta ta samu barci sosai an mata alluran barcine, kasancewar ba karamin wuya tasha ba, tayi nakuda mai tsayi kamin ta samu ta haihu da taimakon kwararrun likitocin asibitin.




Babyn dake nannade cikin farin shawel an mishi wanka an shiryashi cikin tsadaddun kayan sanyi aka mikoma mum, hannu na rawa ta karɓa, tsurawa yaron idanu tayi tana kallo, Dad dake tsaye ganin haka yasa shima ya matso don yaga mai take kallo haka, abinda ya faru da mum ne shima ya faru dashi, kallon yaron sukeyi babu ko keftawa.




Bacci yake yi idanunshi a kulle fari sol ƙato da shi mai kama da Aslam sak, babu abinda ya banbantasu,kwata kwata bai dakko komai na zee ba, duk da mum da Dad basa kaunar Aslam hakan bai hana ɗanshi samun kyakkyawan matsuguni a zuciyoyin su ba, farat daya yaron ya shiga ransu, a kallo na farko.




Gaba ɗaya sun shagala da kallon yaron saida sukaji, muryar nurse tana musu magana sannan suka dawo hayyacinsu,saƙon Dr ta sanar musu na cewa da yayi su same shi a office, Dad ne yabi bayan nurse din zuwa office ɗuin Dr yayinda mum ta rungume yaron tsam a kirginta tanajin wani irin son shi da kaunar shi na huda kofofin zuciyarta.




Saida zee ta kwashe awa shidda kwarara tana barci kafin ta farka, wuraren la'asar, zuwa lokacin kam asibiti ya cika makil da yan'uwa da abokan arziki yan gayu masu abin hannu,yawancin su ma turawa ne wadan da su mum ke hulɗa dasu, kowa ya dauki yaron nan kallon daya zakaji ya shiga ranka, da alama dai baiwarsa ce hakan.




Zee ta farka da sauƙi sosai don bayan Dr ya duba ta, ya tabbatar musu nan da gobe ma za'a iya sallamarta taje gida abinta, bayan mum ta bata shayi mai zafi tasha ta kuma sha magunguna, sannan aka bada daman mutane su shiga su dubata, kowa barka yake mata, bata iya amsawa sai smiling kawai take musu, lokacin da aka bata babyn kuwa tsura mishi idanu tayi tana binshi da wani irin kallo, babu abinda take gani a fuska da jikin yaron sai Aslam dinta, take wani irin kewa da kaunar mijinta ya turniketa, rungume yaron tayi sosai a jikinta tana jin wani irin kaunar shi na huda zuciyar ta, bata San sanda ruwan hawaye ya wanke mata fuska ba, ta shiga risgan kuka harda sheshsheka, ganin haka yasa mum ta miƙa mata hannu alamar ta bata yaron girgiza mata kai tayi alamar A'a dole mum tayi hakuri ta bar mata abinta.




Zuwa dare babyn ya fara kuka, Dr yace ya kamata a bashi abinci yunwa yakeji, Dad yace Dr ya rubuta musu madaran da za'a dinga bashi yaje ya siyo, da mamakin su ji sukayi zee tace , A'a kar a siyo madaran ita zata shayar da ɗanta, Dr yace well dama haka ake bukata, nan wata nurse ta gyara mata shi sosai ta koya mata yadda zata rikeshi a yayinda da zata shayar da shi, nonon aka sa mai a baki ba shiri kuwa yaro ya kama yana tsotsa, duk da matsanancin zafin da takeji hakan baisa ta fasa shayar dashi ba, nurse din data fahimci tanajin zafi ta shiga kwantar mata da hankali da cewa karta damu zai daina, idan ya kwana biyu yana sha, shikenan baza ta kara jin zafi ba kuma.




A asibitin suka kwana zuwa washe gari ta ƙara samun sauki sosai don haka Dr ya rubuta musu sallama suka dawo gida, kulawa sosai zee ke samu daga gurin iyayenta ita da little Aslam dinta, wata babban nurse mai zaman kanta, wayayya mai wadataccen ilmi Dad ya daukar musu ita ke kula da komai nasu ita da babyn bangaren wanka tsaftar su da abincinsu, kai komai ma daya shafe su.




Zee taji dadin yadda iyayenta suka karbi yaron da yadda suke nuna mai kauna da kulawa, bata taɓa zaton haka ba, ganin yadda suka dauki karan tsana suka dorawa uban ɗan.


Kafin sati ya zagayo tayi bulbul ita da babynta gwanin sha'awa, jego takeyi na yayan gata, baza ayi taron suna ba, raɗin suna kawai za'ayi dad ne ya siya duk wani abinda ake bukata na radin suna kamar rago da sauransu,tambayarta sukayi sunan da take so a saka ma ɗanta babu kunya ko kara tace Muhammad Aslam, haka ko akayi, duk da Dad yaso ace sunanshi ta zabar wa yaron.


(kuji min Dad da ƙoƙari wai da sunanshi ta zaba😒 babu kunya ba tsoron allah cikin da yayi niayyar hallakawa)


Hankali kwance take jegonta bata da matsalar komai babu abida ke damunta sai kewar mijinta, bayan haihuwartan nan , abin ma saiya daɗa nunkuwà, kullum dashi take kwana take tashi a zuciyarta ji take kamar tayi tsunstuwa ta ganta a agabanshi, ta mika mishi ɗanshi, cikin farin ciki,ta kusa kai matakin da baza ta iya jurewa ba, jira takeyi yaronta yayi kwari, ta lashi takobin zata koma gidan mijinta koda son ransu ko babu, koda tsiya koda tsiya tsiya.









~9ja~








Yau kimanin wata biyar kanen da auren yan matan mummy,kuma har zuwa wannan lokacin cikinsu babu wacce ta taba zuwa gida da sunan ganin gida, kowacce tana gidanta hankali kwance, duk da kuwa cikinsu ba wacce batayi nacin son zuwa gida ba amma mazajen suka hana wannan kuwa umarnin alhaji baba ne.






Soyayya kamal da khadija ba'a magana, tattalin da kulawa suke ba juna na musamman, idan kaga yadda suke gudanàr da rayuwarsu zaka dauka sunyi shekara goma suna soyayya kafin suyi aure, a halin yanzu Khadijah Nada cikin ta dan wata huɗu.




Haka ma Amir da Amira sukam bama a magana, kalar nasu salon soyayya ta dabance, basa jin kunyar uban kowa a gaban kowa nuna ma juna soyayya sukeyi, ƙiri ƙiri mutane suka guji zuwa gidansu, saboda idan kaje indai kana da kunya, ta baza ka iya awa ɗaya a gidan ba,suma dai a kwai cikin ɗan luv, saidai fatan Allah ya raba lafiya.




Su batool ma yanzu komai nomal,babu abinda suke sai shan soyayya da cokali mai yatsu, bangaren yadda sukeji da cikin su kuwa ba'a cewa komai,tunkan a haife shi, shikaran kanshi cikin yasan shi dan gata ne, abinka da masu abin duk sati ake scanning, ta bangaren maah ma ba'a barta a baya ba, duk abinda ta gani indai na jariri ne siya takeyi ta ajiye, abin kwalama kuwa na masu cikin kullum cikin yi takeyi tana aikama batool dashi, bama ci takeyi ba wani bin saidai Dr yaci idan Wanda zai iya cine, ita dai barta da cabbage dinta, yanzu kam an samu ci gaba ta daina cinshi gaya, saidai ta kwada da kulikuli taci, rigima kam yayi sauƙi a gurin batool saidai kunsan ance mai hali baya fasa halinsa, duk da haka duk randa ya tabota haka zata kwana tana masifa, musamman yanzu da wata Dr a gurin aikinsu ta nace tana sonsa, tunda batool ta samu labari ya shiga uku ko minti talatin ya kara akan lokacin da yake dawowa haka zai sameta ta cika tayi fam, komai zai ce mata baza ta yarda ba kawai gurin Dr basira ya tsaya, kishin sa take sosai da sosai ji take da tana da hali da nikab zata saka shi ya dinga sakawa, saukin shi ma yanzu yana da loggonta data fara zai lalubeta ya fara sakar mata zafafan romance daga nan zancen zai mutun sai kuma na gobe.




A bangaren zahra kam, yanzu babu abida zamu ce sai alhmdllh, tsakaninta da miji babu komai sai tsantsar soyayya da kaunar juna, da gasken fa baby take a gurin Barr Adam ji yake da ita kamar Yar jinjira, musamman yanzu data samu ciki, kula yake bata na musamman kamar ya hadiyeta, tsakanin da maryama yanzu kuwa babu komai sai girmama juna da mutunta juna, dama zahra kwata kwata bata da matsala, matsalar daga maryama ne, kuma a halin yanzu gaba daya tayi laushi, bayan dawowarta Barr a gaba ya sakata ya mata nasiha tare da sanar da ita wlh ta gode ma Allah daya haɗa ta da kishiya irin Zahra bata samu mai irin halinta, nan ya sanar da ita cewa zahra ce ta tirsasa shi ya dawo da ita badan haka ba da har yanzu tana cen, take taji wani nadama ya shige ta lallai ta gode ma Allah dabai haɗa ta da mai irin mugun halinta ba don ta Tabbatar inda itace a matsayin zahra,da wlh zahra tabar gidan kenan har a bada asaidai a bita da takardan ta, tayi nadama, ta tuba taubatan nasuha, washe gari kuwa har part ɗin zahra taje ta same ta nemi gafarar abinda ta mata, Allah sarki zahra dama bata riketa a raiba, nan dai tace ta yafe mata, tashi tayi ta rungume ta tana mata godiya, a haka Barr ya samesu, ba karamin dadi yaji a ranshi ba, take ya haɗa su ya nusu nasiha, tare da nuna musu irin tsantsar farin cikin da yake ciki a ranar saboda hada Kansu da sukayi, tun daga ranar kuwa suke zaune lafiya abin su, yara yanzu sun zama yan gata masu uwaye biyu, maryama suna kiranta da mummy zahra kuma suna kiranta da mum, dakinsu nanan a part din zahra data ware musu, lafiyayye Dan yama fi dakinsu na part din maryama haɗuwa, in sunga dama su kwana a gurin mummy insun ga dama su kwana gurin mum, maryama ce ta fara gane zahra nada ciki, aiko dai tayi farin ciki har zuciyar ta, take ta shiga tsokanarta tana kiranta da maman yan biyu, tun zahra na daukar abin da wasa har dai lamarin ya tabbata, saidai muyi fatan Allah ya raba lafiya.




A bangaren su Asmah kam yanzu sun wuje romeo da Juliet, soyayya suke zubawa kamar zasu cinye juna, da'ker da sidin goshi Asmah ta samu Aslam ya koma wajen aiki, shima da yarjejeniyar, yana aiki suna video call, haka dai tace mishi ta yarda, ta samu ta lallabashi ya tafi ranar farko daya fara zuwa, yana isa ko office bai shiga ba ya kirata ƙin ɗagawa tayi dan burinta a halin yanzu bai wuce ya maida hankali kan aikinshi ba, cikin abinda baifi awa daya ba ya mata missed call yafi hamshi ta share, aiko dai ko Rabin a waya bai kara ba saijin horn din motar shi tayi ya dawo, washe gari kuwa kin tafiya aikin yayi, ganin dai da gaske yakeyi, yasa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads