Showing 12001 words to 15000 words out of 201974 words
Chapter 5 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt
ta nemi rakiyar su zahra amma dukkan su sukace mata baza su samu zuwaba, tayi mamakin yadda yau tayi musu tayin zuwa gidan Mallam suka ce a'a , alhali da su suke cewa azo aje gidan alhaji Mallam ayi Hutu, haka ta shirya ita kadai bello driver ya kaita, ta tarad da kowa lfy sun tarbeta da murna da nuna jin kewanta kamar yadda suka saba , a dakin kakanta wacce take kira da kaka mahaifiyar mahaifinta ta sauka , domin matan Mallam biyu ne ya qara aure amma matar bata haihuba har gashi tsufa yazo , gidan cike yake da yayan yan uwa da kuma daliban Mallam wasu ma harda iyalansu, domin gidan Mallam babban gida ne sosai mai dauke da sashe sashe , ..
Sai da daddare ta samu ganawa da alhaji Mallam bayan sun gaisa ya tambayeta yadda ta baro mutanan can gidan nasu tace lpy qlau nan suka Dan taba hira yana ta janta da Dan wasa na kaka da jika ita kuwa sai kunya takeji don bata saba irin wannan wasanda shi ba kuma gata bamai yawan magana bace, saida suka Dan taba hiran ya koma serious face dinshi shima, nan ya shiga sanar da ita abinda suka yanke akan aurad da ita ga dan uwanta Aslam, ya daura da yi mata nasiha mai ratsa jiki ya qare da cewa "wannan shine babban dalilin da yasa nace a turomin ke ni zan sanar miki da kaina,
Don haka ki zama mai biyayya a garemu, wannan wata dama ce Allah ya baki domin samun miji natsattse mai hankali kamar aslam a wannan zamanin abune mai matuqar wuya dan haka sai ki gode ma Allah da irin zabin da ya miki" tuni Asmah ta daina fahimtar abida alhaji Mallam ke fad'a tundai ta fahimci aure ne akeson a hadata da babban maqiyinta mutumin da ta tsana a duniya fiye da kowa ,,,...
Take wani zazzafan zazzabin farad daya ya lullubeta ci gaba Mallam yayi da yi mata nasiha wanda duk bata fahimtar komai ta Lula duniyar tunanin makomar rayuwarta, kaka ma data shigo ta same su daurawa tayi da nata nasihar,
Kafin magriba zazzabin nan yaci qarfita saida Mallam ya kira family doctor dinsu yazo ya dubata ya bata magani da allurai, kafin Safiya zazzabin ya sauka saboda qarfin alluran da akamata ,
Kwanata biyu a gidan alhaji Mallam ta dawo gida, bayan dawowanta sai ta koma wata iri da ita bata walwala gata dama ba mai yawan magana ba sai ta qara komawa wata silent , kullum saidai ta zauna tana tunani duk ta rarrame kamar wata Mara lpya , koda yake itama Mara lpy ce don garama wani na kwance a asibiti a kanta ,.....
Alhaji baba ma yasa an kirata shima dai nasihar ya mata sanna ya maimaita mata abinda Mallam ya riga ya fada mata, ya qara da cewa "amma baza muyi miki dole ba inkinga zaki cutu game da wanna lamari to kiyi magana wlh ni zan tsaya miki a fasa wanna auren, duk da cewa wanna cikar burinmu ne zamu haqura , haka Allah yaso ". Duqad dakai Asmah tayi qirjinta na bugawa wata zuciyar tana raya mata kawai ki gaya mishi bakison shi suyi haquri, yayinda wata zuciyar kuma ke tuna mata matsayin alhaji baba, daddy da mummy, a gareta bazata ta'ba iya cewa bata son jinin su ba intayi haka tayi butulci ,, wata zuciyar ta qara tuna mata da karatunta kenan yanzu onta yarda burinta na zama yar jarida yasha ruwa kenan sai dai taga su zahra suna zuwa school ita banda ita ,,,dago kai tayi da niyar furtama alhaji baba batason aslam kawai sai ta tsinci kanta da furta"alhaji bani da ja akan wannan zabin da kukamin, kune gatana , ban isa in take maganrku ba duk da kun bani zabi ,na amince da auren Dan uwana kuma yayana ya Aslam domin cikar burin ku na alkhairi , Allah ya tabbatar mana da alkhairi " qara duqad da kanta kasa tayi tana dauke hawayen dake zubo mata a idonta da wayau don kar alhaji baba yagani, ...
Murmushi alhaji baba yayi yace alhamdulillahi, Allah ya yi miki albaraka dama nasan ke mai biyayyace a garemu, bazaki taba kunyatamu ba tashi kije insha Allah zaki samu y'ay'an da zasu miki biyayya fiye da yadda kika mana ,...
Ta bangarn kamal da yaji labarin auren Aslam da Asmah ba qaramin tashin hankali ya shiga ba ranar da zazzabi ya. Wuni saida yayi kwana uku a kwnace kafin daga bisani ya lallashi zuciyarshi , ya tabbatar ya rasa asmah rashi na har abada, .... Shi babban tashin hankalinshi yadda aslam da Asmah zasuyi rayuwa a gida d'aya daki d'aya a matsayin mata da miji, yafi kowa sanin abinda ke tsakanin su ,tabbas yasan in akayi auren nan akwai matsala , yana dai roqon Allah yasa komai yazo da sauqi , ji yakeyi aranshi da zai iya da yaje ya samu iyasumu alhaji baba ya fada mai , amma ina! Ko giyan wake yasha yasa bazai taba iya tunkaran alhaji baba da wannan maganar ba
Date: Oct 7, 2022
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Page 25 & 26
Yau kimanin wata daya kenan da faruwar wannan lamari , gida ya dawo normal kamar ba'ayi biki a ciki ba, ba'ki na nesa duk sun wuce , mutanen gidan kuwa yaransu da manyansu sun dauki dangana akan abinda ya faru , ko maganar babu Wanda ya sake tayarwa , sun maida abin kamar ba'ayi ba , Asmah ma da suke tunanin zata shiga damuwa sai suka akasin hakan , don ko'a jikinta, saima walwalarta data dawo sabanin da da take cikin qunci,
Ta bangaren Aslam da'ker ya samu ya shawo kan iyayen shi suka daina fishi da shi suka yafe mai, saida alhaji baba ma yasa baki, duk da haka ba Ba wani sake mai fuska sukeyi ba daga mummy har daddy,... Shidai tunda ya samu sun yafe mai suna amsa gaisuwar shi , shike nan, sakemai fuskar ma yasan zasuyi a hankali,... Don shi har yanzu baiga ya aikata wani kuskure ba akan sakin da yama Asmah , ko so daya bai tabajin nadama akan hakan ba , shi yama manta da wata Asmah ya shafe babinta a rayuwarshi ,don tuni ma har ya gayawa zainab ta sanar ma iyayenta iyayenshi zasuzo next week,....
Itako zee anata bangaren ba qaramin farin ciki tayiba jin cewa iyayen Aslam zasuzo naman aurenta, duk da tasan akwai qura a gabanta , Hakance kuwa don tana sanarma mahaifinta have shi bai shirya aurad da ita yanzu ba ,.. Kwata kwata shekararta nawa da zata ce amata aure , to shi bai shirya ba idan Aslam zai iya jira nan da shekara bakwai to, idan kuma bazai iyaba to ya haqura kawai,...zee dama tasan hakan zai kasance don haka ta riga ta shiya ma hakan dama, rigima sosai akayi ta dage aure takeso kuma da Aslam , yayinda shi kuma mahaifinta yace ba yanzuba mom kuma ta goyama mijinta baya , zee gani wankin hula na Neman ya kaita dare, yasa ta dauki waya ta kira wan mahaifinta dake Nigeria, Wanda dama koda mahaifinta ya amince wurinshi za nemi aurenta , shima dai dan bokon ne kamar qanin nashi saidai shi duk abinda y'ay'anshi suke so shi yake mushi, banbancin shi da dad mahaifin zee kenan ,.....sanarai da abinda ke faruwa tayi nan ko yace tace iyayen Aslam din suzo gurinshi, zai daura mata aure da duk Wanda takeso, karta damu , kuma zai kira dad dinta ya mishi magan cikin jin dadi tace "to Daddy na gode" yace "karki damu y'ata abinda kikeso shi zan miki"
Alhaji abdurrahim wan mahaifi zee ya kira dad ya kuma nusar dashi illan hanata auren tunda dai ita ta kawo mijin tace tana so,
Shiko dad duk da haka bai gamsu da maganar wannashi ba karshe dai saida aka kai ruwa rana ya amince ganin zainab din ta dage kai da fata, itako zee tayi hakane saboda tasan hakan ne kadai mafita a gareta inba hakaba kuma tabbas zata rasa Aslam dinta, abinda kuma zuciyarta bazai gaba dauka ba kanan wato rashin Aslam.
Ya kasance weekend yan matan mummy ne zaune a main falon mummy sai fira sukeyi anata shewa kamar yadda suka saba, ko wacce ta sheqa wankanta tayi shiga irinan zaman gida domin shan iska ,dukkansu qananan kaya suka sa amma ba mai bayyana jiki ba, zahra ce kawai ta saka dogon rigar material mara nauyi , safiyace don gama yin breakfast dinsu kenan suka dawo falo suna kallo suna hira,
Ya kamal ne yayi sallama a qofar falon tare da shigowa fuskarsa dauke da murmushi kamar ko yaushe ,yasha kwalliya cikin qananan kaya shima sai zuba kamshi yakeyi , kusan hada baki sukayi gurin amsa mishi sallama tare da fara gaishe shi , amsa musu gaisuwar ya shigayi da sakin fuska kamar yadda ya saba musu , zaida kallonshi yayi akan zahra kasancewar yafi d'asawa da ita yace "sisto me zan samu a nan ne na breakfast" ya fada yana shafa cikin shi alamar yunwa, yaci gaba da cewa"wai tea suka sha, ni kuma wlh na gani da tea dinnan "
Murmushi zahra tayi tace "aiko ya kamal kai kai taki sa'a yau dan yau Asmah ne ta mana masan nan nata mai shegen dadi da shi muka karya , kuma naga akwai saura bari zubo maka " murmushi kamal yayi jin abinda zahra ta fada sosai yake daukin cin masan badan masa ta dame shi ba saidan jin cewa Asmah ce tayi masan, . ...don wannan karon ya shirya tsab ba gudu ba ja da baya , bazai qara maimaita kuskuren daya , bazai yarda ya sake aikata iri sakacin daya aikata a baya ba, duk da cewa har cikin zuciyarshi baiji dadin abinda Aslam ya aikata mataba , amma shi a ganinshi wata dama ta biyu ne ya sake bashi akanta , kuma bazai yi wasa da damarshi ba , ... Zahra ce ta katsemai tunani ta hanyar ajiye mai filet din masan datayi serving dinshi a gaban shi, kamshin miyan taushen da yaji naman rago, hade da kamshin soyayyen Masan shinkafa ya daki hancinshi lumshe ido yayi tare da budesu akan Asmah sake zaune kushin din dake kallon nashi, filet din Masan ya daga sama yanaci yana Kallonta a fakaice , yana jin wani irin soyayyarta na qara narkar da zuciya, yayinda ita gaba daya hankalinta baya kanshi, yana kan amira da batool daketa musu akan wani Indian series da take haskawa a TV tashar Bollywood...
9:00am dai dai Aslam ya farka daga baccin safen daya koma bayan asubah, miqewa yayi ya shiga toilet yayi wanka , shiryawa yayi cikin jeans da t-shirt baqaqe masu kyau , main falo ya sakko yana shafa cikinsa yana yamutsa fuska alamar yunwa na sakad'arsa, frige ya bude ganin babu wani abun tabawa yasa dole ya fito direct kuma part din mummy ya nufa , daidai lokacin da kamal ke cin masa yayinda yan matan mummy ke zaune suna kallo....
Kuyi manDate: Oct 10, 2022
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
page 27 & 28
Gaidashi su zahra suka shiga yi, a daqile yake amsawa ganin haka yasa Asmah qin gaisheshi,...kamal ne ya miqa mishi hannu suyi musabaha da'ker ya mika hannunshi sai wani babbata rai yake, haka kurum yaji yana jin haushin kamal din, ...shiko baima San yana yi ba ci gaba da cin abincinshi yayi, yana yi yana kallon sahibarsa,.....
Sake maida kallonshi yayi kan Asmah ganin kowa na gaishe shi ita ta dauke kanta kamar bata ganshi,..gyaran murya yayi "uhummm" dago kai tayi ta sauke idanunta cikin nashi , dukansu saida gabansu ya fadi , ...rabonshi da ganinta tun ranar da yasa mummy ta turo mishi ita part dinsu, gabanin Bikin nan ranar da ya mata warning da wuqa , da idanun shi ya mata alamar kallon fa, dauke kanta tayi daga kallon shi ta mayar kan tv still bata gaishe shiba, a zuciyarta tana cewa "wlh wannan ba Asmah da ka Sani da bace , eheeee wannan wata sabuwar Asmah ce da take daidai da rashin mutuncin ka, wacce kana ce mata kule zata ce maka cassss, don yanzu ba tsoranka nakeji, don duk wani girmanka a idona ka zubar ni kuma nasa qafata na taketa" duk wannan a zuciyarta take fada ,...shiko Aslam mamakinta ne ya kamashi ganin yadda ta dauke kai daga kallon shi kamar taga wani banza, ba wannan rawan jikin da tsoron shi dayake gani kullum a tattare da ita , shi sai yake ganima kamar kallon tsana take jifanshi dashi ma, ...kwafa yayi yana girgiza kai ya nufi dakin mummy ganin bai ganta a falon ba, ,a zuciyarshi kuwa yana aunawa Asmah zagi, mayya kawai mai idon mayu kurwata kur wlh, haka kawai da sassafen nan tasa gabana nata faduwa,.shiga dakin mummy yayi bai ganta ba. falon ya sake dawowa,batool ya kalla tare da cewa "kee mummy fa" da sauri batool ta amsa mai da tana part din daddy , hanyar fita falon yayi tare da ce mata "ki kawo min abinci part dina yanzu" ya fada fuskar nan a murtuke cike da isa, ya fice a falon, bai cewa kowa komai ba, batool ce ta mike cikin zumbura baki ta nufi kitchen, ta hado mai koma da komai a tire ,... Dukkansu basa son zuwa aikensa , saboda sunsan ba,a wanyewa dashi lpy karshenta mutum yasha rankwashi ko mari, yamafi Aiken amira duk cikin su, a cewarshi tafisu hankali da nustuwa ,...
Ajiye Tiren batool tayi a kan table din dake tsakiyar falon, murtike fuska tayi exactly yadda Aslam ke murtuke musu fuska , gyara tsayuwarta tayi ta fara irin tafiyan shi, d'akin mummy ta nufa cikin kwaikoyan irin tafiyanshi, duk ido suka bita dashi yuuu suna kallonta, fitowa tayi daga d'akin mummy tana ciccin magani kallon zahra tayi tace "kee mummy fa" tana 'kwai'kwayan muryan shi, aiko gaba d,aya suka kyalkyale da dariya jin yadda ta kaurara murya irin na bosawa wai ita tana kwaikwayan muryan Aslam, itako batool bako alamar murmushi a fuskarta ta dake abinta, qara kallon zahra tayi dake kwasan dariya , ta sake cewa cikin 'kwai'kwayan Aslam "ki kawomin abincina part dina yanzu "ta fada exactly yadda ya fada tana mai fita a falon cikin irin takun shi , amira cikin dariya tace"Allah yasa kina leqawa Ku had'a ido" aiko dai tana leqawa ta hangoshi , Allah yasota ya juya baya bai ganta ba , da gudu ta kwaso ta dawo ciki tana haki tace"wlh amira bakin kai shegen kaifi gare shi "dukkansu qara kwashewa sukayi da dariya zahra tace"yar banza ga tsoro ga mugun aiki" ...."eh din "batool tace tare da kinkiman tiren tayi hanyar waje don kai mai abinci,....kamal daya gama shan dariyar diraman batool ya miqe tare da kallon Asmah yace "sister anjima da yamma zaki rakani shopping , inason inma budurwata shopping , kuma kinga ni bansan kan kayan mata ba ," ya fada yana langwabar da kai yayi fuskan tausayi don kar tace baza taje ba , murmushinta mai narkar mai da zuciya ta sake tare da cewa "to ya kamal Allah ya kaimu anjiman, zan sanar ma mummy inta amince"... Amira tace "Allah sarki ya kamal zanje nima" zahra tace "nima haka ya kamal don Allah" harara wasa wa watsa musu tare da cewa "Allah ya kiyaye wa zai fita da Ku, yara sai shegen rawar kai kaman ana kadaku da ruwan hanji, Ku bari gobe bello ya kai Ku," ya fada yana ficewa a falon don karma su qara hada shi Allah,... Yana fita Asmah ta tashi tana kwaso shoki tana musu gwalo, filon kujera amira ta dauka ta bita dashi, kwasa tayi da gudu hanyar qofa , saiga mummy ta sawo kai saura kadan suyi karo Allah ya kiyaye, ...mummy tace"ya haka amira mekefaruwa "langwabe kai amira tayi tana turo baki cikin shagwaba tace "mummy gwalo fa take mana " mummy tace"gwalo akan me" zahra ce ta labartawa mummy abinda ya faru,... gwalesu mummy tayi da cewa "aikam dai kamal yana da gaskiya, inya kwasheku ai sai kusa aje ata nunashi ana dariya, tsabar rawar kanku gara dai yaje da Asmah don itace ma dan dama dama a cikin ku'......
Da misalin qarfe hudu da rabi yan matan mummy ne dukkan su a cikin makeken dakinsu dake part din mummy , daki ne babba mai dauke da madaidaitan gadaje har guda biyu, iri daya da kuma maka makan wardrobe mai qofa shida shida shima har biyu , da kuma madubi babba guda daya shaqare da kayan kwalliya na mata da turaruka masu tsada kala kala, wannan duk aikin mummy ne,...
Komai na dakin pink and milk colour ne idan ka cire fridge da kayan kallo da suka kasance baqaqe, hatta painting dakin pink and milk ne, dakin ya hadu sosai gwanin birgewa ,.
.duk da wadan nan kayan dake dakin still akwai space sosai a dakin, domin ba qaramin babban daki bane,dukkan su a kwance suke akan rug carpet kowa na abinada take so batool na karanta novel, amira da zahra na charting a wani WhatsApp group dinsu na yan mata, Asmah kuma da fitowarta kenan a toilet tana tsaye a gaban dressing mirror tana kwalliya ,saboda shopping din