Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 201974 words

Chapter 3 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1694

Ads at the middle of Article

gaba da shi kafin Allah ya kawo mata wani mijin "




Sannan Abu na gaba"abdullahi ,Aisha,Yusuf, maryam da amina, inason Ku zama shaida na kamar yadda aslam ya Nina baya qaunar zabina asmah, to naji amince, amma babu aure zakanin shi da asmah a nan gaba na harantashi.......na haramta aure tsanin Muhammad da asmah ko bayan raina ban amince ba duk Wanda ya sake bashi auren asmah ko bayan raina ban amince ba,"




"Abu na karshe kai Muhammad ka sanar da iyayen ita yarinyar da kake so din cewa rana ita yau iyayenka zasu shigo gida ayi magana"


Yana gama fadin haka ya miqe yabar parlon matarsa ma bin bayanshi tayi don ta rarrasheshi ganin ranshi ya baci sosai ,


Daddy ne ya fara miqewa yabar parlon Mummy ma bin bayansa tayi ko kallon inda aslam yake basuyiba , ummi ma da ranta ke matuqar bace da abinda aslam yayi ta kama hannun asmah suka fice daga falon,


Sosai abbah kema aslam fada mami na taya shi saida suka tabbatar jikinshi yayi sanyi sannan suka qyaleshi ganin dare yayi
đź’–DAMA TA BIYUđź’–


BY


~AYSHA NALADO~


FREE BOOK




{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}


Page 15 & 16




Sosai abbah kema aslam fada mami na tayashi.. Saida suka tabbatar jikin shi yayi sanyi sannan suka qyaleshi ganin dare yayi, bayan sun qara tabbatar mai lallai lallai ya nemi gafarar iyayen shi da kuma alhaji baba domin fushinsu a gareshi ba alkhairi bane.....dole aslam ranar a gida ya kwana don dare yayi sosai,




Washe gari gida ya tashi a hautsine sakamakon farkawa da sukayi da wannan mummunan labari ...


Baqi da sukazo daga nesa duk suna nan wasun su dama yau zasu wuce, sai ga wannan labari mara dadi,


Duk wani masoyin wannan familyn saida yaji ba d'ad'i akan abin da aslam ya aikata...abune da bai taba faruwa ba a tarihin familyn ...yayinda a daya bangaren wasu da dama keta farin ciki da faruwan hakan kamar su zuna ruwa a qasa su sha saboda tsabar farin ciki, bama kamar zeee don tuni labari ya isketa kunsan abin duniya baya boyuwa mussan abin da bana alkhairi ba irin wannan an dinga yama d'id'i dashi kenan,


Alhaji baba da kanshi ya sanarma kakan asmah Wanda yake babban aminin shi abinda ke faruwa, bai samu halartar bikin ba saboda baya qasa yaje aikin hajji kasancewar lokacin aiki haji ne... baiji d'ad'i ba amma kuma haka ya d'auki qaddara karshema shiya koma rarrashin alhaji baba Dan ganin alhaji baba yafishi d'aukan zafi akan lamarin ...


Baqi dangin mahaifin asmah da dangin mahifiyarta da suka zo daga garuruwa mabanbanta don halarta bikinta a ranar suka jujjuya da labari Mara dadi ...suka bar asmah a gidan ba wanda yace zai tafi da ita tunda sunsan nan ne gidanta don tun tana qarama alhaji baba ya d'aukota bayan rasuwar mahaifanta yazo ya danqata a hannun mummy da daddy suka zame mata sabbabbin iyaye suka hadata da nasu yayan suka riqe ba tare da sun nuna mata wani banbanci ba ,,, yayinda a gefe guda alhaji baba da alhaji Mallam kankan asmah su kadai suka San dalinsu na zaman asmah a gidan..


Ba wani dalili bane kuma illah nason hada zuri'a a tsakanin su domin tun akan yayansu sukeda wannan burin, sai kuma ya kasance yayansu duka maza suka haifa alhaji baba Nada yaya uku, abdullahi mahaifin aslam Wanda ya kasance shine babba yana da matar shi d'aya Aisha mummy yayansu hudu Muhammad aslam ne babbah Wanda yaci sunan alhaji baba sai mai bi masa rabi'ahtu itama taci sunan hajiya mama ne tayi aure last year harda yarta daya hanifa, sai
kuma yan biyu mummy wato zahra da batool


Sai mai bi mishi Amina take auren wani Dan uwanta suna zaune a abuja itace mahaifiyar, amir Wanda ya kasance amini kuma Dan uwa ga aslam kasancewar tsararrakin juna Dan rana daya akayi bikin ta Dana daddy saboda kasancewarta mace,

Sai kuma Yusuf shine mahaifin kamal da amira shima matan shi daya maryam mami, amira tsaran su batool ne shi kuma kamal ya kasance mate din rabi'ah ,
Daddy da abbah dukansu suna zaune ne a gida daya da mahaifinsu babban gidane kowa da part d'inshi


Shi kuma alhaji Mallam kamar yadda jikokinshi ke kiran shi yaya biyu ya haifa kuma duka maza mahaifin asmah aminu shine babba sai kuma qanin shi Ahmad mahaifin Khadijah,


Amintarsu ya samo asaline tun akan iyayensu da suka kasance suma aminai haka aka haifesu suka tashi tare ko ina zasu tare makaranta da gida yau suna gidan can gobe suna can har suka gama secondary school alhaji baba mahaifin shi shararren Dan boko ne kuma Dan kasuwa yayinda mahaifin alhaji Mallam ya kasance babban malamin addini.... Haka kowannensu ya gaji mahaifinsa yanzu haka alhaji Mallam babnan malamine da akeji dashi a fadin Nigeria,, inda iyayensu suka rasu suka barsu, amintarsu har taso tafi na iyayensu Dan daya baya aiwatar da komai saida shawaran daya....lokacin da sukayi aure sun qudurci niyyan idan Allah ya basu zuri'a zasu hadasu aure domin zumunci ya tabbata na har abada... saidai kicin ikon Allah yayansu suka kasance maza mace daya alhaji baba yake da ita Amina kuma sai ta kasance tsaran aminu( mahaifin asmah )saboda alhaji baba ya Riga alhaji Mallam yin aure Dan haka ya rigashi haihuwa,,lokacin da amina ta isa aure kasancewarta mace aminu ya mata yaro don haka tayi aurenta da wani Dan uwanta ta dangin mahaifinta....


Haka su alhaji baba suka haqura da wanna burin nasu na hada zuri'a ganin yadda Allah ya tsara lamarinsa, saidai lokacinda da suka fara samun jikoki burinsu nason had'a zuri'a ya dawo sabo dal ganin Allah ya fara azurtasu da jikoki maza da mata... Iyayen asmah sun rasa ransu ne ta dalilin hadarin mota da sukayi lokacin asmah na noziri sun ajiyeta a school kenan zasu wuce anguwa da kannenta biyu kasancewar ita ta fara zuwa school baza aje da itaba suka biya suka ajiyeta tana kuka zata bisu suka mata wayau suka wuce basuyi nisa da school dinba tayar motar ta fashe, motar ta dinga tambul akan titi, nan dai gaba dayansu suka mutu, sai mummunan labari alhaji Mallam yaji, sunji mutuwarnan sosai kowa sai tausayin asma u yakeji , bayan share makoki alhaji baba ya nemi abashi riqon asmah ya hadata da yan biyu tayi karatu don tafi sakewa cikin yara tunda nan ba wasu yaran tunda lokacin Ahmad baiyi aure ba ana dai shirinyi ne, anan alhaji baba yace idan ta girma kuma sai a hadats aure da dan'uwanta aslam,, nan take alhaji Mallam yayi na am da hakan saidai yace shi baida burin ya mace tayi karatu mai zurfi yafison tayi iya secondary in yaso in mijin ta ya aminci taci gaba a gidanta, take kuwa alhaji baba ya mishi alqawarin indai tagama secondary zai aurad da ita ga aslam din taci gaba a gidan shi anan suka binne wannan sirrin nasu suka barshi a ransu sai lokaci yayi kowa yaji inda sukayi fatan Allah ya hada kan aslam da asmah kafin lokacin don komai yazo musu da sauqi, sai dai kuma hakan bata kasance ba,


Zuwan asmah gidan lokaci tanada shekara hudu a duniya yayinda aslam keda goma sha hudu, hannun mummy da daddy alhaji baba ya danqa amsah inda suka hadata dĂ su batool suka riqe tsakani da Allah amira qaurowa tayi daga part din mami ta dawo part din mummy kullum tanacan in akace tazo ta wuce part dinsu har kuka takeyi ganin haka yasa mami barinta wa mummy ta hada duka su hudun ta riqe yayinda mazan kuma suka kasance yan dakin mami


...tun fil azal aslam baya qaunar asmah domin tun ranar daya fara ganinta ya dauki karan tsana ya daura mata bata mai komai ba shidai kawai abinda ya Sani idan ya hada ido da ita gaban shi faduwa yakeyi tun daga gani na farko hakan yasa ya tsaneta baya so ganinta har mayya take kiranta a cewarshi inba maitaba ya za'ace daka hada ido da mutum gabanka ya ringa faduwa, haka ya takura wa rayuwarta kwata kwata a gidan idan aslam nanan asmah bata da sukuni... Wani irin mugun tsoranshi ya dasu a zuciyarta saboda yadda yake azabtar da ita, duka zagi mari punishment haka yake sakata, yasha kulleta a toilet tun safe sai yamma, suma sauran qannenshi bawai sun sha bane a hannunshi suma yana dukansu amma ba kaman na asmah ba, a haka har suka shiga jss 1lokacin ne kuma aslam ya gama secondary school shida amir inda aka shiga fafutukar naman musu admission a qasar waje har lokacin ba abinda ya canja a tsakanin aslam da asmah yanda yakejin mugun tsanarta itama haka ta tsane shi.......
đź’–DAMA TA BIYUđź’–


BY


~AYSHA NALADO~


FREE BOOK


{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayenmu}


Page 17 & 18




Duk wannan abinda ke faruwa a tsakanin su iyayensu basu da labari, iya yara yaran gidan ne kawai suka san abinda ke faruwa su kuma ba daman fada tsoranshi sukeji kar su fada ya dake su,
Kamal ne ma yake qoqarin hanashi in yana dukkanta yai ta bashi haquri amma ko kallon banza baya isansa, Rabi'ah kuwa tun ranar da tayi mai magana ya tsinka mata mari lokacin batayi aure ba taja bakinta tayi shiru ta zuba ma sarautar Allah ido.......


Kamal yana matuqar tausayin asmah saboda irin abubuwan da aslam ke mata, haka zai sameta yaita rarrashinta yana bata baki akan tayi haquri wata rana sai labari, wani irin kulawa yake bata Wanda ko qannenshi baya basu irin wannan kulawan, kamal ya kasance mai yawan magana Dan haka zaizo yasata agaba yaita mata labaran ban dariya duk Dan ta manta da abinda aslam ke mata agidan...
A hankali wani irin shakuwa ya shiga tsakanin,


Su asmah sun shiga jss 1 lokacin aslam na shirye shiryen wucewa karatu kasan waje,,, FGC abbah yakaisu inda asmah da batool A class zahra da amira B class su hudu suke rayuwarsu gwanin sha'awa,, basuda wasu baren qawaye su hudun nan sune qawayen junan su.


Ranar da aslam da amir zasu tafi makaranta a kasar Malaysia zo kuga murna gurin y'an mata mummy, bama kamar asmah har wani Dan qaramin party suka hada a dakinsu su hudu na murnan tafiyan aslam ...


Tabbas y'an matan mummy sunji dadin tafiyan aslam, asmah tuni ta saki jikinta a gidan don dama aslam ne kadai matsalarta ... Agidan kowa nasonta babu mai nuna mata wani banbanci ta zama yar gida babu mai sanin rikonta akeyi a gidan ,,, alhaji baba ma qarara yake nuna mata soyayya fiye da sauran jikokinsa, domin ita din jinin amininsa ce mutum mafi soyuwa a gareshi, sosai yake kula da dukkan lamarinta,, hakan ya saka mata wani irin matsanancin kaunar tsohon da ganin girmanshi a zuciyarta, sosai take girmama shi, sosai take girmama dukkan lamarinsa, yanda ko layi yaja yace kar ta tsallake to bazata taba tsallakewa ba kuwa har illah masha Allah,


Ta bangarenb kamal kuwa shaquwan dake tsaninshi da asmah ya rikide ya koma soyyaya a gare shi ,domin kuwa shi kadai yake kidanshi da rawanshi ita batasan yanayiba, ta dauka kawai sabon da sukayi ne yasa yake mata wasu abubuwan kamar na soyyayya, saidai kuma duk Wanda yaga yadda suke mu'amala saiya saka musu ayar tambayaâť”, su zahra sunsha tambayarta wai kod'ai soyayya takeyi da yaya kamal, takanyi murmushi tace musu a'a ita yaya kamal yayanta ne ba wannan maganar a tsakanin ta dashi,, sukance mata ba wani nan intayi wari maji,


Su aslam sunacan kasar Malaysia suna karatu hankali kwance tunda ya tafi bai taba dawowa gida Hutu ko ganin gida ba , yanadai kiran iyayenshi a waya suma suna kiranshi musamma mummy da mami,
zuwansu da shekara shida suka hada karatunsu akan business, amir ya tattaro ya dawo qasarmu ta gado, shikuman gogan ya zauna ya fara aiki acan da wani babban kamfanin mahaifin abokinsa da sukayi karatu tare.....
A Malaysia ya hadu da zee school dinsu daya amma ba Abu daya suke karantawa ba,
zainab abdussalam yariyan wani. Hamshaqin attajirin Dan boko ne haifaffan Nigeria ma zaunin Malaysia,, zainab yar gata ce gurin iyayenta kasancewar ita kadai suka Haifa sangartatciya na qarshe,, bata iya komai ba sai rashin kunya, sai kuma ayi wanka a qure kwalliya a fita yawo da qawaye akashe kudi kamar basusan ciwonshi , kodayake basuwan ciwonshi ba tunda basu ke wahalar nemowaba,
Zainab ta kasance kyakkyauwa ce yar kwalisa kuma macece mai class don ba kowani gara take kulawaba saita tabbatar kai wani ne ko Dan wani sannan zata yarda ta kulaka kuyi soyayya,, kana kawo mata maganar aure zaku watse don ita kwata kwata babu aure a gabanta, haka iyayenta, a cewarsu bata isa aureba shekara ashirin da shidda, wai saitakai thirty five zasu aurad da ita,


Ranar da zainab ta fara ganin Aslam ta kamu da matsanancin soyyayyar shi, saidai shi baima son tanayiba kasancewar sa ba mai kule kule kulen mata bane , a hankali zee tafara shigema aslam, bayan tayi bincike sosai akanshi ta gano ko shidin wanene , sosai ta saka mishi ido a school din inyana waje zatazo ta zauna ta dauko book din ta tana karatu, tun bai lura da ita har ta fara daukan hankalinshi, tun bai riqe face dinta ba har yayi making face dinta a kwakwalwarshi ,, zainab ta hada duk abinda aslam yakeso a y'a mace , yana son kyakkyawar mace kamardai zee, yanason wayyayyar mace yar boko wacce tayi karatun boko mai zurfi,, yanason mace mai aji wacce ta iya daukar wanka wacce batada rawan kai irin na yan matan zamanin nan wacce in ya shiga da ita cikin taro baza'a raina shiba, zee ta gama hada duk wadan nan qualities din,bai tunkaretaba saida yayi bincike akanta ya gano ko ita wacce ce, sannan ya baiyana mata manufarshi, ba wani dogon Jan aji ta amince masa nan da nan suka qulla zazzafan soyayya


Date: Oct 4, 2022


đź’–DAMA TA BIYUđź’–

BY


~AYSHA NALADO~


FREE BOOK




{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayenmu}




Page 19 & 20


A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yaune su asmah suke candy sun kammala secondary school dinsu, sun zana waec & neco harma da jamb dinsu cikin aminci , sai zaman jiran result , sun samu kyaututtuka da dama musamma ma amsah data kasance head girl dinsu kuma daliba mafi qoqari a duk set dinsu, qanin mahaifin ta alhaji Ahmad da mai dakinshi mahaifan Khadijah , sunzo mata daga suleja inda suke da zama harma da Khadijah da kannenta maza guda biyu,


A daidai wannan lokacin kuma ya aslam cika shekara 7cif cif a Malaysia kuma yake shiri dawowa qasarsa ta haihuwa wato 9ja ,


Ranar wata asabar gaba daya gidan ya hautsine da shirye shiryen tarban Muhammad aslam, kowa ka gani a gidan yana cikin farin ciki ba y'an qannenshi ba ba iyayensu ba, to ai dole shekara 7 fa ba kwana 7 bakwai ba ,...


Asmah kam tunda taji labarin dawowar aslam Har zuwa yau da jirginsu ya taso gabanta faduwa yake ko kad'an bata farin ciki da dawowar shi, dariyar ya'ke kawai takeyi a yan kwana kin nan Dan kar jama'an gidan su gane halin da take ciki, su zahra sunyi matuqar mamakin yadda take nuna itama tana farin ciki da dawowarshi bayan sunfi kowa sanin tsananin su...Itakam a zuciyarta takance hmmmm kudai kawai fuskata kuke gani, bakusan abinda ke zuciyataba amma na ciki na ciki.....


Kamal ne kawai ya fahimceta, ya kuma kwantar mata da hankali cewa ai yanzu ta girma bazai dinga mata abinda yamata shekarun baya ba ....da haka dai ya kwantar mata da hankali....




Mummy, daddy, abbah, da kamal sune sukaje daukoshi a airport jirgin su na sauka mutane suka fara saukowa daya bayan daya shine kusan na karshen sakkowa,, zaro ido waje mummy tayi tare da d'aga hannunta kamar zatayi addua ta kulle bakinta, ganin yadda aslam dinta ya koma kamar yani balarabe ya girma ya zama cikakken namiji kwata kwata ya sauya ya qara kyau kamar bashiba. ...shima saida yayi arba da iyayen nashi ya tabbatar yayi missing dinsu sosai da sosai, rungume shi mummy tayi tana hawaye tanabubbuga bayanshi tane hawaye sai fadi take "idonka kenan babana" shi kuma sai maimaita "mummyna mummyna I miss u yakeyi" haka suka rankaya suka dawo dawo gida...... Lokacin da yayi arba da yan qannenshi sai murna sukeyi sukazo suna mishi barka da dawowa , ya kallesu duk sun zama yanmata yace "lallai yaran nan kune kuka girma haka kuka zama yan mata Ashe mun kusa shan biki ya fada cikin zolayarsu " amira da zahra boye fuska sukayi waisu irin sunji kunya nan, batool da yake itace rasa kunya tace kai ya aslam mufa yarane bamu isa aure ba,.... Kallonta yayi yace ja'ira kina nan yadda kike da shegen surutun nan har yanzu ko tayi dariya ,,,,,,, hajiya mama dake zaune gefe tace, "eh lallai ba shakka aslam ka shahara harda wani cewa wadannan berorin sun girma ka kusha shan biki ko.....to ai sai ka bari ka fara auren

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads