Showing 135001 words to 138000 words out of 201974 words
Chapter 46 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
yana zaro ido, can kuma yace "au na manta a shefa kai sirikina ne yanzu bai kamata na dinga faɗa maka irin wadannan maganganun ba" Aslam yace "kaidai ka sani da iskancinka, kuma wlh Abi min kanwa a hankali ba motar hawan mutum bace da zaike hawa any how" Dr bash yace "sannu fa yaya mai kanwa, inace kaima kanwar wani ka ajiye a gidanka, kake hawa " Aslam yace "karya kakeyi ba kanwar kowa na ajiye ba kanwata ce" bash yace "nafa ga alama, daɗin abin nima dai inada kanwowi bama kanwa ba" Aslam yace "to naji parrot sarkin surutu, ni yanzu duk ba wannan ya kawoni ba" gyara zama bashir yayi, ya maida hankalin gaba daya ga Aslam dama tun farko ya fahimci kamar yana da damuwa, "ina jinka friend meke damunka" huci mai zafi ya furzar daga bakin shi, sannan ya kalli Dr bash fuskar shi ta koma serious alamar abinda zai fada mai mahimmanci ne yace, "wlh neman mafita nakeyi shawara nakeson ka bani" bash yace "ina saurarenka abokina menene damuwarka"tiryan tiryan Aslam ya shiga ba bashir labarin abinda ya faru tun farkon aurensu har zuwa halin da suke ciki a yanzu.
Tun kafin labarin yayi nisa wani mugun dariya ya turnike Dr bash, matsewa kawai yakeyi saboda yana son yaji karshen labarin kuma a yadda Aslam yaci serious akan maganar yana yin dariyar nan zai bata komai karshenta ma yayi zuciya ya tashi ya wuce, saidai idan ya faɗi abinda bazai iya jurewa ba yayi sauri ya tsuguna kasan table ɗin dake tsakiyarsu kamar yana duba wani Abu anan zai samu yayi dariyar shi mara sauti sannan matse ya dago yaci gaba da sauraren Aslam yana gyada kai kamar yana jimamin maganar.
Saida Dr bash ya tabbatar Aslam yakai karshen labari, ya kalle ya kece da wata irin dariyar keta har yana dukewa yana rike ciki,a hargitse Aslam ya zaro ido yana bin bashir da kallo, a fili yace "kan bantan uba " ina bashir baisan yana yi ba, a fusace ya miƙe tare da dukan table din dake tsakiyar su da karfi, sannan ya juya yayi hanyar fita, bugun table dinne ya dawo da bash hankalinshi, da sauri yabi bayan Aslam ya riko mai hannu, still kuma bai daina dariyar ba, Aslam kallo shi yakeyi a zuciyar ji yake kamar ya buga mai kulli a baki sai hakoranshi sun zubo kasa,
Fisge hannun shi yayi, ya kara yunkurin fita a office din, a karo na biyu Dr bash ya sake riko hannun shi, Aslam yace"bashir sakeni ko na maka gula wlh, wato ga kasurgumin mahaukaci ko, na baka labari ka sakani gaba kana min dariya wato ga sabon kamu daya kwanto daga sakatiri" da'ker bashir ya sausauta dariyar shi, yana haki yace"dan Allah da manzonsa friend kayi hakuri, wlh in ban samu nayi dariyar nan ba bazan iya magana bane, dan Allah kayi hakuri ka koma ka zauna pls for d sake of Allah badan niba" zare hanninshi yayi cikin na bashir ya koma ya zauna ammafa fuskar shi babu alamun rahma.
Shima bashir mazaunin shi nada ya koma ya zauna, da'ker ya saisaita kanshi sannan ya kalli Aslam yace,"A gaskiya Abu baiyi dadi ba abokina sannu fa da hakuri, har ina tambayar ka ya amarci,mutanen gari duk inda kabi ana ango kasha mai ashe ko ruwa baka sha, Ashe kai har yanzu muna ango ne, ayya wlh abin tausayi, amma fa indai zan faɗa maka gaskiya kaji, zance kayi wauta, ta yaya zakace mace budurwa ba wai bazawara ba diyar Mallam bahaushe ta fara nuna bukatar ta akan ka sannan ka kusanceta, na farko fa bawai kun tabayi bane fa, haba haba Aslam kaima kasan wannan lamarin bamai yuwuwa bane, kumama kai ba wai ka taba nuna kana so bane fa ta hana balle kace ka kyaleta sai Randa ta so, yoo ni dana nuna inaso aka hana ai ban tsaya daukar wannan iskancin na amaren zamani ba kof daya na mata kawai aka wuce wurin, to balle kai dana tabbata a yanda ka bani labari irin soyayyan da kukema juna wlh baza ta hanaka ba, ka cire tsoro ka jaraba abokina wlh zakazo ka bani labari nina gaya maka, idan kuma baka da isashen lafiya ne kana tsoron karta rainaka, ka faɗa min na hada maka yan kwayoyin da zasu taimake ka baza ta gane ba " harara Aslam ya watsamai tare da cewa "an gaya maka kowa ma irin Kane,ni duk ba wannan ne ke damuna ba" Dr bash yace "to meke damunka, na gane Mallam kawai tsoronta kake, me tsoron mata kawai" ya kare maganar cikin sigar zolaya, Aslam yace "kaima shaida ne niba matsoraci bane, koda cen balle yanzu" Dr bash yace "na sani ai ba tsoron kowa nake nufi ba tsoron Asmah nake nufi" Aslam yace"ko ita bana tsoron ta" bash yace "karya kake yi meyasa ranar da asirinka ya tonu ta gane ciwon karya kakeyi ka kasa tun karanta kai tsaye saida kaga ka kasa bacci sannan kaje " Aslam yace "ai laifi na mata shiyasa bawai dan tsoro bane" Dr bash ya kwashe da dariya tare da cewa "ka yarda kawai Mallam kana tsoronta" ran Aslam fa ya fara baci ganin yadda Dr bash ya dage akan tsoron Asmah yake" haka sukaita musu, Aslam na magana a zafafe, yayinda yake ta kokarin kare kanshi, bashir kuma nata kwasan dariya da gangan kuma yaketa kokarin kunna Aslam din" saida ya tabbatar ya kunnu iya kunnuwa sannan yace" yanzu naji, kadai dage ba tsoron ta kake ba, to naji amma fa bawai na yarda bane, idan kana so na yarda yau ka tabbar min da hakan ni kuma Wlh idan har yau kayi dis virgin dinta zan yarda ba tsoron ta kake ba, musa bet ma wlh ka faɗi duk abinda kake so " Aslam cikin huci yace "haka kace ko to shikenan ni kuma zan tabbatar maka da hakan yau basai gobe ba" a haka suka ajiye wannan caftar suka kama wata, basu suka bar asibiti ba sai da ana kiran mangaruba, a masallacin bakin asibitin sukayi sallah bayan sun fito bash yace "sai ina yanzu" Aslam yace "gidan Rabi'ah zanje na dauketa muje gida daga nan kuma mu gaisa da ummi" bash yace "nima nan zani na dauki batool to amma da nace sai nayi sallan isha'e amma muje kawai kasan ance tafiya bibbiyu yafi dadi" kowanne motar shi ya shiga suka dauki hanyar anguwan fadukwai inda gidan ya Rabi'ah yake.
Suna isa kofar gidan motar Abban hanifa na shawo kwana ta dayan hanyar, dukkansu kusan a tare sukayi parking nan suka shiga gaisawa, Dr bash sai lokacin yamai barka baki da baki, nan kuma ya kira Rabi'ah ya gaya mata gashi dasu Aslam, sannan suka shiga, bama kowa a falon duk suna ciki, zama sukayi Abban hanifa kam dakin shi ya nufa, basu fi 5 minutes da zama ba Ummi tayi sallama a falon, fuskar washe take cewa "oyoyo yarana sannunku da zuwa ina azkar naji Rabi'ah na fadin isowarku" daidai nan ta karaso ta zauna a daya daga cikin kujerun falon, Dr bash ne ya fara saurin sauka daga kan kujera ya shiga gaisheta tare da mata barka da isowa lafiya, Aslam kam matsawa yayi gabanta ya tsuguna tare sa kamo hannunta daya ya rike fuskar shi cike da farin cikin ganinta yace"sannu da zuwa ummi fatan kin iso lafiya," murmushi tayi tana daura daya hannunta akan tarin suman kanshi, tace "lafiya qalau my son fatan na sameku lafiya" yace "lafiya qlau , nayi kewarki sosai ummi " tace "nima haka my son, ya aiki ya iyali" yace "alhmdllh ummi" tace "masha Allah, Allah ubangiji ya muku albarka, baki daya,ya karamuku zaman lafiya da kwanciyar hankali ya Baku zuri'a dayya ba" kusan haɗa baki sukayi dukkansu bashir, Aslam, ya Rabi'ah da batool da fitowarsu kenan daga ciki da kuma Amir da shigowar shi kenan falon, gurin cewa "amen ummin" sai sannan ta sauke hannunta akan Aslam shima sakin hannunta yayi ya nemi guri kusa da kafarta ya zauna, Amir kuwa hannu yaba Aslam da Dr bash sukayi musabaha, sannan ya tsuguna ya gaida ummi, kafin ya koma kusa da dr bash ya zauna, ya Rabi'ah data zagayo ta zauna kusa da ummi ne tace "ya Aslam ya Amir da Dr ina wunin ku" Amir ya amsa da lafiya qalau sisto, Aslam ya amsa da ina gajiya yayinda Dr bash yace lafiya qalau anty Rabi'ah barka fa Allah ya raya, da amin suna amsa, batool ma karasowa tayi ta gaida Aslam da Amir ta nemi guri ta zauna, a fakaice Dr bash ke hararanta,ganin ta gaida kowa ban dashi, hararanta ummi tayi tace "shi bashir din uwa ya kashe miki hala" kallon ummi tayi tana dan zumɓuro baki sannan ta kalleshi tace "to ina wuni" duk dariya suka saka mata, banda Aslam daya kalleta ya dauke kai, shifa har yanzu baijin zai iya sake musu fuska , don rashin son raini a jninsa yake, Asman shi ne kawai zai laminci ta raina shi ita ma albarkacin soyayya.
Daidai nan Amira ta shigo falon samun tayi suna dariya, bata San ko na meye ba, ta dai ƙaraso, zama tayi a hannun kujera kusa da ya Rabi'ah ta kalli su Aslam da Dr bash ta gaishesu a tare, amsa mata sukayi, gaba daya, sannan ta maida kallonta kan Amir da tunda ta sawo kai falom yake ta binta da kallon luv yana murmushi tace "yayana barka da dare, ka dawo lafiya ya aiki" fuskar shi a washe cikin farin ciki da annashuwa ya amsa mata cike da kulawa, ya Rabi'ah tace "oh ni Rabi'ah duniya mutane kala kala wancen taki gaida nata mijin,wannan kuma saida ta ware shi dabam sannan ta gaishe shi bata hadashi cikin jam'in mutane ba,lallai yaran mummy kuma sha'anin ku, kai kuma ya Amir babu ko kunya kake mata irin wannan kallon a gaban mu " hararanta Amir yayi, sukan dan taba wasa da Rabi'ah kasancewar su abokan wasa, ummi ce ta kalle ta tare da cewa "ya isheki haka Rabi'ah saka idon ki ya fara yawa ina ruwanka wai" dariya ya Rabi'ah tayi.
Su Asmah da zahra da khadijah ma fitowa sukayi bayan gaisuwa suka zazzauna aka shiga dan fira jefi jefi, ya Rabi'ah ta mike ta kawowa su Aslam Abinda tabawa, Abban hanifa ne ya fito yayi wanka ya canja kaya, kallonsu yayi yana ba amir hannu Wanda shine basu gaisa ba yace " Ah'ah guys kuce duk kana nan kenan" matar shi ta amsa da "ba dole ba kowa ya biyo sahu" dariya yayi sannan ya shiga gaisar da ummi, daidai nan kuma aka fara kiran isha'e, kallon yayi yace "nidai nayi masallaci" Amir ne ya mike tare da cewa "muje nima" sauran ma suka mike, Aslam ya kalli ummi yace" umminmu bari muyi sallah" tace "to sai kun dawo" sannan suka fice.
Suma matan ciki suka koma sukayi sallah, dama sun riga sunci abinci, nan ummi ta bude jakar Asmah ta kwaso sauran magungunan data bata tace "karbi ki shanye ki bani hannu tunda kinci abincin anan shikenan yanzu inkinje gida ba lallai kisha ba" saida ummi ta mata kat a lokacin nan, sannan ta barta haka.
Koda su Aslam suka dawo basu shigo ba' Abban hanifa ne daya shigo ya shaida musu, mazajensu na jiransu waje, kowacce kuwa ta tattaro kayanta sukayi sallama da ummi suka fito har main falo suka rakosu, har Asmah zata fita daga falon ummi ta kira ta a kunne ta raɗa mata "daga yau ki dinga mayar mai da martanin kinji" cike da kunya ta gyada kai, Rabi'ah data gama kasa kunne bata jiyo komai ba tace"wai umminmu nifa ban gane ba" ummi tace "ai baza ki gane ba rabi, kuje oh abinku karku ɓata musu lokaci sai da safe, kuzo gobe da wuri kunji ko" da to ummi suka amsa sannan suka fice.
Kowacce motar mijinta ta shiga suka dauki hanyar gidansu,suna fita layin kamal na shigowa, shima bai wani dale ba ya dauki deejanshi suka wuce.
A hankali yake tukin cike da kwarewa, zuciyar shi kuwa cike take da annashuwa, yanayi yana kallon ta yana murmushi, itakam Asmah gaba daya hankalinta naga maganganun da sukayi dazu da ummi, babu abinda yafi tsaya mata arai irin cewa da ummi tayi, ta dinga mayar mai da martani, Aslam ganin tayi nisa yasa ya kunna wakar *saida ke* na hamisu bireka yana bi a hankali, sautin wakar ne ya dawo da hankalinta kanshi a kan dan bakinshi ta sauke idanunta inda yake motsashi a hankali yana bin wakar.
Karki barni, sahibaaata♪
Karki ƙini ki fahimmmta♪
Saidake zani huuuta♪
Zuciya ta dake ne ta lallabo♪
Ta amince ki madani dan dako♪
Shiru tayi tana sauraren wakar da yakeyi, har cikin zuciyarta ko wani baiti daya na wakar ke tabawa, ji take kamar ita aka rairawa wakar,har suka karaso gida babu Wanda yayi ma wani magana cikinsu, bayan ya kashe motar yayi parking, zagayowa yayi ya buɗe mata kofa, dagowa tayi ta kalle shi fuskarta dauke da murmushi tace "nagode Mr Aslam" kashe mata ido yayi tare da cewa "u ar wlcm" fitowa tayi ya kulle motar tare da daukar Jakarta suka shiga ciki, suna shiga falo ya zauna a kujera yana cewa "wash yau nagaji gaba daya jikina ciwo yake min" ita kam Jakarta ta dauka tare da karasawa ciki, wanka tayi ta shirya cikin kanana kaya marasa nauyi tayi wanka da daddaɗan turarenta sannan ta fito fallon, tana baza kamshi, a tsaye ta same shi, yana niyyar shiga ciki, kallonta yayi tayi mai kyau sosai, murmushi ya sakar mata tare da cewa "har kinyi wanka," murmushi tamai itama ba tare da ta tanka ba, yace "to nima bari nayo nazo ki bani labarin abinda ya faru yau a gidan aikin suna" tace "aiko je ka dawo kasha labarai bari na Samar maka abinda zakaci kafin ka fito" yace "OK tnx" ya wuce ya shiga ciki ita kuma ta wuce kitchen.
Jelop din spaghetti da yaji kifin gwangwani da kayan lambu ta mai, sharp sharp kuwa ta gama ta kwashe, ta kawo dinning , tana cikin jerawa ya fito shima cikin ƙananan kaya, kujera yaja ya zauna, tare da cewa "masha Allah yar aljannah sannu da kokari" murmushi tayi tare da daukar plate ta shiga serving dinshi, shake plate tayi taf sannan ta tura mai gaban shi, fork ya dauka ya d
ɗibi taliyar ya kai loma daya bakin shi, ajiye fork din yayi yana lumshe ido tare da muymuy da baki, hannu yakai ya rike kunnenshi daya yana murzawa yana gyada kai, tana ganin ya fara haka tasan karshen maganar, dariya ta kwashe dashi,tana cewa "zaka fara kenan ko" bude idanu yayi yana murmushi yace "to aike ne wlh kin iya girki mai dadi da saka mutum santi, test din girkin ki daya dana mummy, kai naki ma yafi nata dadi, dan yanzu ita tadan manyanta komai nata ya rage quality" zaro ido tayi tace "innalillahi Mummyn kake cema haka, to kuwa sai na gaya mata" dariya ya kwashe dashi yana cewa "ai nasan baza ki iya bane yarinya", haka yake ta cin abincin suna fira cikin nishadi harya kammala.
Falo suka dawo ya zauna akan 3 sitter tare da daukan remote yana chanza Chanel, zuwa tayi ta kwanta a kujeran daya zauna tare da yin pillow da laps dinshi tana kallon fuskar shi, shima kallonta yayi bayan ya gama canza Chanel din ya saka Wanda yake son ya kalla, kashe mata ido yayi tare da cewa yanzu kuma sai ki bani labarin abin da ya faru yau a gidan Rabi'ah, murmushi tayi tare da cewa "oya karkabe kunnenka kasha labari" karkabewan kuwa yayi, tiryan tiryan ta fara bashi labarin tun daga zuwanta gidan irin rungumar da suka ma juna ita dasu batool da irin farin cikin da sukayi na ganin juna, har aka gangaro batun ciki.
Kallon fuskarta yakeyi, babu ko keftawa zuciya cike da wani irin rauni, tunda ta fara bashi labarin batun cikin da yan uwanta keda shi zuciyar shi ta karye tausayin Kansu ya kamashi, daga yanayin yadda take bashi labarin cike da zakuwa da shauki ya tabbatar mai da abin ya shigeta sosai, take yaji a zuciyar shi ya zama wajibi yau shima ya ajiye duk wani Abu gefe ya kusanceta, ko suma zasu samu nasu cikin, gefe guda kuma ga bet dinshi da Dr bash dake dawo mai dalla dalla a zuciya kamar a yanzu suke kullawa.
tuni idanunshi sun rine ya ma daina fahimtar labarin da take bashi, da wani irin sauti ya kira sunanta, take hankalinta ya dawo kanshi ta dago da idanunta ta sauke a cikin nashi, ji tayi gabanta ya fadi meya same shi ne haka yanzu yanzu, shima yana kallon cikin idanunta yace "kina son ciki kema" jim tayi kaɗan kafin a hankali ta gyada mai kai don da gasken tanaso itama, ya sake cewa, "kin amincemin a yau na baki ciki da yardan ubangiji"duk da ta daɗe tana jiran wannan rannan saida gabanta ya yanke ya fadi......
Me kuke tunani zai zama amsar Asmah, yes or no, 😅
Oum Ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fisabilillah🙏.
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO ~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}
Page 113
Duk da ta daɗe tana jiran wannan rana saida gabanta ya yanke ya faɗi, zuba mata rinannun idanunshi yayi yana kallon fuskarta,zuciyar shi na bugawa da wani irin sauri, cike yake da fargaban amsar da zai fito daga bakin ta.
Asmah kam gabanta ne yaci gaba da faɗuwa, ta sani a yadda take jin soyayyar shi a zuciyarta a halin yanzu babu abida zai nema a gareta ta hanashi muddin tana dashi, kuma bugu da kari ai ciki yace zai bata, wanda a halin yanzu babu abunda take bukata sama dashi.
Ganin tayi shiru tana tunanin amsar da zata bashi, yasa ya sake