Header Ads
Showing 150001 words to 153000 words out of 201974 words

Chapter 51 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

2095

Ads at the middle of Article

mashin din sai sunyi sama duwawunsu ya rabu dakan sit din mashin din sannan su dawo su zauna daɓar, tuni beebaloo ta fara kuka hawaye uku uku, basu suna sauka akan kabu kabu ba saida sukayi tafiyar awa biyar kwarara.




A wani dan tsukukun kauye suka sauka, a tunanin beebaloo sun ido ne, amma sai taji hajo na cewa "a nan zamu kwana beebaloo gobe da asuba ba sai mu daura da kafa mu karasa aslin kauyen da mallam kamsusi yake, da kafa zamu karasa domin daga nan ne mashin ke iya tsaya wa a gaba babu hanyar mashin."


A wargaje beebaloo ta zaro idanunta da suka kankance sukayi jajur tsabar azaba tace "hajo kina nufin dama ba nan bane asalin inda muka zo." Hajo tace "eh ba nan bane karki damu kawata munyi rabi, ni na saba zuwa ,kema dan yaune zuwanki na farko yasa kike ganin wahalar shi.




(Hmmm akace sa kai yafi bauta kuji hajo wai ta saba zuwa)






A nan dan tsukukun kauyen suka kwana, inda suka dunga bin gida gida daker suka samu wacce ta amshe su ta basu dakin awaki su kwana a ciki, ba tare da damuwa ba hajo ta shiga ta nemi guru ta zauna, babu alamar damuwa a tare da ita da alama dai ta shiryama faruwan hakan.


A darare bebalo ta samu guri itama ta rakube, a haka gari ya waye musu, hajo tadan gyangyada yayin da beebaloo idanunta Kamas, yadda taga dare haka taga rana, duk wannan azabar wahalan da suke sha,idan ta tuna at the end zata mallaki aslan ɗinta sai ta saki murmushin farin ciki.




Da asuban fari suka dauki hanya suka fara shatatawa da ƙafa babu batun sauke farali bare salati, tun suna tafiya suna dan taɓa fira har kowa yayi gum sai Jan kafa sukeyi shakataf shakataf, jefi jefi sunan hadu da mutane a hanya wasu na shiga kauyen wasu na fitowa, a haka suka hadu da wata a gwai suka sayi fura da nono babu ko suga suka shiga kwankwaɗa, basu suka shiga asalin kauyen da mallam kamsusi yake ba saida rana ta take, sun tarar da layi sosai, amma basu damu ba, hankalin beebaloo ya kwanta ganin ta gata ga bukkar mallam kamsusi, inda take da tabbacin zai share mata kukan ta gani takeyi kamar ta auri Aslam ta gama.......












Shin mai ya faru ne burin beebaloo na auren Aslam bai cika ba har yau, duk da kuwa zuwa wajen mallam kamsusi da tayi, ku biyo diyar nalado danjin yadda z
aka kaya.












Oum Ummeetarh
07041130088










Share
And
Comment
Fisabilillah🙏
💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~




FREE BOOK








{Nasadaukar da wanna book din ga suka wacce ta rasab mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}






Page 118










Saidai sukayi zaman fiyye da awa uku sannan layi yazo Kansu, zuciyar beebaloo wasai yau tazo inda take da tabbacin za'a share mata kukan ta, tare suka shiga cikin bukkar mallam ɗin ita da hajo, guri ya nuna musu suka zauna kan shimfiɗar buzu, so ɗaya beebaloo ta iya kallon fuskar mallam kamsusi da sauri ta dauke kai gabanta na faɗuwa, duk inda muni yake Allah ya tattarawa mutumin nan, baƙi ƙirin dashi, gashi dan cukuli kamar a kife da kwando sai katon kai, yasha wani uban rawani ƙato a kanshi, gaban shi kuma kasa ne mai kyau fari tas , hannun shi rike da wani dogon carbi irin mai guda dubu ɗinan yana ja sai wani musmus yake yi da baki.


Tun shigowar su ya kafe mici micin idanunshi akan beebaloo, yana kare mata kallo daga Sama har kasa, yana sauraren radar da aljani dan misra ke mai a kunne game da ita, lallai ta tafi da nutsuwa shi, gani ɗaya yaji ranshi ya biya kuma bawai na lokaci daya ba inso samu ne yana bukatar ya aureta, ido ya zura mata kamar mai bukatar hango wani abu a jikinta yayin da ita kuma ta kasa kara dagowa ta kalle shi.


Hajo ne ta fara cewa cikin dukar da kai da tsantsar ladabi "barka da war haka ya babban malami,
malamin malamai na duniya baki daya, gani na sake dawowa gareku da bukatata,fatan na same ku lafiya" sai lokacin ya dauke idanunshi akan beebalo ya dawo da shi kan hajo, fuska a murtike babu alamar fara'a yace "mun amsa gaisuwa hajo, fatan kin isa gida lafiya" tace "lafiya lau mallam aiki yayi kyau tun kafin na ƙarasa gida ma komai daidaita yanzu haka ko kara na ajiye baya iya tsallakewa." Sai lokacin mallam kamsusi ya saki wani shegen murmushi, cikin sa'a saidai lokacin beebaloo ta ɗago kai da niyar ta saci kallon shi a karo biyu, idanunsu ya sarke dana juna, ba shiri ta mayar da kai kasa tana karanto duk addu'an daya zo bakinta, ita wallahi tsoro yake bata, gaba daya fuskar shi kamar ta buri hancin nan a nane.




Lokaci daya ya maida fuskar shi ya murtike sannan ya fuskanci hajo yace"kwarai kuwa muna da labarin komai domin tun kina nan gabanmu zaune muka aika dan auta yaje ya cika miki aiki,yanzu me ke tafe dake." Hajo tace "Allah yaja zamanin babban malami wannan kawata ce itace na rako gareka da bukatar ta." Maida kallon shi yayi kan beebaloo, yana ci gaba da binta da wani irin mayen kallon har wani lashe lips yakeyi kamar wani tsohon maye.




Saida ya kalleta son ranshi sannan yace"menene bukatar ki." Firgita tayi ta kara kasa da kai jikinta na rawa jin yana mata magana, shiru tayi ta kasa magana, ganin haka yasa hajo ta mika hannu ta tsunguleta a gefen ciki, dagowa tayi ta kalli hajo suna hada ido ta mata alamar yi magana mana, baki na rawa tace"ma malam, umm dama dama, wani ne Wanda nake son ya aure ni, nake son shi, shi kuma baya sona kwata kwata baima San kalar fuskata ba, shine nake son dan Allah a taimaka min ya soni ya aure, dan Allah mallam."




Tunda ta fara magana mallam kamsusi ke gyada kai,shi kadai yasan me yake sakawa a ranshi, yace "to zamu taimaka miki mu miki abinda ya dace, kuma bama bukatar ko sisin ki, zamu muki aiki da zaici kamar yankan wuka, amshi nan" ya karashe maganar yana mika mata wani Abu nanade cikin ganye, hannu na rawa ta karba tana godiya ammafa idanunta na kallo gefe don ta kasa haɗa ido dashi, yace" kije ki daka wannan ciyawar ki shanya ya bushe ki raba shi gida biyar ki jiƙa kashi ɗaya kisha, kashi ɗaya ki zuba a ruwan wanka, kashi ɗaya kiyi hayaƙi dashi kashi ɗaya ki zuba a baki ki tattauna kashi daya kuma ki kwaba da fitsarin ki ki shafe a jikin ki da daddare idan zaki kwantar, to insha Allah in dai kikayi yadda nace zaki mallake shi duk inda kike zai biyo ki ya aureki, zai soki sonda bai taba yiwa wani mahaluci a duniya ba, zaki juya shi sai yadda kikayi da shi da dukiyar shi." godiya suka shiga jero mai ita da hajo kamar bakin su zai tsinke.




Dakatar dasu yayi mici micin idanunshi nakan beebaloo sai murmushi yake yi, yana lasar lips, lambar wayar shi ya rubuta ya mika beebaloo dan yasan tabbas ta aikata abinda ya umarceta daidai dole zata bukaci lambar shi.






Yadda suka shatata da kafa sukaje haka suka kara shatatowa suka fito saidai wannan karan ko kadan beebaloo bata ga wahalar hakan ba tunda ta samu biyan bukata, dan gani take kamar ta auri Aslam ta gama, banda yadda zata sha soyayya da Aslam da yadda zata zuba mulki a gidan shi babu abinda take tunani,sai alkawarurruka take ma hajo kala kala, harda cewa ita ce zata zama mai bata shawara na hannun daman ta, a wannan tsukukun kauyen suka kara kwana washe gari suka kara hawa kabu kabu ya fitar titi suka samu mota suka dawo gida.




Koda ta dawo bata bi takan faɗan da iyayenta ke mata ba suna tambayar ta ina ta je ta kwana har kwana biyu, tace musu tafiya tayi kuma bata ga daman ta gaya musu bane,taja tsaki tare da shigewa dakinta ta banko kofa yana gungumi da kananun zage zage ƙasa ƙasa.




Kuka mahaifiyar ta ta fashe da shi, tana cewa "ni kike zagi beebaloo insha Allah saikin haifi wacce zata miki dukan tsiya kije kici gaba duniya ce ai faɗi gareta." Mahaifinta ne ya shiga rarrashin mahaifiyar ta, yana kwantar mata da hankali da cewa"yi hakuri marka baryi mata baki, aiko baki buɗi bakin ki kince komai ba, wannan hawaye da tasaka kika fitar hakkin su ya ishe ta." Cikin kuka mahaifiyar ta tace"mallam barni nayi mata baki, wannan wannan baza taga annabi ba, taƙi zaman aure tasa ana zagin mu a gari, sannan mu kuma a gida bata kyale mu ba, cin mutuncin yau dabam na gobe dabam, aiko bamuyi tsirar komai ba baci albarkacin haihuwar ta da mukayi, wasu ma banza da bamu Haifa ba sun girmama mu balle ita." Girgiza kai mallam yayi cikin tsananin takaici, yace "wallahi babu abinda yafi ban takaici game da beebaloo irin kin zaman aure da tayi abin yana taɓa min zuciya bani fatan na mutu na barta a haka tana gantali."


Tana jinsu daga ɗaki sai tsaki takeja, tace " yen yen yen yen, mugaye kawai yan bakin ciki, zanyi aure ai zan auri zabin raina cikar burina, kyakkyawa mai kuɗi dan babban gida, wallahi inna yi kudi bazan taimaka muku ba yadda na same ku a tsiya ce haka zan barku ku mutu a tsiya ce." Ita kadai take ta sababin ta basu ma San tanayi ba.




A ranar ko hutawa batayi ba ta aikata duk abinda mallam kamsusi ya umarce ta dayi, cike da annashuwa take aiwatar da komai, duk yadda yace mata haka tayi ba tare da ta yi mistake ba, da tazo kwanciya tayi fitsayi ta kwaba kashi na, karshen ta shafe jikin ta da shi, takwanta da yaki nin ta auri Aslam ta gama.




Washe gari beebaloo ta farka da wani saban lamari, tun da ta farka taji a rai da zuciyar ta babu Wanda take son gani sai mallam kamsusi, zuciyar ta babu Wanda take so da kyauna sai mallam kamsusi, da ta rufe ido mummunan fuskar shi ya mata gizo, zuciyar ta har wani tafasa takeyi saboda tsananin kaunar shi, ji takeyi idan bata sanya shi a ido ba zuwa dare zaucewa zatayi tuni ta manta da wani Aslam, mallam kamsusi kawai take ji da gani, hannu na rawa ta jawo Jakarta ta zaro number shi daya bata, ba shiri ta antaya mai kira, yana daga wa, ta sauke wani wawan ajiyar zuciya kamin baki na rawa ta shiga gaishe shi, tare da cewa "mallam beebaloo ce kawar hajo." Daga cen bangaren yace "nagane ya akayi beebaloo." Take ta fashe da kuka kafin kuma ta tsinci bakin ta da cewa "mallam dan girman Allah ka taimaka ka aureni wlh sanka nakeyi, bazan iya rayuwa babu kai ba, na fasa auren Aslam ɗin yanzu kai nakeso na maji na tsane shi kwata kwata a rayuwar dan Allah ka taimakeni ka taimakeni ka aure mallam." Wani shedanin murmushi mallam kamsusi ya sake tare da cewa "karki damu beebaloo zan taimakeke na aurenki kamar yadda kina bukata, zaki zauna dani inada mata biyu, kuma a wannan kauye da kikaje anan nake rayuwa ta kin amince zaki zauna acen." Baki na rawa tace "wlh mallam na amince ko ta biyar ce ni na yarda, kauye kuwa ko gaba da nan ne zan je." Yace "to shi kenan ki sanar da mahaifan ki zanzo jibi."




Kafin jibin kullum sai ta kirashi fiyye da so goma a rana, ta zama wata zautacciya soyayyar mallam kamsusi kawai ke nukurkusar zuciyar ta,gaba daya bata cikin haiyacin ta, ta sanar da iyayen ta za'a zo Neman aurenta jibi, mahaifinta dan murna kamar ya zuba ruwa kasa yasha, ko ba komai zai rabu da mugun iri.




Jibin kuwa mallam kamsusi ya dira a cikin garin minna shi da mukarraban sa su uku, ba ɓata lokaci ya kira beebaloo, da kanta tazo ta tare su, jikina rawa ta masu jagora har cikin zauren gidan su saida ta gabatar musu da lafiayyen girkin da ta musu suka cinye Tass suka kora lemon kwalba sannan ta musu iso gurin mahaifinta, wanda shida kanin shi da abokin shi ne suka tare su.




Mahaifinta yayi mamakin ganin mal kamsusi amatsayin Wanda beebaloo ta tsayar zata aura, kasancewar ya San burin beebaloo nasan auren mai kuɗi kuma kyakkyawan na miji, amma wannan ai ko cikin munanan sarkin su ne, yadda take ta rawan jikin ya dauka wani shahararraen dan masu dashin da take burin aura ne ta samu.


Cikin abinda baifi awa daya ba suka gama tsayar da duk abinda zasu tsayar ciki harda daura auren beebaloo da mallam kamsusi, a ranar kuwa ya bukaci tafiya da ita,ba Wanda ya hana shi matar shi, suma iyayen nata neman kai suke da ita, itama kuwa burin ta kenan ta ganta gidan shi matsayin matar sa shine kwanciyar hankalin ta.


Mutum biyu ne kawai suka mata rakiya daga kanwar mamarta uwa daya uba daya sai, kanwar ta mai bi mata da take aure nan kusa da su da ƴaƴan ta biyar.




Tun a hanya yan rakiya suka fara shan jinin jikin su, itako beebaloo ko a jikinta, basu shiga tashin hankali ba saida suka ga yadda ake ta zurarawa da su cikin gungurmin daji a mashin, tafiya yaki karewa, hankalin su bai idasa tashi ba saida akazo gurin tafiya da kafa, sunayi suna hutawa ,kanwar mamarsu kuwa sai zagin beebaloo takeyi take, tana cewa da tasani da bata zoba, a galabaice suka isa.


Gida ne fankacece mai dauke da dakuna hudu ƙananan, daya uwar gidan daya na mai bi mata daya na miji sai daya na yara wanda nan aka gyara wa beebaloo,abinda yaba yan rakiyar beebaloo matukar mamaki, yadda suka ga da murna da farin ciki sauran matan mallam kamsusi suka amshe su, tuni suka gabatar musu da tuwan dawa da miyar gari harda ruwan randa mai sanyi, gaba dayan su ba wacce ta iya hadiye lomar farko na tuwon, saboda rashin dadin sa mayar salam sai uban yaji, karshe da yunwa ta ciwo su dole dama tuwan sukayi suka sha shi kamar koko, Allah Allah suke gari ya waye su baro kauyen.




Da safe uwar gidan mallam kamsusi ta kawo musu kunun garin dawa da dumame, cikin fara'a ta gaishe su babu alamar kishi ko kaɗan a fuskarta, kasa hakuri kanwar beebaloo tayi tace"baiwar Allah naji ance mana kece uwar gidan shi, kuma banga alama ba nace koba ke bace." Cikin washe baki tace "wlh nice uwar gidan shi." Da mamaki ta kara ce mata"shine babu ko alamar kishi a fuskar ki." Kallonta matar tayi da mamaki tace"kishi fa kikace baiwar Allah,kishin wa?kishin mallam wai, aini idan yau mallam zai karo wata matar ya cike ta hudu sai nafi kowa farin ciki, ko ba komai raba kwana zamuyi, aini nafi kowa farin cikin da auren nan na mallam badan kar nayi karya ba da sai nace har shi nafishi farin ciki da auren, kardai na cika ku da surutu bari na barku ku kimtsa." Ta faɗa tana mikewa ta fice, kallon juna yan rakiyar beebaloo sukeyi, cike da mamakin wanga lamari, to duk yadda akayi a kwai lauje cikin nadi.........










Oum Ummeetarh
07041130088






Share
And
Comment
Fisabilillah🙏
💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~




FREE BOOK






{Nasadaukar da wannan book ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}






109








~MALAYSIA~
Bayan wata uku






Dad ɗin zee na hango zaune a cikin wani ƙaton falo mai dauke da kujeru sama da guda hamsin, a cikin falon akwai wani ɗaki mai wawakeken kofar glass, zaune yake ya zuba tagumi da hannu bibbiyu yayinda gabanshi kaɗan mum ne sai safa da marwa takeyi ta kasa zaune ta kasa tsaye, basu kaɗai bane a falon a kwai wasu mutanen amma kowa da abinda ya dameshi babu mai shiga harkar kowa,




Daga kaina nayi na kallin sunan da ke rubuce a saman dakin ~labour room~ abunda idanuna suka hango min kenan.




Suna a wannan yanayin bini bini dad kan amsa call a waya yayinda mum kam gaba daya bata cikin hayyacinta, sai yi take tana aza hannu a kai tana saukewa, can bayan kamar 30 minutes sukaga an budo kofar glass din an fito, wani mutumi ne fari sol kamar zabiya sanye da kayan likitoci ya fito daga dakin, da sauri Dad ya zabura ya mike,shida mum har suna rige rigen isa gareshi, a ruɗe. Dad ya fara cewa "Dr ina daughter ta haihun,ko har yanzu?" Mum ma cewa take "pls Dr ina daughter na, wani hali take ciki, Dr idan abin bazai yuwu ba kawai ayi mata theater" Dr kam rasa ma wani amsa zai basu yayi, ganin yadda suka tare shi, gashi shi kuma sauri yakeyi yasa yace musu"excuse me pls" tare da dojewa ya wuce su da sauri, hannu mum ta daura akai tana hawaye tare da ambaton "innalillahi wainnailaihi rajiun" Dad kam bin bayan Dr yayi da sauri saidai kafin ya cin masa ya shige wani office, Wanda babu mai ikon shiga sai likitocin asibitin, dawowa yayi jiki a sanyaye ya nemi gurin shi Nada ya kuma zama.


Tsakanin shida mum an rasa mai jarumtar rarrashin wani, kimanin awa goma kenan da suka kawota asibitin, tun cikin dare naƙuda ya tasar mata gadan gadan, ba shiri kuwa aka shige da ita labour room, saidai har zuwa yanzu karfe goman safe bata haihu ba kuma ba Wanda yace musu wani Abu game da ita, saidai kawai gani sukeyi likitoci da nurses nata zirga zirga a ɗakin.




Hankulansu gaba ɗaya yakai matukar ƙololuwar tashi, tsoron su gaba ɗaya kar su rasa
ta, itace farin ciki su, ita kaɗai suka mallaka suna matukar tsoran rasata.




A wannan yanayin maimakon su tayata da addu'a, amma ina abinka da jahilai, Dad sai zufa yake hadawa idanunshi sun rine

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads