Header Ads
Showing 123001 words to 126000 words out of 201974 words

Chapter 42 - DAMA TA BIYU completet A'isha Nalado .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1749

Ads at the middle of Article

kai ta yadda wata rana ita da kanta sanda zata mika maka kanta bata da labari, amma yanzu idan kayi haka saita dauka ba soyayyar gaskiya kake mata ba wani Abu kake bukata a jikinta, da wannan shawaran ya dingayin kasa da hannun shi harya maida shi inda yake da.




Ajiyar zuciya ta sauke jin bai karasa can ɗinba, shiru sukayi suna sauraren bugun zuciyar juna kowannen su zuciyar shi cike da anashuwa, kusan awa daya a haka kafin a hankali wani irin daddadan barci da ta daɗe ba tayi irin shi ba ya kwasheta.




Saukar nunfashinta da yaji ya tabbatar mai da barci ya kwashe ta, murmushi ya saki tare da kissing tsakiyar kanta, shima a hankali ya lumshe idanu ba bata lokaci barci ya kwashe fuskar shi dauke da kayataccen murmushi.






Wani irin barci mai dadi sukayi ranar wanda suka daɗe basuyi irin shi,bacci suke hankali kwance kowannesu furkarshi dauke da murmushi mai kayatarwa, gaba daya ya kanannadeta a jikinshi ta yadda ko kwakkwaran motsi tayi saiya a farka.




Basu suka farka ba kuwa saida hasken rana ya ratso cikin dakin,ita ta fara farkawa,gani tayi haske gaba daya ya cika dakin alamar har rana ya bullo, bin jikinta tayi da kallo ganin yadda ya kanannadeta gaba daya, ya saka ta ajikin shi bata da damar motsawa kallon fuskarshi tayi, fayau da shi yana dauke da murmushi sai sharar barcin shi take hankali kwance, kura mishi idanu tayi ta kalle shi son ranta,gaskiya yaya Aslam kyakkyawa ne ajin karshe, ta ayyana hakan a ranta, murmushi ta saki, bata San sanda takai ɗan bakinta tamai kiss a wuya ba, ahankali kuma ta shiga zare jikinta daga nashi, harta gama ta yunkura a hankali zata mike karaf taji ya cafkota ya maidata ya kanannade har fiyye da da, cikin murya mai ciki da barci ya shiga ce mata a kunne "ina zakije? Dan Allah karki gusa kibar mahaukacin masoyinki shi kadai" cikin in,ina tace"gari ya waye fah" ba shiri ya waye idanunshi tare da sakinta ya mike zaune yana furta"subhanallah astagfirullah" mikewa yayi ya shiga toilet din dakin da sauri yayi brush tare da dauro alwala ya fito, a bakin bed ya sameta zaune ta ziro kafafunta kasa, jin motsinsa yasata dagowa ta kalle shi murmushi ya sakar mata tare da mika mata hannu alamar ta miƙo nata, ba musu ta mika mishi, Dan ta daukarwa ummi alkawain cewa duk abinda ya umarceta zatayi matukar bai sabawa Allah ba.


Ita kuma ummi tayi amfani da wani hikima ne ta manya ta daurawa Asmah wannan nauyin tasan hakan zai bada gagaruman gudunmawa wajen daidaita tsakanin su.




Har cikin toilet din ya kaita, tare da kokarin yi mata alwala, tana da uzirin kama ruwa, ganin baida niyyar fita, yasa ta naimi alfarman ya bata waje zata kama ruwa, ba musu kuwa ya fice daga dakin ma baki daya, kama ruwan tayi tare da yin brush a karshe ta dauro alwala, koda ta fito baya dakin, direct gaban wawakeken wardrobe dinta ta nufa, wani dogon Riga Mara nauyi ta fitar tare da hijjab din da take sallah dashi ta ajiye a bakin bed, cire kayan jikinta na barci tayi, har pant din kuwa bata bari ba dan bata yarda da tsarkinsa ba, dama babu maganar saka bra, wani sabon wankakken pant ta dauka ta saka sannan ta dauki dogon rigarta, ta daga zata zira kenan ya shigo dakin dauke da sallama, kallo daya ya mata yayi saurin dauke kai kamar baiganta , yayinda ita kuma tayi saurin karkare zira rigarta, sannan ta saka hajab dinta.




Sanye yake da jallabiya na maza ruwan hanta mai guntu hannu, direct inda take ajiye pray mat ya karasa dauka yayi ya shimfida duka biyun, nashi a gaba nata a bayan nashi daga gefen dama, ganin haka bata tsaya bata lokaci ba, ta daidaita sahu, jam'i ya jasu kara'i saboda makaran da sukayi, bayan sun idar kuwa, sunyi tasbihi, ya shiga kwararo musu addu'o'i manya manya, batayi wani mamaki ba kasancewar ta riga tasan shiɗin yana da ilimin addini sosai tunba yau ba.






Bayan idar da dukkan addu'o'in juyowa yayi da murmushi a fauskar shi yana kallonta, cikin sa'a kuwa itama ta dago kai tana kallon shi, wani irin kyau kwarjin da haiba taga ya kara mata ba shiri tayi kasa da kanta tare da cewa "ina kwana ya Aslam" shiru yayi bai amsata ba, bai kuma daina kallonta ba, jin shiru yasa tayi tsammanin ko baiji bane, hakan, yasa ta sake maimaita gaisuwarta, da Dan karfi wannan karon, still ba amsa, hakan yasa ta dago kanta ta kalle shi, tare da sake cewa"ina kwana Mr Aslam" maimaikon ya amsa mata sai gani tayi yakai Dan yatsan shi manuniya kan labbanshi, yace mata "shiiiiiiii" da mamaki take kallon wannan irin ikon Allah, murmushi ya saki tare da cewa, "daga yau na haramta irin wannan gaisuwar a tsakanin mu indai a ba agaban mutane muke ba" kamar sokuwa haka take binshi da kallo ganin haka yasa yace kinsan wani irin nake so, girgiza mai kai tayi alamar A'a, yace kina son ki sani, sake girgiza mai kai tayi alamar Eh.




Aiko kafin tayi wani tanani taji ya janyota jikinshi ya hade bakinsu ya lalubi harshenta ya cafke ya shiga bata wani irin slow kiss mai saurin kashe gaɓɓai.




Wani irin zaro idanu Asmah tayi, take firgici mamaki da tsoro suka diran mata a lokaci guda, tunda take a rayuwarta wannan ne karo na farko da wani mahaluki ya sumbaceta...............














Comment dinku shine zai tabbatar min da cewa kunyi farin cikin dawowana online😍
Daga yau posting zai ci gaba insha allahu har sai mun ɗire💖






Ɗinbin godiya a gareku masoyana masuson farin ciki da da cigaba na, wadanda sukayi contributing din kudi domin su bani kasancewar sun samu labarin wayata ta samu Matsala, na gode muku Allah ya saka muku da alkhairi Allah yabiyaku da Gidan aljannah madaukakiya, inayinku over💋


Wadanda sukayi niyar bayarwa Allah bai basu iko ba kuma na gode Allah yaga niyyarku, wadandama basu niyya ba duk na gode Allah yabar kauna😬














Oum Ummeetarh
07041130088




















Share
And
Comment
Fisabilillah🙏.
💖DAMA TA BIYU💖

BY


~AYSHA NALADO~




FREE BOOK






{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce tarasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}










Page 107




Tun daga wannan rana rayuwar Aslam da Asmah ya canja, wani irin kulawa da soyayya yake nuna mata kamar ya hadiyeta, gaba daya ya sangartar da ita ya koyar da ita soyayyar shi mai tsanani bataji bata ganin kowa a halin yanzu sai Mr Aslam ɗinta, tun daga wannan rana basu kara raba gurin kwanciya, kullum Daren duniya tare suka bacci rungume da juna, yanayi yana lallatseta da wayau musamman gurin yi mata addu'an barci yace zai shafa mata, wani bin sarai takan gano shi saidai tayi murmushi a ranta wani bin kam har yayi abinda zaiyi ya gama bata fahimtar komai kasancewar shi gwanin iya pretending, tun tana ɗari ɗari da shi har ta saki jikinta dashi sosai, zuwa yanzu ko kasheta akace za'a idan bata rabu da Aslam ba, saidai a kashe ta kam, badai ta taba furtawa mashi so ba, amma ko ita karan kanta a yanzu ta shaida ba karamin so take mashi ba, komai tare sukeyi a Gidan suyi girki tare suci abinci tare suyi aikin gida tare suyi wasanni tare, harda kallon kafa yi suke ga TV game daya koya mata shima sunayi, tun bata iyaba in sun zauna saidai yaita cinyeta harta kware itama, wasa harda su goyo goyo da doki duk yi sukeyi, wanka ne kawai basayi tare shima ita ta taka mai burki, Dan indai tashine tasan wannan duk mai sauki ne a gareshi, duk wannan sabon da sukayi bai taba nuna yana son ya kusanceta duk da kuwa a kullum burin shi bai wuce hakan ba, har addu'a yakeyi idan yayi sallah akan hakan, alkawari ya daukarwa kanshi na cewa saita saki jiki dashi, saiya haukatar da ita da soyyar shi ta yadda duk randa ya bukaci hakan baza ta iya hanawa ba , duk da ko yanzu yasan tana tsananin kaunarshi fiyye da yadda ya zata, yasan kuma ko a yanzu bazata iya hana shi kanta ba.




A bangaren Asmah kam a halin yanzu ba kanta ba ko duniya idan tana dashi Aslam ya nema a gurinta da gudu zata mallaka mai, balle kuman kanta, ita kanta a halin yanzu bata da burin da wuce su zamo Abu guda, saidai koda wasa baza ta taba nuna mai hakan ba koda kuwa a fuska ne domin kuwa ita macece, mace kuma da kunya da kamun kai da kuma aji aka Santa, bancin haka wannan ba irin tarniyar da mummy ta basu kenan ba, amma kuma a shirye take tana maraba dashi a duk sanda ya gama kwana kwanan shi ya dawo kan hanya.






~BATOOL~






Yau kimanin wata ɗaya kenan da bayyanar cikin batool, babu abinda sukeyi sai barzar amaraci, batool fa da gaske ta zama jarababbiya ta karshe kullum indai Dr bash na gida suna makale da juna ana harka idan kuwa ya fita ta ta dinga damunshi da kira kenan tana tura mai text a kai a kai, wata ran har daga asibiti sai ya dauki excuse ya dawo idan ta saka mai kuka.




Shima a nashi bangaren yana matukar kokarin biya mata bukatarta amma duk da haka saida ta nemi ta kure shi duk da kuwa cewa shima ba baya ba, ganin haka yasa dole ya nemi wani ingantaccen maganin bature na kara karfin maza yana hadawa dashi, zuwa yanzu tasan da ciki a jikinta kuma tayi matukar farin ciki, yadda ta nuna farin cikinta abin har yaso yaba Dr bash mamaki, haka suka shiga tattalin cikinsu a tare cike da tsantsar soyayya da kulawa,




Dr bash wannan karon da kanshi ya samu maah ya gaya mata batool ta samu ciki, maah najin haka tace "ahaf dama ai na fada kake min musu" da'ker Dr bash ya samu maah ta fahimci yanzu ne aka samu cikin da babu, yayi haka ne kuwa Dan yaga yadda taketa lissafin watannin cikin kar azo lokacin data lissafa za'a haihu taga ba'a haihu ba su shiga uku, Dan sarai yafi kowa sanin rigimar maah farin sani.




Da kanshi ya kira Aslam ya fada mai batool nata hana shi amma yaki ji, da wai harda su daddy zai kira ya fada musu, saida ta saka mai kukan shagwaba tana daka tsalle sannan ya bari, yana dan Allah ta rufa mai asiri ta daina wannan tsalle, tum daga nan batool ta samu logon shi,da tace Abu yaki yi sai ta saka kukan shagwaba karshe ta tashi ta kama dira tana tsalle ko baima Allah dole ya mata.




Lokacin da Dr bash ke sanar da Aslam batun cikin batool wani irin tsam Aslam yaji a ransa take zee ta fado mai a rai, har a bada bazai taba manatawa da abinda zee ta mai ba na salwantar mai da gudan jininsa da tayi, sharewa yayi ya shiga taya Dr bash murna karshe ya shiga tsokanar shi kamar yadda suka saba yima juna matsayin su na abokai, dariya Dr bash yayi jin abin da Aslam dinke cewa, bai tankashi ba kamar yadda ya saba saima cemai yayi"duk abinda zakace kace bazan tanka ka ba kasan yanzu kai babban yayan mune,ni wlh ma yanzu kunyarka nake ji" Aslam bàisan Wanda ya lailayo ashar ya durawa bashir ba, ba shiri ya katse kiran yana tikar dariya, bayan gama wayarsu Aslam zama ya gyara ya kwantar da kanshi a jikin kujeran da yake zaune a falon shi, wani irin kwadayin son haihuwa ne ya taso masa, gaskiya yana son yara sosai yana matukar son yaga jinin shi a doran kasa shiyasa har yau ya kasa yafewa zee abinda ta mai, damuwa sosai ya wuni dashi a wannan ranar,har saida takai Asmah ta fahimci halin da yake ciki duk da kuwa kokarin boye matan da yaketa yi.




Bayan sunyi shirin kwanciya yana daga zaune tsakiyar bed yana karanto addu'o'in Neman tsari yayinda mutum zai kwanta barci, zuwa tayi ta zauna a gabanshi ta kwantar da kanta a kirjinshi, saida ya gama addu'o'in ya shafa, sannan ya tsinkayi muryarta tana cewa"meyake damunka ne yau Mr Aslam gaba ɗaya yau baka cikin walwala kamar wani Abu na damunka, Dan Allah ka sanar damuwarka muyi shearing matsalolin mu shine amfanin zaman tare" yaso ya boye mata amma haka kurun yaji ya kasa, take ya labarta mata abinda ke damunshi ba tare da ya iya boye mata komai.




Duk da taji dadi sosai tayi farin ciki da jin cewar batool nada ciki, amma bata nuna hakan a fuska ba saboda halin da mijin ta ke ciki, kwarai ta tausaya masa, sake kamkameshi tayi da kyau, cikin murya mai nuna tsantsar tausayawa ta shiga cewa, "kayi hakuri ya Aslam hakika zainab bata kyauta maka ba, ta zalunceka, kaci gaba da addu'a Allah zai baka wasu masu albarka "ba karamin dadi yan kalmominta da basufi a kirga ba suka mai, take yaji wani irin nutsuwa ya saukar mai a zuciya, dago da kanta yayi yana kallon fuskarta, itama nashi fuskàr ta kalla idanunshi ya sarƙe da juna, a hankali cikin sanyin murya ba tare da ya dauke idanunshi cikin nata ba yace"husnah ta kin tabbatar da abinda kike fada" cike da garfafa gwuiwa ta girgiza mai kai kafin tace"duk wani mumini na kwarai baya taba yanke kauna da rahamar ubangiji, insha Allahu ya Aslam Allah zai musanya maka da wadansu yayan masu albarka" ciki da tsananin jindadin kalamanta ya kankameta da karfi yana sauke ajiyar zuciya, itama luf tayi a faffadan kirjinshi tana sauraren bugun zuciyar sa.






~ZAHRA~




Misalin karfe takwas da rabi na dare, zaune suke gaba daya su a falo ita da yan yaranta, Ahmad na rungume a jikinta yayi lamo alamar yana shirin barci , Anisa kuma tayi pillow da cinyarta, yayinda hanan ke kwance akan 2 sitter, suhail kuma na daga gefenta, wani cartoon suke kallo mai dadi a mbc 2, gaba dayansu cikin ado da kwalliya suke musamman ma ita uwar gayyan, kullum haka zaka gansu fesfes kamar wasu kwankwasan injin, gaba daya hankalin su ya raja'a akan kallon da sukeyi.


Sallaman Barr ne ya dawo dasu hayyacinsu, da gudu duka yaran suka nufeshi, suna fadin daddy oyoyo, daddy oyoyo, ba shiri kuwa ware musu hannayenshi ya rungume su gaba daya, dago kai yayi ya kalleta ganin ita bata taso tamai oyoyon ba tare da yara kamar yadda suka saba kullum, suna hada ido saima yaga ta dauke kanta ta mayar kan TV, murmushi yayi a zuciyar shi yace "babyna Yar daru" daukar Ahmad yayi ya rike hannun Anisa yayinda hanan da suhail suka amso kayan hannun shi karaso cikin falon sukayi, ya nemi waje ya zauna yaran kuma suka baibaye shi, kallon shi tayi ba yabo ba fallasa, a dole tana fushi dashi tace"sannu da dawowa daddyn hanan"
"Daddyn hanan! ya maimaita sunan da ta kira shi dashi yau, maimakon habibi da take kira kullum ko a gaban waye kuwa share wa yayi ya amsa ta da "yawwa my baby ya gida ya yara" a takaice take "lafiya" tare da mikewa tace bari na haɗa maka ruwan wanka, ta riga ta sani wanka yake fara yi idan ya dawo kafin yayi komai, dakatar da ita yayi ta hanyar cewa, "ki barshi bari na hada da kaina ki zauna da yara ina zuwa" ba musu kuwa ta dawo ta zauna, mamakin tane ya kara baibayeshi, ya Tabbatar lallai yau baby na fushi dashi, inda haka kurum ne yace tabar hada ruwan wankan nan baza ta taba yarda ba, cewa zatayi zai hanata samun lada, amma yau yana mata magana ba musu ta bari.




Mikewa yayi ya wuce ciki, domin yin wanka, dakinshi daya ke nan cikin part dinta ya nufa,dan tun bayan tafiyar maryama ya kulle nashi part din ya tattaro ya dawo nan baki daya, Dan bazai yuwa su dinga tafiya can suna barin yara su kadai ba.




Bayan shigewar shi ta dauki ledar tsarabar daya kawo musu ta bude ta damkawa kowa nashi, kayan kwalama ne dangin su chocolate biscuits, sweet da sauransu, nan suka zauna kowa ya shiga cin nashi, bayan sun gama har zuwa lokacin bai fitoba, ga dare nayi kuma yara gobe akwai school, kawai tace su tashi ta rakasu dakinsu, ba musu kuwa suka tashi, kinkiman Ahmad tayi da ya riga yayi barci suka wace, saida ta gama musu komai na shirin kwanciyar su, ta musu addu'a tana shirin kashe musu wuta ta fice ya shigo dakin, karasawa yayi shima ya musu addu'o'i ya shafa musu shima, ganin ya gama ya mike zai fice yasa ta saurin ficewa ba tare data jira shi ba.


A dining ya sameta tana serving dinshi dinner, kujera dake facing dinta yaja ya zauna, yana kallonta sai wani ciccin magani take tana kumbura fuska, dariya yake mata a zuciyar shi sarai ya gane abinda takeyiwa fushi, shi mamaki ma take bashi, lallai Zahra tanada kyakkyawan zuciyar.




Plate ɗin data tura mai gabanshi ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya Lula, kallonta yayi yana murmushi tare da cewa "nagode amaryata inasonki sosai babyna" wani harara ta zuba mishi mai kayatarwa, dariya ya kwashe dashi tare da cewa "wow wannan kallon luv din gaskiya ya kayatar dani, ki dinga min irin shi kullum kiñji my baby" jin haka yasa ta gimtse hararan tare da dauke kanta gefe, tana turo baki, a haka ya gama cin abincin yana yi yana tsokanarta, yana mata dariya, ita ko sai kara kunbure fuska take a dole tana fushi.




Mikewa yayi bayan ya ajiye cokalin ya daukin tissue yà goge baki, gyatsa yayi yana shafa cikin shi, tare da cewa ”alhmdllh girki yayi dadi yama fi na kullum dadi, inaci

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads