Header Ads
Showing 168001 words to 171000 words out of 201974 words

Chapter 57 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1733

Ads at the middle of Article

formatting lin komai daga kwakwalwar ta.


Daidai nan daddy ya shigo Amir na biye dashi ko zama basuyi ba Abba ma ya rafko sallama, duk da suma sun kaɗu da ganin zee tare da yaro mai kama da Aslam hakan baisa sun ruɗe ba kasancewar su mazaje masu dakkakkiyar zuciya.zama sukayi domin amsa kiran Alhaji baba, babu Wanda ya furta koda A ne daga cikin su, domin duk sanda Alhaji baba yayi irin wannan kiran kowa natsuwa yake yi ya saurare shi babu mai ikon yin magana har sai yaba da umarnin yin hakan, kamal ma ya karaso daga gurin aiki yake ma ya dauki excuse ya taso, Allah yasa ba sa wani Abu mai mahimmanci.


Aslam kawai ake zaman jira kasancewar an bashi umarnin ya taho harda Asmah, kuma yana office dole saiya biya gida ya dauko ta hakan yasa yayi jinkirin isowa, falo yayi tsit sai kallo kallo akeyi a tsananin juna, fuskar kowa cike da zaƙuwan sonjin ta yaya akayi matankaɗi ya shiga gora, domin dai dukkanin su kallo daya suka ma little suka tabbatar cewa lallai shiɗin jinin su ne, kamar yadda yaron ya kasance mai farin jini da saurin shiga rai tun haihuwar sa, farin jinin shi nanan har yau babu abinda ya dakushe a ciki saima ƙaruwa da yayi, domin dukkansu a kallo ɗaya yaron ya shiga ransu kaunar shi ya kama zuciyoyin su kowanne su burin shi ya ɗauki yaron saidai babu daman yin hakan saboda girmama wa ga Alhaji baba har sai ya gama fadar abin da yasa ya tarasu sannan zasu samu daman yin hakan.


Bayan kamar minti goma da haduwar kowa da kowa a falon Alhaji baba, motar Aslam ta faka a farfajiyar gidan, jiki a sanyaye ya buɗe motar ya fito, tunda ya tashi barci yau gaban shi keta faɗuwa lokaci zuwa lokaci har sai da takai ya gayawa Asmah, abin da ke damun shi, har yake cewa shi bai da tafiya bazai iya fita office ba, ita ta karfafa mai gwuiwa tare da cewa yayta ambaton innalillahi wainnailaihi rajiun, a haka ta samu ta lallaɓa shi ya tafi. Lokacin da kiran gaggawa daga Alhaji baba ya riskeshi ji yayi bugun da kirjinshi keyi ya nunku fiye dana da.


A bangaren Asmah kam ita ma kwarai da gaske jikin ta a sanyaye yake tunda maganar kiran nan ya risketa haka kawai take ji a jikin ta wani Abu Mara daɗi zai bakunci rayuwar ta.


Kasa fitowa daga motar tayi saida ya buɗe Mata tare da cewa "bismillah husnah muje Allah yana tare da mu koma meke ciki in-sha Allahu zaizo mana da sauƙi." Mika mata hannu yayi yana sakar mata murmushin karfafa gwuiwa, itama martanin murmushin ta mayar mai kafin ta mika hannun ta ta saka cikin nashi ya mayar ya damƙe gam kamar wani zai kwace mishi ita a haka suka doshi falon Alhaji baba hannun su cikin na juna............




Oum Ummeetarh
07041130088


💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~




FREE BOOK




{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya,Allah kajiqan iyayen mu}






*ASSALAMUALAIKUM SISTERS*


abun d mamaki Tayanda watan axumi yaketa qaratowa cikin Dan taqin lokaci,
Me kika tanadarwa kanki dama yaranmu yar uwa?
Munada kyawawan kayan Yara na dinki masu kyau sosay d bama zakice dinkawa akayiba yaro/yarinya sufito gwanin burgewa kowa yanasan barka,07046881166


Kayanmu sauqinsu yyi har kamar kyautane,zaki iya samunsu dga 2k harzuwa abunda yyi Sama,kizo kiyi sarin kayanmu kisamu alkhairi me tarin yawa,07046881166


Akway takalma Suma kyawawa dgakan 1k zuwa sama,07046881166


Sannan munada tsala tsalan frames d madubai n gyaran gida masukyau d arha sosay,07046881166


Akway leshina d atamfofi,abayas sewanda kikazaba duk a farashi mesauki,07046881166


Karna cikaku d surutu ku kira:07046881166 domin qarin bayani,karku manta alkhairin Tari maganin mantuwa zaku iyashiga Instagram handle namu don ganin kayayyakinmu: everythng_handmade,


Semunjiku 07046881166






Page 124




A tare suka haɗa baki wurin yin sallama kafin su sa kai cikin falon hannun su sarƙe da juna. Tunda ta jiyo muryar shi yayi sallama , zuciyar ta ya shiga wani irin luguɗen bugu da karfin gaske. Ƙofar shigowa falon ta kafe da idanun ta tana kallon jiran tsammani. Shine ya fara bayyana a falon kafin ita, kamar had'in baki daga shi har ita idanun su, akan fuskar zee ya sauka,wani irin wawan burki ya taka daga bakin ƙofar, yana bin ta da wani irin kallo mai cike da tsantsar mamaki. A firgice ta mik'e tsaye tare da zaro dukkan girman idanun ta waje, furgici da tashin hankali ne suka bayyana ƙarara akan fuskar ta, kallon Asmah take yi kamar wacce keson ta tantance shin ita d'in ce kokuwa idanunta ne ke mata gizo, mayar da idanunta tayi kan hannayensu dake sarƙe dana juna, sannan ta ƙara sauke idanunta akan Aslam dake tsaye yana kallon ta kamar wata sabuwar halitta.


Gaba d'aya mutanen falon shiru sukayi suka zuba musu idanu, cikin su ukun an rasa Wanda zai fara janye idanun shi daga kan wani, kowanne da ma'anar kallon da yake bin ɗan uwan shi da shi. Zee tana bin Asmah da Aslam ne da kallon furgici da tsananin tashin hankali tare tambayar kanta shin meye alaƙar mijin ta da Asmah da har suka shigo cikin falon Alhaji baba a tare hannunsu sarƙe da juna, duk da tasan ita d'in burin shi ce zabin shi ce abar kaunar shi ce, tun kafin ta bar gidan shi, amma bata taɓa kawo tunanin cewa bayan bata zai mallake ta ba, saboda a gaban ta ranar Alhaji baba ya tsayar da lokacin bikin ta da kamal a wancen ranar, shin menene alakar su? Take zuciyar ta ta bata amsa da cewa Aure, ji tayi numfashin ta na neman gagarar ta ja, indai ko alaƙar aure ne a tsakanin mijin ta da Asmah ta shiga ukun ta, domin ita shaida ce akan irin tsananin so da kaunar da yake ma Asmah wanda tana da tabbacin ko rabin rabinshi baya mata.


Asmah kam kallo tsoro da zallar madarar kishi take bin zee da shi, shin meya dawo da ita rayuwar su a daidai wannan lokacin? me tazo nema me ya kawo ta? A daidai lokacin data shaku da Aslam ta zama shi ya zama ita ta miƙa mishi dukkan ragamar rayuwarta, lallai akwai gwarama, don a yadda take kaunar Aslam a halin yanzu bata jin zata iya raba shi da wata p
ƴa mace a duniya.


Shi kam Aslam da wani irin kallon mai cike da tsantar mamaki yake bin ta, har ga Allah ya manta da ita gaba ɗaya a shafin rayuwar shi, bai taba kawowa a ranshi a kwai wata rana da zata juyo ya sake haɗa idanu da ita ba,tun daga ranar da ya mallaki Asmah,bai ƙara kallo duk wata diya mace da sunan mace ba, yakan tunata a wasu lokatan musamman idan yana cikin alhini rashin samun haihuwa, a duk sanda ya tunata ranshi ne ke mugun baci, bai taba tuna alkharin ta ba ko kaɗan, a duk sanda zai tuna ta baƙin ta kawai yake tunawa,nadama da dana sanin auren ta kawai yake yi a duk sanda ya tuno ta, sau da yawa yakan furta ta cuce shi kuma yana ji har duniya ta nade bazai taba iya yafe mata abin da ta mashi ba, shin me ya kawo ta gare shi a halin yanzu?


"Mommahhhhhh." Zazzakar muryar yaron ne ya katse musu tunani gaba ɗayan su, har cikin zuciyar shi sautin muryar yaron ya daka , kusan a tare dukkan su ukun suka juyo dan kallon mamallakin wannan muryar, ruɗu, al'ajabi, mamaki, ne suka ziyarci shi a lokaci guda, wani irin waro ido yayi waje yana kallon yaron da ke zaune a jikin hajiya mama yana yana miƙa ma zee hannu alamar ta dauke shi, Asmah kam suman tsaye tayi, take kuma a lokaci guda taji kibiyar so da kaunar yaron ya caki zuciyar ta, har sai da ta dafe daidai saitin kahon zuciyar ta, duka idanunta ta baza tana kallon tana yaro mai kama da Aslam ɗin ta sak kamar yayi kaki, shin ɗan waye wannan a cikin ahlinsu bata taba ganin shi ba, kuma dai kallo ɗaya tamai tasan lallai shi ɗin jinin ahlin gidan ne.


Gyaran muryar da Alhaji baba yayi ne ya dawo da hankalin kowa kanshi, kallon su yayi yace "Muhammad, Asma'u, zainab ku nemi waje ku zauna." Jiki a sanyaye suka nemi guri suka zauna, Asmah kusa da mummy ta zauna a tare da kwantar da kanta akan cinyar mummy Aslam kuma kusa da Abba, yayin da zee ta koma mazaunin ta nada kusa da mami ta zauna.


Bayan kowa ya nutsu ya bada dukkan hankalulin sa, kallon Abba Alhaji baba yayi yace "bismillah Yusuf a buɗe mana taro da addu'a." Amsawa Abba yayi da "to Alhaji." Kafin ya shiga kwararo addu'a suna amsawa da amin, bayan sun shafa addu'a, shiru falon ya dauka na yan wasu mintuna, sauke numfashi Alhaji baba yayi kafin ya bude bakin shi cikin dattako da kamala da Allah ya hore mishi yayi sallama cikakkiya, kusan gaba ɗaya hada baki sukayi gurin amsa sallamar shi, yace "alhmdllh alhmdllh alhmdllh har kullum ina godewa Allah daya bani ku a matsayin yaya da kuma jikoki na, Allah ubangiji ya muku albarka baki ɗaya." Da amin suka amsa gaba dayan su kamar ɗazu, yaci gaba"dalilin da ya saka na muku wannan kiran na gaggawa shine, maryam (mami) tazo ta same da wani lamari mai girman gaske, ba komai bane kuwa face, zainab matar muhammad wacce kowannen ku a nan yasan irin rabuwar da sukayi da Muhammad badan ya sake ta ba, da kuma dalilin rabuwar tasu, to sai gashi zainab ta zo gare mu tare da ɗa bayan tsowon shekara ɗaya da rabi wanda ta gabatar min da shi a matsayin ɗan Muhammad ne." Kusan kowa a falon saida ya dago ya kalli Alhaji baba cike da kaɗuwa jin Abinda ya faɗa,bama kamar Aslam da Asmah da suka fi kowa shiga shock, duk da cewa dukkansu tun kallon farko da suka ma yaron suka tabbatar da cewa lallai jinin su ne amma basu taba kawo cewa zai zama dan Aslam ba, duk da kuwa ganin zee da sukayi zaune a gurin saboda suna da labari duk abinda ya faru tsakanin ta da Aslam wanda har hakan yayi sanadiyar faruwa a bubuwa da dama a baya ciki harda rabasun da mahaifinta yayi na tsayin shekara ɗaya harda ɗoriya. Ci gaba Alhaji baba yayi da cewa "duk da ba'a gaban mu zainab ta haifi wannan yaron ba jikina da zuciyata sun gama aminta da cewa lallai wannan yaron jinina ne, amma dai kafin mu yanke kowannen hukunci akan wannan lamarin zamuso ji daga bakin zainab shin ta yaya a kayi cikin da kowa ya tabbatar da zubewar shi ya rayu." Ya karashe maganar tare da kallon zee dake zaune kusa da mami kanta a kasa tana sauraren shi, dukkan su kuwa ita suka zubawa idanu alamar suna son jin Karin bayani daga bakin ta kamar yadda Alhaji baba ya umurta.


Ɗago da kanta tayi ta kalli little da ke ta wasan shi a hannun hajiya mama, take kuma wasu siraran hawaye suka ziraro mata, a hankali cikin sanyin murya da sanyin jiki ta shiga basu labarin abinda ya faru tun daga auren ta da Aslam da haɗuwar ta da beebaloo barin ta Nigeria halin da ta shiga bayan komawar ta Malaysian, bayyanar cikin little har zuwa haihuwar shi haduwar ta da Dr bala labarin beebaloo,da kuma dawowar ta Nigeria a karo na biyu domin ta zauna tare da mijin ta su raini ɗansu a gaban su.


Ta karashe labarin tare da fashe wa da matsanancin kuka zamowa tayi daga kan kujerar da take zaune ta sanya gwuwowin ta biyu a ƙasa ta haɗe hannayenta alamar roko da neman gafara, cikin kuka tace "ku dubi girman Allah da darajar da Allah yayi wa ma'aiki yaku wadannan ahli masu mutunci da karamci ku yafe min.a baya nasani na aikata muku abubuwa da yawa na rashin ɗa'a da rashin ganin girman ku da mutuncin ku a matsayin ku na iyayen mijina wanda nake tsananin so da son kasncewa da shi har karshen rayuwa ta, nasan ban kyauta ba kuma nasan ba Abu me kyau nake yi ba a lokacin to amma rashin ilmin addini da jahilci ke ruɗa na a waccen lokacin, amma yanzu wlh na sauya zainab din da kuka sani a da ba ita bace kuke gani yanzu a gaban ku, na muku alkawarin zaku same ni fiye da yadda kuka yi zato na, dan Allah ku karɓeni a cikin ku a karo na biyu." Ta kara she maganar cikin kuka sosai.
Gaba ɗayan su jikin su yayi matukar sanyi, irin su Asmah da mami kam tuni sun fara tsiyayar da hawaye, tsit falon yayi kowa da Abin da yake saƙawa a ranshi, mummy ce tayi karfin halin miƙewa ta ta isa wurin zee ta ɗago ta daga duƙen da take ta rungume ta a jikin tana bubbuga bayan ta alamar rarrashi, kafin kuma ta maida ta mazaunin ta nada ta zaunar da ita.

Gyada kai Alhaji baba yayi cike da tausayin zainab da kuma gamsuwa da tuban ta, domin kallo daya zaka mata ka tabbatar abin da take faɗa daga zuciyar ta yake fitowa, cike da isa da yarda da kai akan zantar da ko wane irin hukunci a tsakani ahlin sa yace "ya isa haka zainab mun fahimce ki, mun kuma yafe miki akan abin da kika mana kuma mun karɓeki a karo na biyu a matsayin suruka kuma jika a gare mu kije ku zauna tare da mijin ki da ɗanki da kuma abokiyar zaman ki." Da wani irin sauri Asmah ta sauke idanun ta akan Alhaji baba dake magana, kafin kuma ta juya da dasu kan zee da ake cewa suje su zauna tare, itama zee ɗin kan Asmah ta sauke idanun ta da suke nan gaje gaje da hawaye, kallo kallo suka shiga bin junan su da shi, kowacce da abinda take rayawa a zuciyar ta.


Muryar Aslam ne ya dawo dasu hayyacin su, cikin wani irin dakkakkiyar murya mai nuni da cewa abin da yake faɗi daga cikin zuciyar shi yake fitowa yace "Alhaji a gaskiya bazan iya zama da mace fiye da ɗaya ba ahalin yanzu ba, bazan iya haɗa husnah da kowacce mace ba a halin yanzu, bazan iya yin adalci a tsakanin su ba, idan kuma ka takura to lallai zaka jefe rayuwa ta cikin halaka."yana gama fadin haka ya miƙe tare da daukar little dake kan cinyar hajiya mama ya nufi har yar barin falon, har ya kai bakin kofar fita ya tsinci muryar daddy yana cewa "Muhammad kada ka kuskura ka fita daga falon nan, kuma umarni nake baka ba shawara ba."........




Oum Ummeetarh
07941130088
💖DAMA TA BIYU💖


BY


~AYSHA NALADO~




FREE BOOK


{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya,Allah kajiqan iyayen mu}
Hg


*ASSALAMUALAIKUM SISTERS*


abun d mamaki u watan axumi yaketa qaratowa cikin Dan taqin lokaci,
Me kika tanadarwa kanki dama yaranmu yar uwa?
Munada kyawawan kayan Yara na dinki masu kyau sosay d bama zakice dinkawa akayiba yaro/yarinya sufito gwanin burgewa kowa yanasan barka,07046881166


Kayanmu sauqinsu yyi har kamar kyautane,zaki iya samunsu dga 2k harzuwa abunda yyi Sama,kizo kiyi sarin kayanmu kisamu alkhairi me tarin yawa,07046881166


Akway takalma Suma kyawawa dgakan 1k zuwa sama,07046881166


Sannan munada tsala tsalan frames d madubai n gyaran gida masukyau d arha sosay,07046881166


Akway leshina d atamfofi,abayas sewanda kikazaba duk a farashi mesauki,07046881166


Karna cikaku d surutu ku kira:07046881166 domin qarin bayani,karku manta alkhairin Tari maganin mantuwa zaku iyashiga Instagram handle namu don ganin kayayyakinmu: everythng_handmade,


Semunjiku 07046881166






Page 125




Cak ya tsaya a bakin ƙofar shi bai tafin ba kamar yadda yayi niya kuma bai dawo ciki ba kamar yadda daddy ya umarta, mummy ce cikin fushi tace "Wai ba dakai ake magana bane, kana jin mutanen." Daga yadda yaji amon muryar mummy yasan ranta a bace yake, take jikin shi gaba ɗaya yayi sanyi duk wani karsashi da yake da shi tuni ya neme su ya rasa, baya kaunar abin da zai sa mummy tayi fushi da shi komai ƙanƙantar abin yana gudun bacin ranta a duniya fiye da yadda yake gudun na kowa, ba ta da sauki idan tayi fushi, har gara Fushin daddy so goma akan nata.


Jiki a sanyaye ya juyo ya dawo mazaunin shi daya tashi ya zauna. Shiru falon ya sake ɗauka kamar babu wani ɗan Adam a cikin shi, miƙewa Alhaji baba yayi fuskar shi a kame yadda ba kasafai mutum zai gane yanayin da yake ciki ba, kallon daddy da Abba yayi yace "Na riga na gama yanke hukunci akan wannan lamarin." Iya abin da ya faɗa kenan ya bar folon, duk da kallo suka rakashi har ya ƙule ma ganin su, bo kowa bane a falon ya fahimci inda Alhaji baba ya dosa sai su ɗin da ya ma maganar, rai bace daddy ya juyo ya kalli Aslam cikin tsananin fusata yace "kai ƙaramin mara kunya wlh baka isa ba, mu nan mu muka haife ke ba kai ka haife mu ba har kai dan ƙaramin alhaki dakai zaka zauna a gaban mu mahaifin mu yana faɗa kana faɗa, kai waye me ka taka, kai ɗin banza, to wlh ka sani babu inda zainab zata je kamar yadda Alhaji ya umarta, dakin ta zata koma ta zauna ta raini ɗan ta, idan ka isa kuma ka cika cikekken mara kunya, ka hana ta shiga gidan, maganar banza maganar hofi, inace nan akan zainab din ne ka wulakan ta mana namu ɗiyar, wani irin rashin mutunci ne baka mana ba akanta, sai yanzu saboda ka maida mu yan iska ka kalle mu kace kai baka sonta, to wlh baka isa ba, dama ina jiraye dakai akan abin da ya faru kwanaki, kaga nayi shiru bance komai ba shine yanzu ma zaka sake bijiro mana da makanman cin shi, to karyar ka tasha karya, daga yau ni Abdallahi ɗan Muhammad nayi rantsuwa da girman Allah baka isa ka

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads